← Book details So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 54

Sashe 53

So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
```(Mamie)```

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```🤜🤛

*~Safiya Bello K*

*Wannan shafin kyauta ne a gareki sister Safiya Bello saboda soyayyarki gareni da kuma dukkanin littafaina, dan haka nima dole na baki tukuicin 'kauna, wannan page d'in naki ne ke d'aya kiyi yanda kikaso dashi,😍😘💋 i love you over over soyayyar sojoji😂😂*

*YAN NIGERIA🗣🗣🗣🗣🗣*

*DAN GIRMAN ALLAH MU TAIMAKI KANMU MU FITO RANAR ZAB'E DUK MU DANGWALAWA BABA BUHARI YA CIGABA DA AIKI DAGA INDA YA TSAYA, KARMU BAWA AZZALUMAI DAMAR SAKE MULKARMU BILLAHIL AZEEM IN HAKAN TA FARU ABINDA SUKA FARU SHEKARUN BAYA ZAMANIN MULKIN MUGAYE SU ZASU CIGABA DA FARUWA, KARKI BARI AI ASARAR 'KURI'ARKI KI AJIYE KATIN ZAB'ENKI A GIDA KICE KE BAZAKIY ZAB'E BA, WANNAN BA DAI-DAI BANE, AI DUK ME KATIN ZAB'E KAWAI YA FITO YA DANGWALA, IN KUMA KIKA FITO KIKA ZAB'I MUGU WANNAN SHIMA BA DAI-DAI BANE, KUMA YIN HAKAN ASARA CE BABBA, KINYI ASARAR LOKACINKI DA KUMA 'KURI'ARKI, WALLAHI ALLAH MU DA KANMU MUNGA CANJI A RAYUWA A SHEKARUN NAN DA BABA YAYI YANA MULKI, HMMMM SAURAN JIN DA'DIN MA DA KWANCIYAR HANKALI YANA GABA INSHA ALLAH, SABODA HAKA IDAN KA SAKE KA BAIWA MUGAYE MASU BURIN CUTA K'URI'ARKA TO WALLAHI KANKA KA CUTA, MUDAI MUNCE SAI BABA BUHARI INSHA ALLAH BAZAMU TAB'A GAJIYA DA MULKINSA BA HAR ABADA, KARMU SAKE MU BAR HASKE MU TSUNDUMA A CIKIN DUHU*

🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚

PAGE 225 to 230

Wannan matar ce ta kalli Abba Ahmad ta fara magana tace "sannunku da zuwa, munji dad'in ganinku sosai wallahi, ni sunana Rabi'atu kuma nice matar Salisu, wannan d'ana ne, ta nuna Insp Yahya wanda kanshi ke sunkuye yaketa faman had'a zufa, sannan ta cigaba da cewa yana da 'kanni maza guda biyu, a ta'kaice dai 'ya'yanmu uku kuma duk maza ne, biyu Ishaq da takwaranka Ahmad wanda muke kira da Baba 'karami suna 'kasar waje suna karatu, gaskiya munji dad'in had'uwa daku sannunku da zuwa, sedai abinda ban gane ba shine naga Amir ya sha'ke Yahya meyasa, kuma me ya faru?"

Ahmad yai murmushi, sannan ya bata labarin duk irin abinda ya faru a baya.

Banda harara da tsananin tsana babu abinda Amir da Amira suke yi akan Insp Yahya, shi Amir ma haushi yake ji a zuciyarshi yana fad'in Allah ya sawwa'ke mutum irinka me halin karnuka ya zama d'an uwana.

Amir yace "banyi mamakin abubuwan da ka aikata ba duba da irin gidan da ka fito a cikinsa," Abba ya daka wa Amir tsawa, abinda bai tab'a yi mishi ba, yace "ka kiyaye harshenka kuma kasan me zaka fad'i akan d'an uwana."

Abba Ahmad ya kalli Mahaifiyarsu Insp Yahya yace "ni yanzu duk ba wannan ba, ina d'an uwana Salisu yake?"

Nan da nan idanun Rabi suka ciko da hawaye, tace " labarin yayanka ba dad'in ji, domin yana kwance rai a hannun Allah, bambancin shi da matacce kawai shi yana da rai har yanzu."

