← Book details So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 54

Sashe 49

So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta ri'ko hannunshi ta had'a da nata tana zubar da hawaye ta fara magana ita kad'ai, "Amir d'ina kayi ha'kuri ka yafe min, tunda ka had'u dani kake fuskantar barazana a kaina na rasa rayuwarka, amma koda wasa hakan baisa ka 'kini ba saima 'kara 'kaunata da kake, kuma har kullum burinka ka tseratar da tawa rayuwar daga fad'awa cikin halaka, ba dan komai ba sai dan saboda in ka rasani kaima bazaka iya cigaba da rayuwa ba, wallahi ko a tarihin masoya banga kamarka ba Amir wanda zai yarda ya mutu domin ceto ran wanda yake so," tana kai nan a zancenta ta sake fashewa da kuka matsananci.

Turo 'kofa aka yi aka shigo, Uncle ne shi da likita, Uncle ne ya kalleta ya fara fad'a yana fad'in "haba Amira ke da zakiy wa Allah godiya Amir d'inki yana raye sai ki zauna kina ta faman kuka," sannan ya cigaba da rarrashinta likita yana tayashi har tayi shiru, sannan likita ya kalli Amira yana murmushi yace "ranki ya dad'e kema ina ganin baki gado zamuyi mui jinyarku a tare," gaba d'aya dariya suka sa harda Amiran, haka likitan nan yaita sa Amira dariya da yake mutum ne shi me barkwanci.

Bayan 'yan awanni sai Amir ya farfad'o, wayyo masu karatu kar kuso kuga farin ciki gun Amira, sai nan nan take dashi, ko yaya taga ya yamutsa fuska itama sai ta canza ta-ta fuskar, nan da nan ta had'a mishi tea ta bashi yasha, sannan yasha magungunanshi, akai mishi allura cikin 'kan'kanin lokaci ya koma bacci.

Bayan komawar Amir bacci Uncle yacewa Amira zai tafi gida domin sanar dasu halin da ake ciki, suka yi sallama da Amira ta fad'a mishi abubuwan da take so a taho mata dasu in zasu dawo.

Ko da Uncle ya koma gida ya tarar da Dad ba lafiya shima jikinshi har yai zafi, kuma anyi anyi dashi ya bari a kaishi asibiti ya'ki yarda.

Dole haka nan Uncle ya kira Doctor yazo har gida ya dudduba shi, anan ne ya tabbatar musu da cewa jininshi ya hau, ya kamata ya rage damuwa da tunani da sauransu.

Ko da Doctor ya tafi Uncle ya je rakashi, ko da ya dawo ya tarar Dad ya samu bacci.

Mum d'in Amira ta kalli Uncle tace "sannu da 'ko'kari, Allah dai ya biyaka, ya kamata dai kaje ka huta," nan ya fad'a mata Amir ya farfad'o, ya kuma sanar da ita asibitin da yake, sannan ya fad'a mata sa'konnin da Amira tace akai mata.

Mum ta tashi ta haye sama d'akin Amira ta dubo sa'konnin ta kawo aka baiwa driver yaje ya kai mata, Mum kenan ha'kurarriyar mata, Allah ya sa mata ha'kuri da juriya dan da bata da su miji irin Dad kam da tuni ta fece.

Bayan kwana biyu jikin Dad yai sau'ki har Amira ma ta samu labari tazo ta dubashi ta koma.

Dad ne zaune a d'akinsa gefenshi kuma Uncle ne, sai d'aya b'angaren matarshi ce Mum d'in Amira.

Dad ya kallesu d'aya bayan d'aya sannan yace "abinda yasa nace kuzo shine kan maganar wad'annan yaran ne, ni bazan hana Amira komawa gidan Amir ba, amma ku shaida musu da ita da shi kanshi mijin nata kar su sake takowa inda nake, duk wannan halin da nake ciki ba komai bane ya jawo min illah wannan talakan yaron Amir me 'kashin arzi'ki, dan haka ku fad'a mishi karsu sake takowa inda nake."

