Sashe 20
So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Insp Yahya yace " wannan labarin da kunnena yaji ya k'ara tabbatar min da cewa kaine kayi kisan nan Amir, ko ba kai bane to kana da hannu a ciki."
Amira ta tashi tsaye tare da takawa har inda Insp Yahya yake tace " Insp rashin mutuncin naka ya isa haka, taya za'ai wai ka rik'a jifan Amir da wad'annan kalaman ko dan kaga ina dakatar dashi kan d'aukar mataki a kanka, karka manta ubana shine shugaban k'asar nan zai iya sanadin rabuwarka da aikin nan, kuma karka manta wanene kake fad'awa magana a kaina, jarumi ne shi kuma sadauki wanda zai iya yin komai a kaina."
Insp Yahya yai dariya sosai tare da tafa hannaye, sannan ya kalleta yace "gaskiya naji dad'in furucinki na k'arshe da kikace Amir zai iya yin komai a kanki, tunda kin tabbatar da haka bakya tunanin har kisa ma zai iya yi a kanki? ko kin manta cases d'in da aka yi a baya na dukan maza da yaita yi a kanki, kin manta furucin da ya yi a k'arshen ranar da na kulle shi a gabanki? to bari na tuna miki cewa ya yi in har za'a cigaba da tab'aki to bazai tab'a daina kai duka ba, wannan fa akan wanda ya kulaki ne kawai ko ya tab'aki Amira to ina ga kuma wanda yaji yace yana sonki ko yaga yana gwada miki k'auna."
Amira ta dakatar dashi tare da d'aga mishi hannu, tana nuna mishi k'ofa alamar ya fita ya bar mata gida, Insp Yahya yace "na tafi amma kiyi dogon tunani akai ki gani," yana kai nan a zancensa ya fita ya bar gidan.
Amira ta duk'e a k'asa tana dafa kai tare da fashewa da kuka, Amir ya k'araso zuwa inda take ya duk'a tare da dafata, fad'awa jikinsa tayi tana kuka tace " Amir d'ina kayi hak'uri dan Allah da k'azafin da wannan d'an sandan ke jifarka da su, babu wanda ya isa ya canza min ra'ayi a kanka, ni na fara tunani ma ko Dad ya sashi ya rik'a bibiyarmu, to wallahi Amir ko kisan kai ka yi a gabana ina tare da kai ban tab'a gudunka duk rintsi, nan fa sukai ta kuka daga k'arshe kuma suka rarrashi kansu, sauk'in da Amir yaji ma da bata yarda da zancen Insp ba.
Amir yace " bari inje gida in d'an kwanta duk da yamma tayi ma," Amira tace " ka kwanta a nan mana," Amir yace " a'a Amira kalli fa yanda na fito daga singileti sai gajeren wando ni tsoro na ma kar wannan masharrancin ya sake yimin wani sharrin."
Amira kuwa sai a lokacin ma ta lura da yanda yake, duk da halin da suke ciki amma be hanata dariya ba kamar me harda rik'e ciki tana nunashi tana dariya, shima sai a lokacin ne yai murmushi sannan yace " duk ba ke kika jamin ba kukanki ya birkita tunani da duk wani lissafi nawa ya sakani fitowa a haka ba, wallahi kaf duniya b'acin ranki kad'ai yafi komai d'aga hankalina balle kuma har inji kukanki sai inji kamar na haukace saboda tashin hankali, kafin had'uwa dake bana tunanin rayuwa tana da sauran amfani gareni kuma banyi tunanin zan samu canji haka ba, amma bayan had'uwa had'uwa dake na gane cewa wannan tunanin da nake kuskure ne, wallahi mijinki ya more da mata, iyayensa sun more da suruka yaranki sun more da uwa ta gari ina kaunarki Amirata."
Amira tai murmushi sannan tace "ina sonka Amir d'ina matarka zata more da kulawa tare da dad'ad'an kalamai," Amir yai murmushi sannan yace "zan tafi anjima zan dawo," Amira tace "wallahi idan muna tare bana so mu rabu Amir."
Amir yace "karki damu bazan d'auki lokaci me tsawo ba zan dawo gareki, wanka kawai zanyi domin baccin da nake ji ma ya gudu kamar yanda duk lokacin da kike cikin bak'in ciki walwalata ke guduwa hakama baccin da ke idona ya gudu na nemeshi na rasa," dukkanin su suka sakarwa juna murmushi sannan ya saka d'aya daga cikin kayan da zata wanke mishi dan tace bata yarda ya koma a haka ba matan dake waje su gane mata jikin miji, daga nan suka yi sallama da juna ya fito ya shiga mota ya tafi gida.
