← Book details Tame Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 59

Sashe 30

Tame Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dagowa tayi ta dubeshi a hankali ta mayar da kanta ga abinda takeyi a wayar tace mishi to dai yaya a dinga saita harshe in an tashi tambaya dan kasan ni fa amsa nake bayarwa dai dai da yadda aka tambayeni

yana shirin yin magana sajida ta shigo ta kafesu da ido kallon da take mishi ya qara tunzura shi yace

wato yusuf ne ya siya miki waya ko?
ke har kin kai namiji ya baki abu ki karba ko nawa kike duka da zaki rike waya yanzu duk iskancin da kikeyi ina kyaleki ne badan ina jin tsoronki ba sai dan gani nakeyi wannan jikin naki idan na tashi dukanki babbalaki zanyi dan haka ki mikomin wayar nan in mayar masa da abarsa tun kafin ranki ya baci

ko kallonsa batayi ba ta shiga kallon wayar datayi dialling har akayi picking kafin cikin sanyin muryarta ta furta

barka da wannan lokacin my daddy

shuru ta danyi alamun ana magana daga daya bangaren

murmushi ta saki kafin tace kowa lfy shine ma yace yana son magana dakai tana fadar haka ta mika masa wayar

cikin bacin rai yace uban waye ?

ubanka ne yaji an fada daga cikin wayar take yadauki murya cikin rawar hannu ya karba kafin cikin girmamawa ya shiga gaida daddy

naji kana tambayar uban waye shine nace ubanka ne yanzu ka gane ai ko?

ah ah wlh daddy ba haka bane ina tambayarta wanda ya siya mata waya ne to shine.....

ai duk ana nan dai dan ni na siya mata wlh habeeb kasake naji wani abu marar dadi ya faru game da zaman yarinyar nan a gidan nan saina saba maka da har naji dadi ganin yadda kuke kula da ita amma yanzu na lura tunda mahaifiyarku ta fara kawomin korafe korafe nasan saita zuga ku kunyi abinda be dace ba to wlh ku kiyayeni wannan karan daga ku har ita zan saba muku

insha Allah daddy ba abinda zai faru

Allah yasa Allah kuma yayi muku albarka

Ameen

ina ita khadijan baban bata wayar

wulla mata yayi kan cinyarta ta karba inda tasa wayar a kunne suka gama da daddy sannan ta kashe

harararta habeeb yayi kafin ya jefa mata ledar gurin yusuf yace ga kayan da kk rokeshi nan kwadayayyiya

kallon ledar tayi kafin ta miqe ta shiga tattara abinda ya zubo cike da rashin damuwa da maganar shi kafin ta tattara ta dauka sannan tace

ai kaima yaya kasan ba halina bane roko dan haka ka daure ka dingamin shaidar kwarai ni kunga nayi nan inje inyi waya da my choice tana fada ta juya abinta ta barshi da sakin baki

my choice?

ya maimaita kalmar

sajida ce tace nifa ban gane nufinka ba habeeb naga duk ka wani hargitse

ba dole na hargitse ba kina jin abinda 'dan iskan can ke cewa

to sai me ?ni banga wani abu a maganar da yayi ba in yarinya taga tana sonshi ba shikenan ba bakaji yace matarshi bata da matsala ba

ashe kema bakida hankali yarinya karama kamar khadija za'a yiwa aure duka nawa take ?

eh lallai fa qaramar yarinya amma ai duk ga kayan more mace nan a tattare da ita kuma nawa akayiwa auren da basu kaita ba suka zauna harda haihuwa

ai shiyasa kuwa suke gamuwa da yoyon fitsari kinga ni ban son shashanci ki kyaleni kawai dan na lura kema jirgi daya ya kwaso ku yana fadar haka ya shige daki bammm ya bugo kofa yayin da ta zauna sharaf kan kujera ta shiga tunani to me hakan ke nufi ?
wata zuciyar ta saka mata mugun tunani wata kuma ta bata me kyau daga karshe dai tace kai gaskiyarshi fa duka nawa yarinyar take da har za ai batun wata soyayya bare ma nasan habeeb dina bayada wannan tunanin da nakeyi bari inje in rarrashi abina ta fada tana me miqewa ta shiga daki

*****

sannu a hankali rayuwa ke tafiya yayin da su dije suke zana jarrabawarsu cikin sauqi da kwanciyar hankali

zamanta gidan su habeeb kadaran kadahan babu wata sakin fuska gurin sajida da shi kanshi me gidan har gara naseer ma amma ko ita yusra wani lokacin cin magani takeyi yayin da itako dije bata ko kula da yadda takwe mata iyakarta inta iske naseer a gida suyita hirar su inda zaita tsokanota tana bashi labarin kauye yana dariya abin har mamaki yake bata yadda ya canza mata lokaci daya

yauma ta fito kenan da niyyar komawa part din su habeeb din inda ta jima gurin su yusra suna hira dan ba laifi yau itama yusran ta saki jiki da ita sun danyi hira

tana shiga parlon taji hayaniya inda ta shiga da sallama

duka juyowa sukayi suka bita da wani kallon rainin hankali kafin suka kwashe da dariya

ganin yadda suka mata yasa tayi niyyar shigewa amma saita tsinkayi muryar wata na cewa

