Sashe 23
So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dattijon nan yai shiru can sai ya numfasa, kafin yai magana Amir ya sake cewa ‘’dan Allah Baba ka taimaka mana mu ba masu cutarwa bane nasan tunanin da kake yi kenan a zuciyarka, wallahi ba zamu cutar daku ba, ka taimake mu domin girman Allah zaka ji dukkanin labarin mu daga baya.‘’
Baba yace ‘’to shikenan yaro ku biyo ni muje,‘’
Shi dai Baba ya yi shahada ne ya tafi dasu ba don hankalin shi ya kwanta da bayanan da suka yi mishi ba, haka suka tafi Baba yana gaba suna binshi a baya har cikin k'auyen, suka tsaya a bakin wani k'aramin gida irin gidajen k'auyen nan amma k'aramin gida ne sosai.
Kai tsaye Baba ya basu izini suka shiga gaba d'ayan su, matar shi ta amsa tare da fitowa daga d'aki tace ‘’sannu da zuwa mai gida, tare da bak'i kake tafe ne sannunku da zuwa,‘’ ta shiga cikin d'aki ta fito da k'atuwar tabarma ta shimfid'a sannan suka zazzauna.
Bayan sun gaggaisa sannan mai gidan wanda su Amir suka kira da Baba ya kalli matar shi yace ‘’wad'annan bayin Allahn bak'inmu ne, a hanya na had'u da su suka nemi taimakon masauki a wajena na wasu kwanaki, tunda wancan d'akin da A'i tai aure ba kowa a cikinsa to a gyara musu su sauka a ciki.‘’
Wannan dattijuwar matar da Baba ke mata dukkanin wad'annan bayanin sai ta sake kallon su Amir cikin fara'a ta sake musu sannu da zuwa, ta mik'e da nufin zuwa ta gyara d'akin, sai Amir ya dakatar da ita ta hanyar fad'in ‘’ dan Allah Umma ki bar gyaran d'akin zamu gyara, ai mun gode ma da kuka bamu masauki Allah ya saka muku da alkhairi, Allah ya biyaku da gidan aljanna firdausi.‘’
Duk yanda su Amir suka so su hana Umma gyara d'akin tak'i bari, a cewarta ai su bak'in su ne be dace ace yau daga zuwansu ta barsu sunyi aiki ba, dolen su suka hak'ura suka k'yaleta, bayan ta gama gyarawa ta yi musu izinin shiga, suka shiga suka zauna aka kawo musu abinci da ruwa.
Suka ci abincin suka sha ruwan sannan suka ci gaba da kallon d'akin suna tunanin yanda zasu kwana a cikinsa, tabarmi ne guda biyu a cikin d'akin aka had'e su waje guda, sai wata tsohuwar gana mas go, Amir yace ‘’kiyi hak'uri Amira ni na jawo miki kwana irin wajen nan, gobe in Allah ya kaimu zamu san yanda zamu yi mu sami 'yar k'aramar katifa mu sa a d'akin kafin mu tafi.‘’
Amira ta kalle shi tace ‘’ a'a in dai don saboda ni ne to karka damu, ina ma muka ga kud'i mu da muka fito ko shiri babu, ka kwantar da hankalinka zan iya zama a ko ina ne muddin ina tare da kai, amma d'azu a hanya naji ka cewa Baba zaka bashi labarin mu, to kar ba shiba ma karka tab'a fad'awa wani abinda ya faru har abada, ko da ka tashi baiwa Baba labarin kawai kace musu mu miji da mata ne, kan hanyar mu ta zuwa garinmu akai mana fashi shiyasa muka sauka a wannan k'auyen.‘’
Amir ya kalleta yace ‘’to shikenan Amira ta, yanda kika ce haka za'ai.‘’
Da dare yayi suka ja tabarmin suka raba su shi Amir yana farkon d'akin, ita kuma Amira tana can ciki, sedai sam sun kasa bacci, daga k'arshe ma hirarsu suka sha, sannan suka yo Alwala suka yi nafila da addu'o'in neman mafita wajen Allah mahalicci, sai da asuba sannan suka kwanta amma sam bacci yak'i ziyartar su.