Mum cikin zubar da hawaye tace "wai dan Allah sai yaushe zaka sauya ne, wannan ba'kar a'kidar da canfe-canfen marasa tushe ba zaka barsu ba ko, yanzu duk abinda ya faru dakai bai zame maka ishara ba."

Uncle shima ya d'auka yace "maganar gaskiya banji dad'in maganganunka ba wallahi, nai tunanin wad'annan abubuwan da suka faru zasu zama ishara a gareka, meyasa kake wa yaron nan irin wannan tsanar ne haka, wallahi yaron nan ba ma'kiyinmu bane masoyinmu ne, hasalima alkhairi ne a garemu tunda shine sanadin kub'utarku daga hannun wad'ancan azzaluman, su ya kamata ka tsana kuma kaji haushi ba wanda ya sadaukar da ranshi saboda kai da 'yarka ba," Dad cikin tsawa yace "sadaukar da ranshi na banza, ya barni su kasheni mana, ko menene indai daga gareshi ne bana 'kaunarsa, kuma na gama yanke hukunci."

Uncle ya mi'ke tsaye dan har ga Allah halin d'an uwan nashi ya fara bashi haushi, sannan yace "Allah ya kyauta, kadai yi tunani kar gaba kaji kunya da nadama mara iyaka," Dad yace "ba wata nadama da zanyi hukunci kuma babu sauyi."

Uncle bai sake waiwayowa ba kuma bai sake cewa komai ba ya fice daga d'akin, zama yayi a falo yana 'kara jin takaicin hali irin na d'an uwan nasa.

Mum ce ta fito daga cikin d'akin itama tana share hawaye, zata wuce Uncle ya kalleta yace "ki cigaba da ha'kuri da halin d'an uwana, wata rana sai labari, yanzu ma zanje can wajen su Amiran in dubo halin da suke ciki."

Mum tace "to bakomai nagode, in kaje ka gaishe su," sannan ta wuce sashenta.

Daga nan Uncle asibiti ya nufa, kuma sai yaje a dai-dai an basu sallama Amira nata faman had'a kayansu waje guda.

Bayan sun gaishe da Uncle yaiwa Amir ya jiki sannan suka shaida mishi maganar sallamar.

Uncle yai shiru yana nazarin yanda zai fad'a musu maganar Dad, amma ba yanda ya iya tunda baida muhalli nashi na kanshi da zai kaisu, haka nan ya daure ya sanar dasu sa'kon Dad amma be fad'a musu cewan da yayi shigowar Amir rayuwarsu shine sanadin faruwar komai, sannan ya kalli Amir yace "ka cigaba da ha'kuri da halin sirikinka Amir wata rana komai zai wuce, yanzu ka kaita mazauninka gidan da kake zaune nima zan biku inga wajen, gobe in Allah ya kaimu zanzo muje wata kotu da take nan kusa damu muga wani malami kuma al'kali domin jin abinda ya kamata dangane da hanyoyin da za'a bi domin komawar aurenku.

Jin wannan kyakkyawan labarin na komawar aurensu shi ya wanke damuwar da suka shiga na maganar Dad, sunyi farin ciki sosai daga 'karshe suka yi mishi godiya.

Da yake a motarshi yazo sai suka shiga tasu shima ya shiga tashi suka tafi har gidan su Amir.

Ganin 'kerarre kuma katafaren gidan da ya kutsa dasu ya d'aure musu kai.

Suna fitowa ma'aikata da masu tsaro birjik ta ko'ina sai kwasar gaisuwa suke yi.

Saida suka d'an yi tafiya mai tsawo sannan suka isa babban falon gidan.

Bayan sun zauna aka cika gabansu da kayan ciye-ciye kala-kala, Uncle dai kasa ha'kuri yayi yace "wai ni kam Amir gidan su wa ka kawomu ne?"

Amir yai murmushi, sannan yace "wannan d'aya daga cikin gidajen mahaifina ne, mahaifina shine shugaban 'kasar nan na yanzu."

