Sashe 15
So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dad yai murmushi sannan yace "tun ranar da Amir ya shigo gidan nan nake lura dashi, kuma nasa dukkanin security's d'in gidan nan suna lura da al'amuransu, Amir yaro ne me yawan ibada kamar Amira, baya wasa da sallah, sannan kai da kanka saida ka yabi halaye da d'abi'un yaron, bama kai kad'ai ba, sa'annan tun da Amira tazo halayenta kyawawa babu wanda suka canza sedai ma k'aruwa da sukai da ace munga canji daga halayyarta to daga lokacin zamu fara tsaurara bincikenmu da d'ora zargin canzawarta a kan Amir amma bamu ga wani canji ba, sedai kawai rashin sakin jiki da ta nuna kanmu wannan karon shima nasan saboda abokan karatu ne amma daga baya ta warware, wad'annan abubuwan ne suka tabbatar min da cewa lallai halinsu ne yazo d'aya dashi, sannan a koda yaushe rashin yiwa yaranmu kyakkyawan zato akan haka shi ke sawa su fad'a ga halaka, ni dai tunda ba soyayya suke ba to Alhamdulillah, kuma zansa security's suje a b'oye su rik'a bincika min komai game da su dan zuciyata bata gama gasgata bayanin da Amira tai min a kanshi ba, kuma binshi da nace tayi na gwadata ne in ga yanayinta, in har na gano sab'anin abunda Amira ta fad'a min hmmmmm," bai sake cewa komai ba ya juya ya shige ciki suma suka mara mishi baya.
Basu d'auki wani lokaci me tsawo ba suka k'araso tasha, kuma ba tare da wani b'ata lokaci ba jirgin su ya d'auki hanya sai Kano ta dabo tumbin giwa yaro ko dame kazo an fika.
K'arfe d'aya dai-dai suka iso Kano, kai tsaye gidan Amira suka wuce, da yake ita tana da 'yan aiki a gidanta kuma ta sanar da su cewa yau zata dawo su gyara mata ko ina, dan dama tai niyya da Amir ya taho ko basu dawo tare ba zata biyoshi a ranar, Amira ta kira Dad da Mum da Uncle duk ta shaida musu ta dawo.
Wanka suka yi, sannan suka canza kaya sukai sallah, aka kawo musu irin abinci wanda Amir yafi so ta bada umurnin a girka suka ci abinci sannan Amir yace ta d'auko mishi jakarshi zai tafi gida ya d'an kwanta anjima zai dawo.
Amira tace wallahi bazata bashi ba sai ta wanke mishi kayan da ya cire yau in yaso anjima in ya dawo sai ya tafi dasu, ba yanda bai yi da ita ba akan ta barshi amma ta k'i ba yanda ya iya saboda yaga ta fara b'ata rai dole ya hak'ura, yai mata sallama ta tashi ta rakoshi ya shiga cikin mota ya tayar tana d'aga mishi hannu shima yana d'aga mata har ya fice.
Amir yana komawa gida ya rage kayan jikinshi daga shi sai singileti da gajeran wando iya guiwa sannan ya kwanta sai bacci.
Amira kuwa tana komawa cikin d'aki ta jawo jakar Amir ta fara fito da kayan ciki tana ware wankakku tana cire masu datti zata wanke mishi dan tace da kanta zata wanke mishi kaya, saida ta fito dasu duka sannan ta hango wata takarda da hotuna a zif d'in jakar ta ciki, wasik'ar ta fara cirowa tana bud'ewa taga an yi rubutu da manyan harafi an rubuta *SO MAHA'DIN RAYUWA, SO TUN NA YARINTA HAR GIRMA, LALLAI K'AUNA BATA TAB'A GOGEWA.*
Take zuciyar mata ta fara hasssala kishi ya motsa, rai ya b'aci, cikin sauri ta maida wasik'ar tare da zaro hotunan tana dubawa d'aya bayan d'aya.
Hoton farko da ta fara gani yasa ta zazzaro idanu tare da mik'ewa tsaye rik'e da hotunan cikin firgici, hoton ta ne tana k'arama.
K'ara kallon hoton ta yi, duk da haka bata yarda ba, cikin sauri ta jawo jakarta ta shiga neman hotunanta aikuwa nan take taci karo dasu, wani hoto ta jawo tana kallo iri d'aya sak da na jakar Amir, bakinta na rawa tana hawaye take furta sunanshi "Ameeru," mayar da hoton da ta ciro cikin dakarta ta yi ciki, sannan ta cigaba da kallon hotunan, hotonta ne da tana k'arama, sai hotonshi shima yana k'arami, sai hotunan su da suka d'auka da shi da ita, da kuma wanda suka d'auka harda sister d'inta, ta kalli hotunan nan sau ba adadi kamar yau ne rana ta farko da ta fara ganin su, hawaye na jik'a hotunan, ajiye hotunan tayi gefe, kuka take sosai sannan ta jawo wayarta ta lalibo number d'in Amir ta doka mishi kira.
