← Book details So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 54

Sashe 46

So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaban Amir ne ya fad'i, sam be so komai ya fito tun yanzu ba, Amir ya mayar da wayar gefe ya ajiye, sannan yace "mahaifinka ne ya kira yace kaje yana nemanka, wai ya samu labarin anga Amir a cikin garin nan kaje ku shirya abinda ya kamata a gaba."

Wani irin birki Nura yaja tare da kallon, Amir had'e da zazzaro ido, yace "meyasa wannan d'an iskan zai bayyana yanzu?" wayarsa ya d'auka ya kira Babanshi suka tattauna sannan ya tabbatar mishi da yana zuwa nan bada dad'ewa ba.

Bayan sun gama wayar ya tayar da motar suka cigaba da tafiya.

Amir sam baya son Nura ya gane gidansu balle har ya gane wanene shi, gashi yau ya d'aukoshi a motarsa dan yau cewa yai masu tsaronsa su juya da dukkanin motocin, dan haka suna zuwa dai-dai wani super market yace ya ajiyeshi a nan zai duba wani abokinshi a ciki.

Bayan Nura ya faka motar Amir ya fito, suka yi sallama yaja yai gaba a yayin da shi kuma Amir ya koma gefe ya samu wani benci dake kusa da 'kofar shiga super market d'in ya zauna, ya ciro wayarshi ya kira lambar da Amira ta bashi, ringing d'aya tayi Amira ta d'auka tare da karawa a kunne, sallama tayi da sassanyar muryar nan ta-ta me d'an karen dad'i, lumshe idanu Amir yayi sannan ya bud'esu, shima a hankali ya kira sunanta yace "Amira."

Amira cikin sauri ta mi'ke tsaye tace "Amir d'ina ina ka shiga har zuwa tsawon wannan lokacin, kasan halin da tunaninka ya jefa rayuwata a ciki kuwa? kowa yana ta cewa ka mutu amma ni nasan ba zakaimin haka ba, ba zaka mutu ka tafi ka barni ba," ta fashe da kuka, sannan ta cigaba da cewa "amma meyasa tsawon wannan lokacin ka tafi ka barni ba tare da ka nemeni ba?

Amir yace "haba Amira ta ina zan nemeki bayan mahaifinki ya dage sai ya rabamu ta 'karfi da yaji," nan ya kwashe duk abinda ya faru ya fad'a mata, Amira ta tayashi murnar ganin iyayensa da yayi, yai mata godiya sannan ya cigaba da fad'in "yanzu abinda yasa na kiraki shine in fad'a miki ki kwantar da hankalinki, zaki dawo wajena nan bada dad'ewa ba mu cigaba da zaman aure, amma yanzu idan nace zan bayyana gaban Dad inaso a dawo min da matana bazai yarda ba rigima za'ai ta tafkawa, shiyasa nafi so sai na tona duk wani asiri nasu tukun, na samowa Dad babbar hujja a kansu, abinda nakeso dake shine karki tab'a yarda dashi domin kuwa nafara gano manufar abinda yasa aka aureki, kiyi taka tsan-tsan dashi, kuma zamu ri'ka waya dake duk in baya nan," Amira tace "to shikenan," nan suka d'an tab'a hira daga 'karshe suka yi sallama.

B'angaren su Nura kuwa zaune suke shi da Baban shi suna magana akan Amir, Nura yace "waima to kai wa yace maka ya ganshi anya shi aka gani kuwa Baba?"

Baba yace "to ni na ganshi da idanuna kaine baka sanshi ba, baka tab'a ganinshi ba, amma ni na sanshi, mahaifin Amiran ya nuna min hotonshi lokacin da mukaje gidan da kai maganar aurenku, sai gashi yau na ganshi da idanuna sun wuce tare da wasu mutane masu ba'ka'ken kaya a mota, saboda haka yasa na kiraka mu nemi mafita."

Nura yace "in kuwa haka ne bayyanarsa a dai-dai wannan lokacin zata b'ata mana shiri, amma kar kaji komai Baba in dai ka yarda dani kabar komai a hannuna," da wannan maganar ta Nura suka kawo 'karshen maganar.

