← Book details So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 54

Sashe 28

So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amir ya kalli Amira wadda itama shi take kallo suka yiwa juna murmushi, sannan ya maida kallon shi ga su Baba yace "Baba, Umma, wallahi bazamu tab'a mantawa daku ba har abada, saboda kun d'aukemu tamkar yaran da kuka haifa," Amira tai karaf tace "kuma kuka yi mana abinda iyayenmu da 'yan uwa suka kasa yi mana, wallahi har mu mutu ba zamu daina 'kaunarku ba da kallonku a matsayin iyaye wad'anda suka haife mu, idan mun yi muku laifi a zaman mu daku ku yafe mana, in Allah ya yi da sauran ranmu zamu dawo gareku, in kuma an kashemu to ku tuna damu cikin addu'armu."

Insp Yahya ya kalli Amira yace " wai ke Amira meyasa kike son sa kanki cikin laifin da babu ke a cikinsa ne?"

Amira ta balla mishi harara sannan tace " ina ciki nice babbar me ruwa da tsaki ma kuwa tunda kuke bibiyar burin raina Amir d'ina da mugun sharrin ku, kuma a kanku zai 'kare," ta 'karashe maganar tare da murgud'a mishi baki.

Insp ya kalli bataliyar jami'an nan yace a saka su a mota, kamar jira suke suka nufi su Amir, sai da suka je daf da su Amira ta daka musu tsawa tare da d'aga hannu tana fad'in "ku dakata ba sai kun kama mu ba, zamu shiga da kanmu ku kaimu duk inda zaku kaimu, ni dai nasan duk hukuncin ku baku iya canza 'kaddarar ubangiji, ta kalli Amir sukaiwa juna murmushi a karo na biyu suna ri'ke da hannun juna, sannan ta cigaba da fad'in " Amir d'ina tunda Allah ya cika mana burin mu na zama ma'aurata to mu bisu su dafa mu a babbar tukunya in zasu iya, muje koh?" Amir yai murmushi sannan yace "eh mana me muke jira."

Har suka shiga mota Insp Yahya na tsaye yana kallon ikon Allah yanda gaba d'ayansu suka nuna rashin tsoro ko damuwa a tattare dasu, ga kuma wata magana da yaji wai sun zama ma'aurata.

Aikuwa Allah Allah yake su isa station ya sanar da Dad, saboda gun sauri ya manta da wayarsa a office jin an gano inda su Amiran suka gudu.

Suna cikin tafiya tayar motar su tai faci, sai aka faka ana tsayawa Amir ya fara 'ko'karin guduwa shi da Amira, Amir ya bubbuge wad'anda ke kusa da su, ya ja Amira suka runtuma a guje, sun fara gudu kenan sai Insp Yahya ya saita Amir da bindiga ya harbeshi a gefen ciki ta baya, nan Amir ya saki wani irin 'kara Amira ta juyo itama sannan ta ankara da harbin da aka yi mishi, hakan yasa dole Amir ya zube a nan, nan da nan 'yan sanda suka kewaye su, aka maida su cikin mota aka nufi asibiti, cikin emergency aka nufa dashi cikin Saudi, kuma duk abin su Amira sai da ta shiga, aka cire mishi riga domin suga sun yi 'ko'kari sun cire mishi bullet d'in, ana cire rigar sunan Amira ya fito rad'o-rad'o a 'kirjin shi, kuma daga gani tsaga jikinshi aka yi aka rubuta a fatar jikin nashi irin wanda ba zai tab'a gogewa ba ko ya b'ace har abada.

Amira na ganin sunanta a 'kirjin Amir taji 'kaunarsa ta dawo mata sabuwa tare da jin matsanancin tausayin shi, tabbas tayi imani cewa ba zata tab'a samun masoyi kamar Amir ba.

Bayan kwana biyu Amir ya warke sarai aka sallame su, kai tsaye station aka wuce dasu.

Ko da isar su suka tarar da mahaifin Amira ya zo, cikin 'karaji da fusata Dad yace "ku saka shi cikin cell, ita kuma Amira ku kai min ita mota, sannan ku gaggauta had'a duk wasu bayanai da hujjoji ku tura shi kotu tunda kun kasa tsareshi har ku tuhume shi sosai ya amsa laifin sa, ku tabbatar kun mik'a shi kotu."