Washe gari Amir da Amira suka tashi suka je d'akin su Umma suka ci sa'a Baba yana nan, bayan sun gaisa sai Baba ya kalle su yace ‘’ya kamata ku sanar da mu sunanku da labarin ku da kuma abinda ya kawo ku wannan k'auye namu.‘’
Amir ya gyara zama sannan yace ‘’sunana Amir, wannan kuma ya nuna Amira matata ce sunanta Amira,‘’ nan fa ya kwashe duk yanda Amira ta zayyana musu ya fad'a musu, sun tayasu jimami tare da yi musu Allah kyauta gaba, nan shima Baba ya basu labarinsa a tak'aice ya fad'a musu yana da yara har hud'u dukkansu mata, kuma dukkansu an yi musu aure, kasancewar auren k'auye daban da na cikin birni, sun dad'e suna hira kafin daga k'arshe Baba ya tashi zai tafi gona Amir ma yace zai bishi suka tafi tare, a ranar tare suka yi aikin gonar domin Amir ya dage lallai sai ya yi, haka itama Umma da Amira tare suka yi dukkanin aikin gidan.
Bayan kwana biyu Amir da Amira suka murmure suka saki jikinsu tare da sabawa da komai na k'auyen daga kan cimarsu har zuwa suturun da suke sakawa kasancewar su Amira dama ba kaya suka shigo k'auyen daga su sai na jikin su.
Kuma daga lokacin da suka shigo k'auyen basu k'ara barin iyayen gidan su sunyi wani aiki ba, Amir shi yake wa Baba duk wani aiki na gonarsa, itama Amira ita take duk aikace aikacen cikin gida, sun hutar da wad'annan dattijan daga yin kowane irin aiki, to dama shi Amir ya riga da ya saba da wahalar rayuwa tun yarintar shi, Amira ce ma kafin ta saba ta sha wahala sosai saboda rashin sabo ta riga da ta saba komai se dai ai mata, d'an aikin da take wa kanta be taka kara ya karya ba.
....................
Insp Yahya ne zaune a office yana waya, be wani d'auki lokaci me tsaho ba ya gama wayar, d'agowa yayi ya kalli d'an sandan da ke k'ame a gaban shi yace ‘’ya ake ciki, an samu nasara kan abinda na turaka bincike akai?‘’
'Dan sandan da ke tsaye gaban Insp Yahya yace ‘’yes sir na samo bayanai gasu nan a cikin wannan takardar, mahaifin ita Amira shine shugaban k'asar nan ma a yanzu, kuma har lambarsa ma duk na samo, shi kuwa Amir bamu samu wani cikakken bayani a kanshi ba, sedai labari da muka samu ya tab'a rayuwa a kusa da gidan su Amira amma ba wani labari kan iyayensa,‘’ ya 'karashe maganarsa tare da mi'ka mishi takardar bayanin dukkanin abubuwan da ya fad'a mishi.
Insp Yahya ya karb'i takardar nan ya duba sannan ya d'ago fuskar sa d'auke da murmushi, yace ‘’da kyau mutumina kayi aiki me kyau, zan kira mahaifin Amira in sanar dashi duk abinda ke faruwa, kaga shi zai taimaka mana sosai wajen kama Amir cikin sau'ki, kuma dole mahaifin Amira shima ya d'auki mataki akan Amir in yaji 'yar shi bata makaranta tana tare da wani 'kato 'katon ma makashi, zaka iya tafiya kayi aiki me kyau na jinjina maka.‘’
Bayan d'an sandan nan ya yi godiya ya sara sannan ya fice, Insp Yahya ya d'auko wayarsa ya shigar da lambar mahaifin Amira cikin waya sannan ya rangad'a kira.
