← Book details So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 54

Sashe 7

So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suka fito daga shagon Amir yana rik'e da kayan, fura da nono Amira ta hango wata bafulatana tana siyarwa a tsallaken ti-ti sai ta kalli Amir tace " ya kai kayan tana zuwa, Amir ya kalleta yace " ina zakije?" Amira tace " kai dai ina zuwa can tsallaken zan je abu na hango," Amir yace " to karki sake ki dad'e," Amira tai murmushi sannan tace " to ranka ya dad'e," ta juya ta tsallaka ti-tin ta siyo abinda zata siyo ta juyo zata dawo."

Ta zo zata tsallaka ti-ti kenan wata mota ta taho a guje a dai-dai Amir fito daga motar, da k'arfi ya k'wala mata kira yana ta koma da baya amma ina, hakan yasa yai kukan kura ya shiga ti-tin a guje saura k'iris motar ta latse Amira ya sa hannunshi duka biyun ya turata gefe, a yayin da shi kuma motar tai awon gaba da shi.

Amira ta taso daga fad'uwar da ta yi, tare da k'wala k'ara ganin yanda Amir yake zubar da jini kuma tamkar ma babu alamar rai a tare da shi.

Kanshi ta yi da gudu tana jijjiga shi, nan da nan mutane suka cika wajen, kuma da yake bakin ti-ti ne 'yan sanda na kusa da wurin, suma babu b'ata lokaci suka k'araso, wanda ya kad'e shi kuwa yai k'ok'arin guduwa amma cikin yardar Allah aka kamashi, aka wuce da shi station, a yayin da shi kuma Amir aka sa shi a cikin motar shi a baya, Amira ta shiga ta zauna kusa d shi, d'an sanda ne yaja motar, a yayin da ragowar suka biyo su a tasu motar.

Suna k'arasowa cikin sauri aka shige da shi emergency, likitoci suka rufa kanshi ana ta duba shi.

Sun d'auki dogon lokaci suna duba shi, ganin haka ya k'ara tayar da hankalin Amira sosai, banda kai kawo da kuka babu abinda take yi, sam ta rasa natsuwarta gaba d'aya, tashin hankalin da take ciki a yanzu ko lokacin da Sadeeq ya mutu bata jishi ba, sabod ita ta san tabbas Amir yana da babbam matsayi a gareta saboda ya damu da ita fiye da kima, wannan dalilin ne yasa ta shiga firgicin da bata tab'a shiga irinsa ba, tsoro take shima karta rasa shi, can k'asan zuciyarta kuma tausayin shi take ji, yanda ya sadaukar da ranshi domin ceto ta-ta rayuwar.

Wani d'an sanda ne ya kalleta cikin tausayawa yace " madam ki kwantar da hankalin ki insha Allah mijinki zai samu sauk'i, kiyi hak'uri ki d'an zauna ki huta wajen awa d'aya da rabi sai kai kawo kike yi."

Amira tace " mishi to nagode," amma ta kasa yin abinda ya rok'a, ta kasa zama, ci gaba ta yi da kai kawonta har likitocin suka fito tare da shi an nad'e k'afafu, da kai da hannu guda d'aya da bandeji aka kai shi wani d'aki da keb'antacce.

Da dai likitocin sun so su hana Amira shiga, amma d'an sandan ne yai magana yace " dan Allah ku k'yaleta matarshi ce, ta damu da yawa, ku barta ta zauna duk da nasan bakwa bari ana jinya anan kuna da masu kulawa da marasa lafiyan, amma ita ai mata wannan alfarmar."

Bayan sun shisshiga d'akin da aka kwantar da shi, duk da haka Amira bata daina kukan ba, Likita ya kalleta yace " ya kamata ki bar kukan nan haka baiwar Allah addu'a ya kamata kiy mishi ki ma godewa Allah da k'wak'walwarsa bata tab'u ba, se dai ya ji raunuka a jiki, sannan ya samu karaya a k'afa da hannu, amma duk mun gyara insha Allah zai samu sauk'i," d'an sandan nan yace " Allah ya bashi lafiya," dukkan su suka amsa da "ameen."

Suka yi mata sallama suka fita, matsawa kusa da shi ta yi ta zauna kusa da shi a wata kujera ta k'ura mishi idanu, sai ta tuna lokacin da tai rashin lafiya yai jinyarta, ji ta yi an fara kiran sallar magrib, ta tashi ta yi sallah sannan ta antayo wa Amir addu'ar samun sauk'i.

Tunani ta fara yi ya kamata ta nemar musu abinda zai ci koda ruwan tea ne idan ya farfad'o tunda likita ya fad'a musu suma ya yi, amma zai farfad'o nan bada dad'ewa ba.

Tunani ta fara yi ya zata yi domin ita babu inda zata iya matsawa ta bar Amir shi kad'ai, tunowa ta yi sun siyo kaji d'azu da yogot da sauran su, se dai suna cikin mota kuma ita fitar ne bata so ta yi sam ta bar Amir.

Tana cikin wannan tunanin sai wata norse ta shigo, bayan sun gaisa tai mata ya mai jiki ta amsa, sai norse d'innan ta bata maganin shi tace ta ajiye idan ya tashi ta bashi gasu nan a rubuce yanda zata bashi, daga k'arshe ta tambayeta ko akwai abinda take buk'ata.

Amira tace mata a'a babu se dai akwai kayan mu cikin mota dan Allah wa zaki sa ya taimaka ya d'ebo min?" norse tace " ba damuwa bani makullin in kwaso muku, kuma ki fad'a min kalar motar."

