Sashe 6
So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan Alk'ali ya kammala rubutun shi sai ya baiwa Barista Muhammad Auwal damar yi wa Abdul tambayoyi, ya mik'e tare da zuwa gaban Abdul yace " malam Abdul fad'a ya had'aku da Sadeeq a kan Amira sanadin rungumarta da kayi kana cikin maye har kun yi cacar baki da shi ko baku yi ba?" Abdul yace " eh mun yi," Barista Muhammad yace " wane furuci kuka fad'awa juna a ranar?" Abdul yace " Sadeeq ne ya ce min sai ya kashe ni idan na k'ara tab'a Amira, ni kuma b'acin rai yasa na mayar mishi da martani kan cewa nima sai na kashe shi," Barista Muhammad yace " ok shine ya baka damar kashe shi?"
Objection my lord abinda Aisha ta fad'i kenan bayan ta mik'e, tace ya kamata Barista ya san irin maganar da zai rik'a fad'a, har yanzu ana kan bincike ne ba'a tabbatar da shine ya yi ba ko ba shi bane nagode," Barista ya kalli Alk'ali yace ranka ya dad'e abinda yasa nake mishi tambayar nan saboda akwai wasu hujjoji na ne wad'anda suka sa dole sai na yi mishi wannan tambayar."
Alk'ali yace " Barista Aisha k'orafi be karb'u ba, Barista Muhammad kana iya cigaba da yi mishi tambayoyin."
Barista Muhammad yace " muna saurarenka Abdul nace wannan b'acin ran yasa ka kashe shi saboda kar ya zama barazana a soyayyarku da Amira?" Abdul yace " wallahi ba ni na kashe shi ba," Barista yace " da kyau dama amsarka nake jira," Barista ya dawo wajen zaman shi ya d'auko wuk'ar da aka kashe Sadeeq da ita tare da takardu, ya nuna wa Alk'ali tare da fad'in " ranka ya dad'e wannan wuk'ar da ita aka yi amfani wajen kashe Sadeeq bayan kokawar da suka sha dashi wajen ceton ransa da yai k'ok'arin yi, wannan takardar kuwa hotunan d'akin shi Sadeeq d'in ne wanda 'yan sanda suka d'auka ranar da abun ya faru, d'aya takardar kuwa ta likita ce wadda ya tabbatar mana da cewa shaidar hannun Abdul ne a kan wuk'ar," bayan ya gama fad'i sannan ya bayar aka mik'awa Alk'ali domin ya nazarce su, sannan ya sake cewa " kafin kisan bincike ya nuna cewa a daren da abun zai faru Sadeeq ya shawu kuma hakan ne ya baiwa Abdul damar kashe shi duk da kuwa yana cikin maye amma sai da yai k'ok'arin ceton ranshi, amma ya mamaye shi ya kashe shi, akwai d'aliban da suka tabbatar mana da Sadeeq ya shawu a ranar, kuma sunga dawowar shi cikin gida, a yayin da suka hango wani wanda basu ga fuskar shi ba kuma yana binsa a baya sun d'auka tare suke shiyasa a lokacin basu kawo komai ba," nan dai ya gabatar da su d'aya bayan d'aya, suka yi rantsuwa sannan suka fad'i iya abinda suka gani a daren ranar, bayan Alk'ali ya gama 'yan rubuce rubucensa sai ya d'ago ya kalle su yace " kotu ta ji duk bayanai da hujjar kowa, sai rana ita yau zamu dawo domin jin hukuncin da kotu ta zartar.
Muje zuwa
*🅱K CE*😘💋
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (🅱K)*
```(Autar marubuta)```
SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
_(Mamie)_
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```
PAGE 30 to 35
Yau litinin, kotu cike take mak'il da mutane, suna sauraren hukuncin da Alk'ali zai yanke a kan Abdul.
Bayan rubuce rubuce da ya yi, sannan ya d'ago ya kalli Barista Aisha Isa yace " kinada wasu tambayoyin ne ko shaidu da zaki gabatar?" Aisha ta mik'e duk ta sare saboda bata da hujjar da zata kare Abdul da ita, tace " a'a ya mai shari'a banda abun cewa," Alk'ali ya sake kallon inda Barista Muhammad yake yace ko kana da wata shaidar ko k'arin tambayoyi da zaka gabatar?" Barista Muhammad yace " a'a ranka ya dad'e."
Bayan Alk'ali yai rubutu na wasu lokuta sannan ya d'ago kai yace " bayan sauraren bayanai da muka yi daga gun lauyoyi, tare da hujjojin da aka gabatar, kotu ta gamsu da cewa Abdul shine yai wannan kisan, dan haka ga hukuncin shi kamar haka, kamar yanda muka sani ne cewa wanda ya kashe rai shima hukuncin shi kisa ne, dan haka kotu ta yanke wa Abdul hukuncin kisa ta hanyar rataya, wanda ake k'ara yana da damar sake shigar da k'ara a wata kotun kafin nan da wata uku, ana gama fad'in haka Abdul ya fad'i k'asa a sume, Amira tayo kanshi da gudu tana kuka zata d'aga shi aka dakatar da ita, su preety ne suka janyeta suka fita daga wajen kowannen su kuka yake zuciyoyin su duk ba dad'i.
Surutai Amira tai ta yi musu cikin mota tamkar tab'ab'b'iya, tana fad'in na zama silar mutuwar mutum biyu, yanzu kenan duk wanda ya rab'eni kashe shi za'a rik'a yi kenan, na hak'ura da karatun zan kira Dad yazo ya d'auke ni in koma gida, tana kaiwa nan a zancenta sai ta k'ara fashewa da kuka.
