← Book details So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 54

Sashe 21

So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da isarta ta faka motar ta bud'e ta fito, ganin motarshi ya tabbatar mata da cewa tabbas yana ciki, da sauri ta k'arasa ciki tana k'wala mishi kira, koda ta shiga baya falo hakan yasa ta wuce ciki da sauri, ta duba kicin baya ciki, ta shiga bedroom d'insa a nan ta hango shi kwance kan gado, kiran sunan shi Amira tayi tare da k'arasawa kanshi da sauri, tana fad'in " Amir d'ina me ya faru da kai ne, tana tab'a jikinshi taji wani irin zafi, tai saurin d'auke hannun tare da sakin salati.

Nan fa ta rud'e cikin sauri ta tashi ta had'a mishi tea yasha kad'an sannan ta bashi magani yasha, bayan yasha magani sai ta d'auko ruwa da tawul ta shiga tsoma tawul d'innan cikin ruwa tana goga mishi a jiki duk dan saboda ta samu zazzab'in nan ya sauka, sai wajen goma saura minti goma sannan zazzab'in ya fara sauka sab'anin yanda tazo ta tarar da shi, kuma har ya samu bacci ya d'auke shi.

Amira kuma ganin halin da yake ciki yasa sam hankalinta bai kwanta kan ta tafi ta barshi ba, hakan yasa ta yanke shawarar kwana anan, wannan shine karo na farko da Amira ta kwana a gidan Amir, tana zaune ta kwantar da kanta saman gadon a haka bacci ya d'auke ta ba tare da tasa komai a cikinta ba da daren.

Tun asuba yunwa ta tayar da Amira daga bacci, ta tashi tai sallah tukun bayan ta idar ta shiga kicin ta had'a musu abun karyawa.

Tana fitowa falo d'auke da abincin a dai-dai Amir ya fito daga cikin d'aki yana mik'a kamar ba shi bane jiya kwance cikin zazzab'i, suka kalli juna suka sakarwa junansu Murmushi, cikin sauri ta ajiye abincin kan tebur d'in dake tsakiyar falon tare da k'arasawa wajenshi da sauri tana fad'in " ya jikin naka, ina fatan kaji sauk'i, yanzu ina ne ke maka ciwo?"

Amir yai murmushi sannan yace "to wanne zan fara amsawa a ciki Amira na, ki kwantar da hankalinki lafiya lau na tashi kuma yanzu ba inda ke ciwo a jikina."

Amira ta saki numfashi tare da sakin doguwar ajiyar zuciya tace "Alhamdulillah Allah na gode maka da ka baiwa mijina lafiya," Amir yai murmushi, suka zauna suka ci abinci sannan ta zuba mishi ruwa ya shiga wanka, kafin ya fito ta gyare ko ina.

Tana cikin gyara mishi kayan taga wani agogon me kyau ya fad'o cikin kayan, d'ago agogon tayi tare da zaro idanu tace " me ya kawo agogon Sadeeq cikin kayan Amir, " bincike ta cigaba da yi can sai taga wani littafi shima na Sadeeq d'in ne duk kalaman soyayya ne a ciki, can kuma sai ta hango wani zobe na Sadeeq d'in, jikinta ne yai sanyi ta koma ta zauna k'asa dab'as tare da fara zubar da hawaye.

Fitowar Amir kenan daga bayi ya tsinci Amira a cikin wannan halin, cikin sauri ya k'araso wajen ta yana tambayar ta meke faruwa, ganin abubuwan da ke gabanta ya sa ya tsaya turus tare da zaro idanu, domin shi be yi tunanin hannun Amira zai kai nan ba.

Amira ta kalle shi cikin kuka tace " Amir kana so ka gasgata min zargin Insp Yahya kenan a kanka, kana nufin kai ne ka kashe Sadeeq kuma kayi sanadin mutuwar Abdul?"

Amir ya yi shiru a halin yanzu baida abun cewa tunda shaidu sun fara bayyana a gareta.

Amira tace "wannan agogon, na Sadeeq ne, ko ranar da muka rabu dashi daga filin wasa agogon na d'aure a hannunshi, haka ma wannan zoben yana yatsan shi, kuma ga littafin shi a wajenka wanda yake mallakin Sadeeq wanda ke cike da kalaman soyayya yana bayyanar da k'aunar shi gareni, nasan ka b'oye ne dan karna gani, to gashi yanzu na gani."

Amir ya zame k'asa shima tare da fashewa da kuka me matuk'ar sauti, Amira ta sake kallon shi tace " Amir meyasa ka kashe shi, fad'a min? "

Amir cikin kuka yace " saboda ke Amira, na dad'e da ganowa cewar Sadeeq yana k'aunar ki, haka ma Abdul, ranar da Sadeeq yace zai fad'a miki abinda ke zuciyarshi na tabbatar fad'a miki zaiyi yana k'aunar ki, hakan yasa na yanke shawarar d'aukar mataki a kansu duka harda Abdul."

Amira kuka take yi kamar ranta zai fita shima haka Amir d'in, Amira tace " taya kayi ka kashe shi, Amir ashe zaka iya kashe rai a kaina, inko hakane k'aunar da kake yimin ta zama masifa, ka fad'amin taya akai ka kashe shi?"

Amir ya d'auki kusan minti biyar yana kuka ba tare da ya sake cewa komai ba, itama kukan take yi d'akin ba abinda ke tashi sai sautin kukansu.

