← Book details So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 54

Sashe 22

So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amir ya juya da gudu zai fita ya tsere sai Insp Yahya yai kukan kura ya ture Amira tare da k'wace bindigar dake hannunta Insp Yahya yai sauri ya d'auka tare da saita Amir ya harbeshi a hannu, Amir da Amira lokaci d'aya suka saki k'ara a tare, da gudu Amira ta k'arasa gun Amir d'in wanda ke k'ara azaba tana kuka tana fad'in ya tashi su gudu, Insp Yahya ya k'araso wajen, ganin inuwarshi yasa Amira ta sake d'aukar wani abu dake kusa da su ta buga wa Insp Yahya akai, ba shiri ya fad'i k'asa a sume, hakan ya bata damar d'aga Amir ta rik'eshi suka fita daga gidan, suka shiga motar Amira suka d'auki hanya sunata tafiya k'ok'ari take taga ta kaishi asibitin da ke da nisa da cikin garin, hankalinta ya rabu gida biyu tana tuk'i tana yi tana kallon Amir da yake nishi sama sama na azabar harbin da yasha ga wasu hawaye masu zafi suna fitowa daga idanunshi, itama Amiran kuka take kamar me.

Muje zuwa

*🅱K CE😘💋*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘

RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (🅱K)*
```(Autar marubuta)```

SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
```(Mamie)```

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```🤜🤛

*AISHAN UMMA*
```Auntynah```

*Rashin ganinki sanadi na tunaninmu ya jefa zuciyarmu a cikin k'unci, sabo kenan, Aunty Aishan Umma munyi kewarki sosai wallahi,😰 ki dawo garemu da wuri kafin mu fara kokawa🙏😭*

*AUNTY HUMYLUV ina kika b'oye ne??? nayi kewarki😰*

*taimako abune mai kyau wanda duk ka yishi zaka tarar da amfaninshi nan gaba, ma'ana zai maka rana wata rana, dan haka mu zamto masu taimako akoda yaushe.*

*REAL KHADY*
```(Princess)```

*tabbas ni mai laifi ce a gareki, kuma na amshi laifina ina rok'on yafiya da sassaucin hukunci🙏😰*

PAGE 90 to 95

Amira tama rasa ina zata nufa da Amir, gudu kawai take yi a mota har ta fara fitowa daga cikin garin kano, har Allah ya kawota wani k'aramin gari a nan ta tambaya inda zasu sami asibiti ko kemis, aka raka su wani asibiti wanda aka k'i karb'ar Amir ganin harbi ne kuma ba d'an sanda kuma shi kanshi Amir d'in ya wahala.

sai da k'yar suka amince suka karb'e shi, amma Doctor d'in da zai duba Amir ya kafe ya dage kan ba zai yi mishi komai ba sai taje ta taho da d'an sanda sannan zasu duba shi.

Ba tare da b'ata lokaci ba aka raka Amira station tai musu bayani akan mijinta ne 'yan fashi ne suka shigar musu gida suka kwashe musu kud'i sannan suka harbi mijinta a hannu, shine akace sai tazo da d'an sanda.

Babu b'ata lokaci aka had'ata da mutum d'aya cikin jami'an suka koma asibitin.

Koda isar su taga yanda Amir d'inta ya k'ara galabaita gashi har yanzu basu tab'a shi ba.

Amira ta haukace musu a asibitin tana kuka tana fad'in su yi k'ok'ari su ceto ranshi, zata basu ko nawa suke buk'ata, in kuwa ya mutu to sai ta k'arar da kowa dake cikin asibitin.

'Dan sandan da aka had'a su tare shine yake rarrashinta tare da bata baki, babu b'ata lokaci jami'in nan ya saka hannu aka fara duba Amir cikin gaggawa, aka cire bulet d'in tare da yi mishi duk wani taimakon da ya dace.

