← Book details Tame Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 59

Sashe 38

Tame Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*TAME GARI*

NA
khadija usman

3⃣7⃣

*A koda yaushe bazan gaji da bawa masu bina pc akan in tura musu tame gari hakuri ba,wallahi banida time din wannan kuyi hakuri abin ne dayawa kunada yawa sosai kuma kowa da wanda yake so,ya kk so inyi ina iyakar kokarina wajen ganin na saurari kowa,amma duk da haka ban tsallake zagi da cin zarafi ba a gurin wasu,amma nagode sosai kuma ni yanzu ba abinda zai batamun rai insha Allah yadda nafara littafin nan tunda ni nayi niyya to saina karasa shi da yardar mai duka dan haka ina mugu mugun sonki all tame gari fans* 😘

__________________

Qara dubawa tayi sosai ko kayan sun zube kasa ne,amma taga wayam ga sanyi daya fara kodar ta yana shiga jikinta,to ya kenan? ko tantama batayi tasan kayan baya suka fada,to ya zatayi kenan,yankewa kanta tayi kawai tayi wankan inta gama ta leko intaga wannan me siffar aljanun tace ta miko mata kayan,in kuma bataga kowa ba tayi shahada ta dauko da kanta,da wannan tunanin ta qara sa hannu cikin ruwan dan ta fara wankan,yana nan dai da zafin sa ga sanyi da iska nata busowa abu ya hadar mata goma da ashirin.

Wani dutse data gani ajiye gefe ta dan raba ta zauna akai,tana jiran ruwan ya huce tayi wankan,ta jima a zaune jin sanyi na niyyar illata ta yasa ta matso da ruwan ta dinga diba kadan-kadan tana watsawa tana gantsarewa tare da rutse ido.

******

Tana fita direct gidan maigari tayi tana zuwa kuwa gida ya amsa kuwwar zuwanta inda aka shiga hirar yaushe gamo ,har maigari suka shigo shida su Habeeb suna biye dashi nan suka zauna aka dasa sabuwar hira.

Ganin dare nayi ne yasa maigari cewa Dije "ke tawajena!! anan zaki kwana ne?,dan naga dare yafara yi.

Ai kaima kasan dole in kwana a gidanka,shekara ta nawa marabin da in kwana, kaga kuwa dole in barje haushina.

Ja'ira baki abin magana,to su 'yan gidan naku ai cewa sukayi inda kike nan zasu zauna to kuma gashi kin gudo kin barsu ya kenan?

To ai nayau ne kawai yanzun ma inada dalilin kwanan anan, dan haka ka kwantar da hankalinka gobe tun da asuba zan koma.

Miye abin tashin hankalin acikin kwanan naki uwar magana!!!

cewar Baba Habiba matar maigari uwar gida,

to ai naga duk kamar bakwa farin ciki da kwanan da nace zanyi ne,duk da mun jima bamuga juna ba.

to ai kece Dije ba'a kewarki wlh duk inda kika zauna sai an so ki karawa motarki mai, saboda addabar mutune da kike yi da rashin jin ki,ai ni naga kokarin wannan yaron (Daddy)da sauran mutanen gidan da suka iya zama dake har tsawon wannan lokacin banji ance kin sabauta wani ba.

Inji wa ya fada miki bata sabauta wani ba ?

cewar Naseer dasai yanzu yayi magana,shi kuwa Habeeb nacan yanata dannar waya ,Sajida yake kira amma bata daga ba,jira yakeyi data daga ya tashi ya basu wuri danshi baya son yawan surutu.

