← Book details So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 54

Sashe 51

So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abba ne ya kalli Dad yace "abokina ya bayan saduwa?" shiru ba amsa kuka kawai yake yi, Abba yai murmushi tare da girgiza kai, sannan yace "wallahi duk wad'annan abubuwan da suka faru ban ri'kesu a raina ba, illah dai abu biyu da kayi a lokacin da kake mulkar 'kasa wanda banji dad'insa ba, kuma shine ma zan iya cewa dalilin da yasa na sake tsayawa zab'e a karo na biyu kuma Allah ya sake bani nasara na sake zama matsayin shugaban 'kasan da nake kai a yanzu, saboda mutane sun koka lokacin mulkinka wanda ni sam banyi tsammanin hakan daga gareka ba, shugabanci fa bawai kaci kasha bane kuma ka gina kanka da iyalenka, a'a amana ne ake d'auka a baka na kula da dukiyar talakawa tare da bincikar matsalolinsu da magance musu, amma yanzu shugabbani ba abinda suka sani sai gina kansu da 'yan'uwansu da iyalensu, wanda su basu sani ba yin hakan da suke kashe kansu suke domin mulki babban abune wanda ya tafiyar dashi dai-dai ya dace, wanda yayi son ranshi ya cuci al'umma kuma ya cuci kanshi kuma ya tab'e duniya da lahira, sannan bayan haka kana 'kyamar talaka tare da guje musu kuma a matsayinka na wakilinsu, to tayaya zaka san damuwoyinsu balle har kai musu maganinta, wad'annan dalilan biyu su suka b'atamin rai har kaga na fita harkarka, domin ni a rayuwa banaso inga ana zaluntar talaka, kuma kai shaida ne ka sani sanadina suka zab'eka, amma komai ya wuce tunda gashi ma har nazo gidanka."

Uncle yai gyaran murya sannan ya kalli Dad yace "d'an'uwa kaga abinda nake fad'a maka ko, kaga irin ranar da nake guje maka zuwanta ko, ranar nadama da jin kunya mara iyaka, ba kai kad'ai ba wallahi mu kanmu kasa kunyar bawan Allahn nan mukeji, kaga illar wula'kanta d'an adam ko, gashi ya jawo maka kaje ka tozarta d'an wanda yai maka rana a rayuwa, d'an wanda yai maka halaccin da kai ka kasa rama mishi, shiyasa ba'a so ka wula'kanta mutum a rayuwa saboda komai talaucinsa to yana da darajarsa, kuma Allah ya karrama duk wani d'an adam sannan ya fifita matsayin mu fiye da halittun duniya."

Abba yace "duk kubar wannan maganar, duk abinda ya faru ni sai jiya ma nake ji, wallahi ni ya wuce a wajena, kuma ban ri'keshi akan wannan maganar ba."

Mahaifiyar Amira ha'kurarrar baiwar Allah, sai yanzu ta bud'a baki tai magana, tace "zafin zuciyarka da tsananta abinda be kai ya kawo ba da 'kin d'aukar shawara duk shi ya kawomu ga kaiwa wannan matakin, duk abinda ya faru ba kowa bane ya jawo sai kai da kanka, kuma ba komai bane sila illah alhakin bawan Allahn nan Amir da ka d'auka."