Alhamdulillah Amir ya samu sauk'i, amma Amira sam bata so ma suka kwana a garin ba saboda hankalinta bai kwanta da wurin ba gani take kamar za'a zo a rabata da Amir d'inta.

Bayan kwana biyu Amira ta matsa aka sallame su, Amira ce ke tuk'a motar a yayin da Amir ke zaune gefe kuma ta rasa ma ina zata nufa da su, har sun fara tafiya sai kuma ta faka motar tare da kallon Amir tace " yanzu Amir ina zamu je kaga shiga cikin gari be kama mu ba saboda duk muka shiga nasan a yanzu kuma a ko'ina neman mu ake yi."

Amir wanda ke zubar da hawayen nadamar halin da ya jefa su a ciki, gashi wadda ya yi dominta yana neman rasata, lallai ya yarda so makaho ne, lokuta da yawa yakan makantar da kai ka aikata komai wanda koda zaka yi nadama ne daga baya sai kayi, Amir yace " Amira dan Allah kiyi hak'uri ki yafe min, bana yin nadamar duk abinda na aikata a kanki koda kuwa abinda nayi zaisa a rabani da raina ne, damuwata d'aya ne a yanzu na jefaki cikin damuwa da nayi, ni kuma duk duniya babu abinda na tsana wanda ya wuce shigarki wani hali balle kuma ace ta sanadina, ina rok'onki Amira muyi hak'uri mu yi nesa da juna har sai na fita daga cikin wannan halin saboda bana so kema ki shiga ciki."

Kuka suke yi sosai kamar ransu zai fita, can sai Amira ta tsagaita da nata kukan sannan ta kalleshi tace " dan Allah Amir kukan nan ya isa haka ba shi bane mafita a garemu, hanyar da zamu ceci soyayyarmu daga rushewa ya kamata mu nema, Amir ban tab'a yin so ba sai a kanka, kuma gaskiya ban shirya rabuwa dakai ba, so nake mu rayu tare ya zama mutuwa ce kad'ai zata rabamu, itama da da hali zanso mu mutu a tare, saboda haka kama daina zancen yin nesa da juna kasan ni da kai duk bazamu iya jure faruwar hakan ba, in har kana k'aunata kuma da gaske baka son rabuwarmu to ka zuba min idanu kan dukkanin wani hukunci da zan yanke."

Amir ya share hawayen shi, sannan yace "Amira gaba d'ayan rayuwata tana gurinki, na gwammace ace na mutu na barki da ace yau ina raye amma na rasaki," Amira ta katse shi cikin sauri tare da fad'in " Amir nima a wannan duniyar muddin babu kai tabbas bak'in cikin rashinka zaisa in bar cikinta, nasha fad'a maka cewa banda rayuwa a cikin rayuwar da babu kai, da kai na saba taya rabuwa zata zama abu mafi sauk'i a garemu, kama bar wannan maganar tana d'aga hankalina, insha Allah zamu rayu tare muyi aure mu haihu, kuma in Allah ya yarda mu mutu a tare."

Amir ya numfasa, sannan yace " to yanzu ya zamu yi, ina zamu nufa?"

Amira tace nima shine abinda nake ta tunani cikin raina, inda zamu je mu kaucewa Yahya daga neman da nasan yana yi mana a yanzu haka," dogon numfashi ta ja, sannan kuma kowanne daga cikinsu yai shiru yana tunanin mafita.

Can Amira ta d'ago cikin sauri tare da fad'in " na tuno inda zamuje ba tare da kowa ya ganmu ba, amma dole sedai mu hak'ura da makaranta in kuma zamu fita to dole sedai mu rufe fuskarmu yanda ba wanda zai gane mu, ina ganin kawai mu tafi gidan marayun nan mu zauna na wasu lokuta kafin mu san abun yi a gaba."