Au ta gwada muku halin kenan ya cewar Baba.

kallon Dije Naseer yayi yaga yadda ta tsareshi da ido saiya tuno duk artabun da akayi da su abaya,ya so kora jawabi amma ya waske yace,

Ai Baba ba karamin dadin zama ke da khadija ba,yarinya ba ruwanta salaha da ita nutsatstsiya,ga hakuri da sanin ya kamata ga.......

ai tun a nan yakamata ka tsaya dan in jikina duk kunne ne ban yadda ba tunda naji ka ambaci kalmar hakuri nasan kadai fada ne kawai ammaina Dije take da hakuri,yarinyar da tun tana goye ko kallonta kayi indai bai gamsar da ita ba saita rama,bare kuma data fara tasawa,dan haka sai dai ka fadawa wasu halin Djje badai ni ba, dan duk wanda ya kwana da sanin haihuwar Dije a garin nan,to yasan da zamanta,dan in tana guri bata buya......

managed pls

*vote*
*comments*
*with*
*Alqalamin khady* ✍
[3/15, 11:24 PM] El~hajj: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀

*TAME GARI*

NA
khadeeja usman

3⃣8⃣

___________________

Haka hirar tasu takasance,inda Naseer ya dage ya dinga yabon Dije na dole,dan gudun kar tarihi ya maimaita kansa.

Shiko Habeeb kiran dayake yiwa Sajida ne bata dauka yasa ransa baci, "ko ina tabar wayar oho" ganin dare nayi yasa ya mike yacewa Naseer,

"toh sarkin zance! inka gama ka iya tasowa mu tafi,dan ni nagaji da jin wannan hirar taku" ya karasa maganar yana kokarin fita daga dakin.

Oh ni 'yasu!! kai dai wannan hali naka baiyi ba wallahi,ace mutum kullum fuska tamke,ji dan uwanka ya tsaya anata hira dashi rai rai rai, amma kai sai wani ciccin magani kakeyi,ka manta lokacin da ka fada komar Dije kenan kazo kanata karkarwa harda su sume-sume,amma yanzu ka gyare ka karo wulakanci,to wallahi in bakayi wasa ba tarihi zai maimaita kanshi,ni dai ba ruwana,naso ma ace kataho da taka matar amma saboda tsabar rowar mu ganta sai shi Nasiru ne ya taho da tasa,kai ban san meya hanaka ka taho da takan ba ko muni ne yayi mata yawa da alama mun fita.

Jin batun da baba tayi ne yasa Dije tunawa da tabargazar da Inna tayi dazu,dan haka cikin boye dariyarta tace,

Ke baba!! har mata nawa kike so ya taho miki dasu,ko kin fara magagin tsufa ne,dan naga har gaisawa kunyi da ita fa sosai.

Wallahi karya kikemun! nadai gaisa da matar Naseeru,sai ita Karima,sai wannan sangamar kanwar tata,sai kuma ke,toh bayan ku indai ba karya ake son nayi ba,to ni banga kowa ba.

Dariya Dije tayi,kafin ta juya ta kalli fuskar Habeeb taga yadda yayi kicin kicin gashi bakin kofa,shi bai fita ba,shi bai dawo ba ya tsaya yana jin cin zarafin da Inna keyi wa matarsa,wadda ya zuwa yanzu abin yafara damunshi,dan kusan duk wanda yaga Sajida saiya nuna basu dace ba,duk da tana da daukar wanka amma shekarunta sun kasa boyuwa saboda girman jiki.

"Ai inna wannan da kika kira da sangama itace matar tashi"

Rike haba baba tayi! kafin tace," Ikon Allah!! ku fa mutanen birni baruwanku da girma ko tsufan mace,inba haka ba kai ina kai ina wannan matar kusan sa'ar mahaifiyarka,abinma ba dacewa wallahi,to amma ya za'ayi ance matar mutum kabarinsa Allah dai yabada zaman lafiya,Ameen.

Sakai yayi ya fice ransa a dan bace,inda Dije da Naseer suka kwashe da dariya wadda har saida ya juyo sautinta ransa ya kuma baci,fuuuuu ya fice yayi side din baba malam.

Naseer wani zaman ya kumayi aka sha hira dashi sosai,har saida baba ta bingire, nan shi da Dije suka dinga kaftawa kamar wasu abokan wasa ko wasu sa'anni,ganin da yayi Dije batada niyyar gajiya yasashi cemata zai je ya kwanta nan yayi mata sallama ya fice yana hamma.

