← Book details So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 54

Sashe 10

So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amir ya k'arasa inda take ya zauna, kallonta ya yi sannan yace " ba sai na tambayeki dalilin kukanki ba Amira tunda na riga da nasan dalili, se dai ina mamakin inda tunaninki ya tafi kika manta cewa akwai wani bawan Allah guda d'aya a gefenki wanda yake da niyyar faranta miki har k'arshen rayuwa, ya kamata a ranki kiji in duk duniya ta gujeki to mutum d'ayan nan tak ya wakilci dukkanin mutanen duniya a wajenki, Amira kukan ki yasa naji ba dad'i gani nake kamar na gaza wajen baki dukkanin farin ciki da kuma mantar dake kowane irin b'acin rai da na alk'awarta, kiyi hak'uri ki daina kukan nan zuciyata na fitar da wani irin tiririn zafi.

Ta daina kukan da taimakon Allah da taimakon nagartattun kalaman shi, labarai ya fara bata na ban dariya yace " bari na baki wani labari."

_"lokacin da nake boarding a secondary school muna kwakkwance da dare wajen k'arfe takwas ina karatu sai fitsari ya matseni, inata juyi nak'i tashi inje in yi kuma ban dena juyin ba, wanda yake can saman gadona yana kwance yana kallona, zabura nayi da gudu dan inje in yi futsarin, se dai gani nai wanda ke can saman gadona yazo ya rigani shallakewa a guje, ina ganin ya d'iba a guje sai nima na bishi a guje, shi kuma koda ya juyo yaga na biyo shi sai ya k'ara dannawa a guje sauran d'alibai kowa sai gudu, saida suka ci karo da malam ya tsayar da shi yana tamayarsa me ya faru yace malam Amir ne yaga wani abu shine na gudu kafin abun k'araso kaina, koda na k'araso malam ya tambayeni me na gani nace malam banga komai ba, akace to meyasa kake gudu nace wannan naga ya runtumo a guje shine na biyo shi, malam ya sake tambayata me yasa na zabura daga kwance nace futsari ne ya matseni, mallam yai dariya mai isarsa, sannan yace shi yana gudunka kai kuma kana gudun abinda yake wa gudu baka san cewa kai yake gudun mawa ba kar abinda yai tunanin ya biyoka ya cimmashi, su kuma sauran d'alibai suna gudun rashin dalili, to ku wuce kuje ku kwanta Allah ya shiryeku tsoro kamar kuraye, malam yana juyawa zai tafi gidanshi sai d'aya daga cikinmu yace malam ga wani abu nan yana binka a baya ai ko juyowa malam be yi ba ya runtuma a guje sai gida d'alibai kowa akaita yi mishi dariya."_

Amira saboda tsabar dariya harda hawaye, a kan kujera take amma har ta kai k'asa tana rik'e ciki, tana dariyar ne taji Amir yace " Amira ina son......., Amira cikin dariyar labarin da ya bata tace "me kake so?" Amir yace " ke nake so, ina sonki Amira."

Lokaci d'aya dariyarta ta tsaya cak, ta mik'e tsaye, shima ya mik'e suna kallon juna, Amira tace " d'an maimaita abinda ka fad'i yanzu," Amir yace " cewa nai ina sonki Amira."

Amira ta zaro idanu jin abinda yace tare da d'aga hannunta ta wanka mishi mari har uku.

Muje zuwa

*🅱K CE😘💋*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘

*RUBUTAWA*
*BILKISU Z. YA'U (🅱K)*
```(Autar marubuta)```

SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
```(Mamie)```

_ina matuk'ar jin dad'in yanda kuke k'aunar wannan novel d'in, da yanda kuke tattaunawa akai masoyan *SO MAHA'DIN RAYUWA* ina godiya kuma ina alfahari da ku wallahi I hrt u all😉😘_

_'yan uwa muna barar addu'arku *Kaduna* ba lafiya Allah ya kawo mana k'arshen wannan bala'o'in dake addabar mu a rayuwa._

PAGE 45 to 50

Amira ta kalle shi ta sake wanka mishi mari cikon na hud'u, sannan ta kama hannun shi ta jashi har k'ofar d'aki ta tura shi waje sannan ta maida k'ofarta ta rufe tare da dark'ushewa a jikin k'ofar tana kuka.

Amir daga waje bugun k'ofar yake yi kamar me, yana fad'in " Amira kece tubali na ginina, kuma kece *mahad'in rayuwata,* har ina jin babu sauran numfashi a tare da ni duk ranar da bana tare da ke, ki duba yanda muka shak'u da juna kiy min sassauci dan Allah, koda bakya k'aunata ki bar zuciyata ta rab'u da taki," yana magana yana kuka tare da cigaba da buga k'ofar.

Amira ganin ya fara karya mata zuciya yasa ta tashi ta bar bakin k'ofar ta koma kan kujera ta zauna, ji ta yi ta zauna kan wani abu ta d'aga bak'ar ledar da Amir ya shigo da ita ce, bud'e ledar ta yi, wani k'aramin kwali ne a ciki sai wani kati me d'auke da kalamai na so, kwalin ta fara bud'ewa wani had'ad'd'en zobe ta gani na zinare da na azurfa, Amira mamaki kawai take yanda akai ya san irin zobunan da tafi so a rayuwarta.

Tsintar kanta ta yi da ciro su d'aya bayan d'aya ta saka a hannunta, ai kuwa sun yi mata kyau sosai kamar dama don ita kad'ai aka had'a su.

