Sashe 44
So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Anisa ta numfasa sannan tace "wallahi da farko nai tunanin gamo nayi ko kuma fatalwarka ce, saboda Amira tace min kayi hatsari ance ka mutu amma ba'a ga gawarka ba, kuma ita tasan ba zakai mata haka ba ka mutu ka barta bayan ka tabbatar mata cewa tare zaku rayu," Amir kuka yake sosai saboda tsabar tausayin Amira da yaji cikin ransa, saida ya yi mai isarsa Anisa na kallonsa itama tana jin tausayin rayuwar wad'annan masoya, musamman ma shi halin da zai shiga yanzu idan yaji abinda zata fad'a mishi game da mutumin da yake tambayarta a kanshi, Amir ya share gawayenshi da suka yi ja kuma suka kumbura saboda kuka, sannan ya kalleta yace "shi kuma wanda na gansu a tare fa?" Anisa ta fara inda-inda, Amir yace "ki fad'a min mana," Anisa tace "eh um wanda ka gansu tare mijinta ne, amma harta shi mijin nata silarka ta aureshi."
Nan da nan idanun Amir suka 'kara jajawur saboda tsabar kishi, hannunshi ya d'aga ya buga akan wani window na glass nan da nan glass d'in ya fashe, hannunsa ya fara fitar da jini sakamakon raunin da yaji, matsawa yayi jikin ginin wajen yaita had'a kanshi da bango, nan da nan goshinsa da kan shima ya fashe ya fara wanke fuskarsa da jini.
Juyowa yayi ya kalleta a hargitse, cikin matsanancin tashin hankali yace "na rantse da mahaliccina babu wanda zai rayu da matata sai ni kad'ai," yana gama fad'in hala yaji jiri ya fara d'ibarsa alamun jikinsa naso ya rikice mishi, jirin ne ya kwashe shi ya fad'i k'asa, Amira kuwa duk ta rud'e ta rasa yanda zata yi da shi, da yake masu tsaronshi a can bakin 'kofar makarantar yake cewa su tsaya, baya bari su shigo ciki, wayarsa ya ciro ya lalibo lambar d'aya daga cikin masu tsaron nashi ya mi'kawa Anisan yace ta kira tace musu Amir na kira, cikin 'kank'anin lokaci sai gasu da gudunsu sun 'karaso, Amir cikin wahalallaiyar murya yana numfashi sama-sama yana dafe da 'kirjinsa yace "ku kaini asibiti, ku taho da waccan yarinyar, kuma karku fad'awa su Dad komai a kaina, duk wanda ya fad'a mishi a bakin aikinsa," cikin sauri suka d'aukeshi tare da tasa 'keyar Anisa suka tafi tare da ita.
*BAYAN AWA 'DAYA*
An duba Amir an gama yi mishi komai sedai an d'an bashi gado ya huta kafin su tafi.
Amir yana daga kwance ya kalli Anisa wadda take cike da tsoro da mamaki har yanzu, yace "Anisa naji kince silata tai aure, meyasa kika fad'i haka?" Anisa tace "eh hakane ita ta bani labari, mahaifinta ne ya dameta ta fito da mijin aure ko ya bata wanda yai niyya, shine ta yarda ta auri Nura bisa sharad'i, sunyi aure ne akan yarjejeniyar cewa idan ka dawo gareta zai saketa ta koma wajenka, amma ita sam batama da niyyar yin auren haka taso cigaba da zama, tirsasawar mahaifinta yasa ma har ta amince tai auren," Amir yace "to Anisa ina neman alfarma daga gareki, dan Allah karki fad'awa Amira komai game da ni, karma ki nuna mata kin ganni, ni nasan yanda zanyi Amira mu had'u in ganta ta ganni kuma har ta dawo wajena, abu na biyu shine ina neman alfarma wajenki ki taimaka ki fad'a min sunan mijinta kuma ki bani lambar wayarki, in kikai min haka kin gama min komai.
