← Book details So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 54

Sashe 36

So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ahmad ne zaune cikin kujera me zaman mutum biyu a falon su shi da matarshi Khadija suna hira, can sai Ahmad yace "naso inje india domin duba halin da wannan yaron ke ciki, gashi kuma zab'e ya kusa, cikin wannan watan ne kinsan zab'en namu, da ni da shugaban 'kasan da yake kai a yanzu, shiyasa komai ya rincab'e min, ya zama lokacina kad'an ne," Khadija ta kalle shi tace "to ka bari mana idan har aka gama zab'en sai mu tafi," Ahmad yace "kin kawo shawara mai kyau, amma a maganarki naji kamar kince sai mu tafi ko?" Khadija tace "eh mana haka nace, ai duk inda zaka tafi 'kafata 'kafarka, shiyasa ma nace karka wani sha wahalar tsayar da mataimaki, tunda gani ni zan zama mataimakiyarka kawai," Ahmad yai dariya itama matarshi tana tayashi.

Amira kam se dai muce Allah ya kyauta domin kuwa komai nata ya sukurkuce, ta daina walwala, ta daina fara'a, ta daina hira da kowa, abinci ma sai mahaifiyarta ta bata a baki take ci, shima kad'an, ta dai koma kamar 'karamar yarinya, ko ta shiga cikin mutane bata walwala sam, sannan bata cewa um bata um-um, babu inda ba'a je da ita ba, babu abinda ba'a kawo mata ba domin ya d'ebe mata kewa amma ina, duk ta rame tayi ba'ki kamanninta duk sun canza, koda yaushe bata da wani aiki sai tunani, wayar Amir kuwa tana hannunta dare da rana tana duba sa'kwannin da ya tura mata da wanda itama tai mishi, munji yanda rayuwar Amira ta cigaba da kasancewa.

Yau talata, kuma a yau ne aka yi za'be, yanzu kowa kawai jiran fitar da sakamako daga al'kalan zab'e ake yi, to bamu san waye kuma zai yi nasara ba, Dad d'in Amira ne ko kuwa Ahmad.

Dukkaninsu gidajen nan biyu suna gaban t.v da redio suna jiran sakamako, biyar na yamma dai-dai aka fara sanar da 'kuri'un shugabannin 'kasa, inda aka tabbatar da Ahmad shine wanda ya lashe wannan kujerar ta shugaban 'kasa.

Murna kam wajen bayin Allahn nan ba'a magana, a yayin da Dad d'in Amira da iyalensa suke ba'kin ciki da rasa wannan kujera da suka yi, kuma ikon Allah sai a ranar ba'kin cikinsu suka ga Amira tai dariya, harda tsalle da murna tana fad'in "Dad ya fad'i Dad ya fad'i."

Gaba d'ayansu tunani suke anya Amira bata samu tab'in hankali ba kuwa, Dad ji yai kamar ya kwad'eta dan ba'kin ciki, tashi yai ya shige cikin d'akinsa.

*BAYAN WATA D'AYA*

Wata biyar kenan cur da fitar da fitar da Amir waje, inda su can gidan su Amira suke ganin yana da wata biyar da rasuwa, shi kuma Ahmad zai ce bayan wata d'aya da hawar shi kan kujerar shugaban 'kasa.

Kwatsam yau suna zaune a d'aki sai ga wayar Aleey yana shaida musu cewa majinyacin nan fa yau ya farka ya bud'e idanu, harma yana ta kiran sunan wata yarinya wai Amira yana cewa a kaishi wajenta, Ahmad ya shaida musu cewa insha Allah suna nan tafe zasu taho gobe in Allah ya kaimu shi da matarsa.

Bayan zuwan su president Ahmad da wata d'aya Amir ya samu sau'ki sosai, amma har yanzu be daina damun su da tambayar ina Amirarsa take ba, ganin da likitoci sukai Amir ya warke yasa suka sallame su gaba d'ayansu su hud'un suka juyo domin dawowa 'kasarmu ta gado wato Nigeria.

Suna durowa already dama motoci guda biyu suna jiran 'karasowar su, suna sakkowa daga jirgin suka shiga mota guda d'aya, d'ayar kuma tana binsu a baya har zuwa gida.

Suna shigowa jami'ai suka zagaye wajen, nan da nan suka bud'e musu mota suka fito, Ahmad da kanshi ya kamo Amir ya fito dashi daga cikin motar, a haka suka shiga har cikin babban falon dake cikin gidan.

Ya zaunar da shi a kujera, sannan shima ya zauna a kusa dashi, Khadija ta zauna a kujerar da ke kallon su, Aleey ma ya zauna a 'kasan kafet, a yayin da security tsaye kowace kusurwa a 'kame.

Ahmad ya cewa securitys d'in su je daga waje zasu yi magana, dukkaninsu suka fita, sannan ya kalli Aleey yace "haba Aleey tashi kaima ka hau kan kujera mana," Aleey ya tashi daga 'kasa ya hau kan kujera.

Ahmad yai gyaran murya sannan yai bismillah ya kalli Aleey yace "Aleey sannu da 'ko'kari, Allah ya baka ladan jinya, a koda yaushe ina 'kara alfahari da kai Aleey, Allah yai maka albarka, ka tashi kaje domin kaga iyalenka kaima, ga wannan dubu d'ari biyar ne ka tafi dashi duk abinda ya 'kare sai ka siya musu tunda mun d'auke musu kai ba aiki har tsawon wata bakwai," Aleey ya karb'a tare da yin godiya, sannan ya fice da zumud'insa yana farin ciki.

