← Book details So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 54

Sashe 43

So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_'ka'ka-k'ara 'ka'ka ko wannan wainar ya za'a toyeta oho, ina fatan masu karatu basu manta da mahaukacin kishin Amir ba😂_

Muje zuwa

*🅱K CE😘💋*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘

RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (🅱K)*
```(Autar marubuta)```

SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
```(Mamie)```

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```🤜🤛

PAGE 180 to 185

Daga shigowarsu cikin garin kano suka tabbatar da cewa lallai shagalin biki ake, kuma shagalin ma na 'ya'yan hamshak'an masu kud'i.

Abba ya kalli matarsa yace "da alama cikin garin nan shahararren biki ake kuma k'ayatacce."

Umma tace "gaskiya kam da alamu, haka suka k'arasa inda zasu je suna tafe suna hira ba tare da Amir yace musu ci kanki ba, har suka k'araso gingimemen gidan Abba dake cikin g.r.a a kano.

Ko da su Amir suka dawo garin kano da zama babu abinda ya canza zani daga gareshi, domin kuwa har yanzu bai ga masoyiyarsa ba, kuma bai dena tunanin da yake yi a kanta ba, da shelar nemanta a ko'ina, kuma a kanon ma duk inda yasan sunyi rayuwa tare da Amira can yake zuwa ya zauna yaita kuka, idan ya tashi da safe gidan shi yake zuwa yaita tuno abubuwan da suka wakana tsakaninsa da masoyiyarsa yana kuka tare da surutai kamar zararre, koda yake mai yin soyayya tamkar zararre yake musamman idan tazo maka da k'alubale me zafi irin na Amir da Amira, daga nan kuma idan ya tashi sai ya wuce d'aya gidan Amiran shima yaita kuka, yanzu a can yake wuni sai dare yake komawa gida, abun duk ya damu iyayensa, su sun dawo dashi nan domin ya samu sauk'i ashe zuwansu nan ne ma zai k'ara sakashi cikin wani mawuyacin hali.

Shawara suka yanke akan a sakashi a makaranta amma itama ba wadda sukayi shi da Amira ba.

Koda suka tuntub'i Amir da zancen makaranta sai ya amince kai tsaye, amma ya dage akan cewa shi lallai wadda yake yi ada a nan kanon ita yake so a saka shi, babu yanda suka iya cikin k'ank'anin lokaci aka gama mishi komai ya fara zuwa.

…………………………………

B'angaren Amira kuwa a ranar da aka d'aura aure a ranar suka tare a wani tangamemen gida, wanda Dad ya mallaka wa Amiran shi halak malak.

A daren ranar bayan an kaita kowa ya watse saura shigowar ango sai Amira ta tashi cikin sauri ta gark'ame k'ofa, ta fad'a kan gado tasha kukanta ba me rarrashi, idanunta duk sun kumbura saboda tsabar kukan da take sha a kullum tun ranar da aka saka ranar aurensu har zuwa yau da aka kawota gidanta na aure.

Ko da Nura ya shigo da abokanansa babu kalar magiyar da be yi mata ba akan ta bud'e k'ofar amma tak'i, dole haka abokansa suka juya kowa da abinda yake sak'awa a ransa, Nura yai musu rakiya ya dawo ya ajiye ledar kajinawa da lemuka da ya siyo a gefe, ya kwanta a d'aya daga cikin kujerun dake falo.

Yana daga kwance ya kira mahaifinsa yana fad'a mishi abinda Amira tai mishi yau, daga can d'ayan b'angaren mahaifin Nura yai murmushi, sannan yace "haba Nura, yau fa aka kawota gidan, kuma kasan dai bata sonka, to a hankali ya kamata ka bi da ita har mu samu mu cimma burinmu a kansu ita da mahaifinta, mu yagi rabonmu mu k'ara wuta," sun jima suna hira da mahaifinsa yana k'ara d'ora yaron nasa akan muguwar hanya, daga k'arshe suka yi sallama.

Washe gari Dad d'in Amira ya kira Nura gidansa ya bashi makullin sabuwar mota, sannan ya bashi takardun wani kamfani nashi ya bashi su halak malak, Dad ya d'ora da cewa "wannan ba komai bane akan abubuwan da zanyi maka a gaba muddin ka kulamin da 'yata," Nura yaita godiya sannan suka yi sallam ya fito yaja sabuwar motarshi d'aya daga cikin security kuma ya ja mishi tsohuwar suka taho zuwa gida, a hanya ne ya kira mahaifinsa yake sanar dashi abinda Dad ya bashi yanzu, sai mahaifin Nura yace "kaga abinda nake fad'a maka ko," Nura yace "wallahi Dad na gani, wai harda wani in kula mishi da 'yarshi yanda ya kamata," mahaifin Nura yace "eh yanzu ai kyautata mata da zaka yi shi zaisa mu samu komai cikin sauk'i a wajen mahaifin nata, tunda ka samu sabuwa zanzo ka bani d'ayar taka tunda tawa dama duk ta tsufa, Nura yai dariya yace "to sai kazo ai in komai ya kankama ma har jirgi sai a baka ba mota ba Baba," Baban nashi yace "yauwa na gode Allah da ka fahimci komai yanzu ka dawo kan hanya, ai duk fafutukar nan da kaga inayi duk saboda kai ne Nura na," nikam naci kaji uban wofi sai kace dukiyar da guminsa ya tara ta.

