← Book details So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 54

Sashe 14

So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau Alhamis, tashin Amira kenan daga bacci agogon d'akin ta kalla k'arfe tara na safe, zaro idanu tayi sannan ta kai dubanta kan gado wayam Amir baya nan, ta je bakin k'ofar bayi ta k'wank'wasa shima shiru, ta bud'e ba Amir a ciki, ta shiga kicin ta duba nan ma wayam baya ciki, hankalin Amira fa ya fara tashi, ta fito daga cikin d'akin ta bi ta baya ta dudduba duk inda suke zama duk babu alamun shi, hankalin Amira fa ya kai k'ololuwar tashi, kuka ta fashe dashi tana tunanin ina Amir ya tafi gashi ba wanda ya sani a garin, komawa cikin d'akinta ta yi ta d'akko mayafi ta yafa tare da zarar makullin motar Mum da ta gaje mata take hawa tunda ta dawo, ta fito ta babban falo sam ta kasa natsuwa, ta fito tana hawaye, tazo ta wuce ta gaban su Dad duk suna zaune a falo zata fita Dad ya k'wala mata kira, yace " ina zakije?" ina harga Allah bata ji shi ba hankalinta yai gaba, ta fad'a mota taja ta tafi, haka taita bi lungu da sak'o na unguwar tana dubawa ko Allah zaisa ta ganshi amma ina, maida motar gida ta yi ganin wasu guraren ba damar kutsawa da mota, ta sake fitowa a k'asa, duk ta fita hayyacinta kuka sosai take yi tana cikin tafiya sai ta hango shi zaune a wurin da bazata tab'a mantawa da shi ba har abada domin kusa da gidansu ne wurin ta can baya inda wani dad'ad'd'en gidan marayu ke wurin, lokacin tana yarinya nan ne wajen zaman su, har Amira ta k'ara so wajen bai san da ita ba, sai da ta dafa kafad'arsa tare da jijjigashi sannan ya dawo daga duniyar tunanin da ya lula.

Kallonta ya yi tare da yi mata murmushi, zama Amira ta yi kusa da shi tare da rungume shi ta fashe da kuka sannan tace " meyasa ka fito ba tare da na sani ba, yanzu da wani abu ya same ka fa, Amir d'ina bazan tab'a iya jure rayuwar da babu kai a cikinta ba, dan Allah karki barni, kuma karka sake yin nesa da ni."

Amir ya d'ago ta tare da share mata hawayen idanunta, idanunta duk sun kumbura ya kalleta yace " wa ya fad'a miki zamu rabu, insha Allah na kusa mallakarki ma a matsayin matar aurena da zarar kin gama karatunki, kuma abinda yasa na fito saboda naga kina bacci ne, kuma ban yi tunanin zaki tashi da wuri haka ba saboda nasan jiya mun dad'e muna hira bamu kwanta da wuri ba shiyasa, amma kiyi hak'uri tuba nake bazan k'ara ba," ya k'arashe maganarsa tare da rik'e kunne.

Rarrashin Amira ya yi, sannan suka tashi suka juyo da niyyar komawa gida suka ga Dad da su Mum tsaye a kansu suna musu wani irin kallo, Dad ya kalli Amira cikin d'aga murya yace "ke Amira waye wannan," ya k'arashe maganarsa tare da nuna Amir da hannu, ba Amir da Amira ba hatta ni Bk sai da na razana da ganin iyayen Amira a wajen, hakan yasa na yarda komai nawa na runtuma a guje sai gidan su Bloodynah kai tsaye bayi na shige na fara zawayi na fargaba.