Anisa tace "insha Allah ba abinda Amira zata ji daga gareni, sannan ta ciro biro ta rubuta mishi sunan Nura harda inda yake aiki da adreshin gidan aurensu da kuma lambar wayarta da ya tambaya, Amir ya karb'a ya duba, yaji dad'i sosai, yai mata godiya, sannan ya bata kyautar dubu d'ari, kuma ya bada umurnin d'aya daga cikin masu tsaronta ya kaita har gidansu, suka yi sallama ta tafi.
Sai a yanzu hankalin Amir ya kwanta harda murmushi, domin shi yasan Amira ta dawo gareshi ta gama insha Allah, dama so yake ya tabbatar amanarshi taci ko ya abin yake kuma ya tabbatar.
Amir ya sake yin murmushi sannan yace "Nura zan bi da kai ta lalama, in kuma har ka k'i to zan d'auki matakin gaggawa a kanka, ya sake yin shiru, can kuma sai ya sake cewa Allah sarki Amira na," ko me ya tuno oho Allah kad'ai ya sani sai kuma shi da abun ya shafa.
Muje zuwa
*🅱K CE😘💋*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (🅱K)*
```(Autar marubuta) ```
SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
(Mamie)
*RUKAYYA, TA CIKIN BK GROUP,*
&
*AUNTY HAUWA TA CIKIN MAHAKURCI GROUP*
*WANNAN PAGE 'DIN NAKU NE NA BAKU SHI KYAUTA KUYI YANDA KUKA SO DASHI BABU MAI CE MUKU DAN ME, KUMA INA GODIYA DA 'KAUNARKU GARENI, ALLAH YA BARMU TARE YA K'ARA MUKU SONA😂🙏😍😘💋*
*MUMMY'S FRIEND*
(Tawan)
*Allah ya d'orar miki da lafiya d'orarra, ya yaye miki dukkanin damuwarki.*
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah) ```🤜🤛
PAGE 185 to 190
Bayan kwana biyu Amir ya samu lafiya sosai ya warke garas, daga lokacin kuma ya fara tunanin abinda ya kamata ya yi domin ceto soyayyarshi da take 'ko'karin tarwatsewa.
Yau ta kama juma'atu babbar rana, Amir ne keta faman shiri da sassafe yana 'ko'karin fita, Umma ce ta fito daga d'aki tana kallon Amir dake shirin fita ko karyawa be yi ba, tace "yaron kirki sai ina haka da sassafe? "
Amir ya d'ago ya kalli mahaifiyar tasa yana murmushi yace "wallahi Umma cikin makaranta zan shiga," Umma tai murmushi sannan tace to Allah ya dawo da kai lafiya, Allah bada sa'a. "
Amir yace "ameen, " Umma, ya rungume mahaifiyar tashi sannan ya fice daga gidan cikin sauri.
Amir na fitowa masu tsaron shi suka taso a guje suka bud'e mishi mota, sannan suma suka shisshiga tasu, mota wajen bakwai uku a gaba uku a baya ta Amir tana tsakiya, a haka suke fita duk inda zasu.
Makaranta suka shiga kai tsaye, suna shiga suka faka motocinsu, securityn duk suka fito suka zagaye motar Amir kasancewar har yanzu be fito daga cikin motar ba.
Amir yace wa masu tsaron shi su koma zai nemesu akwai abinda yake so yayi, babban cikinsu ne yace "oga idan muka koma gida yanzu mahaifinka ya dawo dole zai tambayemu ina kake, hakan zai iya jawo mana rasa aikinmu, kayi hak'uri dai ka barmu mu jiraka a bayan makaranta in baka so a ganka tare damu ne. "
Amir yai shiru yana nazarin maganar su, can sai ya d'ago ya kallesu yace "ok kuje bayan makarantar ku jirani, idan na gama abinda nakeyi zan nemeku a waya. "
Bayan tafiyarsu Amir ya sauya rigar jikinshi, sannan ya saka glass no respect, ya zauna zaman jiran 'karasowarsu Amira.
