Sashe 45
So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nura yace "af tsaya kaji mana, ina zaman zamana, Babana ya b'ullo da zancen aure auren da aka yishi domin wata manufa tashi, ada naso in bijire, amma da naga yarinyar naji ina 'kaunarta, naji ta kwanta min a rai, shiyasa na amince akayi auren, amma aurenmu da ita dashi da babu shi duk d'aya ne, domin har yanzu hoto ne ni a gurinta sunan wai nayi aure ne amma har yanzu ta'ki amincewa dani. "
Amir yace "to meyasa ta'ki amincewa da kai? "
Nura yace "saboda akwai wanda ta fara aure ya mutu amma ba'aga gawarshi ba da yake mahaukaciya ce wai shi take jira, aurenmu ma saida ta gindaya min sharad'i akan sai na yarda in aka ga tsohon mijinta zan saketa ta koma mishi. "
Amir shima ya kwashe mishi da dari, Nura yace "dariya ma kake min? " Amir yace "ramawa nayi, Allah sarki ka bani tausayi, kace kai har yanzu baka shaida kayi aure ba," Nura yace "wallahi kuwa, ni har ta fara bani haushi, amma insha Allah sai burina ya cika a kanta."
Sun dad'e suna hira kamar sun dad'e da sanin juna, daga 'karshe suka yi musayar lamba tare da fad'awa juna sunayensu, sannan suka yi sallama kowannensu ya shiga mota suka bar makarantar.
Koda yaushe haka suke yi, Amir yana riga su Nura zuwa makarantar, amma baya zama cikin motar yanzu, b'oyewa yake saboda kar Amira ta hangoshi, sai ta shiga aji yake fitowa susha hirarsu suyi da matansu sannan suyi sallama su tafi.
Hakan ya jawo shak'uwa me 'karfi a tsakaninsu har takai ga Amir yana ziyartar Nura a wajen aikinshi su sha hira.
Yauma kamar kullum Amir suna zaune a cikin office d'in Nura Amir ya kalli Nura yace "ya kamata mu had'a matanmu su san juna, amma sai ka fara zuwa gidana na gabatar da kai wajen matata tukun. "
Nura yace "a'a ban yarda ba gidana za'a fara zuwa muje ka gaisa da matana, yanzu ma tunda ba abinda kake yi idan mun tashi daga nan kawai sai mu wuce bari ma kaga in kirata in sanar da ita muna da babban ba'ko."
Abinda Amir yake so yaji Nura ya fad'i kenan dama, hakan yasa yai farin ciki da jin haka kuma be yi mishi musu ba.
Nura ya d'auki wayarsa ya kira Amira ya shaida mata cewa anjima zasu taho gida tare da ba'ko ta shirya mishi abubuwan tarba na musamman, to kawai tace sannan ta kashe wayar, ita Amira ada tana sakin jiki dashi har suyi hira kafin ya aureta, amma yanzu haka kawai taji wani irin haushi yake bata, hakan kuma baya rasa nasaba da kishin kanta da take taya Amir.
Sun dad'e suna hira bayan wajen awa biyu suka tashi suka nufi hanyar gidan Nura.
Cikin 'kan'kanin lokaci suka 'karaso gidan, Amir kanshi ya jinjina da yaga gidan domin yasan an narkar da kud'i wajen gina narkeken gida da 'kawata shi.
Fakin sukayi, sannan suka fito, Amir yaja ya tsaya, Nura yace "muje mana, " Amir yace "nasha zaka sanar da ita tukun,? " Nura yace "haba muje mana nace," suka wuce Nura na gaba Amir na baya har suka shiga tangamemen falo, ba kowa a falon sai kayan kallo da suke kunne suke ta aiki.
Nura ya juyo yace wa Amir "bismillah zauna, bari in shiga in kira matar tawa ku gaisa, " yana gama fad'in haka yai shigewarshi ciki, Amir kuwa wani irin kishi yake ji matsananci a duk lokacin da yaji Nura ya kira Amira da matarsa, ji yake kamar ya sha'keshi ya bar duniya.
Be zauna ba, yana tsaye yana jiran ta inda zaiga fitowar Amira, Nura ne dai ya sake fitowa, yace "ya baka zauna ba kuma sai kace wani ba'ko? "
Amir yai dariya sannan ya zauna, Nura dake tsaye yace "gata nan fitowa ku gaisa, sorry dan Allah bari inje in watsa ruwa in fito.
Amir yace "ba damuwa sai ka fito. "
Nura ya koma ciki ba dad'ewa Amira ta fito falon d'auke da sallama a bakinta, hannunta ri'ke da faranti ta ri'ko abubuwan motsa baki, shi kuwa Amir tunda ta fito kallonta kawai yake aikinyi, yau yaga ta rame da yawa ko dan yana ganinta daga nesa ne be fahimci haka ba, kanta na du'ke har ta 'karaso ta ajiye farantin a gabanshi, sannan ta zuba mishi abinci ta zuba lemo shima ta ajiye a gabanshi, tace "ga abinci nan, " ta yun'kura zata tashi taji cikin 'karamar murya Amir yace "Amirata!"
A razane ta d'ago saboda tasan duk duniya mutum d'aya ne tak ke kiranta da wannan sunan.
Wanda take tsammani ne kuwa ta gani a gabanta wato Amir d'inta, zabura tayi ta mi'ke tsaye tana dafe da 'kirji ta bud'e baki zatai magana Amir ya toshe mata baki, sannan yace salon ki tona mana asiri mijinki yaji. "
Amira nan da nan hawaye ya fara wanke mata fuska, cikin kuka tace "Amir meyasa zaka yimin haka? " dama kana raye amma ka nisanta kanka da ni. "
Kuka Amira takeyi sosai na tsananin farin ciki da ganin mahad'in rayuwarta Amir ne yake ta rarrashinta, sai da 'kyar ya samu tai shiru sannan ya zaunar da ita kan kujera, suna zama sai ga Nura ya fito kamar an jeho shi.