Katin nan ta ciro ta fara karantawa

_So wani abu ne da yake jigatar da zuciya ya cikata da damuwa a wasu lokutan, amma tunda na same ki nasan zaki zamo min maganin warakar dukkan wata damuwata a so, dan Allah ki taimaka ki amince da ni mu rayu tare._

Bayan ta gama karantawa ta yi ajiyar zuciya tare da juya bayan katin taga an rubuta

_Amira ta Amir_

Amir ne ya cigaba da bugun k'ofar tare da yin magana da k'arfi yanda zata ji, yana kuka yace " Amira ya kike so in yi ne wai, da k'aunarki da ta maida ni tamkar mahaukaci zan ji ko da hukuncin da kike min a yanzu, haba Amira ki ji tausayina mana, ki tausayawa zuciyar da bata san komai ba sai so da k'aunarki da kuma farin cikin ki, karki barta mu rayu tare mu mutu tare dan Allah, wallahi in baki bud'e min k'ofar ba zan kwana a nan."

Amira tana jin duk abinda Amir yake cewa, itama kuka take sosai amma har yanzu bata da niyya ko alamar zuwa ta bud'e mishi k'ofar.

A haka suka kasance abinda ke tayar da Amir daga bakin k'ofar nan sallah ce kad'ai har dare ya rufa yana zaune bakin k'ofar, itama Amira a falo ta kwanta se dai bacci babu shi a idanun su duka daga Amir d'in har Amira.

Amir rakub'ewa ya yi a jikin k'ofar ya kwanta kamar wani mara gata, a haka suka kasance har zuwa k'arfe uku na dare idanun su biyu, se dai ita Amira duk a tunaninta Amir ya tafi gida saboda jinshi shiru.

Amira ta ji gabanta ya fad'i a zuciyarta tace yanzu idan har yanzu yana waje fa, mik'ewa tsaye ta yi, so take kawai ta tabbatar yana nan ko baya nan lek'awa ta yi ta windon d'akin amma da yake windon a can gefe yake bata hango k'ofar d'akin ta ciki, hakan yasa ta hak'ura ta koma kan kujera ta kwanta.

Amir sanyi ne ya fara kad'a shi, nan da nan ya fara rawar sanyi, zazzab'i ya fara kama shi.

Washe gari wajen k'arfe takwas Amira ta gama shirin tafiya makaranta, haka ta tashi sukuku ba k'arfi a jikinta, abun kari kuwa dama bata ta tashi, bud'e k'ofar ta yi domin tafiya ta ci karo da Amir kwance a bakin k'ofar, shima jin bud'ewar ne yasa ya bud'e idanun da su kansu zafi suke yi mishi saboda ciwon kai.

Jakarta ta yar, tare da duk'awa inda yake cikin sauri ta tallabo shi sannan ta fashe da wani irin kuka jin jikin shi da ta yi kamar garwashi saboda zafi, tabbas tasan a nan ya kwana.

Amira kuka take tana fad'in baka da hankali ne Amir, meyasa zaka kwana a nan," ta sake fashewa da kuka.

Amir cikin wahalalliyar murya yana fitar da numfashi da k'yar yace " ina hankali da tunani ga wanda yai zurfi a so, dan Allah Amira karki gujeni, ki amince da ni, Sonki ne *mahad'in rayuwata,"* hawaye ne yake gangarowa kan fuskar shi, a yayin da Amira kuma ke kuka sosai kanshi yana jikinta tama rasa da me zata fara taimaka mishi, ji ta yi yai mata nauyi a jiki, ta jijjiga shi tana fad'in tashi in kama ka mu shiga ciki," ina babu amsa Amir ya sume.

Rud'ewa ta yi tana kurma kuka me d'an karen k'ara tana fad'in "shikenan na kashe shi."

Sauke kanshi ta yi daga jikin ta, ta fita waje neman taimako, wani dattijo ne Allah ya had'ata da shi suka shigo tare har zuwa inda Amir yake, tab'a shi ya yi, yace ta kawo mishi ruwan sanyi, da gudu Amira ta shiga ciki ta fito da ruwa a gora ta kawo mishi, karb'a ya yi, ya bud'e ya zuba a hannu ya shafa mishi a fuska da wuraren wuyan shi, ya ajiye ruwan a gefe, ba'a fi minti biyar ba da watsa mishi ruwan sai ya fara motsi da hannu tare da k'ok'arin bud'e ido, bakin shi na ambaton sunan Amira.

Wannan tsohon yace " Alhamdulillah tashi ki kama shi mu shiga da shi ciki," suka kama shi suka kaishi cikin d'aki suka kwantar dashi kan kujera.

Tsohon nan ya kalleta yace " ki samu ruwa me sanyi da tawul ko tsumma ki rik'a sawa cikin ruwan sanyin kina goge mishi jikin shi saboda a samu zazzab'in jikin shi ya sauka, Allah ya k'ara sauk'i."

Amira tace " ameen Baba, nagode da taimakon da kai min Allah saka da alkhairi," bayan tafiyar wannan tsohon Amira ta yi duk yanda ya fad'a mata cikin ikon Allah zazzab'in ya fara sauka, kuma sai a lokacin ya samu bacci.

Itama Amira tana zaune a doguwar kujerar ta jingina, shi kuma Amir yana kwance kanshi na jikin Amira hannunta na dafe da jikinshi a haka dukkan su bacci ya d'auke su suna ramuwar na jiya da basu samu sun yi ba.

Sai wajen k'arfe d'aya Amira ta tashi, cikin sauri ta zame kan Amir daga jikinta ta kwantar da shi kan kujerar sannan ta yo alwala tai sallah, bayan ta idar ta fad'a kicin domin nema musu abinda zasu ci.

Jelop d'in taliya tai musu wadda ta ji kayan ciki, _ni kuwa BK har ina had'iye miyau ina fad'in Allah sa su rage min, saura makaranta kuce inada kwad'ayi☹😏_
Chapter 10 · 0% Book details