Sashe 25
So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dukkanin su sun saita su da bindiga, Amira kuwa cikin sauri da tsoro ta tsaya gaban Amir tare da kareshi kar a harbeshi, Dad kuwa cikin tsananin b'acin rai yake kallon Amir, cikin d'aga murya kuma ya bada umurni kamar haka "ai mishi shegen dukan da zai kasa tashi tun a nan kafin mu tafi dasu."
_wayyo ina cikin firgicin ganin za'a raba masoya ta k'arfi da yaji shiyasa kuka yaci k'arfina baran iya cigaba da typing ba,😭 kunji dai gaskiya na gaji da typing ne yasin😂 sai kuma gobe😜_
Muje zuwa
*🅱K CE😘💋*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (🅱K)*
(Autar marubuta)
SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
(Mamie)
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛
*DARLING INSPECTOR YACE A FAD'AWA 'YAN TEAM D'IN AMIR YANA GAMAWA DASHI TO KANKU ZAI DAWO DUK SAI YA GARK'AME KU D'AYA BAYAN D'AYA, INA TAUSAYA MUKU KUKA SHIGO HANNUN DARLING INSP KAFI 'KARFIN MUGU BA SASSAUCI😂😂😂😂😂 SAURA SU O'O ACE NI BK NICE NA FAD'A MISHI😏😏*
*SA'KO ZUWA GA MASOYANA💌*
*Amincin Allah su tabbata ga masoyana ma'abota aminci,🙏😊 wasu daga cikin masoya sun kirani wasu sun yo min test message wasu sun tambayeni ta watsapp wai sun sami labari ni 🅱K nima na maida littafina na kud'i, ma'ana sai an biya kud'i zan tura wai shiyasa na daina typing kwana biyu, wasu kuma rok'ona suke yi dan Allah kar nima ince zan maida novel d'ina na kud'i, to maganar gaskiya bansan da wannan zancen ba, hasali ma rashin lafiya nake shiyasa kuka jini shiru kwana biyu, duk wainar da ake toyawa bansan da ita ba sai da sak'onnin masoyana ya iso gareni, to masoyana ku kwantar da hankalin ku novels d'ina duka kyauta ne babu kud'in da zansa akai ince ku biyani, abu d'aya nakeso kuyi ku biyani dashi shine dan Allah kar ku manta dani cikin addu'arku a yanzu da nake a raye da kuma bayan na mutu, addu'arku gareni itace zata tabbatar min da cewa kuna k'aunata k'auna ta gaskiya, Allah ya barmu tare, wallahi na matuk'ar jin dad'in k'aunar da kuke gwada min yanda kuka nuna damuwarku kan lamurana da kuma abinda ya shafi novel d'ina, kamar yanda nake jin farin ciki mara misaltuwa a duk lokacin da naci karo da masoyana ko kuma nai magana dasu kai tsaye*
*NAGODE! NAGODE!! NAGODE!!!*
PAGE 105 to 110
Insp Yahya shi da wasu murd'a murd'an 'yan sanda suka yo kan Amir, Amira ta tsaya gaban Amir tare da 'kan'kame shi tana girgiza kai tare da kallon bataliyar 'yan sandan da suka yo kansu domin jibgar mutum d'aya tak, tace "karku sake ku tab'ashi ba shi bane yai kisan fa Dad ni na kashe shi da hannuna," Amir da ke shirin yin magana ta ri'ke hannun shi sannan cikin rad'a tace " kar kace komai Amir muddin kana son mu cigaba da rayuwa a tare."
