← Book details So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 54

Sashe 13

So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna zuwa Insp Yahya ya kalli Amir yai murmushi sannan yace " malam Amir kenan, daga ina haka, ko daga gun mutuniyar kake?"

Amir yace "eh" a tak'aice.

Insp Yahya ya sake yin murmushi, sannan yace " a kwanakin baya kai da Amira ne kuke ta magana kan hujja hujja ko, to albishir nazo in yi maka nan da d'an wani lokaci zan gabatar da shedar da zata tabbatar da cewa daga Abdul har Sadeeq kashe su aka yi, kuma sai na gabatar da wanda ya kashe su duka," yana gama fad'in haka ya juya ya shige mota tare da sauran jami'an tsaron suka tayar sukai tafiyarsu.

Amir hankalin shi ya tashi matuk'a, tunani yake yi meyasa Insp zai rik'a danganta shi da kisan nan ne, haka nan dai ya ja motar shi ya k'arasa gida jiki duk a mace kuma cike da damuwa me d'auke da d'umbin tashin hankali.

Amira kuwa kuka take yi kamar ranta zai fita, duk idanunta sun kumbura, zuciyarta ce ke fad'in ashe haka masoya ke ji a duk lokacin da wani abu zai raba su, lallai ko menene mutum zai iya yi akan so musamman idan har yaga ana nema a rabashi da abinda yake k'auna, tun da suka shiga cikin jirgin Amira bata bar zubar da hawaye ba, har suka k'araso cikin garin Abuja Dad d'in nata ta kira ta sanar da shi sun iso, bata dad'e da sanar da shi ba sai ga motoci rututu an turo su d'auketa, nan da nan ta shiga suka ja suka tafi.

Amir kuwa yana k'arasawa gida wayarsa ya ciro yaga 10 missed call's d'in Amira, mamaki yake yi yanda aka yi sam be ji ringing d'in wayar ba, ya kira wayar tare da karawa a kunnensa.

A dai-dai lokacin da yake kira Amira sun k'araso gida an bud'e mata k'ofa zata fito daga cikin motar, 'yan uwanta da iyayenta duk gasu nan a tsaye harabar gidan sun fito tarbar Amira.

Ta sak'alo k'afafunta kenan zata fito daga motar kiran Amir ya shigo, ta d'aga cikin sauri tare da karawa a kunne tace " hello Amir d'ina wallahi nayi kewarka," Amir ya sauke sassanyar ajiyar zuciya sannan yace " Amira kema kinsan rashinki dole sai ya tab'a ni, bazan ma iya misalta miki adadin rad'ad'in da rashinki ya haifar a gareni ba, kin kai gida ko har yanzu kuna hanya?"

Amira tace " gani cikin gida yanzu muka k'araso ina ma cikin mota ko fitowa banyi ba naga kiranka, ya naji muryarka duk ta canza, kayi kuka ko, ba na hanaka yin kuka ba, kasan dole naji ba dad'i idan ina jinka a irin wannan yanayin ko, kodai in juyo in dawo ne nima jina nake kamar mara lafiya Amir ashe haka nisa da masoyi ke haifar da rad'ad'in jiki da na zuciya."

Amir ya katseta ta hanyar fad'in " ki daina fad'in maganar dawowa mana Amira kowa ya ganki yana murna kice kuma zaki juyo, tunda dai kin riga da kin kai lafiya to nagode wa Allah, mu yi hak'uri na d'an lokacin da zaki yi ki dawo, yanzu dai ki shiga gida ki huta Anjima zan sake kiranki," nan suka yi sallama ya ajiye wayar ya fad'a cikin bayi domin yin wanka, ita kuwa Amira tana fitowa daga cikin motar idanun 'yan gidan gaba d'aya yana kanta, ta k'ak'aro fara'a ta k'arasa wajensu, sister d'inta ta fara rungumeta suna murna, sai suka rungume juna da Dad d'inta, sannan yace mata " dawa kike ta waya ne haka my daughter?" Amira tace " Dad wata friend d'ita ce, ta saki Dad d'inta da sauri saboda sanin halinshi na tambayoyi zai iya sake jeho mata wata tambayar taje ta rungume Mum d'inta sannan ta je gaban Uncle kawunta wato mahaifin wadda za'ai bikinta shima ta rungume shi ya shafa kanta tare da sa mata albarka, sannan suka d'unguma dukkansu suka shiga ciki.

Wanka ta fara yi a k'erarren d'akin da yake mallakinta tamkar aljannar duniya, sannan ta shirya suka fito tare da sister d'inta, direct dining table suka wuce aka ci aka sha, daga nan suka dawo babban falo suka zauna ana ta hira, ita dai Amira ba wata walwala sosai banda eh ko a'a bata cewa komai, hankalinta yana wajen tunanin Amir, sisternta ce ta kalleta tace " wai Amira ya naga duk kin canza ne, ina lura dake fa ko abincin kirki baki ci ba," Dad dake jinsu shima yake kallon Amira yace " kin rigani magana ne nima abinda nake so in tambaya kenan, kamar daughter bata farin ciki da ganinmu. "

Amira zata yi magana kenan sai ga kiran Amir, tashi ta yi tace musu zata je ta d'an kwanta a d'aki, bata jira taji me zasu ce mata ba ta haye sama cikin sauri.

Amira ta d'aga kiran shi tare da karawa a kunne ta fad'a gado tace " kamar kasan kai nake tunani, Amir yai murmushi sannan yace "ai zuciyoyin mu had'e suke da juna," sun dad'e suna waya kiran sallah ne kad'ai ke dakatar da su daga jin muryar junansu.