Amira jin ance za'a tafi da ita yasa hankalinta yai mugun tashi, tunanin mafita ta fara yi cikin ranta, can sai ta hango bindigar Insp Yahya a kan tebur tai wuf ta d'auka hakan ya yi dai-dai da jefa Amir cikin cell da aka yi, aka rufo wajen.

Cikin sauri Amira ta nuna d'an sandan dake k'ok'arin rufe 'kofar da bindiga, sannan ta umurceshi da ya bud'e 'kofar, cikin sauri ya bud'e ta shige ciki itama sannan ta sake nuna shi da bindiga sannan tace " rufe mu," aka rufe su ita da Amir a ciki sannan ta kalli mahaifinta wanda shima ita yake kallo yana mamakinta tace "Dad zuwa yanzu yaci ace kun ha'kura, a yanzu Amir mijina ne domin an d'aura mana aure ni da shi, muddin za'a cigaba da tsareshi to wallahi se dai a tsare mu dukkan mu ni da shi, Dad babu shaidar da zata nuna Amir shi yai kisan, kuma in dai za'a cigaba da tsareshi da tuhuma to tabbas zan cigaba da bashi kariya ta hanyar maida laifin kaina."

Amira cikin kuka ta cigaba da cewa " Dad wallahi in na rasa Amir nima zaka rasani, ka yi ha'kuri ka barmu mu tafi."

Amir shima cikin kuka ya kalli Dad d'in yace " dan Allah Dad ka tausaya wa rayuwata, wallahi zan iya rabuwa da komai in ha'kura amma banda Amira saboda itace *MAHA'DIN RAYUWATA* dan Allah Dad," Dad be ce komai ba ya juya zai tafi, sai da ya kai bakin k'ofar fita sannan yai magana ba tare da ya juyo ba, yace" tunda kin zab'i zama dashi a kanmu zan d'auki matakin k'arshe, kai kuma Insp ka aiwatar da abinda nace maka," yana kai nan a zancen shi ya fice yai tafiyarsa.

Muje zuwa

*🅱K CE😘💋*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘

RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (🅱K)*
```(Autar marubuta)```

SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
```(Mamie Nah)```

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```🤜🤛

*ALLAH SARKI RAYUWA! SHEKARAR DUBU BIYU DA SHA TAKWAS TA WUCE KUMA BAZATA TAB'A DAWOWA BA, MU ZAUNA MUYI NAZARI ME MUKA AIKATA A CIKINTA, SHIN AIYUKAN ALKHAIRINMU YA RINJAYI NA SHARRIN KO KUWA A'A AIYUKAN SHARRIN NE SUKA RINJAYI NA ALKHAIRIN, MU ZAUNA MUYI NAZARI DA TUNANI, WUCEWAR LOKUTA DA SHEKARU BA ABUN MURNA BANE ABABEN TUNATAR DA BAYIN ALLAH NE SU GANE CEWA LOKUTANSU FA NATA TAFIYA, MU RIBACI RAYUWARMU DA AIKATA ALKHAIRI KAFIN MUTUWARMU, MUYI TUNANI ME MUKA AIKATA A BAYA, KUMA ME ZAMU AIKATA A GABA NA ALKHAIRI, YA UBANGIJINMU KA YAFE KURAKURENMU NA BAYA KA BAMU IKON AIKATA ALKHAIRAI CIKIN WANNAN SHEKARAR WADANDA ZASU ZAMA SILAR SHIGARMU ALJANNA👏👏👏👏👏😭*

```INA MIK'A SAK'ON GODIYATA GA 'DUMBIN MASOYANA DA SUKA KIRANI DOMIN TAYANI TA'AZIYYAR RASHIN UNCLE 'DINA SULAIMAN DA NAYI, DA WA'DANDA SUKA KIRA DOMIN GAISHENI DA JIKI DOMIN RASHIN LAFIYA DA ALLAH YA JARABCENI DA ITA, KA'DAN DAGA CIKI SUNE```

*MAMAN LABYB*
(Mamie Nah)
```KODA YAKE KE AI MAMIE JIGO CE TA RAYUWAR BK😉😊 IDAN NACE JIGO INA NUFIN KECE KOMAI NAWA, AMMA DUK DA HAKA WAJIBI NE IN GODE MIKI DOMIN TABBAS KIN DAMU DANI FIYE DA KOWA, K'AUNA BATA IRGUWA SONDA NAKE MIKI BAI MISALTUWA😍😘💋.```

