Sashe 29
So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan shiru na wasu lokuta saboda nazartar takardun da aka mi'kawa Al'kali da yake yi, can sai Alk'ali ya d'ago ya kalli Amir, sannan ya maida kallon shi kan Amira yace "malama ki koma ki zauna har sai an kira ki," Amira tace " ranka ya dad'e zargin da ake wa Amir mu biyu ake zarga, shiyasa ma na biyo shi muka fito gabanka muka tsaya a tare."
Al'kali yace "duk da haka ki koma ki zauna sai an nemeki," Amira ta kalli Amir shima Amir ya kalleta idonta har ya ciko da 'kwalla, sai ya d'aga mata kai alamar taje ta zauna, Amira taje ta samu waje ta zauna.
Al'kali ya kalli Amir yace "malam Amir kaji irin tuhumar da ake yi maka na kashe Sadeeq, shin ka amince kai kayi kisan ko baka amince da hakan ba?
Amir yace " ba ni na kashe shi ba Allah gafarta malam, ni lokacin da aka yi kisan ma bana wajen, washe gari da na shigo ne naga gawarshi cikin school mutane sun kewayeta.
Al'kali ya d'an yi rubutu sannan ya d'ago yace a gabatar mishi da 'yan sandan da suka yi bincike kan case d'in.
Insp Yahya yazo gaban kotu ya tsaya, Al'kali yace yana son yaiwa kotu bayanin yanda suka gudanar da binciken su har suka tabbatar da Amir shi ya kashe Sadeeq.
Nan Insp Yahya ya fara kwakuso bayani tun daga kan soyayyar da Abdul da Sadeeq suke mata harma da Amir d'in, amma shi sai ya b'oye nashi saboda wani manufarsa da ya barwa kanshi sani a lokacin, sai daga baya yai amfani da damar da ya samu na fad'an da Abdul da Amir suka yi har da ikirarin kashe junansu, Insp ya cigaba da cewa " da wannan damar yai amfani ya kashe Sadeeq tare da barin shaidun da zasu sa a yarda cewa Abdul ne ya kashe Sadeeq, bayan faruwar haka sai na fara bincike kan Amir d'in da Amira, anan na gano ashe shima Amir d'in yana son Amira, amma be nuna mata ba sai da ya kawar da masoyanta Sadeeq da Abdul, sannan na jiyo da kunnena yana baiwa Amira labari cewa shine ya kashe Sadeeq saboda ita."
Al'kali ya rubuta bayanan da ya samu daga Insp Yahya, sannan yace wa Insp ya koma ya zauna, Al'kali ya kalli Amir yace "malam Amir kaji abinda Insp Yahya yace?" Amir yace "eh ya me shari'a," Al'kali yace "kana da ja ko babu?" Amir yace "eh ya me girma me shari'a ina da ja, domin ban tab'a kashe kowa ba."
Al'kali yace "wanene shaidanka?" Amir yace " Allah ne kad'ai shaida ta, sannan kuma ni banac cikin makarantar ranar da akai kisan, washe gari ne da na shigo makaranta na tarar da gawar, in kuma su sunada shaida akan haka to su gabatar, sannan ni da mamatan dukkaninsu muna da kyakkyawar alak'a ko musayar yawu be tab'a had'ani dasu ba."
Al'kali yayi rubuce-rubuce, sannan ya sake kiran Insp Yahya domin ya gabatar da shaidun da yake da su na tabbacin Amir yai kisan bayan wad'anda ya bayar, Insp Yahya ya kira wasu daga cikin student d'in makarantar guda uku su bada shaida, sedai dukkansu a bayanan su kaf sun tabbatar da cewa basu ga Amir ba a wannan daren, lokacin da Sadeeq ya shigo a buge Abdul ne ya biyo bayan shi ba Amir ba, bayan an sallame su sun koma sun zauna Alk'ali yace " Amir shima ya gabatar da shaidun sa wad'anda zasu tabbatar da baya nan ma aka yi kisan kuma be san ma da rasuwar ba sai washe gari da ya shigo makarantar domin d'aukar karatu.
