← Book details So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 54

Sashe 17

So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dad ya zauna a d'aya daga cikin kujerun da suke falon nan, tare da zaunawa yana tunani gaskiya yarinyar nan ta fara canzawa, wani yaro ne wannan ta damu da lamuranshi haka, wayarshi ya d'auka ya kira d'aya daga cikin manyan security's d'in da ke kula da ita a ko ina musamman idan zata je makaranta, bayan yazo ya kalle shi yace " wane yaro ne Amira take min maganar shi kullum?" Securityn nan yace " ba d'an makarantar su bane, wani Almajiri ne a tsallaken bakin ti-tin unguwar nan da yake ta bayan gida, duk in zamu je makaranta tana tsayawa su gaisa sannan ta wuce, ai yarinyar akwai taimako da tausayi tun tana k'aramarta wall......." Dad ya katseshi cikin fushi me tsanani, yace " akwai taimako tabbas amma gashi nan ai ya jawo ta fara tunanin d'aukar min kud'i ba tare da ta tambayeni ba, zan canza mata makaranta kuma daga yau bana so ku sake barinta ta kula wannan yaron.

Yau Litinin da zumud'inta ta shirya tare da zarar kud'i cikin na break d'inta da d'aukar jaka ta fito, Dad d'inta ya kalleta yace " ai ba zaki cigaba da zuwa wannan makarantar ba, na canza miki makaranta Daughter na samo miki wadda tafi wannan kyau da tsada," an gama komai, ga ma uniform d'in nan zo kisa in kaiki da kaina," jiki a sanyaye ta k'arasa wajen Mahaifin nata ya cire mata na jikinta tare da saka mata na sabuwar makarantar da aka canza mata, yana lura da yanayin ta ya kalleta yai mata murmishi sannan yace " nasan me kike tunani, yaron nan kike tunani yau bazaki had'u dashi ba ko, to zamu biya ku gaisa sannan mu wuce makarantar," ai kuwa nan da nan ta saki ranta sai zubo mishi surutu ma take," Dad kaima kaje ka ganshi ko, ka tausaya mishi ko, yana ban tausayi Dad kuma inaso ka sashi makaranta kuma ya dawo gidanmu mu cigaba da zama tare," shi dai banda to da eh baya ce mata komai, bayan ta shirya suka fito security's suka taho da gudu aka bud'e musu mota suka shiga suka fita da motoci masu yawa kamar shugaban k'asa ne ya fito.

Suna k'arasowa kuwa suka ganshi yana zaune a wajen da ya saba zama, ga dukkanin alamu shima ita yake jira domin sai waige waige kawai yake yi, suna k'arasowa wajen shi Ameeru ya taso da sauri ta kalle shi ya canza kaya yai kyau, tace " kayi kyau sosai," Ameeru yai murmushi sannan yace "nagode," ya mik'a mata wani abu a cikin leda yace "dama ke naketa jira ki k'araso kin gani abubuwan da na siya miki," wani agogon roba ne ba ma na gasken nan ba irin wanda yara ke siya su d'aura, sannan ya ciro tabarau shima kalar agogon ya bata, ya sake ciro wani zobe k'ato da warwaro ya bata se dai zoben da tasa yai mata yawa, amma duk da haka tace tana so zata aje har ta girma sannan ta saka, duk da kasancewarta 'yar hamshak'in me kud'i amma haka taita murna akan kayanda dukkansu bazasu siya ribom d'in kanta guda d'aya ba, yanda suke murna hatta Mahaifin ta sai da yai mamaki, sai bayan sun gama murnarsu sannan ta nuna mishi Dad d'inta ya k'arasa kusa da shi ya durk'usa ya gaishe shi, Dad ya kalli wasu daga cikin security's d'in wajen yace su d'auke Ameeru daga nan baya so ya sake ganinshi a wajen nan, nan da nan suka sab'a shi a kafad'a yana zillewa yana kuka, itama Amira na k'wala mishi kira tana kuka, haka Dad d'inta ya jata ya turata cikin mota suka tafi makaranta, su kuma sauran suka tafi nisanta Ameeru da kusa da gidan su Amira.

Dad d'in Amira ya kalleta yace " ko kukan jini zaki yi sedai kiyi, karatu nakeso inga kin zage kinyi kafin ki fara tunanin taimakawa wasu ba shirme da shiririta ba.

Kuka take sosai kamar me har suka k'araso makarantar, ya yi magana da malaman wajen kan kar su rik'a barin Amira tana fitowa har sai an tashi.

Daga wannan ranar bata sake saka Ameeru a idanun ta ba, bata san kuma a wane hali yake ciki ba.

Kuma daga wannan lokacin ta daina walwalarta kamar yanda take yi ada, in ta dawo makaranta tana shigewa d'aki bata k'ara fitowa, haka zata tasa kayan da ya bata taita kuka, duk ta rame bata wani ko cin abincin kirki.

Bayan kwana biyu Dad ne da matar shi da Uncle shima da matarshi suna hira sai matar Dad tace " gaskiya halin da Amira take ciki kwanan nan ya fara bani tsoro, bata cin abinci duk ta rame kullum cikin kuka ta dena walwala, koda yaushe tana d'aki," Dad yace taje ta taho da ita, ta tashi ta tafi, tana zuwa d'akin ta tarar da jikinta yai zafi sai rawar sanyi take yi, hakan yasa ta dawo da sauri ta fad'awa Dad d'inta halinda take ciki, hakan yasa suka garzaya aka d'auketa sai asibiti, a asibitin ne Uncle ya kalli Yayan nashi yace " Yaya kasan yanda shak'uwa take tsakanin yaro da yaro, in kace zaka rabasu ta haka tunda sun saba ta rik'a shiga cikin irin wannan halin kenan, kaima ji yanda duk ka rud'e kafi kowa son yarinyar nan in wani abu ya sameta sai ka fimu shiga cikin tashin hankali, saboda haka tunda dama ta rok'i ka taimaka mishi to ko bazaka kawo shi cikin gidan nan ba be kamata ka rabasu ba sai kasa a kaishi koda gidan marayu ne, kuma kasa a sakashi a makarantar su kaga ka samarwa Amira da farin ciki kan taimakon da takeso taga kayi, kaima kuma hankalina zai fi kwanciya akan irin halinda take ciki a yanzu."

