← Book details Tame Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 59

Sashe 37

Tame Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko da Dije ta ganshi ba karamin jin dadin ganin mahaifin nata tayi ba da sauri ta taso ta isa gabanshi ta tsugunna ta shiga gaisheshi cikin girmamawa da fara'a,amsawa ya shiga yi tare da tambayarta bayan rabuwa.

Daga nan kuma suka shiga hirar bayan rabuwa,sosai suka shiga hira ta shiga taya Inna aiki dan baba yasa an yanka kaji da zabbi dan ayi farfesu a kuma soyawa baki,fura Dije ke damawa dataji nono sosai.

magariba aka kira,hakan yasa baba mikewa dan tafiya masallaci,yana fita itama Dije ta daura alwalar ta shiga daki ta bar Inna na karasa aikin,itama tana gamawa tayi alwalar ta shiga yin sallar.

*** ********** ***

Baba suke jira ya shigo dan ya samo yara su kai kayan nan gidan mai gari.

suna zaune har akayi sallar isha'i sannan baba ya shigo nan yake sanar musu cewa maigari yace su mamy sunce nan zasu sauka ita da matan su Habeeb dan haka a gyara musu guri.

Tunda Dije taji haka tasan shirin mamy ne tasan kuma tayi haka ne kawai dan cin zarafi,ba bata lokaci kuwa suka mike ita da Inna suka kara gyara dakinta na da,sun gama kenan sun dawo sun zauna sukaji sallamar su tare da Haruna dan gurin baba zakariyya da wasu yaran dauke da akwatunan su niki-niki,bayan sun gama shigo da kayan ne su mamy suka iso da su yusrah wadanda dukan su sai yatsina sukeyi dan dama zani ce ta tadda muje su da mamy sam ba sa son mutane indai ba nasu ba basa kuma son rayuwar kauye duk da yadda sukayi tsammanin kauyen ya kasance sunga sabanin hakan amma a cewar su kauye kauye ne.

Ganin kamar a gajiye suke yasa mamy shimfida musu tabarma babba nan suka zauna duk da garin da sanyi kasancewar lokacin sanyi ne,Dije ce ta fara yi musu magana kamar abin dole suka dinga amsa mata a daddakile Sam bata wani damu ba dan dama ta saba da hakan,ita kuwa Inna sam sai taji ba dadi ganin yadda sukayin hakan na nufin kenan 'yarta a haka take rayuwa?kai ba haka bane watakil gajiyar mota ce da wannan tunanin ta barwa ranta suka shiga gaisawa ba yabo ba fallasa,bayan an kawo musu abin tabawar da ak tana dar musu duk da ba wanda ya kula da farko amma ita yusrah abinka dame ciki,tana shakar kamshin dabgen dahuwar daddawar da naman kajin nan yasha tuni yawunta ya guda ,ta jawo kwano kuwa ta shiga dandanawa an taji zakwai,dan ji tayi kamar a duniya bata taba jin test irin wannan ba ai nan da nan ta shiga korawa cikinta jawabi,ganin yadda take cin ne yasa su mamy suma suka dan fara tabawa,sai gashi su mamy an manta a gaban surukai ne sun sheke abinda ke cikin kwanon yusrah kam harda sudi kamar taga makerin kwanon.

Ganin sanyi yafara yawa yasa Inna tace su shiga ciki,bayan sun shiga sunyi mamakin ganin yadda aka gyara dakin duk da gadon karfe ne amma da katifa sai wata katifar a qasa wadda aka sawa zanin gado nan mamy ta zauna su kuwa suka gefen gadon suka zauna.

Wanka Dije tayi tasa riga da wando na bacci tare da hijabi ta fito taga inna nata kokarin kankanta kaya tana kokarin shiga kicin,sannu da kokari innata ta karasa tare da karbar kwanukan ta shiga dasu kicin din ta fito ta tadda Innar tana nade tabarmar da suka tashi,shima karasawa tayi ta karbi nadin tabarmar ta nade kafin ta kaita daki ta fito inda Innar ta kalleta tace sannu Dije,ashe yanzu kinyi hankali da son aiki,ai na dauka zaman birni ya bata ki kema dan naji ance matan birni basa son aiki, dariya Dije tayi kafin tace,

kai! inna waya fada miki matan birni basa son aiki?