_shin ya zata kasance? ku biyoni muje_

*🅱K CE😘💋*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘

RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (🅱K)*
```(Autar marubuta)```

SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
```(Mamie) ```

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah) ```🤜🤛

*SANARWA!!!🗣 ina makaranta litattafan Hausa? to ku saurara da kyau kuji,👂 shahararriyar marubuciyar littafin SHARRIN ASHQEEY mai suna RUKAYYAT BINT DAWUD (QUEEN RUKEEY) ta sake gangamo muku gingimemen labarinta mai suna JARRABAWAR RAYUWA, kar ku sake kuyi sakaci a barku a baya, sunan littafin JARRABAWAR RAYUWAAAA*

*Wallahi ina matukar jin dad'in comment d'inku, ina yinku fiye da duk wani tunani naku, Allah ya barmin ku masoyana😍😘*

*TABBAS SO MAHA'DI NE NA RAYUWA, DOMIN YAKAN ZAMA SILAR GYARA RAYUWAR WASU, A YAYIN DA YAKE ZAMA SILAR GURB'ATA NA WASU, SO TSANI NE NA TUSHEN GINA KYAKKYAWAR RAYUWA IN KA YI DACE DA MASOYI NA K'WARAI, SO YANA ZAMA NASARA GA RAYUWAR WASU A YAYIN DA YAKE ZAMA FA'DUWA KO KOMA BAYA GA RAYUWAR WASU SO YAKAN KASHE WASU RAYUKAN, A YAYIN DA YAKE BAWA WASU DAMAR CIGABA DA RAYUWA, SO RAYUWA CE, AMMA WASU LOKUTAN MUTUWA CE, DUK WANDA YA K'ULLA SO A RAI TO TABBAS YA K'ULLA HARDA ABU BIYU WATO FARIN CIKI DA BAK'IN CIKI, SANNAN LOKUTA DA DAMA KUMA MAFI YAWANCI SOYAYYA TAKAN MAKANTAR DA MASOYA TA YANDA BASA GANE DAI-DAI DA RASHINSA, IDAN KAI DACEN SO NA GASKIYA TO TABBAS RAYUWA NA D'OREWA CIKIN FARIN CIKI DA WALWALA BAYAN JURE DUKKANIN WANI RU'DANI.*

PAGE 60 to 65

Zuru-zuru suka yi dukkanin su, a yayin da Amira ta fara inda-inda, sai Dad ya sake yi mata tsawa tare da tambayarta waye wannan, Amira ta dake domin kar mahaifinta ya gane akwai wani abu da take b'oye mishi, ta kalli Dad tana d'an murmushi tace " Dad abokin karatuna ne wannan, duk k'ok'arin da nake yi kusan shine sanadi saboda yana taimaka min sosai a karatuna, kuma yazo mana biki ne zuwanshi ma kenan."

Dad jin an sako karatu a ciki sai ya sassauta fushinsa don shi mai son yaga yaranshi na maida hankali ga karatu ne sosai, amma duk da haka be gama yarda da maganarta ba saboda sunga lokacin da ta wuce tana hawaye.

Dad yace " ku biyoni muje gida," daga haka be sake cewa komai ba suka juya suka tafi, suma su Amira suka bisu a baya har suka iso har cikin babban falo inda kowa ya samu waje ya zauna.

Amir yabi kowanne daga cikin 'yan gidan ya gaishe su, sannan Dad ya cewa d'aya daga cikin yaran gidan su kaishi d'akin bak'i ya huta, Amir ya bi bayansa suka fice daga d'akin, sannan Dad ya dawo da kallon shi ga Amira yace " Amira karfa ki manta mu iyayenki ne ba sa'anninki ba da zakiy mana wasa da tunani, idan biki yazo ina kayanshi tunda da sauran kwanakin yin bikin, kuma meyasa kika fita kina kuka har na kiraki baki ji ba?"

Amira tace "Dad lokacin da na fita ina kuka fad'amin yai wata Friend d'ina ta rasu shiyasa hankalina ya tashi har kuka ga na fito ina hawaye, jakarshi kuma tana cikin mota."

Dad yace "amma ai ba da mota muka ga kin fita ba," Amira gabanta ya fad'i, saboda ta tuna ta dawo da motar gida, ta kalle shi sannan tace " Dad kenan, ai ba ni kad'ai na fita ba da driver ne, kuma sauka muka yi anan inda kuka ganmu nace drivern ya k'ara so kafin mu taho muma."