Abba ya hau salati tare da mi'kewa tsaye yana fad'in "yanzu yana ina?"

Mahaifiyar su Yahya tace "yana cikin d'akinshi a kwance."

Cikin sauri Abba ya nufi d'akin da ta nuna mishi da hannu, su Amir suma suna biye dashi a baya.

Kwance suka tarar da Salisu ya tsomare ya rame kamar me ciwon 'kanjamau, idan ma ba ka sanshi ba mugun sani in ka ganshi zaka rantse ba shi bane saboda rama da kuma canjawa da halittarsa tayi.

Babu inda yake motsi a jikinshi, kuka sosai Abba keyi, suma kansu su Amir kukan sukeyi domin duk mai imani in yaga halinda Salisu ke ciki sai yayi kuka mara iyaka.

Abba cikin kuka yace "yaya kaine a cikin irin wannan halin," ya sake fashewa da kuka, su Amir kuwa tsoron Allah ne ya 'kara ziyartarsu, ganin gadai dukiyar da yake kwad'ayin samu ya tara kamar hauka amma babu halin morarsu, tunda gashi nan kwance yana tsakanin rayuwa da mutuwa sedai a juyashi a kwantar a tayar kamar gawa baya iya komai ko motsi baya yi.

Abba ya kalli matar yayan nashi yace "yanzu saboda Allah yana cikin irin wannan halin kuma kuka barshi a gida kuka zuba mishi ido a haka ba'a kaishi asibiti ba?"

Mahaifiyar su Yahya tace "wallahi babu irin asibitin da bamu jeba har fita dashi 'kasashen waje munyi amma ina jikin ya'ki dad'i har yanzu."

Abba yace "gaskiya bazan barshi a irin wannan halin ba in cigaba da kallonshi, zan fita dashi India gobe in Allah ya kaimu, yau zanyi mana tanadin komai ni dashi."

Washe gari jikin Salisu ya 'kara tsananta ko kafin su bar gidan yace ga garinku nan, Allah ya karb'i abinshi, shima yabi iyayenshi da ya kashe, yaje yai zaman jiran ranar hisabi.

Sai da akayi arba'in sannan kowa ya watse, har su Dad ma anan suka zauna akayi zaman makoki dasu.

Abba Ahmad yaci kuka kamar me, be so d'an uwanshi ya yi irin wannan rayuwar ba, kuma be so ya mutu a haka ba, yaso sai ya nemi gafara mai yawa wajen mahalicci, wad'annan abubuwan sune idan ya tuno suke sakashi kuka.

Rayuwa kenan, abinda yake yi mawa wato dukiya da jin dad'in duniya duk ya barsu a inda ya tarar dasu, bayan rasuwar tashi ne ma suke jin labarin wai ya dad'e yana jinya kafin ma ta kwantar dashi yana ciwon sama - sama har ta kai ga yi mishi kwaf d'aya, ance yaita kuka yana surutai marasa kan gado dan shi beyi tunanin Abba Ahmad yana raye ba.

To dama dai 'karshen kowa kenan 'kabari, sedai duk wanda yai me kyau shi yake murna da ita, wanda yai mara kyau kuma kuka yake mara iyaka domin tanadin da Allah yai mishi na azabobi iri-iri.

Bayan arba'in aka raba gado yanda addinin musulunci ya shar'anta aka baiwa kowa nashi, sannan Abba yace zai tafi da su Ishaq da Baba 'karami wanda yaci sunan Abba, idan sun dawo daga waje karatu zai ri'kesu a wajenshi, sannan zai cigaba da kulawa da hidimomin karatun nasu kafin su dawo.

Shi kuwa Insp Yahya da yake tun bakwai shi ya koma kano, to hakan yasa Abba ya barwa Mahaifiyarsu sa'ko akan in yazo tace yaje yana son ganinshi.

Kwance tashi ba wuya yau wata uku kenan da rasuwar Salisu, tuni yaran Salisun suka koma hannun Abba da zama a Abuja tunda dama Amir ya zama d'an Dad.

Duk wani gata yana basu wanda ko shi ya haifesu sai haka.

Bayan sati d'aya Abba ya zowa da su Dad albishir d'in ya gina musu gida kusa da juna su hud'u harda na su Amira a Abuja dan haka zasu koma can da zama gaba d'aya.