Dad da kanshi ya tako har inda Amira take ya sharara mata kyakkyawan mari jin abinda take fad'a, sannan ya kama hannunta ya jata har cikin mota ya sakata ciki sannan ya rufo ya dawo ya bada umurnin aiwa Amir wanda ke ta faman kwad'a wa Amira kira yana kuka tunda aka b'anb'areta daga jikin shi duka, Insp Yahya shine kan gaba, kafin ya fara dukansa ma bayan sun k'araso gabansa sai da ya kalli Amir yai mishi wata irin dariyar da ke d'auke da ma'anar yau gaka a hannu na me 'kwatarka sai Allah, haka sukaita dukansa ba ji ba gani kuma Insp Yahya yafi kowa jibgar Amir.
Nan fa suka rufar mishi da duka ta ko'ina tun yana iya yin 'kara har muryarsa ta disashe kuma duk da haka Dad be bada umurnin a daina dukansa ba, Amira ce ta fito daga mota da gudu Allah ya bata sa'a ta warce wata bindiga dake hannun wani d'an sanda cikin sauri kuma ta saita kanta da bindigar tare da fad'awa kan Amir tana saite da bindigar, Dad ne ya k'wala mata kira da k'arfi, Amira tana kuka tace "wallahi Dad nice na kashe shi, Amir ya yi hakan ne kawai domin ya kub'utar dani daga fad'awa hannun 'yan sanda, sannan yai haka ne saboda soyayyar da yake min shiyasa ya d'ora laifin kansa, Dad kama kuwa gane wanda ke tare da 'yarka har yanzu? to yaron nan ne dai da ka rabamu tun muna 'kanana, zuwa yanzu ya kamata ace ka gane cewa had'uwarmu daga Allah ne, kuma duk abinda Allah yaso faruwarsa babu mai iya canza shi ko wanene, Dad kasan tun ina yarinya ban saba yi maka 'karya ba ko laifi nayi na gwammace in fad'i gaskiya ka hukunta ni, to yanzu ma gaskiyar zan sake fad'a maka duk duniya babu wanda nake so nake 'kauna sai Amir kuma babu wanda zan iya aura in ba shi ba, dan Allah Dad ina ro'konka ka 'kyalemu mu tafi, in kuma ba haka ba zaka rasani na gwammace mutuwa da inga ranar da zaku rabani da Amir domin Amir shine *MAHA'DIN RAYUWATA* " har ta gama magana tana saite da bindigar bata sauke ba, kuma bata daina magiya ba, shima Amir kuka yake suna ri'ke da juna gam kamar wad'anda za'a raba, af ashe fa rabasun za'ai ko😰 jin abinda Amira ta fad'i babu abinda ya 'karawa Dad banda tsananin tsanar Amir, dama shine yaron da sanadin shi ne ya dawo da karatun Amira kacokam garin kano amma duk da haka saida ya biyota nan d'in ma, zuciyar shi fad'i take ashe d'an iskan nan shi ya ruguza min mafarkina a kan Amira, ji ya yi tsanar Amir ta dad'a nunkuwa, cikin fushi yace " ku cigaba da dukansa har sai nace ku daina," Amira ta sake kare shi tare da saita bindigar a kanta tace " wallahi Dad duk suka 'kara dukan Amir sai na kashe kaina da wannan bindigar," Dad ya dakatar da su cikin sauri domin yasan tabbas abinda Amira ta fad'i zata iya aikatawa, tunani ya yi kan dole sai an biyo musu ta siyasa kafin su sami damar tafiya da su.
Umma da Baba kuwa babu abinda suke yi banda kuka, duk da basu san meke faruwa ba amma sun tausayawa yaran dan jinsu suke yi kamar yaran da suka haifa a cikin su.
Dad ya kalli Amira yace " yanzu me kike so ayi?" Amira tace " so nake ka yi ha'kuri Dad ka barmu mu tafi," Dad ya kalleta yace " a'a bazai yiwu ba in barku ku tafi Daughter, kece 'ya d'aya tilo a wajena, kuma kinsan tunda nemanku ake a ko'ina koda kun tafi k'ara kamaku za'ai a wani wajen, kinga kuwa tafiyarku sam bata da amfani muddin ba'a kashe case d'in ba, yanzu abinda za'ai shine ki bari muje station a kashe magana kuma ku saka hannu tukun," sai a lokacin hankalin su ya d'an kwanta, amma ganin irin kallon da Dad ke wa Amir yasa jikin Amir d'in yai sanyi kuma zuciyarshi na kokwanto kan zancen da yai musu.