*BAYAN WATA 'DAYA*

Abubuwa da dama sun faru, ciki kuwa har da komawar Amira makaranta, sedai kuma ikon Allah basu tab'a had'uwa da Amir ba, kuma hakan ta faru ne sakamakon canza kos da Amiran tayi, mijinta Nura shi ke kaita ya kuma dawo da ita, duk wata kyautatawa na mata da miji suna yiwa juna musamman ma shi Nuran, amma duk da haka Amira ta kasa barinshi ya kusanceta, a wautarta ganin hakan take kamar cin amana ga Amir, tunda ita har yanzu zuciyarta bata daina bata yana raye ba.

Yau alhamis, shigowar motar su Amira kenan cikin harabar makarantar, a yayin da shima Amir be dad'e da shigowa ba yana daga cikin motarshi a zaune amma k'ofar motar a bud'e take, k'afarsa d'aya tana ciki d'aya kuma tana waje, yana zaune yana abinda ya saba wato tunanin Amira, kamar ance ya d'aga idanunsa kawai sai akan Amira, gani yake kamar gizo take yi mishi kamar yanda ya saba gani, shiyasa ya 'kura mata idanu, can kuma sai ya murza idanunsa ya sake murzawa ita d'in ce dai yau Allah ya gwada mishi zaune cikin mota, tabbas wannan Amirarsa ce, ya fad'i da 'karfi yana maimaitawa cikin farin ciki had'e da zub da hawaye yana cewa "Amira ce, wallahi Amirata ce, ko cikin miliyoyin mutane Amira wallahi zan shiga in zak'uloki, cikin sauri ya yunk'ura da niyyar zuwa wajenta, se dai abinda ya gani ya sakashi tsayawa cak, wani mutum ya gani ya fito daga b'angaren driver ya bud'e mata motar ta fito.

Tana fitowa yaga wannan mutumin yai mata magan ta bashi amsa fuskar nan ta-ta a d'aure ba alamar fara'a, suna tsaye wata yarinya wadda bata fi sa'ar Amiran ba ta tunkaro wajensu tana dariya, bayan ta k'araso suka gaisa yaji tace "Amira saura minti biyar fa a shiga lecture, nima ke na tsaya jira mu shiga tare tunda mukai waya naji kince min gaku nan nake juranki.

Amira ta kalleta tace "muje," Nura ya kalli "wannan yarinyar yace "Anisa ki kulamin da matata da kyau dan Allah," Amira tace "to insha Allah," suka yi sallama da shi ya fad'a cikin motarsa, yai mata key, ya ja ya tafi.

Duk abubuwan nan da suka faru duk a kan idanun Amir ne, kuma yaji duk abinda sukace, ya k'ara tabbatarwa da tabbas Amirarsa ce, amma abinda be gane ba shine waye wannan mutumin, kar dai Amira amanarsa taci ta sake yin wani auren? ganin su Amiran sun juya sun tafi yasa ya fito cikin sauri yana binsu a baya har saida yaga inda suka shiga.

Waje ya samu ya zauna inda duk wanda zai fito daga wajen zai ganshi, amma shi yana d'an nesa da wajen, bayan kamar wajen awa d'aya yaga anata fitowa d'aya bayan d'aya, hakan ya bashi tabbacin cewa lallai sun gama lecture d'in nasu, yana nan zaune can sai gasu sun fito ita dai da wannan yarinyar wadda yaji an kira da Anisa, rakiya yaga taiwa Amiran har wajen parking suna jiran k'arasowar mijin nata, basu dad'e ba kuwa sai gashi ya shigo, cikin sauri ya fito tare da had'a hannu biyu yana neman afuwar Amiran, daga k'arshe ya bud'e mata mota ta shiga ya rufe, shima ya shiga ya zauna, sannan yaja suka tafi, Amir yana kallo ji yai kamar yaje ya shak'e wuyan mutumin da yake gani da matarsa wanda har yanzu be yarda mijinta bane.

Anisan ce yaga ta juyo tazo zata wuce ta tafi hostel, hakan ya bawa Amir tabbacin a cikin makarantar take da zama.

Cikin sauri ya k'arasa wajenta tare da shan gabanta, kallonshi tayi, tare da k'walalo idanu had'e da ja da baya, har ta juya zata danna a guje ya sake shan gabanta yana fad'in "dan Allah ki saurareni," cikin rawar murya Anisa tace "to ina jinka," dan ita har ga Allah tunaninta aljani ne ko kuma fatalwarsa ce tazo mata.

Kallonta Amir yayi sannan yayi murmushi, yace "Anisa ki kwantar da hankalinki, yanayin yanda kika nuna min ya tabbatar min da kinada labarina a wajen Amira ko?" Anisa tace "eh hakane babu wanda zama zai had'ashi da Amira koda na awa d'aya ne ba tare da ta bashi labarinka ba had'e da nuna hotonka, a yanda na lura a yanzu tana cigaba da rayuwane ma akan dalilan abu guda biyu, na farko saboda tana sawa ranta cewa wata rana zaka dawo gareta sai gashi kuwa, sai abu na biyu shine tana zama da duk wanda yake yo mata hirarka ne kawai domin hakan na mata dad'i taga anata mata maganarka," Amir yace "amma meyasa da kika ganni kika gudu, kuma waye na gani ya d'auketa a motarsa sun tafi tare?"
Chapter 43 · 0% Book details