Can Amir ya fara magana kamar haka:

_a daren ranar da muka rabu dake na fara bin duk inda Sadeeq yasa k'afa, a daren kuma muka shirya zamu shiga club ni da Abdul da Sadeeq, bayan mun k'arasa muna zazzaune Sadeeq yana ta shahuwa domin akwai shi da son giya, mu kam bamu fara sha ba da Abdul da ni hira kawai muke d'an tab'awa, nan Sadeeq cikin maye ya fara bamu labarin irin k'aunar da yake wa Amira, sannan ya cigaba da cewa " gobe in Allah ya kaimu zan bayyana mata abinda ke raina," Abdul nan da nan fuskar shi ta canza ya tashi cikin sauri ya bar wajen nima na mik'e na bishi a baya, ina fitowa na tarar dashi tsaye a k'ofar shiga club d'in yana kai kawo, dafa shi na yi tare da kallon shi nace " Abdul ni nasan kana k'aunar Amira kuma ka rigashi nuna mata," Abdul yai saurin fad'in "eh wallahi, na riga shi, sai nace to ka kawar dashi mana kawai ka huta, da farko ya razana da jin haka, daga baya sai yai na'am da shawarata, muka shirya kan zai kashe shi cikin dare wajen k'arfe biyu, nan Abdul ya saki ranshi muka koma gun Sadeeq muka kamoshi muka shiga mota sai makaranta, na sauke su a bakin gate d'in makarantar Sadeeq ya wuce ciki yana tangad'i, na d'an tsayar da Abdul nace ya d'an bari yai nisa kar a gane tare suke, sai da naga Sadeeq ya d'an bada tazara sannan nace mishi ya tafi, haka suka shiga hostel d'in Sadeeq na gaba Abdul na baya, bayan naje gida na ajiye motata a gida sai nai b'adda kama na dawo makarantar hannuna sanye da safa, k'uguna rik'e da wuk'a na shiga d'akin Sadeeq a ankare ba tare da kowa ya ganni ba na kashe shi na bar wuk'ar anan, bayan na koma gida banyi bacci ba ina gadin lokaci, k'arfe biyu na dare nayi na kira Abdul bayan na b'oye lamba na sanar dashi lokaci yayi, shine fa yana zuwa ya tarar da gawar Sadeeq soke da wuk'a a jikinshi, cikin kid'ima da firgici Abdul ya cire wuk'ar daga cikin shi, tare da k'wala k'ara yana kuka yana tunanin waye ya kashe shi, wannan rik'e wuk'ar da yai da hannunshi ya cireta a cikin Sadeeq ita ta jawo aka ga tambarin yatsun shi, shine ya tashi da gudu ya bar d'akin ya koma nasu yana kuka tare da tunanin waye ya aikata wa Sadeeq haka, shine ya kirani ya fad'amin duk yanda ake ciki, nace ya kwantar da hankalin shi kuma ya dena jin tsoron saboda hakan zaisa a gane shine ya aikata kisan, kinji abinda ya faru."_

Amira da har yanzu kuka kawai take yi tace " haba Amir, meyasa zaka aikata abinda kasan hukuncinka kaima kisa ne?"

Amir yace " a lokacin idanu na ya rufe Amira na zab'i in mutu a kanki da inga wani ya mallake ki ba ni ba, Amira kin sadaukar da komai naki a kaina tun ina k'arami domin canza min rayuwa tare da k'ok'arin ganin na samu farin ciki, banda kowa kuma ban rayu da kowa ba sai ke, kowa ya gujeni kece kad'ai kika karb'eni hannu biyu kuma kika bani zuciyarki da kyakkyawar kulawa, hakan yasa bazan iya jure rayuwa babu rayuwar da zuciya da idanu suka saba da ita tun a baya ba kece rayuwar da nake nufi Amira."

Amira tace " to tunda nake tare dasu bantab'a jin son d'aya daga cikin su ba, kuma koda sun furta Kalmar so a gareni babu wanda zan iya amsa mawa inyi soyayya dashi a cikinsu," yanzu gashi nan ka jefa rayukanmu cikin had'ari don nasan yanda Insp Yahya ke bibiyarmu dole ya gano wani abu nan gaba, cikin kuka ta cigaba da fad'in " meyasa zaka aikata laifin da zai kashe masoya kamar mu masu burin gina kyakkyawar rayuwa," kuka take sosai, sannan can ta tashi ta d'auko dukkanin abubuwan nan ta k'ona agogo da zobe kuwa ta saka shi a cikin jaka tace tasan yanda zata yi dasu, ita yanzu Amir tausayi yake bata ya jefa rayuwarsa cikin hatsari duk sanadin soyayyarta, tun yana k'arami yake fama kanta amma ace har yanzu bai huta ba.

'Dagowa Amira tayi ta kalle shi sannan tace " bayan ni babu wanda ya san kaine ka kashe shi ko?"

Amir yace " babu kowa da ya sani bayan ke," "sai kuma ni," abinda sukaji an fad'a kenan daga bakin k'ofa," cikin zaro idanu tare da mugun firgici suka juyo.

Insp Yahya ne tsaye yana tafa hannayensa fuskarsa d'auke da murmushi, sannan yace " wannan ranar ce na dad'e ina zuwanta, yau Allah ya tona asirinka Amir, ya ciro bindiga ya saita Amir da ita tare da fad'in wuce muje." Amira cikin tsoro da firgici ta d'auki wani abu ta buga wa Insp Yahya ta baya ya saki k'ara ta k'wace bindigar kuma ta rik'e Insp Yahyan gam tana fad'in " Amir gudu."
Chapter 21 · 0% Book details