Dad da ke zaune cikin iyalen shi suna hira yaji wayarsa ta fara 'kara alamun ana kiransa, bayan ya d'aga tare da sallama, Insp ya amsa cikin girmamawa bayan sun gaisa sannan yace ‘’dama na kira ne in sanar da kai abinda ke faruwa da halin da 'yarka take ciki, wani yaro ne Amir yai kisa,‘’ mahaifin Amira cikin sauri tare da 'kosawa ya mi'ke cikin sauri tare da katse shi ta hanyar fad'in ‘’to miye had'in kisan shi da lamarin yarinyata? Insp Yahya yace saboda saurayin Amira ne, kuma tunda aka gano shi yai kisan anzo kamashi suka gudu tare shi da Amiran har yanzu bamu gano inda suke ba, shine na kira domin in sanar da kai halin da ake cik....... kafin ya 'karasa maganarsa Dad ya katse shi cikin tsawa yana fad'in karka 'kara had'a 'yata da makashi in ba haka ba zan hukunta ka wallahi, Insp Yahya yace ‘’ka yi ha'kuri amma in baka yarda ba kayi bincike akai,‘’ Dad be tsaya cigaba da sauraren sa ba ya katse wayarshi, lambar kwamishina dake kano ya fara kira bayan sun gaisa ya tambayeshi waye Insp Yahya, kwamishina ya fad'a mishi cewa jami'i ne 'kwararre kuma me sanin makamar aiki, sai Dad ya bashi umurni akan yana so aje makarantar da Amira ke ciki a bincika mishi Amira tana nan ko bata nan, kuma a binciko mishi waye Amir kuma yanzu yake so, Kwamishina ya amsa suka yi sallama nan da nan ya tashi da kanshi tare da yara suka tafi makarantar, shi kuwa Dad banda kai kawo a tsakiyar d'akin ba abinda yake yi, su kuwa k'aninshi da matarshi da sauran 'yan gidan binshi kawai suke da kallo domin jin wayar da yake sun san tabbas maganar ta shafi 'yar su Amira, suna so suji 'karin bayani amma kowa shakkar yiwa Dad magana yake ganin halin da yake ciki, dama muddin ya shiga irin wannan yanayin to tabbas babu me iya tanka mishi saboda gudun abinda zai biyo baya.
_Hmmm tab' da sauran rina a kaba, Amir ka lallab'a ka tsere tun kafin Dad ya gano kaine._
Muje zuwa
*🅱K CE😘💋*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (🅱K)*
(Autar marubuta)
SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
(Mamie)
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)
*MASOYANA NA NESA DA NA KUSA BANDA ABINDA ZAN SAKA MUKU DASHI KAN K'AUNAR DA KUKE GWADA MIN, SE DAI IN ROK'I MAHALICCINA ALLAH YA BIYAKU DA KYAKKYAWA KUMA YA K'ARA MUKU SONA😍😍😍😘💋*
*Tabbas komai yai farko zai yi 'karshe, RAHEENAT M. ABBAKAR ina tayaki murnar kammala Novel d'inki mai suna 🌲HALIN RAYUWA,🌲 Allah ya bamu ikon amfana da tarin darussan dake cikinsa, ya bamu ikon watsi da kura kuren cikinsa, abinda kikai dai-dai Allah ya baki ladan, kuskuren dake ciki kuwa Allah ya yafe miki, Allah ya 'kara miki basira, d'aukaka, da d'an karen za'kin hannu, sai mun jiki cikin sabon novel d'inki.😍😘💋*
PAGE 100 to 105
Bayan d'an wani lokaci sai ga kiran kwamishina cikin sauri Dad ya d'aga yace ‘’ya ake ciki tana nan kuma kun ganta da idanunku?‘’ kwamishina yace ‘’gaskiya bata cikin makarantar nan domin ta ma dad'e bata shigowa ciki, ance tana tare da wani yaro wai saurayinta ne, se dai ba'a san inda suke ba.‘’