Amira ta bata makulli tare da fad'a mata sunan motar da kalarta sannan norse d'in ta fita, ita da wasu norses d'in sukaita kwaso kayan, bayan sun gama kwasowa Amira tai musu godiya.

Har wajen k'arfe tara Amir bai farka ba, har Amira tai sallar isha'i hakan ya tayar da hankalin Amira sai ta ci gaba da nafiloli tana rok'ar wa Amir lafiya, bayan ta idar ta zage tana ta kwakuso addu'a tun tana yi har kuka ya ci k'arfinta taita yi ba k'ak'k'autawa, ji ta yi ance "Amira ki daina kukan nan dan Allah bana so yana tab'a zuciyata," yanayin yanda aka yi maganar yasa ta gane Amir ne hakan yasa ta zabura ta yo kanshi, bata san lokacin da ta rik'e hannunshi ba tace " Amir sannu ya jikin, da sauk'i ko, ina da ina ke maka ciwo?" Amira yace " da sauk'i ki kwantar da hankalinki, ganinki lafiya babu abinda ya sameki ya kore duk wani rad'ad'i na ciwukan dake jikina."

Amira ta kalle shi tace " Amir meyasa kake k'ok'arin halaka kanka saboda ni, yanzu da ka mutu fa."

Amir yace " ke da kin mutu an fad'a miki zan cigaba da numfashi a duniya ne, ai na fad'a miki da ace kin mutu ko an kashe ki gwara kowa ya mutu ciki kuwa har da ni."

Hararar shi ta yi sannan tace " kai d'in in da ka mutu nima an fad'a maka zan iya jurewa ne."

Nan ta had'a mishi tea ya k'i karb'a wai sai ta had'a tukun tasha a gabansa ya gani sannan zai karb'a shima yasha, don ya san itama ba abinda ta ci, sai da ta had'a ta sha sannan ta bashi shima ya sha, sun dad'e suna hira daga k'arshe suka kwanta, da yake gado biyu ne a d'akin da nashi da wani a gefe ba kowa sai ta kwanta a d'ayan bayan ta yi addu'a, sedai har tai bacci amma shi Amir idon shi biyu, shi kad'ai yasan zugin da yake ji a jikinsa amma so ya hanashi bayyanawa saboda kar hankalin abar k'aunar tasa ya tashi, haka ya kwana bai runtsa ba ko ina ciwo yake yi mishi a jikin shi.

Muje zuwa

*🅱K CE😘💋*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘

RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (🅱K)*
```(Autar marubuta)```

SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
_(Mamie)_

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```

*MY LISSA*
_Kinyi kira na amsa soyayya kin bani nai alkawar zamui zama na amana_💃💃💃💃💃
_cikin raina, na sanyo ki, ki bani guri nima in shigo naki😍😍😍😍😍_
_*MY LISSA* k'aunar da kika nuna a gareni baki ya yi kad'an wajen gode miki, se dai zan yi amfani da shi wajen yi miki addu'ar gamawa da duniya lafiya, kina d'aya daga cikin gagaruman marubutan da ke matuk'ar k'aunar *SO MAHAD'IN RAYUWA* kuma Amir ya ce in fad'a miki duk abinki baki isa ki san komai game da shi ba, nidai ba ruwana sak'o ya bani kuma na isar🙊🏃‍♀😂😜_
_nagode da k'auna, yabo, Addu'a da na samu duka daga gareki Allah saka da alkhairi, ina mugu mugun yinki, iya wuya ana tare My lissatu tawa😉😘_

PAGE 35 to 40

Bayan sati biyu jiki yai kyau aka sallame su suka koma gida.

Washe garin ranar da aka sallame su Amira ce keta faman rama baccin da bata samu ta yi a asibiti ba, ga gajiya da ke tambayarta, tana cikin baccin ne wayarta ta fara ringing har ta katse ba'a d'auka ba, sai a kira na biyu ta kai hannunta ta jawo wayar tare da amsawa ta kara a kunne, muryar Amir ta ji yana fad'in " Amira dan Allah kizo ki taimaka min bana jin dad'i sosai wayyo zan mutu," haba ai ba shiri taji nan da nan ta wartsake daga baccin da take ji, bata tsaya tambayar shi ko jin abinda ke damunshi ba ta katse wayar, mayafi kawai ta zara sai makullin mota ta fice daga gidan cikin sauri kuma cike da tashin hankali.

Da yake bata tab'a zuwa gidan shi ba, amma ya tab'a fad'a mata sunan unguwar, hakan yasa saida ta shiga unguwar sannan ta kira shi ya fad'a mata gidan.

Bayan ta k'arasa k'ofar gidan ta shiga da motar ta tai fakin sannan ta fito ta shiga ciki har tana had'awa da gudu, tana shiga ta ja ta tsaya turus, domin zaune ta ganshi kan kujera ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya yana kallo, Amira ta kalle shi tace " dama lafiyarka lau shine ka tayar min da hankali menene amfanin yin hakan?"

Amir yace " lafiya lau nake se dai zuciyata da ke yi min zafi saboda addabata da take yi da tunaninki, dama saboda kizo in ganki ne in samu maganin rad'ad'in da take min ne kawai, haba Amira tun jiya fa da muka dawo daga asibiti ban k'ara ganinki ba a tunaninki baran cutu ba."
Chapter 7 · 0% Book details