← Book details So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 54

Sashe 2

So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amira itace a tsakiya tana gudu cikin nuna k'warewa da k'wazo, a yayin da Amir yake a can baya, haka yaita wuce wad'anda suke gabanshi har saida yazo daf da Amira ya zamto a tare suke gudun kuma sune kan gaba, kuma kowannensu ya kafe kai da fata sai ya wuce to da yake a cikin masu yin gasar harda Abdul daya daga cikin abokan Amira, ganin da yayi wani na k'ok'arin shiga gaban Amira yasa Abdul yaita tattare wa Amir hanya, idan Amir yazo zai wuce sai ya riga shi, shi ya yarda ya fad'i indai Amirar su tai nasara, hakan yasa Amira ta k'araso wajen su cikin k'warewa, Amira suka had'a ido da Abdul yai mata nuni da kai alamun ta wuce, har ta kusa kawowa dai-dai layin da zaka tsallake ka ci gasar.

Suna gaf da shiga layin a tare duk da Amira ta d'an wuce Amir kad'an, Amir na ganin zata cinye shi yai wani irin tsalle kawai sai gashi a tsakiyar filin wajen da duk wanda ya k'araso yaci.

Ihu aka hau yi ganin yau ga wanda ya kayar da Amira a tsere, sedai wad'anda suka ji haushin ba ita taci ba sunfi yawa musamman Sadeeq d'aya daga cikin abokanta, koda yake shi ya wuce aboki dan bata da wanda take neman shawara gunsa sai shi, a tak'aice ma dai shine wanda suke kasancewa tare a koda yaushe, koda nemanta kake yi in ka tambaye shi kai tsaye zai nuna maka inda take kuma kana zuwa zaka sameta a gun, sedai hakan ma bata taba faruwa ba dan kaf cikin makarantar ko ina take to suna tare da shi.

Yaji haushi da Amira bata samu nasara ba, saida yai hawaye saboda tsabar b'acin rai.

Amir ya k'arasa wajen Amira wadda take ta mamakin irin tsallen da ya yi ya shige cikin filin, yace " haka nake da wannan baiwar duk abinda nasa a gaba to sai na yi nasara akai, idan ba zaki damu ba ina son yin magana dake a wajen shak'atawar d'alibai, ita dai Amira bata ce komai ba, ganin haka yasa Amir ya juya ya tafi.

Koda Amira ta k'arasa wajen ta riga Amir zuwa, zama tayi kan d'aya daga cikin kujerun wajen, tana duba ta inda zai b'ullo.

Daga bayanta taji maganar shi yana fad'in " gani nan ai," Amira tai murmushi sannan tace " ina tayaka murnar samun nasara, amma ya akai ka iya yin wannan tsallen da kayi lokaci guda?"

Amir yace " saboda bana tsoron mutuwa, sannan bana fargabar samun nasara ko rashinta, shiyasa nake samun sa'a akan komai," Amira tace " ai kai ba namiji bane, kuma bana maka kallon jarumi tunda har sai ka yi tsalle zaka ci gasa, kaine mutum na farko da ka kayar da ni a gasa ta hanyar cuwa-cuwa, amma ka kiyayi had'uwarmu da kai a wata gasar ta gaba, dan idan kace zakai tsalle a gasa ta gaba to tad'iyeka zan yi ka fad'i," ta k'arashe maganarta tare da murgud'a mishi baki, Amir bai san sanda ya kwashe da dariya ba, domin yanda tai maganar da fad'a tamkar ma kashedi take yi mishi.

Suna cikin magana Abdul d'aya daga cikin abokan Amira ya hango su ya taho inda suke, yana k'arasowa yace "barkan ku dai Amira," ya mik'a wa Amir hannu suka gaisa, sannan yace " kai ne d'alibin da ya zama gawurtacce a idon d'alibai a ranarka ta farkon fara zuwa makarantar nan, duk da kasancewarka sabon d'alibi."

