Sashe 41
So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
_Zaune nake gaban ogana wato mahaifin matata Khadija, ina jiran 'karin bayani dangane da kiran da yai min, Alhaji ya kalleni yace "Ahmad abinda yasa na kiraka shine 'yan uwana da suke kano da Aminaina ke so in yi takarar gwamnan jihar kano, to kaga idan nace zan amince dole sai na koma can garin da zama, kuma kadarorina dake nan garin babu mai kula dasu, a ta'kaice dai gaskiya banda sha'awar yin siyasa, kuma bana so kujerar nan ta shiga hannun azzalumai, Ahmad kai na talakawa ne me burin taimaka musu a koda yaushe, wannan dama ce ka samu domin 'kara kusanto dasu zuwa gareka, amma me kace a kai, saboda sun dameni sunce su zasu yi mini komai, so nake kaje a madadina," nai shiru ina nazari kan wannan damar da na samu, sai nace mishi ya d'an bani lokaci nai tunani, bayan munyi sallama dashi na koma gida naita nazari zuciyata na bani cewa in amince dama ce wannan na samu na taimakon talakawa da jahata kanta da kuma d'an uwana shima in samar mishi da aikin yi, banyi wata-wata ba na kira iyayena a waya na sanar dasu halin da ake ciki, da farko basu amince ba amma daga baya da nai musu bayani da kyakkyawan 'kudurina akai sai sukayi na'am tare da goyamin baya akai, haka muka koma kano da zama lokacin Khadija nada tsohon cikin yayanka Ammar, mahaifin Khadija ya had'ani da aminanshi aka fara gudanar da maganar zab'e ranga-ranga, kuma cikin yardar Allah nan da nan na samu karb'uwa gurin jama'ar kano, da zab'e yazo Allah ya bani damar lashe zab'en, anan muka cigaba da zama har Allah ya sauki matata Khadija lafiya ta haifi yaronta namiji yaci sunan Ammar, ba yabon kai ba nayi wa 'kasa aiki ba kad'an ba, 'kauyenmu kuwa saida na maida shi ya dawo kamar birni, gidan iyayena ma na gyara musu shi nai musu gangariyan plat, yayana kuwa tuni na dawo dashi kusa dani a kano muna gudanar da komai tare, koda wani zab'en ya zagayo nace to gaskiya ni burina ya cika tunda Alhamdulillah dai-dai gwargwado talakawa sun amfana, na d'auko wani bawan Allah kuma abokina wanda yake takarar kansila ada sunanshi Alhaji Ahmad Tukur, shi na barwa kujerata ya hau kuma cikin ikon Allah ya samu kujerar gwamnan jahar kano, ni kuma daga lokacin na tattara na dawo gida kontagora, tarin kud'in da na mallaka da kuma kadarorina na cigaba da juya dukiyata tare da kula da kadarorinsa, duk da dai gabad'ayan kadarorina na kano na siyar ne na sake siyan wasu a Abuja da kuma kontagora sai nabar 'yan kad'an a kano irinsu gidajena na saka 'yan haya a can, lokacin da na dawo tare muka dawo da yayana ya zama kamar bashi ba yai kyau saboda kud'i sun zauna, ya tara dukiya ba kad'an ba shima, amma duk da haka be bar mummunan 'kudurinsa a kaina ba, kuma koda wasa be tab'a nuna min mugun nufinsa a kaina ba, bayan kwana biyu muna zaune da iyayena muna magana dasu nake ce musu Alhamdulillah yanzu kam burina ya cika tunda talakawan garin nan kowa yanzu yana da abun yi, bama na garin nan kad'ai ba, sannan nima kud'ina Allah ya sa musu albarka yanzu haka inada biliyoyin kud'i a account d'ina, banda kadarorin da na mallaka, nan da nan Sunusi abun ya 'kara 'kular dashi, tunani ya fara yi akan abinda ya kamata ya yi domin yaga ya mallaki dukiyar d'an uwansa ta dawo gareshi, kuma har zuwa yanzu ban daina raba dukiyata ina baiwa