Amira cikin kuka itama ta amshe tana cewa "Dad kaga ikon Allah ko, yau gamu a 'kar'kashin wad'anda ka zalunci d'ansu ka tozarta rayuwarsa tare da nuna mishi tsana me tsanani, ashema d'an abokinka ne, amma da Allah ya tashi nuna maka aya da ishara sai ya turo mutanen da ka yarda dasu wato su Nura da mahaifinsa suka yashe maka komai da ka mallaka suka talautaka gashi yau har wajen zama yana nema ya gagaremu sai da Allah ya kawomu gidan iyayen talakan nan kuma matsiyaci sun taimaka maka da wajen zama kai da iyalinka, yanzu wa gari ya waya tsakanin kai da shi, Dad kud'i sunsa ka shagalta da duniya har ka manta cewa wata rana ranka ma zaka iya rasashi a binneka ba tare da dukiyar da kake wula'kanta mutane dominta ba, kuma ka manta cewa da ranka ma in Allah yaso zai iya 'kwace duk abinda ya mallaka maka, dama ai komai na Allah ne, baka yayi domin yaga yanda zaka tafiyar da ita, sai gashi lokaci guda wanda in na rantse ko kaffara bazanyi ba idan nace kwata-kwata baka tab'a sawa ranka akwai kwatan-kwacin hakan zai faru dakai a rayuwarka ba, yanzu baka ji kunya ba, wanda ka d'auka 'kas'kantacce ashe mahaifinshi ya fika matsayi da dukiyar da kake gadara da ita, hasali ma shine silar duk wani arzi'ki da kake tin'kaho dashi, tana kai nan a zancenta ta sake fashewa da kuka.

Abba ya d'ago kai ya kallesu dukkansu sannan yace "banji dad'in jin irin wad'annan maganganun ba daga bakinku, musamman ma ke Amira, uba ubane fa ko me ya zama kuwa wannan sunanshi na uba a gareki bai tab'a canzawa, akwai hanyoyi da sigar da addini ya warewa 'ya'ya suyi magana da iyayensu, ba irin wanda kikai magana da mahaifinki ba a yanzu saboda haka ki bawa mahaifinki ha'kuri."

Amira ta bawa mahaifinta ha'kuri cikin kuka.

Amir ya tashi ya taka har gaban Dad ya tsugunna, tare da dafa hannun Dad d'in yace "Dad ka umurceni da in nemo iyayena in na kawosu zaka yarda da aurena da Amira, kuma gasu a gabanka a yanzu na kawosu, ashema kunsan juna, Dad dole zan gode maka akan abu d'aya in kuma ro'keka abu guda, na farko ina godiya ga Allah da ya bayyana min iyayena, sannan ina gode maka kaima domin kaine silar jajircewata wajen fita nemansu wanda ta sanadin hakan ne har Allah ya had'ani dasu, sai abu na biyu shine dan Allah Dad ina ro'konka ko sau d'aya ka soni kuma ka karb'eni a matsayin sirikinka kuma ka sa wa aurenmu albarka," ya 'karasa maganar yana mai had'a hannayenshi biyu tare da cigaba da ro'konsa.

Cikin sauri Dad ya d'ago kai tare da ri'ke hannayen Amir, yana cigaba da kuka mai matu'kar sauti, yana fad'in "kai ba siriki bane kad'ai a wajena kai d'ana ne, dan Allah Amir ku yafe min, tabbas na zalunceku na zalunci kaina, gashi yau ina cike da nadama da kuma jin kunya wanda bazan tab'a mantawa dashi ba, kuma bazai goge a raina ba" kuka ya cigaba da yi sosai yana kuma cigaba da magiya akan a yafe mishi.

Shi kuwa Amir wani irin farin ciki yaji wai yau gashi ga mahaifin Amira kuma har yana ri'ke mishi hannaye, itama haka Amira hakan ya tabbatar mata da mahaifinta yai nadama.

Dad ya kalli iyayen Amir yace "kun ganshi nan ya nuna Amir da hannu yace kullum burinshi ya kare rayuwar iyalaina da na 'yata Amira, akan hakan be damu ba ya rayu ko ya rasa ranshi, amma ni kullum burina bai wuce naga na rabashi da 'yata kuma in nisantashi da duniyar ba," ya sake fashewa da kuka me matu'kar ban tausayi.

Abba yai gyaran murya sannan yace "abokina dan girman Allah kai shiru haka nan, damuwar nan zata iya jefaka cikin wani hali, ni wallahi ban ri'keka ba, ka sanni ka san halina bani da ri'ko, mu munzo ne mu gaisheku muka tarar da wannan al'amari ba nufinmu azo aita tayarda abinda ya riga da ya wuce ba, dan haka abar maganar daga yanzu ta wuce kar wanda ya sake tayar da ita."