Har aka kira sallar issha'i suka je suka yi sannan suka dawo suka cigaba da dosa wayarsu, suna cikin wayar ne sistern ta ta shigo tana fad'in yau ina kusa dake sister na a d'akin ki zan kwana," Amira ba don ranta yaso ba tai dariyar yak'e tace mata " to kar dai ki cikani da surutunki malama," sister tace " dan ma kin samu, daga yau ne ai gobe ke kad'ai zaki kwana ni ina tare da k'awayena."

Amir yana jinsu dan basu katse wayar ba, Amira tace mishi ya hau WhatsApp su cigaba da magana.

Nan da nan suka bud'e datan su, suka cigaba da magana a yayin da sister d'inta ta gaji da surutunta Amira bata kulata sai ta hak'ura ta k'yaleta har bacci ya kwasheta.

Su kuma suka cigaba da chat d'insu, Amira tace _"Amir d'ina gaskiya bazan iya cigaba da jure rashinka ba ko abinci fa na kasa ci, har 'yan gida sun gane akwai abinda ke damuna."_

AMIR _"To ko in zo ne?"_

AMIRA _"Amir Dad d'ina nake ji, murd'd'd'en mutum ne, baya so muna kula samari har sai mun kammala karatu, amma kazo tunda shagalin biki ake ba matsala na san yanda zan yi ba wanda zai gane komai."_

AMIR _" na shiga uku! ni yanzu ya zanyi ni da nake so na mallake ki kwanan nan yanzu in aka kasani fa, tunda kince da matsala zuwana to kiyi hak'uri ki bari har ki dawo."_

AMIRA _"gaskiya bazan iya cigaba da hak'urin jure rashinka ba, yini d'aya ma kenan har na rame, ka taho gobe ko kuma wallahi ni na dawo goben."_

AMIR _"to shikenan insha Allah goben ina hanya."_

AMIRA _"to shirya kayanka sai mu cigaba da waya tunda uwar surutu tai bacci, nafi so in cigaba da jin muryarka."_

Suka yi sallama na 'yan mintuna ya had'a kayanshi sannan ya kwanta yana kwanciya ya jawo waya zai kirata sai ga kiran Amiran ya shigo, yai murmushi ganin yanzu damuwarta a kanshi tana nema ma ta zarce tashi, ya d'aga kiran tare da kara wayar a kunne, haka suka kwana basu runtsa ba sai da asuba bayan sun yi sallah sannan ta barshi ya kwanta shima saboda kar bacci ya sace shi ya makara tahowa wajenta.

Washe gari wajen shida dai-dai Amir ya shirya, ya fito tare da kulle ko ina na gidan sannan yaje tasha ya hau mota suka d'auki hanya sai Abuja.

Duk bayan mintuna sai Amira ta kira taji suna dai-dai ina, bayan awanni da suka d'auka suna tafiya suka k'araso tashar Abuja, ya kira Amira tare da shaida mata ya k'araso gashi a tasha, zaune take ana mata lalle sai gani suka yi ta tashi zumbur tare da zuwa ta wanke lallen sannan tai hanyar d'akin Mum d'inta, Amarya na k'wala mata kira tana tambayar ina zata, ita kuwa fad'i take tana zuwa har ta shiga d'akin Mum d'in.

Key d'in motar Mum ta d'auka tana fad'in "Mum bari inje in dawo," bata jira taji me zata ce ba ta fice ta fad'a motar ta figa da gudu sai hanyar tashar Abuja.

Ko da isarta tasha ta hango shi, domin ma kusa da shi ta faka, ta saukar da glas d'in motar tare da yin hon, d'ago kanshi Amir ya yi suka yi ido hud'u da Amira, cikin sauri ya taso ya nufota, itama kasa jurewa tayi ta fito daga motar suka rungume juna suna hawayen farin ciki, kowannensu d'auke da murmushi a fuskar sa, ganin idanun mutane na kansu yasa suka shiga mota suka bar wajen sai hanyar gida.

Suna isowa Amira tai fakin d'in motar ta baya ba tare da ta shigo da ita cikin gidan ba, suka fito suka bi wata b'oyayyar hanya ta baya, suka bud'e wata k'ofa sukaita tafiya har Allah ya sada su da d'akin Amira ba tare da kowa ya gansu ba.

Suna shiga ta maida k'ofar ta rufe tare da sa makulli ta kulle ta ciki, suka zauna sunata hirar yaushe gamo, Amir yace " Amirana har kin rame," Amira tace " wallahi kuwa nesa da kai kamar yin nisa da rabi na jikina ne, kuma kaima ka rame amma baka kaini rama ba."

Dakatar da surutun ta yi ta hanyar mik'ewa tace mishi tana zuwa, ta fita taje ta d'auko musu abinci suka ci, suna ci suna hira.

Haka suka kasance a cikin gidan da dare ne kad'ai yake b'oyewa ya kwana a d'akinta tana k'asa yana saman gado, da rana kuwa shiga yake cikin 'yan biki ayi hidima da shi, amma yawanci ma sunfi tafiya bayan gidan su su zauna sui ta hira har abinci a nan suke ci komai a nan suke yi, aita nemanta in buk'atar hakan ta taso bata nan, se dai in sun dawo ta gilla musu k'arya, kullum a can suke wuni in sun tashi su bi ta k'ofar baya su shige d'aki, kuma Allah ya taimake su har yau babu wanda ya gane abinda ke faruwa.
Chapter 13 · 0% Book details