← Book details So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 54

Sashe 34

So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baba yai shiru yana tunani, can sai yace "eh to gaskiya ni a yanda yace min lokacin da na ganshi da kai a hannu na tambayeshi, cemin yai tsintarka ya yi, se dai har ga Allah ban san a ina ya tsinceka ba," iya abinda ya samu kenan wajen Baba, haka ya gama binciken shi a unguwar nan amma babu wani abu da ya 'kara samu, hakan yasa ya wuce station ya shigar da 'korafi kan ya rasa iyayensa tun be san kanshi ba, yanzu shekaru talatin kenan, koda wasu sun zo neman d'ansu a kirashi ya gansu, duk wata station da take wannan garin sai da yaje ya shigar da wannan bayani, tare da rarraba lambobinsa koda za'a nemeshi, sannan ya juyo kan motarshi zuwa gida jiki a sanyaye.

Yana zuwa bakin 'kofar gidan yai hon aka bud'e mishi ya shiga, kai tsaye wajen fakin ya wuce ya faka motar sannan ya kasheta ya fito ya shiga cikin gida.

Be tarar da kowa ba a babban falo, hakan yasa kai tsaye ya haye sama, ba kowa a d'akin nasu, ko'ina ya duba Amma Amira bata ciki.

Wayarshi ya ciro ya kira wayarta yaji tana ina, Amira kuwa tana sashen mahaifiyarta tana zuba mata shagwab'a, wayarta taji tana 'kara kuma tasan wanda ke kira, saboda itama ringing d'in kiran shi daban ta saka, bata d'aga ba mi'kewa kawai tayi tace wa Mummyn ta hira ya 'kare bari ta koma d'aki.

Mummy tace "oh Allah ya kawomu zamani mijinki ya dawo ya kiraki a waya kin tashi da rawar jiki zaki tafi," Amira ta turo baki sannan tace "ya akai kika gane shi ya kira?" Mummy tace "yanayin zumud'in da kika nuna yanzu mana," Amira tayi dariya sannan tace "kaji Mum dai kema fa tunda nai wayau ban tab'a ganin Dad ya shigo ya wuce d'akinshi kuma ki cigaba da zama wajenmu ba, in dai yana gida to kema a koda yaushe kina wajenshi, idan mun ganki to baya nan ne, nima yasin dan bayanan ne yasa kuka ganni," tana kai nan a maganarta ta danna a guje ta fice daga d'akin.

Mahaifiyarta kuwa salati ta hau yi, tace kaga ja'irar yarinya ta samin ido ni da mijina," matar Uncle d'insu kuwa dake zaune tana jin duk abinda Amiran tace dariya take ta yi.

Amira da d'aurewarta ta shiga d'akin tana cin magani ita a dole tai fushi, kuma tana shigowa kusa dashi ta samu waje ta zauna, jin yai shiru be ce mata komai ba yasa ta d'ago ta fara satar kallonshi, tunani yake sosai idan ma ance be san ta shigo ba ba musu.

Nan da nan Amira ta warware ta nemi fushinta ta rasa, fuskarta ta koma bayyanar da yanayi na damuwa, 'kara matsowa kusa da shi tayi, tare da dafa kafad'arshi tana jijjiga shi cikin damuwa tace "Amir d'ina lafiya, meke faruwa na ganka cikin wannan yanayin, dan Allah ka fad'amin meyafaru?"

Amir yai firgigit, sannan ya numfasa, ya kalleta yace "Amirata kin shigo ashe, wallahi Amira nayi yawon amma ba nasara," ya kwashe komai ya fad'a mata har yanda suka yi da tsohon nan.

Amira ta numfasa sannan tace "shine kabi duk ka d'aga hankalinka, bayan kuma kasan idan ka shiga damuwa ina finka shiga tashin hankali, haba Amir d'ina dan baka ga iyayenka ba sai akace maka mun rabu kenan, ina lura da kai tunda Dad yai wannan maganar ka shiga damuwa, ni nace maka zan barka ne, fad'in Dad ne kawai kaima ka sani, amma duk wuya duk rintsi ina tare da kai, babu abinda zai rabamu insha Allah, ka kwantar da hankalinka ko me za'a yi, kuma ko menene zai faru se dai ya faru amma ban tab'a rabuwa dakai, ban tab'a juyawa soyayyarka baya.

Cikin 'kan'kanin lokaci sai da taga ya dawo asalin Amir d'inta sannan hankalinshi ya kwanta itama ta samu natsuwa, ta had'a mishi ruwa yai wanka sannan ta shirya mishi abinci a gabanshi ya zauna zai fara ci, ya Kalleta yace "wai ina fushin da kike yi dani ya tafi, har abinci fa akace baza'a bani ba," Amira ta turo baki sannan tace "ya za'ai in kula wani fushi na ganka cikin yanayi na damuwa, ni nama manta," haka sukaita hirar su cikin jin dad'i.

Haka Amir yaita sintiri kullum amma ba wani labari, har cikin 'kauyukan garin ya shiga yana bincike amma shiru har yanzu, har wajen wata uku yana zirga-zirgar neman bayani akai amma shiru.

Yau lahadi, kamar kullum yau ma Amir ya shirya tsab domin fita cigaba da neman 'karin bayani kan wanene shi kamar yanda ya saba, bayan ya shirya tsab ya kalli Amira yaga yanda ta had'e rai, yai murmushi sannan yace "wai ke dan Allah meyasa duk in zan fita sai kin b'ata rai ne," Amira ta 'kara turo baki sannan tace "saboda rashin sabo mana," Amir yace ai kuwa ya ci ace kin saba mun shiga wata na uku ina fita fa," Amira ta 'kara turo baki sannan tace ni bazan saba ba, ni yasin yau binka ma zanyi," Amir yace "kiyi ha'kuri yau waje d'aya zanje in dawo bazan dad'e ba insha Allah."