SAI *AISHAN UMMA*
(Auntynah)
*MEELAT A.H.K*
(Bloodynah)
*QUEEN RUQEEY*
(Habibty nah)
*MUMMYS FRIEND*
(Tawan)
*RAHEENAT M. ABBAKAR*
(My heenat)
*HAUWA JAMIL*
*MARYAM M. HASSAN MEEMAH* (Hearty nah)

```Dukkaninku da na lissafo gaskiya bana kallonku matsayin friend kawai, kallonku nake matsayin 'yan uwa, 'yan uwan ma na jini, dalili kuwa shine kun damu dani fiye da kowa, ko na yini d'aya tak in baku ganni ba online sai kun binciki dalili, Allah ya saka muku da alkhairi tabbas irinku ake so, ina da tabbas akan ko bayan babu ni zaku ri'ka tunawa dani har in samu addu'a daga gareku, shiyasa bana had'a matsayinku da na kowa gaskiya, Allah ya saka muku da alkhairi.```

*MASOYANA*
```bazan manta da ku ba masoyana wad'anda suka kwararo min tasu addu'ar ta cikin whatsapp irin su```

*REAL KHADY*
(Princess)
*~HAJARAH GHANDHI*
(Hajjona)
*~MOMYN KHADEEJA🧕*
*~UMMUZAID*
~*MAMAN ARFAT*
~*MUMMYN-SULTAN*
*ASIYA SEE SEE*
*MY LISSA*
*MARYAM KWARE*
*QUEEN BK*
*HAJ CEEYMER UMMEETA*
*MARYAM*
*HAPSY MK*

```Kuna farko farko a zuciyata kun nuna mini so da kulawa nagode 'kwarai da nuna kulawarku kaina, Allah ya saka muku da mafificin Alkhairinsa, duk wad'anda suka tayani addu'ar samun lafiya da masu yimin ta'aziyya duk na gani gaba d'aya Allah ya saka muku da alkhairi ya biyaku, wadanda suka ga ban ambaci sunansu ba suyi hakuri ban gani bane saboda yawancin maessage dina duk waiting suka sa min amma ina godiya Allah ya saka muku da alkhairi gaba d'aya, iya wuya fa ana mugun tare.```

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```Ina godiya da tarin addu'ar da nake sha kullum a wajenku babu dare ba rana, wallahi kunci sunanku 'yan amana, domin d'an amana ne kad'ai yasan mecece amana kuma ya kiyayeta, kuna burgeni ina yinku har abada, kawai a cigaba da basu maamaaki mutanena🤜🤛😉😘😍👯‍♀```

PAGE 120 to 125

Dad ya bada umurni a cigaba da tsare su Amir cikin cell d'in tare da 'yarsa Amira a cewarsa tunda haka ta zab'a kuma taga yafi mata, har zuwa ranar da za a shiga kotu.

Insp Yahya kuwa Allah Allah yake a yanke wa Amir hukuncin kisa ba dan tsanar da yai mishi kad'ai ba ma, ko dan wahalar da suka sha a kanshi, hakan yasa cikin 'kan'kanin lokaci ya had'a dukkanin takardu d'auke da bayanan 'karya aka mi'ka su kotu, wanda za'a halarci kotun ranar Litinin.

Yau litinin, kuma a yau ne kotu ta cika ma'kil domin gudanar da shari'ar su Amir, inda Amira ta 'kara ja mishi kunne kan karya sake duk tsananin wuya ya amsa laifin, sannan ta k'ara 'karfafa mishi guiwa ta hanyar tabbatar mishi da cewa su ne da nasara in Allah ya yarda.

Shigowar Al'kali kenan kowa ya mi'ke, sai da Al'kali ya zauna sannan kowa ya koma mazaunin shi ya zauna.

Kotu tai tsit kowa ya baza kunne da idanu domin bada muhimmanci wajen ganin yanda wannan shari'ar zata kasance.

Da yake shari'ar su Amir itace aka sa a farko shi yasa aka fara karantota, sannan aka umurci gabatar da Amir inda Amira ke biye da shi, can d'aya b'angaren kuma iyayen Sadeeq ne.
Chapter 28 · 0% Book details