Sai a lokacin Dad d'in Amira ya numfasa, sannan yace "to shikenan ya kyauta da yazo mana biki, kuma tunda kin cemin yana taimakon ki kan karatunki zan yi mishi godiya, se dai kar ki kuskura na ji sab'anin wannan zancen kuma," Amira tace " to Dad," Dad yace "yanzu ki tashi kije ki sa a kai mishi abinci da abin sha sai ki bashi wuri ya huta, anjima idan ya fito sai mu yi magana dashi."

Amira ta tashi cike da farin cikin yau Allah ya k'waceta hannun Dad d'inta.

Tun daga ranar Amir bai sake kwana d'akin Amira ba, yanzu kulawarshi ma ba iya Amiran kad'ai ba ta tsaya harda iyayenta da 'yan uwanta, hakan ya k'ara basu damar sakewa sedai ba kamar da ba saboda yanzu basa keb'ewa suyi hira kamar da saboda idanun mahaifin Amira da wasu daga cikin 'yan gidan dake kansu, sedai ko yaushe suna mak'ale a waya da kuma chat.

Bayan ansha biki na kece raini an kai Amarya d'akinta ranar Litinin Amir yace zai juyo ya dawo, bayan ya had'a kayansa yazo falo ya duk'a bayan ya gaisheda Dad da kawunta sannan yace musu shi zai koma, Amira na zaune kusa da Dad d'inta sai aika wa Amir da harara take a fakaice.

Dad yace " ai tunda an k'are shagalin bikin kawai Amira itama ta shiga ta shirya ta bishi su koma tare, cike da farin ciki mara misaltuwa ta mik'e cikin sauri duk aka bita da ido ganin yanda ta mik'e d'in, tai saurin b'oye murnarta ta d'an b'ata rai sannan tace " gaskiya Dad ni ban gaji da ganinku ba, ka bari after five or six day's na koma makarantar."

Dad yace " a'a daughter tashi ki shirya an gama biki me zaki zauna kiyi kuma, kuma mu dama ai bazaki tab'a gajiya da ganinmu ba, oya tashi maza ki shirya," haka ta tashi tana bubbuga k'afa ita a dole bata son komawa, sai da ta kai bakin k'ofa ta juyo suka had'a idanu da Amir ta d'an yi tsallen farin ciki tare da kashe mishi ido d'aya sannan ta fad'a d'aki da sauri.

Amir ya sauke idanunshi yana murmushi a yayin da Dad ke k'ara yi mishi godiya tare da rok'on shi kan k'ara kulawa da karatun su da na Amiran.

Kowa na d'akin yai tsit, hatta kawun Amira mamaki suke yanda suka san duk tsattsauran ra'ayi da dokoki kan yaran gidan da Dad d'in yake amma ya iya yarda ya amince Amira ta bi Amir su koma kamaranta tare, duk sun k'osa su tafi kowa ya fara antayo mishi tambayoyin dalilinshi na yin haka, shi kuwa Dad yana lura da yanayin su duka, murmushi kawai ya yi.

Ba'a d'auki wasu dogon lokaci ba sai ga Amira itama janye da jakarta, d'aya daga cikin security's d'in gidan ne ya karb'i jakarsu ya fice dasu yasa a mota, sannan suka tashi gaba d'aya harda su Dad aka rakosu har bakin motocin da zasu kaisu tashar jirgi.

Sallama suka yi da kowa na gidan sannan suka shiga mota, suka fice daga gidan inda sauran motocin ke mara musu baya.

Bayan fitarsu kawu ya kalli Dad yace "amma yaya yau ka bawa kowa mamaki a gidan nan, yanda kake da tsattsauran ra'ayi kan kowa musamman matan gidan nan akan samari amma yau kai da kanka kake basu damar tafiya tare."
Chapter 14 · 0% Book details