Abba ya cigaba da fad'in "ga gida nan da ke kusa da wannan, yafi wannan da nake zaune kyau da girma ka zauna kai da iyalinka, kuma na baka shi duniya da lahira takardun na wajen 'kaninmu na bashi ya baka, makullan gidan kuma duk suna wajen masu shirya gidan, kuma nasan yanzu haka sun kammala komai kuna iya zuwa ku duba in be yiba a canza wani."

Nan ma Dad kuka yasa yana godiya yana kuka matarshi da Uncle suna tayashi godiyar.

Bayan sun gama godiyar sukai musu sallama sannan suka tafi nasu sabon gidan da ya zama mallakinsu.

Washe gari wajen 'karfe d'aya su Dad suka 'kara shigowa cikin gidan Abba, bayan sun gaisa suka sake yi musu godiya, Abba yace "bakomai yiwa kaine."

Dad yace "ina d'ana Amir yake?" Abba yace "suna can shi da matarshi suna had'a mana kaya gobe zamu koma Abuja gabad'ayanmu harda su."

Ana cikin maganarsu sai gasu sun fito da gudu Amira ce ke gudun neman wajen b'uya Amir na biye da ita yana fad'in "wallahi ki tsaya in rama".

Amira ta b'oye bayan Umma tana cewa "Umma kinga Amir ko ya lakuce min hanci ni kuma na murd'e mishi kunne shine wai sai ya rama."

Umma tace "shi ya isa ma ya tab'a min ke."

Dad yana dariya yace "zo nan kaji Yarona barta zatazo hannunmu ne mu rama wata rana."

Amir jin abun yayi banbarakwai, to be saba ba, ya 'karasa wajen Dad ya zauna a 'kasa ya gaishe da Dad, Dad ya amsa tare da d'agashi ya zaunar dashi a kusa da shi, sannan ya kalli Abba yace "ina ro'kon alfarma ka barmin yarannan a nan su zauna a gidanmu su saba da ni nima."

Abba yace "haba abokina menene na neman alfarma kuma kai da 'ya'yanka, ai ba wani abu su zauna d'in, dama naga kamar sunfi son zaman kanon," Amir ya mi'ke cikin sauri yace "yauwa to tunda mu mun fasa tafiya bari inje in cire kayanmu cikin naku," ya juya ya tafi," Amira ma ta mi'ke tana fad'in "eh wallahi muje na tayaka," dukkansu iyayen nasu suka bisu da idanu suna dariya, Abba yace "dama na fad'a maka sunfi son zaman nan."

Washe gari Abba ya kira Uncle ya bashi kyautar gidan da suke ciki, yace in su Amira sun koma gidan Dad da zama ya dawo nan ya zauna da iyalansa ya bashi halak malak, nan Uncle yaita godiya yana kuka yana fad'in "yau ka yimin abinda d'an uwana na jini ma ya kasa yimin."

Abba yace "ka daina fad'in haka, ai nima d'an uwanka ne na jini, d'an uwa ba sai wanda kuka fito ciki d'aya ba kad'ai yake zama d'an uwa, bare ma yana zama d'an uwa na jini wallahi, to ni haka nake kallonku, ina fatan kuma zaku d'aukeni a haka."

Uncle yai murmushi, sannan yace "wallahi d'an uwa kai na musamman ne, samun irinka sai an tona."

A tare suka shiga gidan Dad Uncle ya fad'a musu abin arzi'kin da akai mishi suka tayashi yin godiya, sannan suka yi musu sallama suka tafi, su Amira sune 'yan rakiyar filin jirgi.

Muje zuwa

*🅱K CE*😘💋
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘

RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (🅱K*
```(Autar marubuta)```

SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
```(Mamie)```

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```🤜🤛

PAGE 220 to 225
Chapter 51 · 0% Book details