Sashe 26
So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haka Amira ta kwana ta yini tana kuka ba ci ba sha, babu abinda take koka mawa irin tunanin halin da Amir yake ciki, ta kasa samun natsuwa zuciyarta ce kawai ke ayyana mata ta gudu taje ta ganshi, to amma tayaya zata fita daga gidan nan ba tare da an ganta ba? tambayoyi taita yiwa kanta wanda ta kasa samun mafita.
A dai-dai wannan lokacin shima Amir ita yake tunani, yasan yanzu tana can tana kuka, ya tabbatar bata ci komai ba saboda sun saba cin abinci a tare, ji yayi kawai wani irin 'karfi yazo mishi, ya mi'ke tsaye tare da kallon Insp Yahya yace "ku bud'e ni inyi futsari," Insp dake zaune kan kujera ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya yana cin gyad'a ya kalle shi yace "yi anan," da Amir yaga in ya biyo mishi ta haka sam bazai saurareshi ba gashi shi a yanzu Amira kad'ai yake son gani, kallon Insp Yahya yayi yace "banza d'an daudu kawai, wai kai menene ribarka in ka raba masoya, muddin na fito daga cikin gurin nan sai naci ubanka d'an iska ba'kin mugu kawai," nan da nan Insp Yahya ya tunzura ya mi'ke a fusace cikin fushi ya nufo 'kofar cell d'in, to dama Amir abinda yake so kenan ya tunzura Insp dan ya samu ya bud'e shi, kiran wani jami'i yayi cikin b'acin rai yace ya bud'e wajen, yana bud'ewa Insp ya shiga, yana shiga Amir ya cakumeshi suka fara gwabzawa, nan fa yan sanda sukai caaaaa a kan Amir amma duk yawansu sai da yai musu shegen duka, daga k'arshe ma har ya saka kayan d'aya daga cikin 'yan sandan wajen ya fice daga station d'in.
Tasha yaje ya tsayar da mota ya hau aka ja suka tafi sai Abuja, a dai-dai tashar Abuja suka sauka Amir ya fito kenan ya hango Amira cikin tasha zata shiga cikin wata mota, tafiya ya fara yi zai je wajenta yaji me motar nan yace "yallab'ai baka bani kud'in mota ba," Amir ya juyo tare da lalibar Aljihu yana duba wa cikin sa'a ya ciro kud'i a aljihun ya biyashi kud'insa, yana waigowa kuma ya duba baiga Amira ba a inda ya hangota, zuwa wajen motar yai da sauri ya le'ka bata ciki, nan fa ya shiga nemanta, yana zuwa bayan kangon tashar ya jiyo kamar numfashi a bayanshi, yana juyowa yaga ashe itace ta b'oye a wajen, wani irin hawaye yaji masu d'umi suna gangaro mishi, ji yayi ana fad'in "ku dudduba ko ina ku kamo ta nasan tunda sun ganta tana nan bata yi nisa ba," Amira sam bata ga Amir ba domin ta juya baya, jin abinda securitys d'in da aka baza su kamota ke fad'i yasa Amira ta yun'kura zata gudu, har ta fara gudu kafin su ganta Amir yai wuf ya jawota ta fad'o jikinsa cikin sauri kuma suka du'ka, ganin d'an sanda ne ya ri'keta ya k'ara rud'ata 'ko'karin 'kwacewa take dag ri'kon da yai mata tana fad'in "dan Allah ka 'kyaleni yallab'ai ka barni inje inga halin da masoyina ke ciki," Amir yasa hannu cikin sauri ya rufe mata baki, a yayin da d'ayan hannun ke rik'e da ita sannan yace, "wane masoyin naki zaki tafi gani bayan wanda yake a tare dake a yanzu haka," jin muryar da ko a mafarki ta jita zata gane yasa cikin sauri ta d'ago tana kallon shi, Amir kuwa a hankali ya d'ago da kanshi tare da cire hular kanshi ta 'yan sandan da yasa ya sakar mata murmushi, Amira ta zaro idanu sai kuma ta rungume shi tare da fashewa da kuka tace " Amir nayi kewarka, mutuwa kad'ai zanyi idan na rasaka a rayuwa," shima rungumeta ya yi, sannan ya rufe mata baki yai magana 'kasa 'kasa yace kiy shiru kar a ganmu a kama mu, ki bari su tafi mu samu mu gudu wani wajen," bayan kamar minti biyar sai suka ji ana fad'in "oga gasu nan sun b'oye anan gasu nan na kamasu."
Muje zuwa
*🅱K CE😘💋*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (🅱K)*
(Autar marubuta)
SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
(Mamie)
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
(Gidan zaman lafiya da amana in sha Allah)🤜🤛
*MY ASIYA IMAM SEE-SEE ina tayaki murnar kammala novel d'inki mai suna 💜MASAKI NA,💜 Allah ya 'kara miki basira d'aukaka, da d'an karen za'kin hannu, sabon novel d'in da kika fara yanzu kuma mai suna 💙BAMU DACE DA JUNA BA💙 Allah yasa yanda kika fara lafiya ki gama shi lafiya.*
*AISHA ISA, MUMMYS FRIEND, (TAWAN) ina ro'kon mahaliccina Allah ya d'orar miki da lafiya mai d'orewa👏😭*
*MEELAT A.H.K*
*(Bloodynah) da ni da ke 'kauna muke domin Allah ba da yaudara ba*👯♀😍😘💋
PAGE 110 to 115
Amir yasa hannu ya kwad'e wannan mutumin da yake ta faman antayo wa sauran kira suzo ya kama su, ya ri'ke hannun Amira suka danna a guje, nan da nan suma suka bisu a baya, wani mutumi ne ya faka mota ya fito Amir ya tura Amira cikin motar ya shige yaja me mota yana ta kurma ihu yana binsu da gudu, suma securitys d'in motocin su suka shiga suka bi bayansu a guje.
