← Book details So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 54

Sashe 42

So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abba ya 'karashe maganar yana kuka, shima Amir kuka yake kanshi na kife akan cinyar Abban nashi, Umma Khadija itama kuka take sosai, duk d'akin babu mai rarrashin wani.

Amir ne ya d'ago kai cikin kuka yace "lallai Abba duniyar nan cike take da abubuwan ban tsoro, in har baka mutu ba zakai ta jin abubuwa kala-kala, amma Allah baya bacci gashi nan be tab'ar dakai ba saboda kyawun zuciyarka, kuma shi kawu Sunusi da sannu zai girbi abinda ya shuka."

Abba yace "a'a na yafe mishi fatana Allah yasa ya shiryu kafin Allah ya d'auki ranshi," Amir yace "Abba kai wane irin mutum ne?" Abba yace "me kwad'ayin samun aljanna."

Amir yace "Abba ka shirya kai da Umma muje gidan su Amira taga iyayena," Abba yace "to my son yanda kace haka za'ai," ko da isarsu gidan suka tarar da gidan a gar'kame da suka tambaya aka tabbatar musu cewa masu gidan sun tashi gaba d'aya.

_Topha tashin hankali wanda ba'a sa mishi rana_

Muje zuwa

*🅱K CE😘💋*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘

RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (🅱K)*
```(Autar marubuta)```

SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
```(Mamie)```

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```🤜🤛

*MAMAN LABYB*
(Mamie nah)
*Kina raina a koda yaushe, tuni kika she'ke zuciyata da 'kaunarki ke ta daban ce, halin kirkinki ma daban ne, ina 'kaunarki 'kauna ta gaske kuma ta har abada, matsayinki ya zarce hakan guna😍😘💋*

*~MOMYN KADEEJA*🧕
*Momyn kadeeja albarkacin 'kaunar da kike gwada min tare da d'umbin kulawarki kan littafin nan, na baki wannan page d'in kyauta kiyi yanda kikaga dama dashi, in kikace ba me karantawa ma sai ke kad'ai ta zauna,😂 ina godiya sosai da comment d'inku ina jin farin ciki sosai wlh akai.🙏😍😘💋*

*Idan so yai so ko masoya na nesa da juna zuciyoyinsu na raya musu abu guda game da juna, ikon Allah kenan😍 yanayin 'karfin so a cikin zuciyar masoyan gaske kenan😍😍😍😍😍*

PAGE 175 to 180

Amir ya fad'i nan 'kofar gidan yaita rusa kuka kamar 'karamin yaro, sai a yau yake ganin wautarshi da kuma rashin kyautawarsa akan share lamarin Amira da yayi, cikin sauri ya d'ago ya kalli mahaifinshi tare da ri'ke mishi hannu yace "Abba wai sun tashi aketa ce mana fa, ina suka kai min matata to? Abba ka taimakeni a nemo inda suke, wallahi Abba in babu Amira bazan iya cigaba da rayuwa ba.

Jiri Amir ya fara ji, ya dafe kanshi da hannu bibbiyu, ya tafi taga taga zai fad'i Abbanshi yai sauri ya rungumeshi, yaita jijjigashi amma ina ya sume, cikin sauri securirty's d'insu suka kamashi aka sa a mota suka shiga sai asibiti.

Haka Amir yaita faman jinya ya mugun sawa kanshi damuwa, a koda yaushe yanzu bashi da wajen zuwa sai unguwar su Amira, ya samu 'kofar gidansu yaita rusa kuka, kullum aikinshi kenan, iyayenshi har sun saba duk in suka ga basu ganshi ba to nan suke nufowa, kuma suna zuwa zasu ganshi.

Babu inda bai je neman Amira ba amma babu ita ba labarinta, kullum cikin tunani yake duk yabi ya fige, iyayenshi duk sun rasa gane kanshi, saida ya zagaye dukkanin station d'in garin ya bada hotunanta ga duk wanda ya ganta ko yaji labarinta, amma har yau ba bayani.

Sunyi yawon shi da security's masu yawan gaske amma shiru kake ji ba wani bayani a kanta.