Ahmad ya dawo da kallonsa ga Amir yace "bawan Allah mun gode wa Allah da ya dawo da kai gida lafiya, Allah ya 'kara maka lafiya, yanzu kamata yai ka 'kara samun hutu a nan kafin muji inda kake muje mu kaika mu yi musu bayanin hatsarin da ya faru da kai, mu sanar da su komai.

Amir kuwa jin an ambaci hatsari ya tuno mishi da komai, yanda aka bugi motarsa ya tabbatar masa da cewa lallai turo su aka yi, cikin sauri ya kalli Ahmad yana hawaye yace "Abba yanzu zan kai kwana nawa ina jinya?" Ahmad yace "ba kwana bane, watanka bakwai kana kwance ba lafiya."

Amir yace "Akwai wani nawa da yasan ina wajenku ne Abba?" Ahmad yace "a'a sai jami'an tsaro wad'anda suke d'aya daga cikin masu kula da ni," Amir yace "to dan Allah ka fad'a musu bana so kowa ya san inda nake har sai na gama binciken da nake yi na gano asalina, kuma in kun yarda zan zauna daku na wasu lokuta, kuma nagode sosai da taimakon da kuka yi min."

Ahmad yace "bamu fahimci bayaninka ba yaro, in ka zauna a nan iyayenka fa?" Amir yace "bansan iyayena ba, zan baku labarina ko dan taimakon da kuka yi min a rayuwa," nan ya fara basu labarin tarihin rayuwarsa tun yana 'karami har girmansa da abubuwan da sukai ta faruwa da shi a rayuwa har zuwa wannan hatsarin, sannan Amir ya d'ora da fad'in "abinda yasa nace ina so na zauna daku na wani lokaci saboda in cigaba da neman iyayena a hankali har Allah yasa in gansu, nasan Dad ne yasa ai min haka, 'kila idan na nemo iyayena zai sassauta tsanar da yake yi a kaina."

Dukkaninsu kuka suke yi, musamman ma Khadija kukanta har da shesshe'ka, labarinshi abun tausayi ne matu'ka ace tun yana yaro be san wani abu wai shi jin dad'in rayuwa ba har girma, kuma sai labarin shi yai musu famin wata dad'ad'd'iyar damuwa da take damunsu a rai.

Ahmad ne ya share hawayensa, sannan ya kalli Khadija da har ta fara tari ciwonta naso ya tashi saboda kuka, cikin sauri, Ahmad da Amir d'in suka 'karasa wajenta a tare suna mata sannu, Ahmad fad'a yake yi, "kinsan yanayin ciwonki baya son damuwa amma daga jin labari kinbi duk kin d'aga hankalinki," maganinta ya d'auko mata ya bata ta sha, sannan yace "muje in kaiki ki kwanta," Khadija tace "a'a barni a nan ma kawai."

Ahmad ya zauna kusa da ita yana yi mata sannu, Amir kuwa ji yayi yanayin rayuwar bayin Allahn nan ta burgesu, kuma sai yaji yana matu'kar 'kaunarsu.

Muryar Ahmad ne ta katse mishi tunani, yace "Amir munji labarinka, kuma mun tausaya maka matu'ka, muma ka ganmu nan, muna jin kusan irin rad'ad'in da kake ji, yaron mu ya ya b'ata tun yana 'karami baida wayau be san kanshi ba, amma har yanzu mun kasa mantawa dashi, gani muke kamar ma zamu ganshi, tun farkon ganinmu da kai Allah ya saka mana 'kaunarka cikin ranmu, irin soyayyar da iyaye ke gwada wa kan 'ya'yansu, idan ba zaka damu ba ka zauna tare da mu, mu zame maka iyaye, ka d'aukemu ka kaimu gidan su yarinyar a matsayin iyayenka na asali."

Amir yace "Abba nagode da 'kaunar da kuka nuna kaina, kuma na yarda zan zauna daku, zan ri'keku matsayin iyaye a gareni na har abada koda kuwa naga iyayena bazan manta da ku ba bazan ma gujeku ba muna tare, amma sedai maganar zuwa gidan su Amira a barta kawai, saboda idan munje yanzu nan gaba zasu iya gano gaskiya, ko kuma bayan munje na nunaku daga baya sai naga iyayena yaya kenan? kawai mu cigaba da addu'a Allah ya bayyana su, kuma Allah ya bayyana muku d'anku, amma kar kuji komai ina tare da ku."

Ahmad da Khadija sun ji farin ciki sosai, domin har ga Allah suna 'kaunar yaron, suna ji a ransu kamar d'ansu ne ya dawo, shiyasa yau suka shiga farin ciki mara misaltuwa, shi kuwa Amir yanda yaga suna farin ciki abin sai ya bashi mamaki da tausayi.

*BAYAN WATA BIYU*

Amir ya warke sarai har sun fara fita da Abbansa, babu inda basa zuwa tare sai d'ad'd'aikun wurare.

Har yanzu Ahmad yana nan da a'kidarsa na 'kin son security na binsa a baya, amma kuma baya yarda Amir ya fita ko nan da can shi kad'ai, koda fita akai dashi ma baya fitowa se dai masu tsaronshi suyi masa komai, duk hanyar da zai sadashi da inda zai ga Amira baya binta kwata-kwata.
Chapter 36 · 0% Book details