_Hattara mata kaicon matan auren da suke sassautawa wajen furtawa mazansu kalamai na so, wata matar ma da ta shiga gidan auren shikenan furucin dad'ad'an kalamai ya k'are, to wallahi ku sani wad'annan kalmomin da kuke rainawa da tattali da kulawa da kuke d'aukarsu kamar kun wuce da ajinsu, to sune makaman ku da kuka yi kafin ku shigo gidan, kuma sune makaman ku da zaku cigaba da jajircewa kansu a cikin gidan aure, kuma karku manta da su ne kishiyoyin da ake muku suke yak'arku har su fiku samun matsuguni da fada a gida, saboda ke kin saki jiki kawai tunda kin shigo fad'awa mai gida I love you a cikin gida da me gida kana raina idan ya fita sun k'are, a'a wallahi so kamar fure ne, koda yaushe yayyafa mishi ruwa ake domin ya k'ara tsiro da girma, haka so yake, ki cigaba da furta kalamai sababbi akoda yaushe kuma dad'ad'a tare da tattali da nuna kulawa shi ke k'ara saka so yai girma cikin zuciyar bawa, Allah yasa an fahimta kuma masu yi zasu gyara, wallahil azeem so na gaskiya baya tab'a gushewa sedai ko bak'in halin mutum da munana zuciyar da kake wa masoyinka ya jawo tsana wanda kuma wannan kai ka gogeta da hannunka sakamakon halinka, Allah yasa mu dace._🙏🙏🙏🙏🙏
Bayan fitar Amir Amira tai sallah tare da wanke kayan Amir ta gama a dai-dai ana kiran sallar magrib, tai sallar magrib d'in sannan ta zauna tana d'an tunani can sai maganar Insp Yahya ne kawai ke dawo mata cikin rai, duk yanda taso ta kawar dashi ta kasa, maganar shi ta k'arshe ce ke dawo mata wadda yace " _(karki manta Amir yace muddin za'a cigaba da tab'aki to tabbas ba zai fasa kaiwa mutum duka ba, wanda ya tab'aki fa kenan ina ga wanda ya furta miki kalmar so ko yaga ana nuna miki,.........zan tafi amma ki zauna kiyi tunani."_
Duk yanda taso ta kaucewa zuciyarta daga barin karta fara zargin Amir a zuciyarta ta kasa, kawai ji take yi zuciyarta na neman fara gasgata zancen Insp Yahya musamman tunano abubuwan da Amir yaita yi a kanta tun tana k'arama har zuwa girmanta.
Tana cikin wannan tunanin ne sai wayarta ta fara yin k'ara alamar ana kiranta, tana dubawa sai taga bak'uwar lamba, hakan yasa ta k'i d'agawa har kusan sau uku ana kira bata d'agaba, sai can taji k'arar message ya shigo, tana dubawa taga lambar da ta kirata ce dai aka turo mata message da ita, bud'ewa ta yi tare da fara karantawa, _Amira Insp Yahya ne, ni har ga Allah taimakonki nake so inyi ya kamata kiyi bincike ne kafin ki k'aryata zancena kan kisan da nake tuhumar Amir akai."_
Amira cikin fushi ta mayar mishi da amsa cikin hassala kamar haka:
_wai me ya shafeka da lamarina ne, rayuwata ce fa ba taka ba, menene naka na bibiyata to bari kaji ko rai d'ari Amir ya kashe ina sonshi a haka, in ma saka aka yi ka yi mishi sharri to beyi tasiri a kaina ba._
Insp Yahya dake cikin office yaji amsar Amira ta shigo ya bud'e ya karanta, sannan yai murmushi kuma a fili ya fara magana shi kad'ai, " dama abinda nakeso inji daga gareki kenan, wato kare makashi kike bayan kinsan me ya aikatawa koh, hahaha zaku sha mamakina yanzu na fara bibiyar lamarinku har sai na gano gaskiya domin kisan nan akwai lauje cikin nad'i, kai kuma Amir a juri zuwa rafi............."
Ku biyoni muje
*🅱K CE😘💋*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (🅱K)*
```(Autar marubuta)```
SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
```(Mamie) ```
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah) ```🤜🤛
*MASOYAN GASKIYA SUN K'ARE KO INCE SUNYI K'ARANCI SAI D'AD'D'AIKU, DUK MASOYIN DA YA SOKA KUMA YA BARKA TO BA CIKAKKEN MASOYI BANE NA GASKE WALLAHI, MASOYIN GASKIYA BAYA TAB'A GUDUNKA DUK RINTSI DUK WUYA ANA TARE, ALLAH KA HAD'AMU DA MASOYA NA GARI.*
PAGE 85 to 90
Amira na gama tura mishi test message ta goge wanda ya turo mata da wanda ta tura dan saboda kar ma Amir ya gani ranshi ya sosu dan ita sam ba zata so hakan ba, tabbas tasan Amir zai iya yin komai a kanta, amma zuciyarta bata tab'a bata damar zargin shi ba balle tace zata yi bincike a kanshi.
Shi kuwa Amir bayan ya koma gida kasa aikata komai ya yi har wankan, ya fad'a gado yana ta kuka kamar yaro, sai a yau ya fara sarewa kan soyayyar Amira, saboda ya tabbatar mahaifin Amira da wuya zai yarda ya bashi ita aure, in kuwa har zai bashi to akwai gagaruman matsaloli a gaba, domin dole ace sai sun san hak'ik'anin iyayenshi, shi harga Allah tunanin shi bai tab'a kawo mishi hakan ba, kuka yake kamar ranshi zai fita, hakan ya haddasa mishi ciwon kai me tsanani.
Amira ce zaune idar da sallar isshanta kenan, tana zaune tana jiran zuwan Amir har takwas da rabi shiru, se dai ta d'an yi mamaki saboda tasan be cika kaiwa wannan lokacin ba tare da ya taho gareta ba.
Tara dai-dai ta kasa hak'uri ta d'auki wayarta taita doka mishi kira gashi dai tana ringing amma shiru ba amsa, har zuwa tara dai-dai tana kiranshi amma ba'a d'agawa, hakan yasa ta gaza jurewa ta tashi ta d'auki mayafi tare da zarar key ta fito ta shiga cikin mota ta tayar sai hanyar gidan Amir.