Bayan sati d'aya da mutuwar Abdul sai aka baiwa kowane d'alibi damar tafiya gida saboda samun natsuwa kan abinda ya faru a cikin makarantar, bayan wata d'aya sai su dawo.
Hakan yasa Amira taji dad'i sosai domin dama hankalinta ba'a kwance yake ba, ta tarkata inata inata zata tafi, tafiyar da ta k'udurta a ranta in ta tafi ta tafi kenan bata fatan ta sake ganin ta dawo makarantar ko a mafarki, ace duk wad'anda ta shak'u da su ana ta kashe su, gwara ta tafi kafin a k'arar da su gaba d'aya.
Bayan ta gama had'a kayan ta jawo jakarta tare da juyowa zata fita sai taga Amir tsaye bakin k'ofa ya jingina jikin k'ofar tare da hard'e hannayensa yana kallonta, idanuwansa kuma suna fitar da hawaye.
Amira ta ajiye jakar cikin sauri ta nufo shi, tana tare da dafa kafad'un shi tana tambayar shi lafiya me ya faru, ganin yanda ta tayar da hankalinta yasa ya sassauta da kukan, ya kalleta yace " kina sauri da zumud'in tafiya ki barmu ko? Amira nasan abinda kike shirin yi, kina son in kin tafi ba zaki k'ara dawowa ba ko? to kafin kiy wannan tunanin kin yi tunanin halin da zan shiga idan bama tare da juna, kinsan yanda na shak'u dake kuwa, Amira adalcinki kenan ki k'aurace mana, ki tafi ki barmu, sai ya fashe da kuka, kuka sosai yake yi, ya durk'usa tare da saka gwiwoyinsa a k'asa tare da had'a hannayen sa ya cigaba da cewa dan Allah karki tafi zuciyata zata cutu idan kikai nesa da ita, nai miki alk'awarin kasancewa tare dake da kuma saka ki farin ciki da walwala, ke nai miki alk'awarin mantar da ke damuwar da kike cikinta ma a yanzu amma nidai rok'ona kawai gareki ki zauna tare da ni."
Yana rok'onta yana kuka, Amira ta k'araso wajen shi jikinta a sanyaye tare da saka hannayenta biyu ta mik'ar da shi tsaye, sannan tace " Amir ina jin tsoron zamana a tare da ku, saboda kar kuma a kashe ku, ni mamaki ma ka bani, kai da zakai farin cikin rabuwa da mutum irina sai ka rik'a rok'on cigaba da rayuwarmu a tare, baka tsoron a kasheka ne?"
Amir yace " to menene dan na mutu saboda ke, bazan damu ba domin ina da masaniyar dole wata rana zan tafi, abun damuwar kawai ke a kashe ki, na rantse da Allah da kuwa na k'arar da mutanen duniyar nan gaba d'aya," Amira tace " har yaushe mukai shak'uwar da kake jin irin haka a kaina?" Amir yace " hmmm kece dai baki sani ba, amma zuciyata ta dad'e da shak'uwa da taki, kuma bana jin tsoro ko shakka ko targabar mutuwa ta sanadinki."
Amira tai ajiyar zuciya, sannan tai shiru tana tunanin yiwuwar tsayawar ta-ta, ganin haka yasa ya k'ara had'a hannayensa yana rok'onta, k'ok'arin sake kai kwiwoyinsa kasa yake yi tace " shikenan na ji zan tsaya, amma ya akai ka san cewa inada k'udurin idan na tafi ba zan sake dawowa ba?"
Amir yace " saboda na san ko wanene hakan ta faru dashi wannan hukuncin zai yanke, amma banda ni," Amira tace meyasa banda kai?" Amir yace " saboda wad'anda nake tare da su zasu ji ba dad'i, babu inda zan matsa saboda su, a koda yaushe yana da kyau mu rik'a tunanin halin da masoyanmu zasu shiga a duk lokacin da suka rasa mu," sun dad'e suna tattaunawa sannan ya sata ta maida jakarta, har yamma suna tare ya k'i yarda ya matsa ko nan da can saboda gani yake kamar yana tafiya zata gudu ne, agogo ya kalla yaga hud'u ta yi, sannan ya sake maida kallon shi gareta, yace " bari na je gida nai wanka na canza kaya in dawo, amma dan Allah kiy mini alk'awarin ba zaki gudu ba bayan na tafi dan Allah."
Yanayin yanda yai maganar ya matuk'ar baiwa Amira dariya, ta kalle shi tace " ka kwantar da hankalinka ba inda zan je na yi maka alk'awari, " Amir yace " to sai na dawo kema ki shirya idan na dawo fita zamu yi," suka yi sallama ya tafi.
Amir be d'auki wani dogon lokaci ba ya iso gida ya faka motar shi sannan ya fito ya shige ciki, wanka ya shiga ya fito sannan ya shirya cikin k'ananan kaya bak'ar tshet da jeans ya yi kyau sosai, ya kalli kanshi ya k'ara kallo, sannan ya fesa turare ya d'auki makullin motarsa ya fito.
Koda ya k'araso itama Amira ta shirya, ya kalleta bayan ya gama kallonta son ranshi sannan yace mata "muje koh," Amira tace "to suka fito suka tafi.
Wani katafaren shago suka tafi na saida abubuwan more rayuwa, ya sakata ta kwashi duk abinda take so amma ta k'i, sai ya zage ya shiga lodar mata duk abinda yake ganin zai yi dai-dai da ita, ganin yanata abu d'aya kuma baida niyyar dainawa yasa ta dakatar dashi haka, suka je aka lissafa Amir ya biya kud'in.