Anyi - Anyi da Amira ta ajiye bindigar hannunta amma ta'ki ajiyewa, tama 'ki yarda a matso kusa da ita balle su 'kwace, dole a haka suka d'auki hanya sai station, ko da isarsu suka tarar da rundunar 'yan sanda da sojoji suna jiran zuwan su, nan jikin su Amir da Amira ya 'kara yin sanyi sosai.
keb'ewa Dad yayi shi da kwamishina suka d'an yi wata magana kawai sai gani suka yi an kama Amir an jefa shi cikin cell, ita kuma Amira aka mamayeta aka 'kwace bindigar dake hannunta aka jata zuwa bakin mota, tana ihu tana tirjiya tana 'kwala wa Amir kira amma duk da haka basu daina janta ba, shima Amir d'in 'kwala mata kira yake ta faman yi, Amira tace " in har kana 'kaunata da gaske to duk zafin kowane irin hukunci kada ka tab'a amsa laifin da ba kai ka aikata shi ba Amir d'ina," abinda take ta faman maimaitawa kenan har aka fice da ita daga station d'in, suka shiga motoci suka d'auki hanyar tafiya Abuja, suna tafiya Amir nan take yaji kamar an rabashi da wani b'angare na jikinshi ne, dur'kushewa yai a cikin cell d'in tare da 'kwala 'kara had'e da fashewa da kuka, nan take ya fad'i 'kasa a sume.
Insp Yahya yai murmushi, sannan yace " zaka farfad'o ne ma, ya baiwa jami'an tsaro damar su shiga su watsa mishi ruwa sannan suita dukanshi har sai ya fad'i gaskiya," yana gama basu umurni suka amsa tare da sarawa suka fara aiwatar da umurnin da aka basu, kwamishina da Insp suka fito ya rakashi har bakin mota, kwamishina yana 'kara fad'a mishi cewa su tsananta tsaro da kuma d'aukar duk wani matakin da ya dace domin ganin ya fad'i gaskiya, daga nan suka yi sallama kwamishina ya shiga mota tare da rundunarsa suka tafi.
Amir kuwa tunda aka kawo shi ake faman dukansa, duk ya suma sai su watsa mishi ruwa yana sake farfad'owa sai a cigaba da dukansa, amma har yanzu ya'ki amsa laifinsa, babban abinda ke basu mamaki dashi shine baya 'kara ko ihu, iyakarsa hawaye, in kuma aka tambayeshi amsar d'aya ce zuwa biyu, bashi bane yai kisan kuma koda shi yayi yana yiwa soyayya biyayya bazai tab'a sab'a umurnin Amira ba.
B'angaren Amira kuwa koda isowarsu suka fito daga cikin mota Dad ya kama hannunta tare da jantahaka ya wuce kowa na gidan ba tare da yace uffan ba, cikin wani keb'antaccen d'aki ya sakata, sannan ya saka masu tsaro masu yawa a bakin k'ofar, bayan ya fito falo kuma ya gargad'i dukkanin mutanen gidan kan be yarda kowa yaje gun Amira ba in har ba abinci za'a kawo mata ba, yana gama fad'in haka ya shige d'aki abinshi, kwamishina ne ya kira Dad yana tambayarshi yanda yake so ayi da yaron, "no ku barshi ya d'and'ana tukun kafin mu yanke shawarar tura shi kotu sai ya karb'i horo da hukuncin sace min 'yata da yayi," abinda Dad ya fad'a kenan, suna gama waya ya kira babban yaron shi tare da bashi umurnin k'ara yara da tsaro sosai a gidan.