*********

In ana sandarewa ya zuwa yanzu to fa ta sandare domin haduwa hakoranta sukeyi gaf gaf saboda wani mugun sanyin datake ji,dan haka ta lallaba ta karaso kofar bayin ta zuro kai dan jin inba kowa ta zagaya ta kwashi kayanta tasa,ganin ba kowa yasata saurin fitowa tana gab da gama fitowar taji motsi ana rufe gida,da mugun sauri ta koma ciki inda garin shigewa harda goge hannu tayi,tana dan lekowa taga baba ne ya dawo ya shige daki,ta goge 'yar kwallar wahalar data farayi da dana sanin zuwa kauye ta kara zuro kafa da niyyar fitowa taga inna ta fito rike da buta,nan ma ta koma da sauri,jin kamar motsi a bayin yasa Inna tasan da mutum a ciki dan haka ta koma ciki.

Ganin abin bana wasa ba yasa ta fashewa da kuka dan ita a rayuwarta bata san wahala ba sam,ganin kukan bazai fissheta ba yasa ta mike a guje ta fito ta zaga cikin sauri ta shiga neman kayan amma bata gansu ba.

wayyo ni Sajida ta fada fili tare da sakin marayan kuka,to ko dai Aljanu ne suma a wannan gidan yasa suka kwashe mata kaya,tunawa da tayi da cakwakiyar su da Dije a Abuja yasa ta tabbatarwa da kanta ba ko tantama su ne suka kwashe mata kayanta,jin sanyin naci gaba da suburbudar ta yasa taja kafa ta koma bayin dan ta yankewa kanta kawai ta kwana nan amma ko gobe wallahi gida tayi.

Tana shiga ta samu gefen dutsen nan tazauna ta tallafe haba ta fara marayan kuka.

Inna ce ta kara fitowa ta nufo bandakin tazo dab da shiga taji sasshekar kuka,ta tsaya jim!! taji daga bayan gidan kukan ke fita dan haka ta ce ,

Da mutum?

jin ana magana a waje yasa Sajida saurin cewa

Eh!!

lafiya kuma naji kina kuka 'yar nan?

Shuru tayi tana tunani ta fada ko tayi shuru,um kada inje in fada su bini suci ubana gara kawai in waske dan haka cikin shakewar murya tace ,

Dama mantawa nayi ban taho da kayan da zanyi amfani dasu ba in na gama wanka.

Shine kuma kike kuka?to bari a karbo miki,ai magana zakiyi ba ki tsaya kina kuka ba,haka Inna ta juya tana juya lamari irin na 'ya'yan birni,yanxu inba tabara da iskanci ba ya za'ayi gundumemiyar mace kamar wannan ta tsaya yin kuka kawai saboda kaya,bata da baki ne da bazata iya kwalawa mutane kira ba,kuma me meyi laifin na jikinta da ta shiga dasu ai da saita dauro ta fito inta shiga saita canza,amma dan sanabe wai sai an canza wasu.

Ta jima tana sallama amma shuru,sai dag can taji mamy ta amsa cikin muryar bacci.

ko da ta fada mata abinda sajida ke bukata,sai da tayi jim tare da yada magana kafin ta hau laluben inda zata ga kayan amma bata gani ba,dole tace yusra ta bada nata,sai da ta gama tata yatsinar kafin ta fiddo da towel da hijabi ta ajiye gefen gadon ta juya tayi kwanciyarta,nan Inna ta matso ta dauka ta fice ta kaiwa sajida

Da kyar ta dawo dakin dan yadda jikinta ke rawa,inda hankalin mamy yayi matukar tashi ganin yanayin datake ciki,dasauri ta kamata ta shiga tambayarta abinda ya sameta cikin kankanin lokaci haka,sam takasa magana illa rawar sanyin datakeyi wadda mamy cikin hanzari tajawo waya ta shiga kiran layin Habeeb,

wanda shi a dai dai wannan lokacin yana kwance rigingine yayi pillow da hannuwansa,yana tunanin maganar mutane akan matarshi,to miye aibun ta,meye dan ya auri age mate dinsa? kai mutane munafunci yay musu yawa wallahi inkayi wasa sai sun hanaka rawar gaban hantsi.
Chapter 38 · 0% Book details