Sashe 27
So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suna cikin bacci suka ji ana tashin su, ashe an zagaye su basu sani ba, firgigit suka tashi Insp Yahya ne du'ke a gabansu yana kallon su d'aya bayan d'aya sannan yai murmushi yace "kun gama gudun?" nan fa aka kama su za'a tafi dasu Amir yai kukan kura ya gwabje wad'anda suka ri'ke shi, Allah ya bashi sa'a ya fisgi wata bindiga hannun wani d'an sanda ya harbi mutum uku a 'kafa, yaja hannun Amira suka saita hanya gudu suke ana binsu a baya, da yake cikin dare ne unguwar tsit kuma garin duhu, gudu suke yi kamar ransu zai fita har Allah ya kawo su wani 'kauye, wani gida suka hango bud'e aikuwa babu shiri suka kutsa ciki kai tsaye, suna shiga a dai-dai wani dattijo ya fito daga ban d'aki yaga mutane tsaye a tsakiyar tsakar gidan su, haska su yayi da toachlight yana fad'in "kai su waye nan……ah ikon Allah Amir, Amira, daga ina kuke cikin wannan daren?"
Sai a lokacin suka fahimci ai gidan su Baba ne Allah ya k'ara dawo dasu ba tare da sun gane ma wani gida suka fad'o ciki ba, da gudu suka rungume Baba suna murna, Umma kuwa jin hayaniyar dake tashi ne itama ta fito daga d'akinta turus taja ta tsaya ganin su Amira tsaye a tsakar gida, nan dai Baba yace su shiga d'akinsu su kwanta washe gari sai su yi magana.
Suka shiga cikin d'aki suka kwanta, Baba kuwa cikin sauri ya rufe gida karma a ganshi a bud'e ai tunanin nan suka shigo.
Amir da Amira kuwa suna shiga d'aki suka rungume juna suna murnar sake ganinsu cikin wannan gida.
Amir ya tsalle yai sufa kan tabarma, Amira kuwa ta zauna kan d'ayar tabarmar, Amir yace " Alhamdulillah Allah ya 'kwacemu, ya kai kallon shi kan ga Amira yace kinga hukuncin Allah ko, ashe gidanmu muka dawo ma muke rab'e - rab'e," Amira tace "wallahi kuwa," Amir da Amira suka kafe juna da idanu kowanne da irin abinda yake ji a cikin zuciyarshi.
Amir yace "taso ki dawo kusa dani mana Amira na," ba musu ta tashi ta koma kusa dashi ta zauna, suka ci gaba da kallon juna, nan take shaid'an ya fara k'awata musu sha'awar junan su.
Har sun fara biyewa shaid'an yana buga musu ganga suna neman aikata zina, cikin sauri Amir ya d'aga Amira tare da komawa kan ta-ta tabarmar ya zauna tare da had'a kai da guiwa ya fashe da kuka, Amira ta mi'ke cikin sauri tare da zuwa kusa dashi ta dafa kafad'ar shi, cikin sauri ya d'ago ya kalle ta yace "Amira ni da ke duk mun sani soyayya tana had'uwa tare da sha'awa ne, kuma duk inda mace da namiji suka keb'e to na ukun su shaid'an ne, 'kaunar da nake miki ta ha'ki'ka ce bazan iya aikata abinda Allah ya haramta ba a kanki har sai ranar da na mallake ki a matsayin matar aure, dan haka dole mu ri'ka d'an yin nesa da juna, saboda kar soyayyar da muke wa juna ta rinjaye mu mu aikata zina kafin aure, ki kwanta a ciki zan fita tsakar gida in kwanta," yana gama fad'in haka ya fice daga d'akin da tabarmarsa a hannu ya shimfid'a a tsakar gida ya kwanta.
Amira ta d'auko tata tabarmar ta biyo shi ta shimfid'a a tsakar gidan itama nesa dashi, ganin in dai Amira ta kwana anan bama ita kad'ai ba har shi zasu cutu domin kuwa dukkansu mura suke yi saboda kwanan daji da suka yi.
Amir ya tashi ya nannad'e tabarmar shi yace itama ta tashi, Amira ta tashi suka koma d'aki suka rufe, shi kanshi Amir yasan Amira ta riga da ta yi mugun sabon da bazata iya kwana inda babu shi ba yanzu, tunani yake mafita d'aya kawai ta rage musu shine a d'aura musu aure.
Haka suka kwanta nesa da juna amma fuskar su tana fuskantar junansu uka Amir ya kalli Amira itama shi take kallo, Amir yace "Amira," Amira tace " na'am," Amir yace kin Amince in fad'a wa Baba gaskiya ya d'aura mana aure gobe?" Amira ta mi'ke tsaye daga kwancen da take tace " eh wallahi a fad'a mishi tun yanzu, bari ma inje in sanar dashi," ta d'auki hanyar 'kofa da sauri zata bud'e ta fita, Amir yace " tsaya mana, banda dariya babu abinda yake mata, kallonta ya sake yi yace yanzu ke dan baki da kunya sai kije taso Baba a wannan daren, to in kika je kika taso shi me zaki ce mishi?" ya sake kwashe mata da dariya.
Amira ta rufe ido alamun taji kunya, ta dawo kusa dashi ta zauna sam tama manta da gargad'in da yai mata na yin nesa da juna har sai sunyi aure, baccin da kuma basu yi ba kenan suka dosa hirar yanda kowa zai ji idan suka mallaki juna matsayin ma'aurata, da kuma yanda zasu rayu da juna bayan aure.