Bayan kwana biyu, Amir ne kwance kan jikin Ummanshi tana shafa kanshi tare da rarrashinsa kan ya rage sa damuwa a cikin ransa gashi nan sanadinta ya kamu da hawan jini kar ya zama silar kamuwarshi da ciwon zuciya.

Suna cikin magana sai ga Abba ya shigo, 'karasowa yai inda suke ya kalli Khadija yace "Sannunku da gida My Love, My Son ya kake, ya jikin naka?"

Gaba d'ayansu suka had'a baki wajen yi mishi sannu da zuwa, ya amsa musu sannan yace "na sameku lafiya?" suka sake had'a baki wajen fad'in "lafiya lau."

Zama Abba yai kusa da matarshi, sannan ya dafa Amir dake kwance kan jikinta, yace "Amir ji yanda ka rame ka lalace, haba Amir, da damuwa da sawa rai suna maganin kowace irin damuwa da tuni sunyi mana tamu maganin damuwar, amma a maimakon haka sai muka ri'ki takobi na gaske wato addu'a makamin mumini, wannan addu'ar da muka ri'ka itace tasa Allah ya dubemu da idon rahma yaji tausayinmu ya bayyana mana kai, saboda haka ka dage da addu'a muma muna tayaka, tunda ba mutuwa tayi ba menene na damun kanka za'a gansu insha Allah."

Amir ya share hawayen dake kwararowa daga cikin idanunshi, sannan ya kalli mahaifinshi yace "Abba Amira ta zama jigo na dukkanin rayuwata, zan jure komai amma akan Amira ban yin baya, Abba wallahi na sani Amira tana cikin damuwar rashina fiye da wadda nake ciki a yanzu, abinda ke sakani kuka kenan idan na tuno Abba bana son damuwarta ko kad'an, wallahi tunda naji zuciyata na zafi itama ta-ta tana can tana mata zafi," yana kai nan a zancenshi ya sake fashewa da kuka.

Abba da Umma sun tausayawa yaronsu matu'ka, domin bai b'oye musu komai ba cikin labarin rayuwarsu da Amira, kuma duk wanda yaji labarinsu dole sai ya tausaya musamman ma Amir wanda ya rayu cikin mawuyaciyar rayuwa.

Nan dai suka 'kara bashi baki, da 'kyar suka samu yai shiru, suna cikin hira shi dai bai saka musu baki, da haka ma bacci ya d'aukeshi.

………………………………

B'angaren su Amira kuwa har yanzu ta kasa dawowa asalin Amirarta, sannan koda yaushe Nura cikin sintirin zuwa wajenta yake, kan dole take sauraronshi shima dan yana mata zancen Amir ne, amma sam bata 'kaunar a dameta yanzu, a hankali tun tana gundura dashi har sabo ya shiga tsakaninsu, dama kowa ya sani cewa muddin mutum yana yi maka zancen wanda kake 'kauna akoda yaushe kuma yana yabawa masoyin nan naka zakaji zuciyarka ta sha'ku dashi, to haka ce ta faru da Amira.

Zaune Amira take gaban Dad d'inta shigowarta kenan falon Dad d'in nata wanda ya kirata a waya yace tazo yana son magana da ita.

Koda ta shiga ta tarar harda Mum d'inta a falon, gefe ta samu ta rakub'e kamar wata marainiya, sannan tace "Dad gani," Dad ya kalleta yace "Doughter abinda yasa nai kiranki shine Nura ya tabbatar min da yana 'kaunarki, mahaifinsa kuma yazo neman aurenki wajena dan hak.........." be kai ga 'karasawa ba Amira ta mi'ke tsaye cike da matsanancin b'acin rai had'e da razana, sannan ta kalli Dad d'inta tace "Dad Nura fa kace!!! to wallahi ban tab'a 'kaunar Nura ba a cikin raina, kuma har abada bazan 'kaunaceshi ba, wai ma Dad ba akan talaucin Amir ka 'kishi ba kuma ka tsaneshi, but why kake so yanzu in auri talaka wanda ubanshi ke aiki a 'kar'kashinka? gaskiya bana 'kaunarshi, kuma ko zanyi aure a nan gaba bazan tab'a auren talaka ba sai irin wanda kakeso mu gani zasu iya ri'ke maka ni kamar yanda Amir talaka bawan Allah ya ri'keni ko kuwa."