yayana Sunusi ba, a wannan rabin nake kula da iyayena da shi kanshi da kuma iyalina har na taimaki wasu ma a ciki, amma duk da haka dukiyata tafi tashi habbaka sosai ma kuwa, a lokacin ne kuma ya fara neman aure ba b'ata lokaci aka sha biki matarshi ta tare a kusa da gidana da na gina mana ni da shi, Sunusi fa ya samu dukiya sedai rashin godiyar Allah yasa yake hangen tawa, sedai ban tab'a sa mishi ido akan dukiyarsa ba balle insan yanda yake tafiyar da ita dan zai iya cewa saboda ni nake bashi nake yi mishi haka, dama already inada gida a kontagora nan muke zaune da iyayena, mun dawo babu dad'ewa Khadija ta sake haihuwa ta haifoka na sa maka suna Bilal, kamarku da Ammar har ta b'aci, ita kuma matar Sunusi tana da tsohon ciki a lokacin kana da wata goma sha uku a lokacin ban tab'a mantawa da wannan ranar, ranar Litinin cikin tsakar dare muna bacci yayana ya buga mana gida cikin tashin hankali muka bud'e yake shaida mana mummunan labari cewa iyayenmu sun mutu 'yan fashi ne suka shigo gidan nemana da suka 'ki nuna inda nake sai suka kashe su, mutuwar iyayenmu ya razanar da ni sosai har wasu sukaita cece kuce akan Sunusi ne ya kashe su in ba haka ba meyasa shi ko rauni ba'a ji mishi ba bayan yana cikin gidan, koda wannan furucin yaje kunnen Sunusi sai yace ai shi da yaji motsinsu be fito ba yana bacci yaji hayaniya ya tashi koda ya bud'e 'kofa har an kashe su shi yasa be fito ba, ni dai ban tab'a zargin d'an uwana ba ko kad'an, bayan wata shida da rasuwarsu wata rana muna kwance a cikin gida da dare muna bacci sai muka ji haurowar mutane cikin gidan d'aya bayan d'aya, ni na fara farkawa, koda na bud'e idanu sai na le'ka hango mutane nayi sun kai su goma sha biyar dukkaninsu ri'ke da manya manyan makamai, abinda ya bani mamaki da tsoro shine ganin Sunusi a cikinsu shima ri'ke da nashi makamin, cikin sauri na tashi Khadija nace ta tashi maza mu tafi, ta d'aukeka a hannunta tana nunamin Ammar nace taje zan d'auko shi na nuna mata wata 'kofa ta baya nace ta fita tanan, suna fita na du'ka zan d'auko d'an uwanka sai ga su Sunusi sun shigo su biyu shi da wani, Sunusi ya buga min wu'ka a hannu, a lokacin Ammar ya tashi yana ta kuka sannan Sunusi ya yanki Ammar da wu'kar nan ina gani, har gobe bazan manta da mutuwar yarona Ammar ba, ganin haka yasa nai wani 'kara tare da yin kukan kura nai kansu na daddoke su na d'auki Ammar a kafad'a na bi ta wannan 'kofar muka fice kuma na rufeta ta baya, na sami su Khadija a tsaye suna jirana nace musu muje, gudu muke, har muka 'karaso bakin mota, zamu shiga kenan muka hangosu sun kusa cin mana, sai muka yanki daji da gudu, muna cikin tafiya Khadija sai kuka take tana kallon Ammar mi'ka mata shi nayi na karb'eka daga hannunta, muna cikin gudu muka ga sun tare gabanmu da bayanmu, gefe kuma daji ne d'od'ar, jefomin wata goora sukai ta tad'iyeni na fad'i, sai na kalli Khadija nace ta shiga cikin jejin nan ita da Ammar su b'uya, Khadija tace ni kuma fa ba zata tafi ta barni anan ba, nace karta damu 'yan sanda suna hanya na kirasu kafin mu fito, ta juya da gudu ta shiga inda na nuna mata, tana tafiya suka zo suka kewaye ni ina ri'ke da Bilal, Sunusi ne ya 'karaso har inda nake ya du'ka kusa da ni, sannan yace "malam Ahmad kenan, kana tunanin duk 'kaunar da nake nuna maka ta gaske ce, to bari kaji