Au har sai an fadamin,mutanen da zaka gansu jiki lukwi-lukwi kamar bawon kwai,ai da kin gani kin san basa wani aikin wahala,yanzu ke baga shi nan ba wa zai ce asalinki nan ne,jibi yadda kika zama kamar ma ba 'yar kasar nan ba,gaba daya kin canza kamar wadda bata cin tuwo,duk da dama su mutanen birni sun maida cin tuwo kauyanci.

Kai! Inna ashe gaskiya ne maganar mutane,da suke cewa ke na gado a zance,gashi nan tun dazu kike ta zuba zance ba commer ba fullstop.

Na shiga uku! sunan su waye kuma hakan?

inna ta fada harda dan dafe kirji

Dariya Dije ta gumtse kafin tace, "au kina nufin yanzu baki san su ba Inna?"

Ta ina zan san su bayan daga jin sunan kin san sunan manyan arna ne.

Ke meya kaiki mu'amulla dasu?,wato duk jan kunnenki danayi bakiji ba ko Dije?

Hmmm! Inna kenan wallahi dan ma bakiga ita commer din ba har wata 'yar lankwasa ta yi.

Saboda tsabar kafurcin ko kuma saboda me?

Inna ta jefo tambayar a guje,wadda tasa dole Dije saida tayi dariyar da take boyewa.

Au dariya ma kikeyi kenan ko?,saboda duk kin koyi dabi'unsu,ba dan ma tun kina shan nono nake yawan maimaita miki kalmar shahada ba tare da karanta miki bisimillah, kulhuwallahu ,falaki da nasi,tare da duk wasu addu'oin tsari, kice da yanzu sun dulmiyar min dake,dan daga jin sunayensu musamman ma na dayar kin san sun koshi da ruwan kafurci,daga ji kin san gadonsa sukayi bawai haye bane.

Au dama ana taka hayen addini Inna?

ke da baki sani ba?

Ah ah ni ban taba sani ba kam.

To kamar yadda suke gudowa daga addininsu na kafurci su dawo namu na muslunci,haka suke fita daga nasu su koma wani dai na dangin arnar dan jahilci wai su sun tuba,to wallahi bari kiji in fada miki ki gaggauta rabuwadasu tun wuri,dan bazan yadda ayimun sakiyar daba ruwa ba,zan kuma cire kunya inyiwa karima magana dan suma da laifinsu da basa sa miki,ido har suka bari kike mu'amulla da dirka-dirkan arna.

ganin da Dije tayi Inna ta dage tanata fada iyakar iyawarta yasa ta yin gum da bakinta tace,

yakamata Inna a dora ruwan zafi dan nasan sai sunyi wanka kafin suyi bacci.

tana ci gaba da fadan ta mike ta hura wuta ta dora ruwan kafin ta dawo kan Dije taci gaba dayi mata fada akan su cammer da fullstop akan ta rabu dasu.

Tare da Innar suka shiga dakin,inda suka iske su zaune suna hira,amma jin shigowarsu yasa su yin shuri,mamy harda jan dan guntun tsaki wanda duka tsakanin Dije da Inna ba wanda baiji ba,amma sai suka share suka nemi guri suka zauna.

Sake gaishesu Inna tayi kafin tace,

Naji ance da ku duka zaku zo harda matan su mai sunan malam,amma naga daya ce tasami zuwa ciki ko dayar tayi nauyi ne?

cikin rashin fahimtar tambayar ta ta mamy ta ce, kamar ya kenan?

Naga ne harda kanwar ki ku ka zo wannan ta kwancen dan naga kun dan yi kama da ita, ta nuna sajida dake kwance saman gadon karfen.

