Sashe 40
So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
_"Kamar yanda ka sani ne sunana Ahmad, ni haifaffen garin Kontagora ne, iyayenmu mu biyu suka haifa, kuma tun muna yara har tasowarmu suna nuna mini 'kauna fiye da d'an uwana yayana Sunusi, wanda ni nasan ba komai yasa suka fi 'kaunata ba illah biyayyar da nake yi musu da kuma kyautata musu, amma ni kaina sam bana jin dad'in abinda iyayena suke yiwa Sunusi domin har akwai ranar da nai musu magana akan be dace suna fifitani akansa ba, sukace ba dan komai suke yin haka ba sai domin ya shiryu ya zama na 'kwarai ya daina abubuwan da yake yi, dan maganar gaskiya Sunusi baya ji kuma baya ganin girman iyayenmu sam, sedai da na nuna musu cewa ai yin hakan ga yaro irinshi kuskurene babba iyaye suke yi, domin tsana bata tab'a gyara kangararren yaro sedai ta 'kara busar mishi da zuciya, suka yi na'am da zancena, kuma daga ranar basu sake nuna mana bambanci ba a tsakanina dashi, to ada kafin nan idan iyayena suka yi wa Sunusi irin haka yana nuna jin haushinsa har yai zuciya da ni, to sedai ni kuma ina 'kaunar d'an uwana har ga Allah bana son ganinshi a irin wannan halin, hakan yasa ma har nakai ga yiwa iyayenmu magana su kuma suka gyara, to daga lokacin muka daidaita da d'an'uwana babu abinda ya sake shiga tsakaninmu har Allah ya rayamu muka girma, ni da Sunusi muna 'kaunar juna sosai, ko kad'an baya 'kaunar yaga wani abu ya sameni, kulawar da muke baiwa juna takai 'kololuwa, iyayenmu talakawa ne ba wasu masu kud'i bane, amma a haka sukaita fad'i tashi sukaita kula da karatunmu hakan yasa muka tashi da burika a ranmu rututu na ganin mun kyautatawa iyayenmu sunji dad'i ta dalalinmu, sedai kash, bayan mun kammala makaranta duk result d'in yayana basu yi kyau ba, ganin yanda yayana ya damu yasa na kwantar mishi da hankali tare da tabbatar mishi da cewa idan har na fara aiki albashina dai-dai zan ri'ka rabawa ni da shi kafin in nema mishi aiki a kusa dani, a zahiri ya nuna yaji dad'in haka, sedai a bad'ini ashe haushina da hassada ce a ransa, bayan na samu aiki a Abuja na fara zuwa duk albashin da na samu rabawa nake kamar yanda na fad'i in baiwa yayana Sunusi rabi in d'auki rabi, kuma ni nawa da yake garin namu a cikinsa ma mu a 'kauyen garin muke kuma duk talakawa ne irinmu, hakan yasa duk na d'auki albashina gaba d'aya talakawan nan nake raba mawa, da yake muna da 'karancin ruwa a wajen sai an sha wuya, hakan yasa shima nasa akai musu famfo da kuma burtsatse, nasha albarka da kuma addu'a wanda nasan sune sanadin da sukaja har nakai wannan matsayin a yanzu, ina matu'kar jin tausayin 'yan 'kauyenmu fiye da tunaninka Amir, saboda zaka ga ka d'auki naira hamsin wadda kai a ganinka ka rainata amma in ka baiwa wani magidancin sai kaga yana godiya harda kuka, wannan dalilin yasa na d'auki alwashin taimaka musu iya iyawata, ana haka wata rana shugabana na wajen aiki ya kirani na zauna, sannan ya kalleni yace "abinda yasa na kiraka saboda dalilai biyu ne, na farko an maka 'karin girma, ka tashi daga 'karamin ma'aikaci yanzu ka zama manaja na wannan kamfanin, kuma in babu damuwa ina yi maka sha'awar auren 'yata Khadija, ba