Bayan sati d'aya ko da iyayen Amir suka ga ya fara warwarewa damuwarshi tayi sau'ki sai suka shirya suka koma Abuja saboda harkokin Abbansa na siyasa dama wasu da yawa da suke can, suka bar Amir da bataliyar masu gadi da tsaronsa a nan kano saboda karatunshi da ya koma babu damar su koma tare dashi, basu san cewa Amir hankalinshi baya wajen karatu sam yana can wajen fafutukar 'kwato soyayyarshi.

Muje zuwa

*🅱K😘💋*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘

RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (🅱K*
```(Autar marubuta)```

SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
```(Mamie)```

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```🤜🤛

*SO TARI DA DAMA MU MUKE BARI SO YANA KUB'UCEWA DAGA HANNUNMU, TA HANYAR RAGE KULAWA, TATTALI, YARDA DA JUNA, RAGE WA'DANNAN ABUBUWAN GA MASOYA SHI KESA SHA'KUWA TAI 'KARANCI, LOKUTA DA DAMA ZAKA GA MASOYA SUNA 'KAUNAR JUNA AMMA SAKAMAKON JA BAYA DA KAYI DA KULAWARKA SAI ALLAH YA KAWO WANDA YA FIKA DUK WA'DANNAN ABUBUWAN TO WALLAHI CAN ZAI KARKATA, DOMIN AKODA YAUSHE ABINDA BAWA YAFI SO A SO SHINE KULAWA, BA TA YANDA ZA'AI MASOYI YA RASA WA'DANNAN ABUBUWAN DAGA GAREKA KUMA KACE DOLE SAI YA CIGABA DA ZAMA DAKAI, IN HAR BAWA YANA SO SOYAYYARSA TA 'DORE FIYE DA YANDA TAKE A BAYA TO NUNKA TATTALINKA DA KULAWARKA ZAKA YI, MU SANI CEWA ITA KULAWAR NAN ITACE JIGON SO BAKA BARI KAI SAKACI DA ITA, WANNAN MUKA RASA SHIYASA LOKUTA DA YAWA ZAMU MALLAKI MASOYA AMMA DAGA BAYA SU ZAMA BA NAMU BA TO WALLAHI SAKACIN DAGA GAREMU NE, BA TA YANDA ZA'AI MA KA DAINA BAIWA MASOYINKA KULAWA KUMA YA YARDA CEWA WAI HAR YANZU KANA 'KAUNARSA, SHIYASA 'KAUNAR YANZU TA ZAMA TA 'DAN LOKACI 'KALILAN SABODA BABU KULA, DOLE IN KA SAMU WANDA ZAI BAKA DUKKANIN KULAWARSA KA KAR'B'ESHI HANNU BIBBIYU, YA ALLAH KA BAMU IKON CIGABA DA BAIWA DUKKANIN MASOYANMU KULAWAR DA TA DACE.*

PAGE 195 to 200

Amir yaji dad'i sosai da tafiyar iyayensa, domin yasan wata 'karin dama ya samu na aiwatar da shirinsa cikin kwanciyar hankali, dan yasan muddin su Abba suna garin wata rana zasu gano komai, kuma idan suka gano zasu dagula komai domin zasu ce zasu d'auki mataki, dan ba zasu tab'a barin duk wani abu da zai tab'a d'ansu ba suna kallo su 'kyale shi.

Bayan kwana biyu Nura yaje ya sami mahaifinsa ya shaida mishi gaskiya shi fa ya gaji, taya za'ai ace sunan yana da mata amma bata bashi duk wata kulawa ta aure.

Bud'ar bakin mahaifinsa sai yace "to ka saketa mana."

Nura yace "ai ina 'kaunarta bazan iya rabuwa da ita ba," mahaifin Nura yace to kuwa tunda kasan haka sai ka daina wannan maganar ma, mata a hankali ake shawo kansu, kuma koda zaka nuna mata halinka sai ka bari sai mun samu biyan bu'katar mu."

Yanzu Amir da Amira har chat suke yi a waya yau ma chat d'in suke tana fad'a mishi cewa ita fa ta gaji zata fad'a cewar ya dawo a maidata d'akinshi.