Da 'kyar ta barshi ya fito ya shiga mota ya fice daga gidan, cikin 'kauye ya nufa, yana cikin tafiya wata babbar mota ta taho da gudu, duk yanda yaso ya kauce mata ya yi amma ya kasa, sai da tabi ta kanshi motar Amir ta hantsila can gefen ti-ti, cikin sauri masu babbar motar suka fito suka ga sam ba alamun numfashi a tare da Amir, d'aya daga cikin su yace "baya numfashi wallahi mui ta kanmu," ai kuwa su duka ukun suka fad'a mota suka jata da gudu suka bar wajen.

Muje zuwa

*🅱K CE😘💋*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘

RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (🅱K)*
```(Autar marubuta)```

SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
```(Mamie)```

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```🤜🤛

PAGE 145 to 150

Da yake ba cikin gari bane motoci d'ad'd'aiku ne suke wucewa kan hanyar, kuma ikon Allah duk wanda yazo kai tsaye yake wucewa babu wanda ya tsaya saboda ba wanda ya kawo akwai mutum a ciki, sedai in zasu wuce daga cikin motar kaji ana cewa kai amma an gwabza hatsari anan Allah ya kiyaye gaba, sai su wuce abinsu.

…………………………………

Ahmad da matarsa Khadija tafe suke a kan hanya, Ahmad yana tu'ki yana yiwa matarshi fad'a yace "wai Hauwa sai yaushe ne zaki cire tunani ne daga ranki, kinsani fa sarai abinda tunani ke haifarwa ko so kike nai rashinki? dan Allah ki daina tunanin nan zuwa yanzu yaci ace kin.........." kasa 'karasawa yayi sakamakon ganin mota a tuntsire, kuma daga gani wannan had'arin be dad'e ba dan ba alamun hakan, ya kalli matarshi yace "kin kuwa hango abinda nake gani a gabanmu? hatsari aka yi, kuma ni kamar ma hannun mutum nake hangowa bari inje in duba," cikin sauri matarsa Hauwa ta ri'ke shi, tace "nifa tsoro nake ji, kasan yanda duniyar nan ta zama, ba mamaki ma 'yan fashi ne," Ahmad yace "kai bana tunanin haka gaskiya, koma dai menene zanje in duba, Allah yaga zuciyata, ba zai bari su cutar da ni ba."

Yana gama fad'in haka ya fita daga motar ya tunkari wajen wannan motar da suka gani, yana zuwa ya le'ka ciki ai kuwa mutum ne ya gani a ciki yaro matashi kanshi na fitar da jini, duk yaji ciwo a jiki, kuma babu alamar numfashi ko kad'an a tare dashi.

Cikin sauri ya fara 'ko'karin neman hanyar da zai fito da shi, da 'kyar Allah ya bashi sa'a ya fito dashi daga ciki.

Matarshi kuwa koda ta hango abinda ke faruwa ta glass d'in motar ta fito cikin sauri ta tunkaro wajen, 'kokarin kamashi suka yi suka sa a mota sannan suka tafi asibiti, a hanya matarshi 'korafi take ta yi tana fad'in kaga amfanin securitys da jami'ai ko, amma kai in za'a fita sai kace baka so suna binka, yanzu gashi nan ai kana komai da kanka, kai kasan ma'abocin taimako ne, kai na talakawa ne, be dace ace baka fita da kowa ba sai mu kad'ai."

Ahmad yai murmushi yace "idan bu'katar hakan ta taso ina nemansu ai, ni dai kawai bana so suna bina a baya gaskiya, ba burina duk inda na fita aga jerin motoci suna kewaye da ni ba, nafi so in ri'ka fita ni kad'ai, bana son duk wani abu da zai yi silar saka min girman kai da d'agawa ya jawo in nisanci talakawa na."

Asibitin suka 'karaso shiyasa ya dakata da maganar, cikin sauri suka fito, aka kira norses aka d'aukeshi kamar matacce aka shiga dashi cikin emergency.

Khadija ta kalli mijinta Ahmad tace "Allah sarki Allah kad'ai yasan halin da iyayensa suke ciki a yanzu, kyakkyawan yaro dashi," nan da nan 'kwalla ta taru a idanunta tana nema tai kuka, Ahmad ya 'karaso kusa da ita, sannan yace "zaki fara ko, kina farawa nima zan tayaki wallahi kuma kinsan zan iya, yanzu kiga kukana ya tara miki jama'a domin kinsan kukan namiji akwai tada hankali saboda an san ba 'karamin abu bane zai saka maza yin kuka."

Khadija ta share hawayenta tare da yin murmushi, shima Ahmad murmushi yayi, sannan ya ciro wayarshi ya kira jami'ai ya sanar dasu hatsarin da kuma inda abun ya faru domin suje su gudanar da bincike a san daga ina yake a nemo iyayensa a had'ashi da su.

Bayan wasu lokuta sai ga likita ya fito ya tunkaro su yana yarfe gumi, Ahmad ya kalle shi yace "mun yi 'ko'karin tsayar da jinin dake fita daga kanshi, kuma duk raunukan da yaji an wanke wurin an saka magani, se dai ya yi muguwar buguwa, kuma kunsan hatsari irin wannan sai an yi gwaje-gwaje domin gane dukkanin inda suka samu matsala a jikinsa, saboda haka zamu cigaba da kula da shi, da bashi agajin gaggawa bari in koma wajenshi."
Chapter 34 · 0% Book details