Muje zuwa
*🅱K CE😘💋*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (🅱K)*
(Autar marubuta)
SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
(Mamien)
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
(Gidan zaman lafiya da amana in sha Allah)🤜🤛
*MAMAN LABYB (MAMIE)da AUNTY LIPSON (Maman Saleem) ina ro'kon Allah mahaliccina ya d'orar da lafiyarsa gareku👏😩*
PAGE 115 to 120
Washe gari Amir da Amira ne zaune gaban su Umma, Amir har ya bud'e baki zai fara magana Amira tai karaf ta fara magana da fad'in "Baba, Umma, iyayena auren dole suke so su yi min ni kuma bana so, saboda yaron da zasu had'amu beda tarbiyya su kuma basa son talaka wannan dalilin yasa suka tsani had'a aurena da Amir," tana kaiwa nan a zancenta sai ta fashe da kuka, d'akin yai tsit banda sautin kukan Amira dake tashi, can sai Amir ya d'ago kai ya kalli Baba yace "Baba dan Allah ka d'aura mana aure dan girman Allah, shima ya fashe da kuka yana ci gaba da yiwa Baba magiya, daga Baba har Umma shiru suka yi, a yayin da tausayin yaran ya gama lullub'esu, kuma tabbas yanda suka sha'kun nan in akace za'a raba su to zasu cutu, dukkanin su sun yi Allah wadai da wannan muguwar d'abi'a ta iyayen Amira kan dole sai sun aurar da ita ga mai kud'i sai kace talaka shi ba Allah ne ya yishi ba, duk wannan tunanin Umma da Baba cikin zuciyarsu suke yinsa.
Baba ya kalle su har yanzu kukan suke ta yi, sai yace "ya isa kukan, bayan sun yi shiru ya cigaba da fad'in kuje cikin d'akin ku ku shirya kafin nan zamu yi shawara da Mamanku, kuma a yanda kuka bamu labari kunce sun biyoku har cikin rugar nan, to tabbas nasan zasu sake dawowa, saboda haka kuje kuyi shiri in mun gama shawara da Ummanku to ko za'a d'aura muku auren ba a nan ba zan tura ku wani 'kauye nan wanda ke ma'kwabtaka da namu wajen yayana sai a d'aura muku auren a can in yaso ma sai ku zauna a can d'in kawai."
Cikin sauri kuma cike da farin ciki suka tashi suka shiga cikin d'aki, can bada dad'ewa ba sai ga Baba yai sallama tare da le'kowa yace su fito su tafi, har sun bar wayar su Baba yace su d'auka in yaso sai su canza sim su karya wancan, Baba da kanshi yai musu jagora suka yi sallama da Umma suka fice daga gidan suka d'auki 'kauyen gidan d'ango, daga 'kauyen damari zuwa 'kauyen gidan d'ango da tazara sosai shiyasa suka jima suna tafe kafin su iso cikin 'kauyen.
Bayan sun 'karasa gidan suka gaggaisa aka kawo musu fura da nono da ruwa mai sanyi suka sha, bayan sun gama Baba ya kora wa yayansa bayanin duk abinda ke faruwa da kuma dalilin zuwan su a yanzu da ro'kon yayan nasa alfarma kan su zauna a 'kauyen har sai Allah ya kawo dai-daituwar komai.
Yayan Baba wanda yaransa ke kiransa da Baffa yace "ba wani abu Allah ya shige mana gaba, yanzu abinda za'ai shine malam Amir in har kana da kud'i a jikinka ka kawo a d'aura yanzu, bari nasa a kira ma'kwabta da 'yan uwa da abokan arzi'ki, Baffa yasa aka kira su wad'anda suke nan nan da nan suka had'u, Baba ya ciro dubu biyar yace "ga sadakin Amir kuma ni ne waliyyinsa," Baffa yace "masha Allah nine waliyyin Amira," wani liman dake unguwar yace " to Alhamdulillah, nan fa babu b'ata lokaci aka gabatar da dukkanin abubuwan da suka kamata, aka d'aura aure sannan aka yi addu'a tare da yi masu fatan zaman lafiya kowa ya watse.
'Daki guda aka samar musu a cikin gidan Baffa, sai da aka gama komai sannan Baba yai sallama dasu su Amir suka rakoshi hanya cike da farin cikin kasancewarsu ma'aurata.
Suna tafe Baba yana k'ara yi musu nasihar zaman lafiya a zamantakewar aurensu, sun d'an fara yin nisa da unguwar Baba ya tsaya yace "to rakiyar taku ta isheni daga nan, ku koma nagode Allah muku albarka."
Amir ya bud'e baki kenan zai yi magana sai ga motoci sun zagayesu ta ko'ina kuma motocin na tsayawa suka shiga fitowa d'aya bayan d'aya, su Insp Yahya ne sojoji da 'yan sanda gaba d'aya suka zagaye su Amira suka saka su a tsakiya, can kuma sai ga Umma matar Baba itama an fito harda ita a cikin motar, Baba ya kalleta yace " meyasa zaki nuna inda bayin Allahn nan suke, yanzu abinda kikai kin kyauta kenan?"
Insp Yahya yai tattaki ya 'karasa har kusa da Baba sannan yace "Baba hala baka san abinda wad'annan suka aikata ba shiyasa kake b'oye masu laifi a gidanka ko, to bari kaji kisa Amir yayi ya kuma sace 'yar shugaban 'kasa ya gudu da ita, idan har da baka san laifin da ya aikata ba to yanzu ka sani, muddin ka 'kara b'oye shi ko kasa aka b'oyeshi to kuma sai mun hukunta ku."
Insp Yahya ya sake yin tattaki ya 'karasa har gaban Amir, sun dad'e suna yiwa juna kallon kallo sannan Insp yai murmushi yace " Amir karka manta da sunana Insp Yahya kafi 'karfin mugu, babu inda zaka shiga ka guje mini in dai kana cikin Nigeria ne, dan haka ku kama shi muje."