Sashe 18
So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Tun daga wannan lokacin k'ok'arin Amira ya dawo sosai, sedai sam shi Ameeru baida k'ok'ari baya gane komai, to da yake ajin su Amira d'aya dashi idan an tashi break zama suke yi tai ta koya mishi tana nuna mishi itafa bata jin dad'in dariya da ake mishi kullum be iya komai ba, Ameeru ya bata amsa da zai dage yai karatu ko dan ita in ya girma ya kyautata mata kamar yanda itama tai mishi, cikin ikon Allah kuwa ya d'an fara ganewa.
Daga kan Malaman makarantar kaf har zuwa d'alibai Ameeru da Amira suna burge kowa, duk inda suka shiga sha'awarsu ake, had'in kansu da shak'uwarsu abun burgewa.
Ko laifi d'aya daga cikinsu yaiwa malami to basa yarda a hukunta d'aya, se dai a hukunta su gaba d'aya, idan horo aka baiwa d'aya dukkansu suke fitowa, in za'ai duka kuma dukkanin su suke mik'a hannu da wanda yai laifin da wanda be yi ba, kowanne daga cikin su k'ok'ari yake yaga an dakeshi shi an k'yale d'an uwansa, wannan shak'uwar tasu ce tasa suka k'ara burge kowa, kuma kowane malami yake k'aunarsu.
Abu d'aya ne yake damun Dad d'in Amira shine, Ameeru baya so koda kallon banza aiwa Amira balle har a tab'a lafiyar jikinta in kuwa kai mata hmmm, yasha targad'a yara da karyasu kai raunika iri-iri a kan Amira, iyayensu na zuwa suna kai k'ara gun shugaban makarantar, da abun ya ishe su sai shugaban makarantar ya kira Dad d'in Amira ya sanar dashi.
Kuma kullum Ameeru yai fad'a kan Amira sai an zane shi, amma hakan be hana shi gobe ma ya yi, shi in za'a tab'ata sau dubu to shima zaiyi fad'a a kanta sau dubu, dukan da ake yi mishi sam be damunsa.
Zaune Ameeru yake a kusa da ajinsu, koyarwa ma ake yi a ajin, wani ya harari Amira ya mareshi, shine malamin ya zaneshi kuma yace ya fito ya bar mishi ajinshi ya saka guiwarsa a rana har sai ya gama ya fito.
Amira na ganin an koreshi itama ta fito, malamin su na kira amma ina sai ma ta danno a guje tazo kusa dashi itama tayi irin horon da aka sashi, suka kalli juna sukai murmushi, Ameeru yace " wato saida kika fito ko," Amira tace " eh mana kana waje saboda ni sai in zauna a ciki," suka yi dariya sannan Amira ta sake kallon shi tace " meyasa kake fad'a a kaina Ameeru?" Amir yace saboda ina sonki, kuma bazan tab'a bari a tab'aki ina kallo ba," Amira tai dariya tace " laaaa ashe kaima kana sona," dukkansu suka sa dariyar murnar suna k'aunar juna, Amira ta sake kallonshi tace " jiya Dad ya kirani yace wai anyi mishi waya ance bama k'ok'ari a makaranta, sai nace mishi eh mana Dad koyaushe cikin karb'ar hukunci muke," Ameeru yace " ni fa tsoron Dad nake kar ya dukeni," Amira ta b'ata rai tana fad'in ka tab'a ganin ya dukemu ne," sufa gaba d'aya rayuwarsu basu da matsala muddin suna tare.
Abun nasu fa sai gaba gaba yake sun fitini kowa dan yanzu itama Amira in d'alibai suka daki Ameeru taron dangi suke yi su biyu su daki koma waye, sannan itama haka in ita aka tab'a taruwa suke su daki mutum, gaba d'aya makarantar yanzu shakkar su ake.
Akwai ranar da Amira ta taho da gudu tana fad'awa Ameeru ga wani can yazo yace yana sonta, da gudunsu dukaje shima suka yi mishi duka, ashe sun mishi targad'e a hannu, tun daga ranar Ameeru ke bawa duk yaron da yaga ya kula Amira kashi, in ma be gani ba ita tana fad'a mishi, domin ta sanar dashi tana jin dad'in yanda yake cin uban mutane a kanta.
Abu fa ya ishi Dad d'in Amira kullum cikin waya ake mishi sunyi kaza da kaza, hakan yasa ya fara tunanin lallai muddin yana so 'yarshi tai karatu to sai ya bar garin nan sun koma wani garin da zama, akan wannan shawarar ya tsaya.