komai ya kawo duk wad'annan abubuwan ba illah kyawawan halinka, domin duk wani ma'aikaci na wannan kamfanin mukan bibiyi rayuwarsa kar muje mu d'auko wanda zai rusamu, to duk a cikinsu ka zarcesu kyawun hali da na d'abi'u ga gaskiya da ri'kon amana, babu abinda ya 'kara burgeni da kai illah tausayin wanda bashi da shi da taimako, dan haka sati me zuwa zaka fara aiki, maganar khadija kuwa kaje kayi shawara duk abinda ka yanke sai ka sanar dani daga baya," na yiwa ogana godiya sannan na tashi na koma gida, bayan iyayena da d'an uwana sun hallara waje guda sai na sanar dasu 'karin girman da akai min da kuma abinda ogana yace akan 'yarsa, sunyi murna matu'ka tare da bani goyon baya akan Khadija suka ce inje d'in in ganta in dai tayi min kawai sai in aureta, jin Sunusi shi bai ce komai ba yasa na juyo na kalleshi nace "yaya kai bakace komai ba," ba tare da nuna fara'arsa ko walwalarsa ba yace "Allah sanya alkhairi," na sake cewa "amma yaya ni nafi so sai ka fara yin aure kafin ni nayi, ko kuma muyi a rana d'aya," Sunusi yace "ai in zaka yi aurenka kayi dan ni gaskiya ba yanzu ba sai nayi arzi'ki tukun," daga haka ya tashi yace kanshi na ciwo zai shiga cikin d'aki ya kwanta, naji mamakin maganar da Yayana yake fad'a saboda albashina dubu d'ari da hamsin ake bani duk wata a lokacin, ina d'aukar saba'in da biyar in bashi saba'in da biyar, amma bansan ya yake yi da kud'i ba dan kuwa komai na gidanmu ni nake yiwa iyayenmu hatta cefane wannan kai komai ma na gidan, shi kanshi idan bu'katarshi ta tashi ni nake yi mishi, amma wai yana fad'in baida kud'i sai yayi arzi'ki, bayan sati na koma bakin aikina, daga lokacin da na fara aiki zuwa yanzu 'yan 'kauyen nan babu wanda baya 'kaunata, har gida ake bin iyayena ana yi musu godiya da yimin addu'a, ashe duk wad'annan abubuwan Sunusi ya ri'kesu a ranshi ne yana kallona dasu, naje gidansu Khadija na ganta kuma na yaba da halayenta, hakan yasa babu b'ata lokaci iyayena sukaje aka sa rana inda mahaifinta ne yai komai aka sha shagalin biki muka tare a gidan da aka bani tun ranar da na fara aiki, madaidaicin plat ne amma ya had'u, mahaifin Khadija wata guda ya bani ina shan amarci, bayan wata biyu da aurenmu na d'auki Khadija na kaita 'kauyenmu domin ta gaida iyayena da d'an uwana Sunusi, tunda sunusi yaga Khadija yake mata kallon 'kurilla tare da washe baki kamar gonar audiga, lura da hakan yasa naji kishi a raina, ada munzo muyi sati ne, amma muna yin kwana biyu nace zamu koma, muka yi sallama dasu muka juya, da yake duk 'karshen wata nake zuwa gida inga 'iyaye da 'yan uwana ina nufin talakawana na garin wad'anda na zame musu tamkar uba ko kuma wani sarkin garin, a lokacin da nazo garin sai na samu mummunan labari daga wajen Iyayenmu wai yaya sunusi ya zama d'an fashi, kuma yana shaye shaye, isowata kenan na tarar da wannan ba'kin labarin, muna cikin maganar sai ga Sunusin ya shigo da gudu wani ri'ka'k'ken d'an daba dake wani 'kauye wanda ke ma'kwabtaka da namu ya biyoshi har cikin gidan, ya d'aga wu'kar hannunshi zai yanki Sunusi da ita kenan sai nai sauri na tare ya yankeni a ciki, nai 'kara tare da zubewa 'kasa dukkansu suka yo kaina