Dad yace "naji Nura talaka ne shi amma ai yana da asali ko, to shikenan in har baki amince da Nura ba to ki zauna da shirin cewa cikin satin nan zan kawo miki duk wanda naga dama."

Amira tai murmushin takaici sannan tace "Dad wallahi ka sauya gaba d'aya, amma ba komai, ni bazan 'ki yi maka biyayya ba akan koma waye zaka had'ani dashi, saboda ba auren so zanyi ba, duk wata so da 'kauna mutum d'aya tak zan iya ba mawa su, kuma na rasashi, to wallahi ba na biyunshi a zuciyata, zanyi maku biyayya kan duk wanda zaku had'ani aure dashi Dad," tana kai nan a zancenta ta fita daga d'akin a guje tana kuka lambun gidan taje ta zauna kan kujera tare da had'a kai da guiwa, ta cigaba da kukanta.

kanta na du'ke tana cikin kukan ne taga alamun mutum a kanta, tana d'agowa taga Nura ne, maida kanta tayi tare da cigaba da kukanta.

Nura ya du'ka kusa da ita yana rarrashinta tare da yi mata magiya kan ta sanar dashi abinda ke faruwa, Amira ta d'ago tace "Nura idan kana tunanin sabon da mukai da kai akwai d'igon 'kaunarka a raina to wallahi ka daina, bana 'kaunarka gwara ma ka janye wannan maganar, Nura ya numfasa yace "yanzu akan wannan kike kuka, ni banma san anyi zancen ba, tabbas ina 'kaunarki kuma na fad'awa mahaifina amma sam bance yazo yai maganar a gidanku ba, indai kan wannan ne ki kwantar da hankalinki ki daina kuka maganar ta wuce, Amira ta d'ago kai cikin kuka tace "ina fa ta wuce Dad yace ko kai ko kuma ya zab'a min koma wanene."

Nura ya numfasa cikin sauri dabara ta fad'o mishi a rai, yace "tunda abun ya zama haka me zai hana ki amince ni ki aureni, ni kuma na d'aukar miki al'kawari da zarar mijinki Amir ya dawo gareki wallahi zan sakeki ki aureshi, da wannan shawarar suka amince kuma a tare sukaje Nura ya sanar dasu amincewar Amiran ita kuma Amira ta baiwa Dad d'inta ha'kuri kan abinda ya faru d'azu, amma iyayenta sunsha mamaki kan canjin ra'ayinta lokaci guda, musamman yanda suka ga ta tayar da hankalinta akai musamman ma akan zancen Nura d'in, to koma dai menene su hakan yai musu dad'i, ba tare da b'ata lokaci ba aka sa ranar aure sati uku kacal, a ranar da aka tsaida rana ma Amira taci kuka kamar me, ita in aka barta tunda babu Amir rayuwarta ita kad'ai zata 'karasata.

Abba da Umma kuwa sun yanke hukuncin dawowa kano da zama, tunda dama Amir ya fad'a musu acan yai makaranta, to so suke su koma can ya cigaba da karatunsa ko Allah zai taimakesu ya rage tunanin da yake yi.

Koda suka tuntub'eshi da maganar be yi wata-wata ba ya amince da zancen dama garin ya isheshi tunda ba masoyiyarshi a ciki, amma sai yace wa iyayenshi in suka tafi kuma Amira ta dawo fa? mahaifansa suka ce mishi ai sun rarraba hotonta ga jami'ai, ana ganin sun dawo a ranar za'a basu labari, da haka ya amince suka fara shirin tafiya kano.

A yau talata su Amir dirarsu kenan a garin kano, kuma a yau talatar dai aka shaida d'aurin auren Amira Ahmad Tukur da Nuraddeen.
Chapter 42 · 0% Book details