Zaune suke a falo dukkanin 'yan gidan Dad ya fad'a musu shawarar da ya yanke, kuma yace ya gama magana babu me canza mishi, zasu koma gidanshi da yake kano saboda 'yaranshi sami ilimi me kyau, kuma ya fad'a musu akan 'yarshi babu abinda bazai iya yi ba kuma zai iya barin k'asar ma da ita domin ta samu ilimin da yake buri, sun riga da sun san halinshi murd'ad'd'en mutum ne in ya kafe a abu juyo dashi abune me wahala, sun gama maganar kenan sai ga Amira ta dawo daga makaranta, tana shigowa Dad d'inta ya kalleta yace " oyoyo My Daughter, zo in miki albishir zamu je kai ziyara kano gobe in Allah ya kaimu, amma bazamu dad'e ba zamu dawo, kuma in har kina sona kuma kina son farin ciki na ban yarda ki b'ata rai ba ko kiy kuka," Amira ta kalle shi tace " harda Ameeru na za'a tafi?" Dad yace a'a ai ba zamu dad'e ba zamu dawo, " ita har ga Allah bata son tafiyar nan, amma sai tace "to bari in je in fad'a wa Ameeru in dawo," har ta juya da gudu Dad d'inta ya k'wala mata kira ta dawo yace ta bari sai goben in zasu wuce sai taje suyi sallama, haka nan ta hak'ura ba dan taso ba.
Washe gari tun asuba kowa ya tashi ya shirya, itama Amira ta tashi tazo sakkowa taji maganar Dad d'inta yana fad'in ai bazan bari su had'u da Ameerun ba," jin ya ambaci sunan Ameeru tasan zancensu ake, hakan yasa ta tabi ta k'ofar baya ta fice, sai kuma ta dawo taje d'akin Dad d'inta ta d'auko k'atuwar jakarshi wadda ke cike da kud'i ta fito da ita kamar zata rinjayeta ma, ta shiga cikin d'aki tare da kwaso hotunan su da wanda suka yi tare da wanda take ita kad'ai shima haka, ta ware d'ai-dai ta saka mishi cikin zip d'in jakar, sannan ta fita tana share hawaye har bakin gate d'in gidan marayun, ta shiga ta tarar da me kula da su Ameerun, bayan sun gaisa ta tambayeta ina yake tace ya shiga wanka, sai Amira ta bata jakarnan tare da rok'on ta ta baiwa Ameeru injita harda 'yar takarda, sannan ta juya ta tafi, a hanya taga su Dad sun fito nemanta sukai kicibis, ya kama hannunta suka shiga gida jikinta duk a sanyaye, aka shiryata suka shiga mota tare da security's d'insu bayan an rufe ko ina, sun fara tafiya kenan sun wuce gidan marayu kenan sai ga Ameeru da gudu yana k'wala musu kira amma ina sesai Amira ta hango shi, bin motar da gudu yake yana kuka, itama tana kuka har ya gaji da gudun ya durk'ushe a k'asa kan ti-tin yana kallon motar Amira na d'aga mishi hannu tana kuka.
Komawa cikin gidan marayun da ya zama gidansu ya yi, ya shiga d'akin da yake mallakin shi ya jawo akwatin da Amira ta bashi, dan Amira ta cewa maman kayan sawanshi ne a ciki saboda su zasuyi tafiya shine ta kawo mishi, hakan yasa bata bud'a ba taga ko miye a ciki har ta bashi.
Koda ya bud'e kud'i ya gani masu uban yawa 'yan dubu dubu cike da jakar, wanda suka sashi mugun razana harda matsawa da sauri kamar wanda yai gamo, hakan yasa yai sauri ya maida zif ya rufe kar a shigo a gani, ya d'auko takardar da ta bayar a bashi had'e da jakar ya bud'e tare da fara karantawa:
_Ameeru nah Dad ya shirya mana ziyara zuwa kano, amma yace bazamu dad'e ba, duk da haka ga kud'i nan ka yi amfani dasu kafin na dawo dan banaso ka koma rayuwar da na sameka a ciki a baya, Dad yak'i bari muyi sallama nasan zaka jirani duk rintsi zanyi kewarka._
*CI GABAN LABARI*
Amir ya k'araso kusa da ita tare da tsugunnawa yace " Amira dan Allah ki saurareni kiji, wato abinda ya faru shine, " sai kuma yai shiru, Amira ta d'ago ta kalle shi sannan tace "ni nasan dama babu abinda zaka fad'i ka kare kanka a wajena, k'aunar da na nuna maka tun yarinta rabinta baka nunamin ba," Amir yace " haba Amira in har kika fad'i haka bakiy min adalci ba, ki tsaya mana kiji abinda ya faru bayan tafiyarku."