Amir yace " nagode," suna cikin magana sai ga su Sadeeq da su preety sun k'araso wajen, nan Amira ta bisu d'aya bayan d'aya ta rungume su sannan ta fara gabatar wa da Amir su da matsayinsu gareta, har tazo kan Sadeeq wanda shine na k'arshe, bayan ta rungume shi sannan tace " wannan shine babban abokina, duk girma da fad'in makarantar nan banda kamarsa."

Shima Amir gaisawa yai da su d'aya bayan d'aya, daga nan aka kawo musu abubuwan sha harda kayan maye, wasu sun sha da yawa wasu kuma sun sha amma kad'an.

Abdul yana d'aya daga cikin wad'anda suka bugu sosai, kuma tunda ya bugu yake ta kallon Amira, tasowa yai cikin jama'a ya rungume Amira tare da fara yi mata wasu abubuwa dai kai daga gani kasan baya cikin hankalinsa, Sadeeq ne ya taso kanshi ya raba shi da Amiran sannan ya fara kai mishi bugu bayan an raba su ne Sadeeq ya nuna Abdul da yatsa, tare da fad'in " idan har ka k'ara tab'ata sai na kashe ka," cikin buguwa Abdul yace " kafin ka kashe ni ni sai na kashe ka nan fa aka janye su suka bar wajen.

Washe gari bayan an tashi daga lecture ta farko suna hutawa, sai d'aukar hotuna suke yi, bayan sun gama d'aukar hotunan sai suka zauna suna dubawa, sai ga Abdul ya k"araso wajen, yace " Amira dan Allah abinda ya faru jiya kiyi hak'uri ba da gayya nai miki ba, buguwar da na yi ce tasa haka, dan Allah kiyi hak'uri," Sadeeq da ke zaune kusa da Amira ne yake ta faman banko mishi harara.

Amira bata ce komai ba, sai da k'awayenta da abokanta suka sa baki sannan tace " shikenan ya wuce."

Da yamma Amira ce keta faman motsa jiki tana (tirenin), tana cikin motsa jikin ne taji sak'o ya shigo cikin wayarta, tana dubawa taga an yi rubutu kamar haka,

_lek'o ki d'auki sak'on zuciyata zuwa ga taki zuciyar._

Fitowa ta yi, a harabar gidan su ta ci karo da wani kwali me matuk'ar kyau, jikinshi duk an k'awata shi da flowoyi, d'auka tayi tana k'ok'arin bud'e cikin kwalin.

Babu komai a ciki sai adon fulawa, can k'asa kuma wata takarda ce a ajiye, d'auko takardar ta yi, sannan ta bud'e ta, rubutu aka yi me matuk'ar kyau da ban sha'awa, an rubuta,

_*SO MAHA'DI NE NA RAYUWA,* so babbar cuta ce ga rayuwa, lallai zuciyata ta harbu da ciwo me azabtar da ruhi, al'amuran so suna da wuya, rabuwarsa kuwa mutuwa a tare._

Sake karantawa tayi a fili, sannan tai murmushi tana k'ara duba takardar, ga dukkan alamu kalaman ciki sun yi mata dad'i, d'agowa tayi tare da d'an duddubawa ko zata ga wanda ya ajiye mata sak'on amma bata ga kowa ba, hakan yasa ta d'auki kwalin, wasik'ar kuma na rik'e a hannunta ta koma cikin gida.

*Washe gari*

Tafe suke Amira tana tsakiyar abokanta da k'awayenta, tana ta maimaita kalaman da aka rubuta mata jiya cikin wasik'a, sai Suhaima ta kalleta tace " wai ke ina kika ji wad'annan kalaman kike ta faman maimaitawa?" nan ta basu labarin duk abinda ya faru, sai Sadeeq yace " gaskiya wannan ko wanene na musamman ne," Amira tace " Sadeeq shiyasa nake sonka tun kafin na furta abunda ke zuciyata kake fahimtar sa ka rigani furtawa, kamar kasan abinda nake shirin fad'i kenan," suna cikin magana suka ji ana fad'in wad'anan kalmomin cikin ajinsu amma da wak'a ake furtasu, da saurin su suka nufi ajin Amira ce kan gaba domin ta k'osa ta gane waye yai mata wasik'ar, se dai suna shiga suka tarar da mazan ajin sunfi goma, kuma dukkan su kalaman suke maimaitawa cikin wak'ar, farko Amir ne ta tarar yana rerawa yana fad'in.