tun muna yara na tsaneka tsana me tsanani saboda fifitaka da iyayenmu suke, kuma sai ka fini ilimi ka fini d'aukaka a rayuwa wanda abun ya dad'e yana damuna a rai, kawai nayi shiru ne saboda banda komai ko nace zan d'auki mataki ko na kawar dakai banda kud'in da zan biya masu tayani yin wannan aikin, nine babba amma maganarka ake ji ba tawa ba, na dad'e ina jin ciwon d'aukakar da ka samu a rayuwa, babban abunda baka saniba shine, 'kaunar da iyayenmu suke nuna maka da kuma rawar jikin da suke a kanka yasa suma kansu na tsanesu, abinda yasa na kawar dasu kuwa saboda sunji lokacin da nake waya ina magana da abokaina kan yanda zamu kawar da kai, yanzu kaima zan gama da kai, abinda yasa zan kasheka a yanzu shine saboda ina so dukkanin dukiyarka da kadarorinka su zama nawa kaga ka hutar dani ma tunda rabin dukiyoyin nawa duk sunana ka saka a jiki be dace in taso cikin talauci kuma in mutu ban dangwali dad'in arzi'ki ba," kasa cewa komai nayi saboda tsabar mamaki, hawaye ne kawai suke ta wanke fuskata na kalle shi nace "yanzu dama akan abin duniya kake neman rayuwarmu yaya, meyasa baka nuna min dukiyata kake so ba tun tuni da wallahi ko zan yi yawo ba ko sisi ni mai iya tattarata duka ne in baka, saboda kai shaida ne akan irin 'kaunar da nake maka ban tab'a tsammanin irin wannan sakayyar daga gareka ba Yaya, kayi ha'kuri karka kasheni, wallahi nafi 'kaunar cigaba da rayuwa tare da kai, na baka dukkanin dukiyata, bana sonta ni kai kad'ai nake so," Sunusi ko gezau be yi ba ya kalli wani wanda ke gefen damanshi yace "Makau d'auke min yaron nan daga jikinshi," Makau yayi-yayi ya 'kwaci yaron nan daga hannuna ya kasa, koda Sunusi yaga haka sai ya d'aga wu'kar hannunshi ya luma min a ciki, a lokacin ne suka samu damar 'kwaceka daga hannuna sun juya zasu bi matata su kasheta itama sai suka ji 'karar motar jami'ai, hakan yasa dukkaninsu suka gudu da kai a hannunsu, koda 'yan sandan nan suka 'karaso inda nake da'kyar na nuna musu inda Khadija ta b'uya nace "Kha di ja na can," ina gama fad'in haka na suma a hannun d'aya daga cikin 'yan sandan, saida nai sati uku a asibiti sannan na dawo cikin hayyacina, sai a lokacin ma ni na san cewa a Abuja muke, ashe tun washe garin ranar da abun ya faru Khadija tai waya da wayar d'aya daga cikin 'yan sandan ta sanar da mahaifinta komai ya turo aka kwashemu dukkanmu aka kaimu Abuja, Ammar kuwa tun kafin na farfad'o aka sallaceshi aka kaishi makwancinshi, kai kuwa bamu san inda kake ba bamu san a wane hali kake ciki ba domin da kai suka tafi a hannunsu, daga wannan lokacin ban 'kara komawa garin ba, bayan wasu shekaru abubuwa da dama sun faru ciki kuwa harda kamuwar mahaifiyarka da ciwon zuciya me tsanani sanadin b'atanka gwara ammar munsan mutuwa yayi mun rasashi kai kuwa a kullum mun kasa cire rai da ganinka, sannan na dawo da dukkanin harkokina nan garin kano ashe alkhairi ne babba dawowana nan d'in, ashe Allah kad'ai yasan abinda ya b'oye sai yanzu yai nufin bayyanuwarsa Allah mun gode maka, to kaji irin abubuwan da suka faru dani a rayuwa My Son, ashe duk kaunar da d'an uwana ke nuna min so yake ya gama samun komai daga gareni ya kasheni, na yarda da d'an uwana fiye da kowa kai fiye da kaina ma, ban tab'a tunanin ko dabba zai iya kashewa ba, nafi jin ciwon rabani da iyayena da yayi fiye da komai._