Suna cikin maganar ne sai ga kiran shugaban makarantar su Amira tana fad'a mishi cewa sam Amira bata maida hankali kan karatunta, banda ma tunani da kuka babu abinda take yi, ya kamata su binciketa kan abinda ke damunta.

Jin hakan yasa jikin Dad d'in Amira ya k'ara yin sanyi, babu abinda yafi k'auna sama da yaga 'yar shi ta maida hankali tai karatu ta zama wata abu a duniya ta d'aukaka fiye dashi ma, Uncle ya kalle shi yace " Yaya lafiya meyafaru?" Dad ya fad'a mishi duk abinda aka kira aka fad'a mishi yanzu, Uncle yace "to kaga irin ta ko, yara ba'a rabasu ta k'arfi da yaji in dai suka shak'u, ta dabara ake yi musu yaya, yanzu ina dad'i ace duk k'ok'arin da Amira keda shi ada ace yanzu babu shi, gaskiya kai tunani akai yaya kuma abinda Amira keso kayi abu ne me kyau fa wanda in kayi lada zaka samu tunda kaga ta fad'a mana labarinshi tun farkon had'uwarsu," Dad yace "shikenan zan yi amfani da shawararka Adam."

Bayan kwana biyu Amira ta gyagije Dad d'inta yai mata Albishir zai kai Ameeru gidan marayu kuma zai saka shi a makarantar su kamar yanda ta nema, tun daga lokacin farin ciki da walwalar Amira suka dawo, sedai abinda yafi damunta da d'aga hankalinta shine ina za'a ganshi, domin an dudduba ko ina da ake tunanin za'a sameshi ba'a ganshi ba, kullum sai sun fita nemanshi amma basa ganinshi, kamar wasa Amira tace a duba wajen da yake zama a wautarta wai tasan zai dawo ya jirata.

Ana dubawa wajen kuwa suka tarar dashi zaune ya kod'e yai bak'i ya rame yana ta kare ranar da take ta kashe mishi ido, tana fitowa daga cikin mota ta kwala mishi kira, yana waigowa ya hangota da gudu ta taho shima ya tashi da gudu suka rungume juna suna kuka, Ameeru cikin kuka yace " tunda kika tafi na dena samun abinci kalli yanda na rame, kud'in da kika bani wannan mugun ya k'wace, dan Allah karki sake tafiya ki barni," hatta Mahaifin nata da sauran tawagar sai da tausayin Ameeru ya saka su hawaye, d'an k'aramin yaro d'an shekara goma amma Sam be san jin dad'in rayuwa ba, Amira ta kalle shi tace "bazan sake tafiya ba, yau ma zamu tafi dakai za'a saka a makarantar mu, za'a kaika gidan marayu kusa da gidanmu nan zaka cigaba da zama muna tafiya makaranta tare."

Dad yace " kuzo mu tafi to sai kuyi hirar a hanya, cikin mota ma suka karad'e su da surutu, Ameeru yace kullum sai na tuno dake, kefa?" Amira tace nima haka ta nuna mishi hannunta tace kaga ma abubuwan da ka siyamun nasa," Ameeru yace "dagaske makarantarku za'a kaini, kuma zamu rink'a had'uwa dake har muna yin wasa?" Amira tace "eh mana," duk hirarsu Dad da uncle suna ji, zuciayar Dad ce ke sak'a mishi cewa tabbas ko yanzu yasan Amira bazata maida hankali ba kan karatunta, dole ya d'auki matakin da zai nisanta su da juna ko ba yanzu ba, cikin hikima ta yanda ba zata gane komai ba kuma ta yanda dole zata hak'ura dashi, har suka k'arasa gida tunanin da yake ta yi cikin ranshi kenan, tabbas yana son farin cikin 'yarshi amma tabbas baya son kasancewarta da yaron nan.

Muje zuwa

*🅱K CE😘💋*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘

RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (🅱K)*
```(Autar marubuta)```

SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
```(Mamie) ```

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah) ```🤜🤛

*Ina mik'a ta'aziyyata ga HAUWA JAMIL, na d'an'uwa da muka rasa, Allah ya ji kansa ya kyautata makwancinsa, Allah ya haskaka kabarinsa, ya yafe kurakurensa, Allah yasa mutuwar ta zamto hutu a gareshi yasa aljanna ce makomarsa, Allah ya bamu sa'an tarar dasu, ya k'ara muku hakurin jure rashi.👏👏👏👏👏*

PAGE 75 to 80

Ameeru yai kwana biyu a gidan su Amira hakan ya k'ara musu shak'uwa sosai, sannan aka d'aukeshi aka kaishi gidan marayun da yake kusa da gidan su Amira, bayan sun gama da nan aka kaishi makarantar su Amira aka gama mishi komai.

Tun daga wannan lokacin tare suke zuwa makaranta, idan Ameeru ya shirya sai ya taho gidan su Amira a d'auke su gaba d'aya a kaisu.
Chapter 17 · 0% Book details