Amir wanda ke kwance a baje yana bacci yaji wayarshi na k'ara, jin k'arar ringing d'in da Amira ce kad'ai mallakinsa yasa shi tashi tare da jawo wayar ya danna tare da karawa a kunne yace " hello Amira nah," Amira tace " kazo yanzu ina son ganinka," daga fad'in haka ta katse wayar yanayin yanda Amir yaji muryar Amira ya tabbatar da ba lafiya domin kuka yaji tana yi, tashi ya yi cikin sauri duk ya rud'e ya zari makullin motarsa sai gidan Amira, yama manta sam da a yaya yake ya manta daga shi sai singileti da gajeran wando iya guiwa, tuk'i yake me matuk'ar gudu, yana cikin gudun ne Insp Yahya ya k'yalla idanu yaga motar Amir da kuma yanayin da yake ciki da office zai je, amma sai ya fasa ya karya kan motar shi ya biyo bayan Amir shima cikin sauri.
_shin menene a b'oye kuma bayan wannan kisan da yake a b'oye wanda har yanzu bamu san makashin ko makashiyatun da suka aikata ba sai ga wani kuma abu daban ya b'ullo kai, wai nifa kaina ya kulle meke shirin faruwa ne kuma?_
Ku biyoni muje🏃♀
*🅱K CE😘💋*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (🅱K)*
```(Autar marubuta)```
SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
```(Mamie) ```
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah) ```🤜🤛
*BABBAN DACE DA NASARA A SO SHINE KASO A SOKA*
*MY HEENAT Allah ya kara miki sauki, ya d'orar miki da lafiya d'orarriya*
PAGE 65 to 70
Gudu kawai Amir yake amma gani yake kamar yau motar bata sauri, a yayin da zuciyarsa ke ta addabarsa da tambayoyi a kan yanzu-yanzu fa ya baro wajen Amira ba dad'ewa, to menene ya sameta ta shiga wannan halin cikin lokaci k'ank'ani.
A bayan shi kuwa Insp Yahya ne ya dage yake ta binsa da gudu saboda baya so Amir ya b'ace masa.
Cikin k'ankanin lokaci ya iso k'ofar gidan inda yake ganin kamar awanni ya yi yana tafiya, yana faka motar ya fito da sauri ya shiga cikin gidan, tsaye ya sameta a falo tana kai kawo shigowarshi ne ya dakatar da ita daga sintirin da take ta faman yi, ta k'araso gabanshi tare da kallon shi ta cakumo rigarshi da hannu d'aya tare da nuna mishi hoton ta da ta gani cikin jakarshi tana fad'in " ina ka san wannan, kuma wa ya baka hotunan nan?"
Amir ya kalli hotunan sannan ya sunkuyar da kai, a yau yasan duk wani b'oyo da yake yi ya k'are, watso mishi sauran hotunan ta yi jikin shi tare da jeho mishi tambayoyi kan a ina ya same su, shi kam Amir baida bakin magana ya kasa cewa komai, komawa da baya Amira ta yi tare da zaman 'yan bori a tsakiyar falon ta sake kai dubanta gareshi tace " shirunka ya tabbatar min da cewa kaine Ameeru na wanda muka taso tun muna yara, meyasa zakai min haka, meyasa zaka b'oye kanka gareni Ameeru why?" tana kai nan a maganganun ta sai ta sake fashewa da kuka.
Amir ne ya k'arasa kusa da ita tare da tsugunnawa shima a gefenta yace " Amira dan Allah ki saurareni kiji, ke kanki saida ce akan irin k'aunar da nake miki tun muna yara wato abinda ya faru har yasa na b'oye miki kaina shine:"
TUSHEN LABARIN
Ahmad Tukur mutum ne wanda aka dama dashi a baya kuma ake damawa dashi a yanzu, a tak'aice dai yana d'aya daga cikin hamshak'an masu kud'in garin Abuja.
Ahmad Tukur matashi ne wanda duka bai wuce shekaru talatin da biyar ba amma mutum ne nagari me kuma kishin k'asarsa, hakan ne ma yasa yake nasara kan aikinsa, se dai Ahmad yanada zafi da tsattsauran ra'ayi, amma in kabi yanda yake so zaku zauna lafiya dashi.
Yana da mata d'aya da 'yar su guda d'aya tak me suna Amira
Suna zaune ne a babban gida kuma k'ayatacce wanda yake tare da d'an uwansa mai suna Uncle Adamu wanda yake da shekara talatin shima yana da mata wadda itama take da 'ya guda d'aya me suna Rukayyat kuma sa'ar Amira ce kasancewar rana d'aya aka yi bikin su kuma tsakanin haihuwar su yaran sati guda ne kacal a tsakani.
Uncle Adamu shi mutum ne me sauk'in kai ba kamar d'an uwansa ba, Amira da Rukayyat shekarar su takwas amma wayonsu da zaro zance tamkar na 'yan shekara goma sha musamman ma Amira, akwai surutu amma kuma akwai tausayi.
A kusa da gidan su Amira akwai wani gidan marayu, koda yaushe da ita mahaifinta ke zuwa yana bayar da taimako da gudummawoyi, kuma ta nan hanyar makarantar su Amira take, kullum sai sun wuce in zasu tafi haka ma in zasu dawo.
Amira 'yar gata ce sosai musamman kasancewar ta 'ya d'aya tilo, gata kam na duniya tana kan shansa, mahaifin Amira yana mutuwar son Amira yana kuma gatanta ta tun tana yarinyarta babu abinda zata nema ko ta nuna wanda baza ai mata shi ba komai wahalar sa ko tsadarsa.