.ah lallai su Aunty kun iya kiwo ji yadda kashi ya fara tofon tsoka anji jar miya an nuna anyi jajir an baro su inna a kauye yanzu hakama an manta dasu sai irin haka ta faru an kira sunansu ake tunawa dasu

dukansu suka sa shewa tare da fadin gaskiyarki kuwa kausar fada mata dai anzo zaman tsegumi sai tsula tsiya akeyi wlh ni Aunty da ace kin fadamin tunda wuri da tuni nayi miki maganin wannan matsalar

sajida da sai yanzu ta tanka tace hmm ku barni dan Allah ni da abinda ke damuna kuje can ku qarata ta fada tare da miqewa tayi cikin dakinta

af kinga ko na fada muku harda laifin Aunty ji fa yadda tayi ba dole yarinyar ta raina ta ba wlh yau sai mun gyara miki zama ke sai ma kin bar gidan nan dan uwarki zo nan

dije data zuba musu ido ta tsaya tana nazarin ta inda zata fara bata gama tunanin ba taji an jawota kiiiiii har an dangwarar da ita zauna dan uwarki yau wlh sai kin san bamuda mutunci

kuriii dije tayi musu da ido daya bayan daya kafin tace

to wai ku in tambayeku me kuke shirin yimin ne kuma me nayi muku?

au tambaya ma kk yi kinga mimi kawai kaddamar mata saita fahimta

dariya dije ta farayi harda rike cike ganin hakan yasan duk suka bita da kallo inda kausar dayake itace qarama tace kutmelesi au dariya ma kikeyi a fusake tayo kan dije ta shiga kai mata duka

duk da dije najin dukan amma dariya kawai takeyi ganin haka yasa kausar dakatawa ta kalli mimi tace anya kuwa yarinyar nan nada lfy kuwa?

ci gaba mana ko kin gaji cewar dije da har yanzu dariyar takeyi

*vote*
*,comments*
*Alqalamin khady*
✍[3/15, 6:37 PM] El~hajj: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀

*TA ME GARI*

na
khadija usman

2⃣9⃣

Au wato ma baki daku ba ne shiyasa kk cewa aci gaba cewar kausar data taso nan tayi kan dije ta shiga tillikar ta itama

duk da dije najin zafin dukan iya ji amma taurin zuciya yasa banda dariya babu abinda takeyi ganin hakan yasa su dakatawa suna kallonta tare da mayar da numfashi dan abinka da jinin hutu har sun gaji

itako dije harga Allah jikinta ya amshi duk sakonnin da suka aika mata ganin duk sun gaji sun tsaya yasa tace

badai har kun gaji da yakin sunkurun ba?

au bakinki be mutu ba kenan to bari ki gani in sa nawa hannun muci uwarki a zo a tattara ki a mayar dake kauye a welbarro

ah ah kinga dakata cewar dije naga abin naku zalunci ya shigo ciki abin taron dangi ne ni da gidan dan uwana amma an kafamin kahon zuqa kawai sbd nazo na zauna kamar akan uwar wani nake zaune

ke dan uwarki mu kk zagi ?

nidai bana son sharri bakiji na zageku ba amma in kunce hakan toh nafada din ta qarasa maganar tana murguda baki tare da gyara tsayuwarta ta coge tana yatsina fuska dan wlh fa ta daku a ranta tace shegu a haka kamar basuda kwari a she nama ya ratsasu da dan sauransu gashi suna shirin halakani

ai na fuskanci sai mun dirje bakin yarinyar nan yadda baxata samu bakin rashin kunyar nan ba rufe mana kofa mu lakadi shegiya yadda batada maceci da sauri mimi ta nufi kofa tasa mata key ta zare ta taho dashi a hannunta

kinga kausar rufe Aunty ta waje dan na lura itama bazata barmu muyi yadda muke soba tana iya hanamu maganin wannan shegiyar

dije dake tsaye taga kausar ta nufi dakin sajida saida ta zura kai ta ciki taga sajidar bata nan da alama tana toilet dan taji karar ruwa aikuwa ta zaro key din ta fito dashi ta waje ta rufe ta dawo falon a take zuciyar dije ta shiga lugude a ranta tace kinga dije ko ba komai sarkin yawa yafi sarkin karfi kuma wadannan kitika kitikan da suka koshi da madara gasu nan kamar shanu ki lababa ki tsere to ai kuma sun rufe kofa ya kenan

lura da sukayi dije kamar ta tsorata yasa su kara kaimin nufota tare da narka mata na maguzawa

dakewa dije tayi amma jikinta da zuciyarta kamar sa fado kasa dan rawa ko kafin mimi ta karaso tace mata kinga balama dakata nifa ba koriyar ciyawar da kk saba ci bace naga kin nufoni gadan gadan kina tande baki dabbar mayu

ai bata karasa ba taji saukar wani shu'umin marin data rasa daga ina yazo bata gama tantancewa ba ta fulanin ta motsa jin ana neman sata jinyar dole aikuwa tayi kan mimi a sukwane cikin sa'a kuwa ta dami gashin kanta dayake kalba ce akayi mata da Attact iya qarfinta ta rike tare da cizgawa

wata kara mimi ta saki wadda tasa su kausar nufo dije da dukkan karfinta ta tunkuda mimi da kanta ya daki karamin center table din dake gurin aikuwa take kai ya fashe ganin jini yasa ta sakin wata karar a karo na biyu

kausar na ganin hakan tayo cikin dije yayin da humaira tayi gurin mimi data bare baki tana kuka tare da shafo jinin a hannunta wanda wannan shine karo na farko a rayuwarta data taba jin ciwo da jini haka
Chapter 30 · 0% Book details