_"SO MAHAD'I NE NA RAYUWA,_ ganin shi ke rerawa har ta fara murmushi saboda dama zuciyarta shi take zargi sai kawai ta ji

Abdul shima ya d'auka yace " _so babbar cuta ce ga rayuwa, lallai zuciyata ta harbu da ciwo me azabtar da ruhi,_

Sadeeq wanda suka shigo tare da Amira shima ya je kusa da su Amir ya zauna, ya d'ora da fad'in _"al'amuran so suna da wuya, rabuwar sa kuwa mutuwa a tare._"

Gaba d'aya duk sun raba mata hankali ta kasa tantance wanda yake da mallakin kalmomin, ta rasa ina dukkansu suka sami wad'annan kalaman suka ji shi, dan tasan cikin abokanta na skul d'in Sadeeq ne a tare da su lokacin da take fad'a, sai Sani, sauran kuma k'awayenta ne mata, babu Abdul da Amir, ta juya zata fita kenan ganin bata da amsar tambayoyin da take wa zuciyarta, tana kallon allon ajin taga an rubuta kalaman da suke ta maimaitawa, sai a lokacin ta gano wato duk a nan suka gani kenan suke maimaitawa, to waye ya rubuta?

Muje zuwa

*🅱K CE😘💋*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘

RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (🅱K)*
```(Autar marubuta)```

SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
_(Mamie)_

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```{Gidan zaman lafiya da amana insha Allah}```

_*FAUZIYYA AMMANI* zama tare da ke alkhairi ne, kuma babbar nasara ce, samun k'awa kuma 'yar uwa ta gari irinki abun alfahari ne, ina rok'on Allah dare da rana Allah ya faranta miki, ina sonki, iya wuya kuma ana tare😍😘💋._

_*TAWAN* ina rok'on mahaliccinmu Allah ya yaye miki dukkan damuwarki, ya bayyanar da farin ciki da walwala a gareki, ya k'ara miki lafiya mai d'orewa._

_dan girman Allah muna cigiyar *BAHAGON TUNANI* daga farko zuwa inda aka tsaya,👏👏👏👏👏😭😭😭😭😭 duk wanda yake da shi ya hana ni *wuta bal bal*😡😏_

PAGE 10 to 15

Yau ta kama Asabar ba makaranta, Amira ce kwance kan k'ayataccen gadonta tana karatu domin gaskiya yarinyar akwai k'ok'ari, sam bata wasa da karatun ta.

k'arar message ne ya shigo cikin wayarta, ta d'auki wayar tare da dubawa, rubutu taga an yi kamar haka.

_Dan Allah Amira ki bud'e zuciyarki ki sakani a ciki, ki tausayawa rayuwata._

Tana gama karantawa tayi k'ok'arin bin lambar da aka turo sak'on da ita, amma tana kira akace a kashe take.

Tunani ta shiga yi wai wanene wannan yake turo mata irin wad'annan sak'onnin, amma koma wanene zan ganoshi kwanan nan da yardar Allah, ta d'auki littafinta ta ci gaba da karatunta.

Washe gari Lahadi kenan Amira ce ita da Sadeeq suke ta faman tsere, a filin wasanni da motsa jiki na makarantar, a yayin da Amir ke zaune kan kujera yana kallon su.

Sun dad'e suna zuba uban tsere da Sadeeq da Amira, Amira sai wuce Sadeeq take yi tana jin dad'i a ranta, can kamar ance ta d'aga kai ta hango Amir zaune babu wanda yake kallo sai ita, idonshi yana kanta ko k'yaftawa baya yi.

Kallon Sadeeq Amira tayi tace tana zuwa bari ta kira Amir ayi wasan tare dashi.
Chapter 2 · 0% Book details