Suna faman gudu ana binsu a baya har Allah ya basu sa'a suka tsere musu, suna yin nisa sosai suka ajiye motar a bakin ti-ti sannan suka nausa cikin dajin dake hanyar, dukkaninsu sun galabaita kan dole suka ja suka yada zango a cikin tsakiyar daji ba dan sun so tsayawa anan d'in ba a'a, saboda tsabar gajiyar da suka yi ne.
Amira ta fara bajewa a 'kasa tana fad'in "Amir 'kishi nake ji," Amir yace " Amira yanzu ina zamu sami ruwa a cikin wannan dajin, amma bari inje in dubo ko zan samu, ki zauna anan kar ki matsa ko ina," Amir ya nausa cikin daji neman ruwa shima 'karfin hali kawai yake amma hatta tafiyar da kanta da 'kyar yake yinta, sai da ya d'auki lokaci yana tafiya Allah ya had'a shi da wani rafi sai a lokacin kuma ya rasa a me zai d'iba ruwan ya kai mata, yana cikin wannan tunanin ne yana waige-waige Allah ya sada shi da wata bishiyar kankana, cikin sauri yaje ya hau bishiyar ya katso 'katuwar ciki ya fafe samanta, har ya kai baki alamar zai sha ya tuno da Amirarsa itama tana can kwance yunwa da 'kishir ruwa na damunta, hakan yasa ya fasa ya fitar da kankanar duka a 'kasa ba tare da ya sha ba, sai da yaga ya yi yanda yake so yaje ya d'ibi ruwa a ciki ya nufi hanyar da ya biyo domin kaiwa Amira ruwan, yafi awa yana kai kawo cikin dajin saboda ya kasa gane hanyar ta b'ace mishi, sai daga baya Allah ya kawo shi har inda take, ko da yazo ya tarar Amira har ta fara baccin wahala.
Amir ya tashe ta tare da mi'ke mata ruwan, Amira ta kalle shi tace "ka fara sha mana," Amir yace "ai na sha kafin in kawo miki," sai da Amira tasha mai isarta sosai, sai da ta kusa shanyewa sannan ta mi'ka mishi, tana mi'ka mishi ya kafa kai ya shanye sauran, binshi tayi da kallo a zuciyarta tace Allah sarki Amir wato saboda kar in 'ki sha idan naji be sha ba shine yace min ya sha, a fili kuwa tace "shine kace min kasha a can ko."
Amir yace "kin fini bu'kata ne shiyasa, kuma bazan iya sa komai a bakina ba muddin ke kina cikin irin wannan halin," nan fa Amira tasa daru ita wallahi bata yarda ba sai an koma wajen yasha shima, ai kuwa haka aka yi suka koma wajen ya katso musu kankana sukai ta sha, daga nan bakin bishiyar suka yada zango bacci yai awon gaba dasu.
Wad'anda aka sa su biyo su Amira kuwa suna zuwa suka ga motar da suka hawo an taho harda me motar ya shiga abarsa yaja ya tafi, su kuwa sai da suka 'kara duddubawa sannan suka juyo domin komawa su fad'awa Dad halin da ake ciki.
B'angaren Dad kuwa koda securitys d'insa suka dawo mishi da bayanin wai Amir yazo ya d'auketa sun gudu kuma basu ga inda suka yi ba, baida aikin komai sai kai kawo, cikin sauri ya buga wa Insp Yahya waya da sauran manyan sojojin sa yai musu kwatancen dajin da aka fad'a mishi anga motar da suka shiga, sannan ya d'au al'kawarin baiwa duk wanda ya kamasu kud'i mai tsoka, bayan ya gama wayar ya kalli yaran nasa yace "bana son sake ganin fuskarku a gidan nan, ku koma dajin kuje a nemo su daku a kawo min su nan gabana, suka juya cikin sauri suka fito suka k'ara nausawa dajin, jefi-jefi kuma suna yin waya da Sojoji da su Insp Yahya yana tuntub'arsu abinda ke faruwa.
Washe gari da sassafe Amir ya tayar da Amira suka sha kankana suka sha ruwa, sannan suka ci gaba da tafiya cikin dajin nan, wannan dalilin ne yasa duk jami'an da aka turo suka kasa tarar dasu sai da sukai kwana uku cikin dajin nan, a koda yaushe in sun sami guri sun kwana inda zasu sami d'an abun tab'awa gari na wayewa sai su sake d'aukar hanya, sam basu zauna gu d'aya ba gudun kar azo a kama su.
A kwana na uku ne Allah ya sake kaisu cikin wani dajin, suka yada zango kasancewar yamma tayi, duk da suna cikin damuwa hakan be hana su cigaba da rayuwarsu cikin walwala ba, a ranar sun dad'e suna hira a wajen sai wajen 'karfe sha biyu sannan suka kwanta, kuma inda Allah ya taimake su har zuwa wannan lokacin Allah bai had'a su da wani abu na cutarwa ba.