Amir ya rarrasheta yana fahimtar da ita cewa yin hakan ba abu bane me sau'ki.

Bayan sati d'aya Amir da Nura suna tafiya kan hanya a cikin motar Amir wanda Nuran ne ke jansu zai kaishi gida sai ya d'auki motarshi ya wuce gida shima, suna tafe sai wayar Nura tai 'kara, yana dubawa yaga Dad d'in Amira ne ke kira, Nura ya kalli Amir da ya du'kar da kai yana chat da Amira yace "d'an akuyan Dad d'in Amira ne ke kirana," Amir ya d'ago yai murmushi sannan yace "to d'aga kaji mana."

Bayan Nura ya d'aga suka gaisa sannan Dad yace "ya kuke ina fatan dai kuna zaune lafiya ba wata matsala ko?"

Nura yace "eh lafiya lau muke zaune babu wata matsala."

"Bayan sun gama wayar ya mayar aljihu sannan yace "sai kayi dana sanin sanina Dad, wai shi me kud'i koda yaushe cikin wula'kanta talaka, hmm."

A dai-dai nan suka kawo 'kofar gidan su Nuran, Nura ya kalli Amir yace "yanzu wucewa zaka yi ba zaka shiga ku gaisa da Madam ba?"

Amir yai murmushi sannan yace "muje," suna shiga cikin falon suka tarar da Amira zaune a kan kujera tana daddanna wayarta, wanda ba da kowa take chat ba face Amir.

Cikin hanzari da farin cikinta ta tashi tana fad'in "barka da zuwa mai gidana, kar kaso kaga farin cikin da zuciyata ke ciki a yanzu na murnar sake ganinka a karo na biyu," Nura ya washe baki tare da d'agowa yana kallonta da mamaki 'karara a fuskarsa na irin tarbar da yake samu a wajenta duk lokacin da suka shigo tare da Amir, sedai abinda ya lura dashi shine sam ba shi take kallo ba, kamar ba shi take yiwa sannu da zuwa ba.

Nura ya wuce ciki tare da kawar da komai daga ranshi, saboda yana tunanin abinda yasa take haka 'kila saboda kar wasu su gane irin yanayin zaman da sukeyi ne.

Yana shiga ciki Amir ya kalleta cikin sauri yace "meyasa kike yin irin haka a gabanshi, so kike sai ya gano mu."

Amira ta turo baki tare da cewa "ai ba laifina bane, bana iya control d'in kaina ne a duk lokacin da na ganka."

Nura ne ya fito daga cikin d'aki tare da zama kusa da kujerar dake gefen Amira, sedai ya lura sam hankalin Amira baya gareshi, ko magana take idonta na kan Amir, shima Amir jefi-jefi yana satar kallonta, haaaaaa wa ya fad'a musu dama soyayyar gaskiya tana b'uya koda anyi 'ko'kari aga anyi hakan.😂

Ganin haka yasa walwalar Nura ta ragu, kuma sannan ya 'ki tashi ya 'kara zuwa ko'ina, hakan ne ya hana su Amir samun damar tattaunawa, daga 'karshe ma tashi yayi yai musu sallama Nura ya rakoshi bakin motarsa ya shiga sukai sallama ya tayar ya tafi.

Sedai abinda ya 'kara d'aurewa Nura kai shine yana dawowa ya tarar Amira bata falon ta shige d'akinta, kuma wannan ba shi bane karo na farko da take yin hakan, idan Amir yazo ya tafi sai ta canza ta koma kamar ba ita ba, ko ta tashi ma tai tafiyarta ta barshi shi kad'ai kamar yanda tayi a yau.

Haka suka cigaba da kasancewa a matsayin ma'aurata har tsawon shakara d'aya harda watanni.

*BAYAN KWANA BIYU*

Yau ta kama Alhamis, Nura na zaune a falo sai ga kiran Dad, koda Nura ya d'aga wayar gaisawa kawai suka yi sannan Dad yace "Nura ko me kake yi ka ajiye kazo office d'ina yanzu ka sameni ina jiranka."
Chapter 46 · 0% Book details