Amir na nan zaune sai ga motar su ta kutso ciki, k'urawa motar ido yayi har ta 'karaso kusa da tashi tai fakin, sannan Amira ta fito ranta a b'ace ta wuce abinta, Amir ya bita da idanu har ta b'acewa ganinshi, idanunsa na fitar da hawaye, tausayinta yake ji matu'ka duk ta rame kamar ba amarya ba.
Amir ya dawo da kallonsa ga Nura, bud'e motarshi Nura yayi ya fito sannan yazo gaban motar ya haye samanta ya zauna, Amir dai na kallonsa yaga ya ciro waya a cikin aljihunsa yai kira ya kara a kunnensa, bayan an d'aga yaji Nuran na cewa gaskiya Baba nifa na fara gajiya da halin yarinyar nan Amira, wallahi bnda taci sa'a ina sonta da kuma 'kudurinmu kanta da tuni nai maganinta, Baban yace "kar kai haka ka bari burinmu ya cika koma menene ka aiwatar daga baya babu me hanaka tunda matarka ce, Nura yace "ni mahaifinta ma ya kwafsamin Baba, so nayi ya d'orani kan dukiyarsa gabad'aya kaga cikin lokaci 'kan'kani zamu tara ma'kudan kud'i, nan dai mahaifinsa ya cigaba da rarrashinsa, bayan sun gama wayar ya kashe tare da maida wayarshi cikin aljihu, Amir na jin haka yai jim yana tunani kar dai akan Amira suke tattaunawa da mahaifinsa, amma koma menene zai gane nan bada dad'ewa ba, cikin sauri Amir ya fito daga cikin motarshi ya nufi Nura, da isarshi wajen yaiwa Nura sallama sannan ya bashi hannu suka gaisa, Amir ya tsaya kusa dashi tare da jingina da motar, sannan yace "Amir ya ciro taba a aljihunsa, abinda bai tab'a kwatantawa ba koda wasa, Amir ya kalli Nura yace "abokina ko kana da lighter? Nura ya d'ago cikin b'acin rai yace "banda ita wallahi, amma kaima da zaka ji shawara da ka daina shan tabar nan saboda tana cutarwa, zuciyar Amir tace ok baya sha kenan, Amir ya cire tabar nan daga bakinsa yace "kai dai bari kawai, matata ce silar jefani a wannan halin, babu wanda na tab'a yin wannan hirar dashi sai kai, kaima naga kamar duk matsalarmu d'aya ne shiyasa zan fad'a maka, dan ina hango tym d'inda matarka ta tafi rai a b'ace ko sallama batai maka ba, Amir ya cigaba da cewa ni tawa kullum fad'a da neman rigima, wallahi har tsoronta nake ji, ta maida ni kamar wani yaron da ta haifa ko bawan da ta siya da kud'inta, ko yanzu ma da na d'aukota daga gida zuwa nan makarantar tasu bala'i taita yimin har muka k'araso, sannan daga 'karshe da ta tashi tafiya abinda matarka tai maka nima shi tawa taimin harda kashedin saura in makara wajen zuwa d'aukota. "
Duk irin b'acin ran da Nura ke fama dashi sai da Amir ya sakashi yaita faman darawa sakamakon labarin nan da ya gama bashi yanzu.
Amir ya 'kura mishi idanu kamar wani dolo yace "ikon Allah ni ina baka labarin damuwata tare da nuna jimamina kai kuma kana yimin dariya." 🤔
Saida Nura yai dariyarsa mai isarshi sannan yace "yi ha'kuri abokina, wallahi dariya ka bani, haba ya zaka zauna mace taita juyaka haka, Amir yasha kunu irin shi yaji haushin dariyar da Nura yai mishi, sannan yace "dad'in abun ai matsalarmu d'aya, in ka gama yimin dariya sai kaiwa kanka. "
Nura yace "a'a wallahi matsalarmu ba iri d'aya bace, ka ganni nan, ni aure baya gabana ma sam da farko, saboda duk macen da naso ina samu da dukiyata in biya bu'katata daga 'karshe in sallamesu," Amir yai caraf yace "wallahi ka huta da wannan wahalar ta rayuwar aure."