shi kuwa d'an daban nan ina jinshi yana fad'in "Allah ya 'kwaceka d'an uwanka ya ceci rayuwarka, amma ba yaawa tunda a nan 'kauyen kake kuna kusa da namu ne ai dole wata rana zamu had'e a lokacin zaka gane kurenka," ya juya suka fice shi da yaransa suna gigije girgije, iyayenmu suka d'aukeni suka kaini wani asibiti dake cikin gari aka dubani aka tsaida jinin tare da d'inkewa sanna aka samin magunguna a wajen, bayan mun dawo gida na kalli yayana wanda tun lokacin har zuwa yanzu kuka yake aikin yi, nace "yaya su waye suka biyoka kuma me kai musu?" Sunusi yace "kayi ha'kuri d'an uwana, na jawo maka an raunataka," sai nace mishi kar ya damu zan iya rasa rayuwata domin kare tashi rayuwar, nan ya fad'a min wai ciki yaiwa 'kanwar wannan d'an daban suke ta nemanshi, jin wannan maganar ba 'karamin tayar da hankalina yai ba, yayana ne shi ya kamata ace yana min fad'a in nayi kuskure ba ni ba, bayan na warke na tafi dashi Abuja yai wata shida a can sannan muka dawo na kaishi wani waje da ake d'inki nace da zama haka gwara ya koya da aikin riguna ne da kuma d'inki sukeyi nace duka a koya mishi, na biyasu a ranar ya fara koya washe gari ni kuma na koma Abuja da tunanin d'an uwana, iyayenmu duk sun rame saboda damuwar da yake jefasu ciki, ina komawa na samu sa'kon kiran gaggawa daga wajen matata Khadija ogana na nemana, haka na tafi ban ko zauna ba gabana na fad'uwa saboda be tab'a yimin irin wannan kiran bazatan ba._
Muje zuwa
*🅱K CE😘💋*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (🅱K)*
```(Autar marubuta)```
SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
```(Mamie)```
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```🤜🤛
*MAMAN LABYB*
(Mamie nah)
*Hajiya mamie ikon Allah, kinyi naki kinyi na me 'karamin 'karfi, hadari malafar duniya, baya goya marayu, keji ba'a yi maki 'kyaure ko an maki sai ya bud'e yasin,😍😉 wuhuhu ina gwanar wasu nidai ga tawa, kainuwa dashen Allah, duk mai 'kaunarki ni yaso, ma'kiyinki ni ya'ki, duk mai 'kaunata to dole ya 'kaunaceki, Allah ya cigaba da d'aga darajarki ma'kiyanki suita ganin cigabanki ba'kin ciki na halakasu😂😂, ina yinki saboda Allah.😍😘💋*
*~MUMMYN - SULTAN👑*
*Mummyn Sultan wannan shafin kyauta ne a gareki, naki ne ke kad'ai kiyi yanda kikaso dashi babu mai ce miki don me😉😍*
PAGE 170 to 175
Muje zuwa
*🅱K CE😘💋*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (🅱K)*
```(Autar marubuta)```
SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
```(Mamie)```
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```🤜🤛
*MAMAN LABYB*
(Mamie nah)
*Hajiya mamie ikon Allah, kinyi naki kinyi na me 'karamin 'karfi, hadari malafar duniya, baya goya marayu, keji ba'a yi maki 'kyaure ko an maki sai ya bud'e yasin,😍😉 wuhuhu ina gwanar wasu nidai ga tawa, kainuwa dashen Allah, duk mai 'kaunarki ni yaso, ma'kiyinki ni ya'ki, duk mai 'kaunata to dole ya 'kaunaceki, Allah ya cigaba da d'aga darajarki ma'kiyanki suita ganin cigabanki ba'kin ciki na halakasu😂😂, ina yinki saboda Allah.😍😘💋*
*~MUMMYN - SULTAN👑*
*Mummyn Sultan wannan shafin kyauta ne a gareki, naki ne ke kad'ai kiyi yanda kikaso dashi babu mai ce miki don me😉😍*
PAGE 170 to 175