Haka kuwa akayi suka koma Abuja da zama gaba d'ayansu.

Bayan komawarsu da sati d'aya Amir da Amira suna zaune a sabon gidansu sai suka ji sallama suka amsa tare da bada izinin shigowa.

Insp Yahya ne ya shigo kanshi sunkuye ya shigo ya 'karaso har kusa da Amir, maimakon ya zauna kan kujera sai ya tsugunna a 'kasa kanshi a sunkuye ya fashe da kuka tare da cewa "dan Allah yaya Amir ka yafemin dukkanin abinda nai maka, dan girman Allah, wallahi ina cike da nadama mara iyaka ban tab'a tunanin kai d'an uwana bane, nayi takaicin irin abubuwan da nai muku, dan Allah Aunty Amira ku yafemin," yana kai aya a zancensa ya sake fashewa da kuka.

Amir ya d'agoshi tare da zaunar dashi, sannan yace "wallahi na yafe maka duniya da lahira, kuma naji dad'i da ka gane gaskiya ka kuma nemi afuwa, yanzu banda kamarku duk duniya, fatana dai Allah ya 'kara had'e kawunanmu."

Soyayya ce mai 'karfi ta 'kullu tsakanin Insp Yahya da Aneesa 'kawar Amira, ba tare da b'ata lokaci ba aka sha biki ango da amarya suka tare gida d'aya da su Amir, domin dama Amir ya rantse gida d'aya zai zauna da 'yan uwansa idan sun yi aure.

Su kuma Ishaq da Baba 'karami sun kammala karatunsu aiki suke yi sosai a cikin kamfanonin Abba.

*BAYAN SHEKARA 'DAYA*

Amir ne ya fito daga d'aki cikin sauri ya d'aga labule yana fad'in "fito a hankali," Amira na gani ta fito da 'katon cikinta tana tafiya da 'kyar, har zuwa kan kujera ta zauna.

Amir ya kalleta yace "sannu Amirata, wallahi tausayinki nake ji, kuma Allah Allah nake inga kin haihu ko ma huta da wannan laulayin da muketa fama dashi ni dake."

Amira tai dariya, sannan tace "wato mu biyu ma muke na'kudar ko," Amir yace "eh mana in aka bincika ma wallahi na fiki shan wahala saboda ni nake d'awainiya dake kuma duk ciwon da kikaji sai na jishi a zuciyata, kinga ke kina jin ciwon a jiki ni kuma ina jinshi a raina kuma ciwon dake cin rai yafi azabtarwa."

Haka dai ya zauna yanata fad'a mata dad'ad'an kalamai masu dad'i itama tana mayar masa, kaji masoyin gaske, wasu mazan da matansu sun sami ciki daina kulawa dasu sukeyi, wasu ma 'kyamarsu sukeyi, amma shi tunda ta samu ba inda yake zuwa koda yaushe suna tare yana kula da abarshi har cikin ya tsufa.

Yau litinin zaune suke a falo suna kallon labarai na 'kasar waje.

Kawai sai suka ga an nuno gawarwakin Baban Nura da shi kanshi Nuran ana sanarwa cewa sun mutu sakamakon harbesu da 'yan fashi sukayi, bayan sun yashe dukiyarsu kuma suka harbesu, wai ana cigiyar 'yan uwansu da suzo su d'ebi gawarwakin.

Amir ya kalli Amira yace "dan Allah duba ki gani," Amira tace "na gani menene abin mamakin to, ai duk wanda yai dakyau to zaiga dakyau wanda yai akasin hakan kuwa sakamakonsa ba zaiyi kyau ba."

Amir ya d'auko wayarshi ya kira Dad ko gaisawa basuyi ba yace ya kunna tv ya gani.

Dad yace "na gani Amir na gansu yanzu haka shi nake kallo, duniya ba'a bakin komai take ba."

Bayan sun gama waya Amir ya kira Abba shima ya fad'a mishi yace ai yanzu suka gama waya da Dad ya sanar dashi.

Bayan kwana biyu da faruwar hakan ashe Dad ya tura an kwaso mishi gawar su Baba da Nura, sudai su Amir da Abba kawai yace musu su shirya zasuje sallar jana'iza nan 'kofar gida.
Chapter 53 · 0% Book details