kafin ma Amir ya bada amsa nan da nan gurin ya hargitse d'alibai sama da Ashirin suka d'aga hannayensu suna fad'in zasu bada shaida akan Amir besan komai ba hatta ma kisan, sai da ya shigo makarantar ya ga gawarshi, Allah sarki cikin masu d'aga hannu harda Amira jikinta har tsuma yake, Allah-Allah kawai take a kirata.
Al'kali ya buga guduma alamar kowa ya natsu yai shiru.
Bayan an natsu sai Al'kali yace " ya kamata ku gane nan kotu ne ba makaranta ba, dan haka kowa ya shiga taitayinsa har sai an kira mutum tukun, Al'kali ya cigaba da cewa amma idan na fahimta yawancinku kunsan duk abinda ke faruwa ko?" da 'karfi suka amsa da "eh" musamman Amira 'kararta tafi ta kowa harda mi'kewa tsaye sai da taga Al'kali ya kallo inda take tai sauri ta koma ta zauna, hakan da suka yi ya baiwa Al'kalin dariya wanda har saida ya murmusa, sannan ya jinjina farin jinin Amir gun mutane, ko be bincika ba hakan ya tabbatar mishi da yana da kyakkyawar ala'ka da mutane.
Alk'ali ya d'an yi rubutu, sannan ya d'ago yace " yanzu lokaci ya tafi, kuma akwai sauran cases a gaba, amma in Allah ya kaimu wani satin zamu dawo domin cigaba da sauraron wannan shari'ar."
Nan aka cigaba da gudanar da sauran k'ararrakin, ana gamawa kowa ya watse.
Aka fito da Amir da ankwa d'aure a hannunsa inda Amira ke bayanshi, su Insp suna biye da su, Amira ta kalli Amir shima ya kalleta suka kwashe da dariya, har aka saka su a bayan mota da wasu 'yan sandan, inda Insp ya shiga gaban motar shi da wani d'an sanda suka ja.
Suna cikin tafiya Amira ta sake yin dariya ta kalli inda Insp Yahya yake tace " Insp Yahya ya kaji shari'ar ta yau, kasan me? shari'ar yau tai dad'i, da alamu wani zai sha kunya, ta juya ga Amir tace Amir d'ina kaima kaji dad'in wasan yau a kotu ko?" Amir yace "sosai ma, wani 'kato zai sha kunya nan gaba kad'an," "Amira tace ai nasan dama nasara tana tare damu, ni fa wallahi saboda ina tare da kai har mantawa nake da wai muna cikin tashin hankali," suka kwashe da dariya, ya d'aga mata hannayenshi da ke cikin ankwa itama ta d'aga nata suka tafa, Insp ba bakin magana amma ya mugun hassala da maganganunsu, sai huci kawai yake, su kuwa cigaba da hirarsu suka yi yanda kasan ba abinda ke damunsu.
Muje zuwa
*🅱K CE😘💋*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (🅱K)*
```(Autar marubuta)```
SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
```(Mamien Bk)```
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```🤜🤛
*MADEENAT*
```(My Deenat)```
*Na gode sosai da kulawarki kan rashin lafiyata, Allah ya saka miki da mafificin alkhairinsa, Allah ya 'kara miki basira marubuciyar SAI NA KASHE MAHAIFIYATA, muna mugun jin dad'in novel d'innan naki a cigaba da antayo mana shi muna 'kwamushewa.😉😘*
*Babu wanda Allah yake nufinsa da alkhairi sai wanda ya sashi a hanyar addini, mu tashi, mu dage, musan addininmu, domin shine sanadin kasancewarmu cikin duniyar nan, Allah kasa mu dace.*
*AUNTY LIPSON*
(Maman Saleem)
*'Yar uwa ina ro'kon mahaliccina ya d'orar da lafiyarsa gareki👏😰😰😰😰😰*
PAGE 125 to 130
Bayan sun isa station d'in aka sake gar'kame su Amir da Amira a cikin cell, Insp Yahya ya d'aga waya ya kira Dad d'in Amira yai mishi bayanin duk abinda ke faruwa, dai yai shiru na wasu lokuta, daga 'karshe yace su jira tukun suga yanda 'karshen shari'ar zai kasance, amma kafin zagayowar ranar zai turo 'kwararren lauya.