Ita kanta mamy tasan duk wanda yaga Sajida yasan ba sa'ar auren Habeeb bace ,amma saita maze ta ce,ai wannan ita ce matar mai sunan malam din,wannan kuma matar Naseer ce duk ta nuna su.

Ikon Allah!!

cewar Innah

kice yaro ya raya sunnah yayi koyi da Annabin rahma,yafara da bazawara,to Allah ya sanya alkhairi ya bada zuriyya dayyiba.

Duk yadda Dije ta so hadiye dariyarta kasawa tayi haka ma yusrah,itako mamy kunya taji yayin da uwar gayyar ko ta cika fam,tama rasa kalar rashin mutuncin da zata yiwa tsohuwar nan.

Itako uwar gayyar inna bata ma san ana yiba,nan taci gaba da sheko addu'a har baba ya shigo ya sake gaishesu ya juya zuwa daki Inna ta tashi ta bishi.

Tana fita Sajida ta kalli Mamy tace,

ina son yin wanka amma naga gidan kamar ba toilet ya za'ayi kenan?,dan wallahi bazan iya kwana haka ba.

Injiwa yace miki ba toilet!,ai wai a haka akwai shi,ai mudai kaddara ta auremu da aka jawomu wannan kauyen ga shegen sanyi,gara ku ma mazajenku sunce ku kuka matsa sai sun taho daku,ni da nasan dawan garin tuntuni, ai ni aka matsawa sai na zo, ta karasa maganar tana kallon inda Dije ke zaune ta wurga mata harara.

Dije yi tayi kamar bata san tanayi ba saima ta mike d niyyar barin dakin taji mamy tace,

"sai ki hada mata ruwan wanka dan tayi ko"

bata tanka ba ta fice tadauki bokiti ta zuba ruwan zafi ta surka, har ta dauka kuma ta ajiye ta kara kandamo ruwan zafi ta kara tasa hannunta taji zafi rau,dariyar mugunta ta saki ta dauki ruwan faki bandaki ta dawo ta leka dakin tace takai mata.

Sai da ta gama yangarta kafin ta mike ta dauki duk abinda zata bukata ta fito Dije tayi mata jagora har bakin bandakin.

Cike da kyankani take kallon gurin inda ta leqa da sauri ta dawo harda toshe hanci,hakan ne ya kara kular da Dije dan tasan dai bandakinsu sumunte yake ,kuma wanke yake fess,dan inna akwai tsabta itaka dai ace baida rufi,ganin datayi ko kallonta Dije batayi ba yasa ta shiga,ta dan jima kafin ta cire kayanta tana ta neman gurin rataye wa ta rasa,dole ta dora saman katanga inda ta dawo ta tsaya tana tunanin yadda zata iya wanka a irin wannan wurin,dan tunda take a rayuwarta wannan shine karo na farko data taba zuwa kauye kuma ta taba shiga irin wannan bandakin.

Itako Dije dake tsaye sajida na aje kayanta ta zura hannu ta kwashe su dan dama tsayuwar datakeyi kenan,tasa kai ta nufi hanyar waje tana fadin zaki gane bakida wayo wato ni zaki rainawa muhallin iyaye ko,tana zuwa zaure ta watsa kayan saman wani buhu dake jingine a gurin itama bata san kona miye ba ta fice tayi gidan maigari tana fadin ni acan ma zan kwana.

******

Gajiya tayi da tsayuwa ga sanyi dake busata ga kyankyani datake ji tasa hannu danta fara wankan,da sauri ta dauke jinshi tayi da mugun zafi kuma dama ita duk sanyi bata fiya son ruwa mai zafi ba.

Mikewa tayi da niyyar dauko kayanta tasa ta fita ta sanar da wannan shwgiyar yarinyar ta kara mata ruwa amma kuma sai me?

wayam ta gani babu kaya babu alamar su.

*Hegiya dije a nzo gidan naku ma saikin nuna hali,to fa!!!*

*vote*
*comments*
*with*
*Alqalamin khady* ✍
[3/15, 11:23 PM] El~hajj: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀
Chapter 37 · 0% Book details