Muje zuwa
*🅱K CE😘💋*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (🅱K)*
```(Autar marubuta) ```
SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
(Mamie)
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```
PAGE 190 to 195
Nura yazo ya zauna kan kujera yana kallon Amir dake 'kokarin komawa wajenshi ya zauna yace "ba dai har zaka tafi ba? haba kai ka fara ma kazo gidana kace zaka tafi yanzu."
Amira kuwa idanunta na kan Amir sam ta kasa d'aukesu daga gareshi.
Amir yace "a'a karka damu ina nan har sai kun gaji dani sedai in amarya ce da kanta ta koreni," ya 'karasa maganarshi yana kallon Amira.
Amira tai murmushi me had'e da dariya tana cike da farin cikin sake ganin masoyinta kuma mahad'in rayuwarta, sannan tace "haba dai, wallahi har abada bazan tab'a korarka ba ko a mafarki bana fatan haka."
Nan fa sukaita hira sai can wajen yamma sannan Amir yace zai tafi.
Nura yace ya manta da makullin motarsa bari ya shiga ciki ya d'auko, bayan ya shiga Amir ya kalli Amira yace "yi sauri ki bani lambarki kafin ya fito, Amira ta fad'a mishi ya rubuta, yana cikin saving sai ga Nura ya fito, Amir ya mi'ke sukayi sallama da Amira sannan suka fice daga gidan, Amira kuwa akwai tarin tambayoyi a cikin ranta kuma a zuciyarta tana ji kamar ta ri'keshi ta hana shi tafiya, amma haka ta bar Amir ya wuce ya tafi ba yanda ta iya dole tai ha'kuri, tambayoyin dake ranta kuwa ta bari sai ya kira sai suyi duk maganar da zasu yi.
Suna tafe a mota suna hira, Nura yace "wallahi tunda muke da Amira bata tab'a zama dani haka munyi hira da ita haka ba har naga ha'koranta sai yau, Amir a zuciyarshi yace "to ba dole ba ai duk wanda yace yana 'kaunarta har ya aureta kallo take a duk duniya bata da ma'kiyi sama da shi," ashe Amir be sani ba maganar da yayita a zuciya ta fito fili, kawai ji yayi Nuran yace "nima kallon ma'kiyinta take yimin kenan, kuma meyasa ma ka fad'i haka?"
Amir yace "eh mana saboda kaima ka shaida mutum d'aya tak take so, to wannan dalilin zaisa taji haushinka tunda ka aureta ka 'kara nisantata da masoyinta na farko."
Nura yai murmushi yace "ba zaka gane ba abokina, duk akwai dalilin yin haka, watarana zan sanar dakai, bayan dalilan ni kaina ina son yarinyar, ban tab'a had'uwa da yarinya me kyau da diri irinta ba," habawa yana fad'in haka Amir yaji kamar an saka mishi garwashi a zuciyarshi saboda tsabar jin rad'ad'in maganar Nura, nan da nan kuwa idanunshi sukai ja ya dage iya 'karfinsa ya buga kanshi jikin glass d'in murfin motar, nan da nan kuwa glass d'in da kanshi duk suka fashe, Nura yace "Subhanallah!" ya faka motar sannan ya cigaba da yi mishi sannu, sannan Nura ya sake cewa "meyasa kayi haka Amir?" Amir yace "wallahi ciwo kan yake min, gashi kuma ka 'kara b'ata min rai, ni yanda na d'aukeka kamar d'an'uwa ashe kai ba haka bane, a tunanina damuwarka damuwata ce, kullum se dai kaita ce min akwai dalilin auren matar da kake tare da ita, to menene amfanin fad'amin akwai dalilin tunda baka iya sanar dani, ka sani ko akwai shawarar da zan taimakeka da ita."
Nura yai murmushi, sannan ya dafa kafad'arshi yace "ba haka bane abokina, kayi ha'kuri yanda ka d'aukeni nima haka na d'aukeka amma dan Allah ka ri'ke min sirrina," nan Nura ya kwashe duk wani 'kuduri nasu akan su Amira da Dad d'inta ya fad'a wa Amir, Nura ya cigaba da cewa "amma fa ni ko na samu biyan bu'kata bazan rabu da Amira ba, shi kuma Dad ya dage indai muna son dukiyarsu muna son zama lafiya dole sai mun kawar da su.
Bayyana tashin hankalin da Amir ma ya shiga ai baya misaltuwa, amma sai yai saurin b'oye razanarshi, sannan yai murmushi yace "gaskiya Dad d'inka yayi tunani, kaga fa in kuka samu yanda kuke so zaka iya mallakar koma wace macece a rayuwa, bayan haka kome kaga dama zakayi domin kud'i sune abokan rayuwa."
Nura ya she'ke da dariya, sannan yace "ashe kaima irin ra'ayinmu d'aya shine na b'ata lokaci wajen sanar dakai tun tuni."
Haka dai suka cigaba da tafiya suna hirar su, abinda yasa Amir ya biye mishi yasan in ba haka yayi ba bazai cigaba da samun labarin komai daga wajenshi ba.
Suna cikin hira wayar Nura tai 'kara, ya cewa Amir ya d'an d'auka ya cewa koma wanene yana tu'ki zai kira later.
Amir na d'agawa kafin yace komai sai yaji mahaifin Nura yana fad'in "Nura ko me kake ka bari kazo, na samu labarin wai anga Amir a garin nan, maza kazo muyi shawarar abinda ya dace muyi a gaba," yana gama fad'in haka ya katse kiran.