Amir yace " sam komawarmu cikin gari a yanzu be kamata ba kamar mun kai musu kanmu ne, sedai mu nemi wata mafitar, suna cikin wannan shawarar ne suka hango motar su Insp Yahya suna nuna hotunansu suna tambayar inda suke, kuma ganinsu tare da d'an sandan da ya raka Amira aka duba Amir a asibiti ya k'ara tayar da hankalinsu matuk'a, ko kafin suyi wani yunk'uri 'yan sandan nan sun hango su, domin Insp Yahya ya haddace lambar motar Amir da Amira duka a kanshi.

Cikin sauri Amir yace wa Amira ta dawo mazauninshi suka yi canje yaja motar cikin k'warewa Amir ke tuk'a motar a yayin da Insp Yahya da tawagar shi suke biye dasu suma da gudu, haka sukaita tsere kan ti-ti k'ok'arin 'yan sandan nan kawai suga sun sha gaban su, a yayin da shi kuma Amir ya dage kawai k'arawa motar gudu yake yi yak'i bari su shiga gaban su.

A haka har su Amir suka fara yi musu nisa, cikin hukuncin Allah kuma suka b'ace musu, Insp Yahya ya daki kan sitiyarin motar yace " shettttt sun gudu," dole suka juya kan motar su domin kuwa hanyar ta kasu har uku ko kafin su k'araso sun b'ace a wajen shiyasa basu san wacce ce hanyar da su Amir d'in suka bi ba.

Su Amir kuwa duk da sunyi nisa sun ma fita daga kano gaba d'aya sun shigo zaria amma ya kasa tsayawa da motar gudu kawai yake yi, har Allah ya kawo su wani k'auye da ake kira Damari, anan suka yada zango a galabaice, suka fito daga motar a dai-dai wani bawan Allah ya biyo hanya yana sab'e da fatanya zai tafi gida, ga dukkan alamu daga gona ya fito.

Amir ya kalleshi yace "sannu Baba ina wuni," dattijon nan ya tsaya tare da amsa gaisuwar su, Amir ya cigaba da cewa " Baba taimako muke nema daga gareka dan Allah, dattijon nan yace " to yaro Allah yasa wanda zan iya ne."

_ayi hakuri da wannan wayar huk take idan nai typing me yawa a bini bashin gobe insha Allah._🙏

Muje zuwa

*🅱K CE😘💋*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘

RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (🅱K)*
(Autar marubuta)

SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
(Mamie)

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛

*AUNTYNAH AISHAN UMMA tana gaishe da kowa da kowa, kuma tace tayi kewar dukkanin masoyanta, tace mu kwantar da hankalinmu tana nan cikin k'oshin lafiya, wayarta ce ta sami matsala amma kwanan nan zata sake wata, tana nan tafe nan bada dad'ewa ba insha Allah, mun gode Allah da jin kina nan lafiya AUNTYNAH😍*

*Ina baiwa MASOYANA hak'urin jina shiru na kwana biyu, mun d'an sha shagalin bikin sister na ne, sannan ranar Alhamis nayi typing nai mistake d'in number, a maimakon insa 95 to 100 sai nasa 90 to 95, dan haka zan gyara lambobin in turo su a tare saboda sam bana so masoyana su shiga rud'u, wallahi ina alfahari daku da yawanku masoyana, da bazarku nake taka rawa.*💃😉

*MOMYN KHADEEJA🧕*🗣🗣🗣🗣
*ungo taki gaisuwar ta musamman🙏🙏🙏🙏🙏 sannan Amir da Amira suna gaishe ki sosai sunce suna mugu mugun yinki, Allah ya bar k'auna da zumunci🤝😍.*

PAGE 95 to 100

Dattijon nan ya kalli Amir yace ‘’to yaro ina jinka Allah yasa zan iya, wane irin taimako kake nema daga gareni? ‘’

Amir yace ‘’mu bak'i ne a garin nan, dan Allah ka taimaka mana da masauki.‘’
Chapter 22 · 0% Book details