Uncle ya jinjina kai yana 'kara jin hukunci irin na mahalicci, a yayin da ita kuma Amira ta zazzaro idanu amma bata ce komai ba.

Uncle ya tayashi murnar ganin iyayenshi sannan ya mi'ke yace shi zai tafi gobe su shirya da wuri, suka yi mishi godiya sannan suka rakashi har bakin motarshi, saida ya tafi suka dawo cikin falon suka zauna suna hira.

Muje zuwa

*🅱K CE*😘💋
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘

RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (🅱K*
```(Autar marubuta)```

SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
```(Mamie)```

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```🤜🤛

PAGE 210 to 215

Bayan sun raka Uncle bakin motarshi ya tafi sai suka dawo cikin falo Amir ya zauna kan kujera, Amira ta fad'a kan jikin Amir tana fad'in "Amir d'ina ka yimin laifi, baka fad'amin Daddynmu shugaban 'kasa bane, kuma baka tab'a had'amu koda a waya ba mun gaisa."

Amir ya d'agata daga jikinshi yana kallonta itama shi take kallo tana neman 'karin bayani akan d'agata daga jikinshi da yayi, ya harareta, sannan yace "dallah d'agani bakisan ke yanzu matar maza biyu bace," ya 'karashe maganar tare da murgud'a mata baki.

Amira ta 'kyal'kyace da dariya, yanda taga yayi maganar cikin turo da baki harda su harara da murgud'a baki, ta sake fad'awa jikinshi sannan tace "wallahi ni mijina d'aya ne tak a duniya har lahira ma insha Allah kuma gashi nan a tare dani."

ya sake turota tare da sake cewa "dallah d'agani," itama turo baki tayi tace "ni wallahi ka daina tureni daga kan jikinka," dariya yai mata tare da yi mata gwalo ta mi'ke zata kai mishi duka, ya tashi ya gudu cikin d'aki itama ta bishi suna tsere.

*WASHE GARI*

Washe gari Uncle yazo dama su tuni sun shirya shi suke jira, babu b'ata lokaci suka tafi.

To dama a addinance mun sani idan irin haka ta faru mata ake baiwa zab'i ta zab'a a cikinsu wanda tafi 'kaunar zama tare dashi, kuma ba wanda ta zab'a sai Amir, dan haka aka 'karashe duk wasu abubuwa da addini ya tanadar cikin lokaci 'kan'kani aka maida auren Amira kan Amir.

Suka cigaba da zamansu cikin jin dad'i da kwanciyar hankali.

Zaune suke a falo suna hira Amira ta kalli Amir tace "wallahi Uncle yanada kirki, ina ma shine mahaifina ba Dad ba."

Amir ya rufe mata baki, sannan yace "ki daina fad'in haka, Dad ne Allah ya hukunta matsayin mahaifinki, kuma bai tab'a canzawa daga wannan matsayin a wajenki, kuma shima Uncle ai matsayin uba yake a garemu, dan haka dukkaninsu iyayenmu ne."

Amira ta kalli Amir tace "Amir d'ina dan Allah kayi ha'kuri akan irin abinda mahaifina yake maka, kuma ina 'kara godiya a gareka da sadaukar da rayuwarka da kayi wajen ceto tawa rayuwar da ta 'yan'uwana."

Amir yace "Amirata karki damu da duk abinda Dad yake a kaina, ai nima wallahi Dad mahaifine a gareni, kuma mahaifi yanada damar yin komai akan yaranshi, kuma ni inhar za'a barni na rayu dake to komaima ai mini wallahi bazai dameni ba zan jure tunda ina tare dake, dan haka karki damu, sannan kuma ki daina godemin, idan na ceto ranki rayuwata na ceta domin ban iya cigaba da numfashi in babu ke a tare dani, dan haka a shirye nake da in cigaba da sadaukar da tawa rayuwar domin ceto rayuwarki, karki manta raina fansa ne a gareki Amirata."

Sun dad'e suna hirarsu cikin nishad'i da walwala.
Chapter 49 · 0% Book details