Bayan sun kammala wayar sunyi sallama Dad ya fara kai kawo a 'kerarren 'kayataccen d'akin shi, tunani yake a ranshi me ya kamata yaiwa yaron nan yana nema ya rabashi da 'yarshi, yaro d'aya tak ya zame mishi matsala yana nema ya zauta shi, cikin b'acin rai ya kaiwa iska naushi, tunani ya cigaba da yi yasan yana da damar da zai iya yin komai a kanshi ba tare da an sake koda waiwayen labarinsa ba ma, amma in yace zai b'atar dashi to siyasar shi yake ji, saboda sabon zab'e ya kusa, kawai mafita shine ya bari tukun a gama shari'ar in basu yi nasara ba sai ya nemo wata mafita amma bazai tab'a bari ya yarda ta auri Amir ba, da haka ya tsayar da tunanin tare da cigaba da harkokin shi.
*BAYAN SATI 'DAYA*
Yau litinin, kamar kullum yau ma kotu cike take ma'kil da mutane, Al'kali ya d'an yi rubuce-rubuce, sannan ya d'ago tare da fad'in " ina fatan dai masu 'kara da wanda ake 'kara sun tanaji lauyoyin su?"
Wani ne ya tashi cikin isa da ta'kama, ya sha ba'ka'ken kaya irin na lauyoyi, ya d'an rissina sannan yace " sunana barista Kamal Ibrahim lauyan gwamnati, ni ne nake wakiltar b'angaren wanda ke 'kara wato b'angaren Sadeeq," bayan ya kammala jawabinsa ya koma ya zauna.
Sai Al'kali ya kalli Amir yace "malam Amir kai baka da lauya ne?" har Amir ya bud'e baki zai yi magana kenan sai suka jiyo maganar wata matashiyar kyakkyawar mace ta shigo cikin takunta na 'kasaita, itama sanye take cikin kayan lauyoyi wad'anda suka yi matu'kar yi mata kyau, shigowa take tana magana tana fad'in "ayi ha'kuri ranka ya dad'e nazo a makare cinkoson ababen hawa ya hanani 'karasowa da wuri," ta k'araso wajen da aka tanada domin zaman su ta tsaya a tsaye tare da rissinawa tace "sunana barista Yasmeen Ahmad Abubakar, ni lauya ce me zaman kanta nice lauyar da ke kare wanda ake 'kara, wato Amir" tana gama fad'in haka ta samu waje ta zauna tana dudduba abubuwa a takardun dake gabanta.
Amir yayi matu'kar mamakin jin abinda Baristan nan tace, saboda shi yasan be d'auki lauya ba, kuma ba wani wanda sukai maganar d'aukar lauya dashi, kallon gefen da Amira take yayi ya d'aga mata gira da d'an d'aga kai alamar tambayar itace ta kawota, sai Amira tai murmushi sannan ta d'aga mishi kai itama alamar eh itace.
Barista Kamal ne ya fara mi'kewa yace "ina son kotu ta bani damar yiwa Amir da Amira tambayoyi," Al'kali yace "an baka, ina Amira take ta fito," Amira ta fito ta tsaya ya kusa da Amira, suka kalli juna suka sakarwa junansu murmushi, ni kuwa nace ikon Allah har a kotun ma sai kun nuna ku masoya ne.🤔