← Book details So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 54

Sashe 4

So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babban jami'in nan ya kalle su yace " alamu sun nuna kashe shi aka yi, saboda wuk'a aka caka mishi, kuma d'akin a hargitse, hakan na nuna ya yi k'ok'arin ceton ranshi kafin a far mishi, amma muna dai kan bincike tukun har sai mun gano gaskiya."

Amira kuwa bayan har suka k'araso gida kuka take yi, Amir ya kalleta sannan yace " Amira dukkan mai rai fa mamaci ne, kuma a koda yaushe idan tazo baka isa ka k'ara koda sakwanni ba a duniya, ki sa wa ranki hak'uri, tabbas Amira kinyi rashin babban amini, hakan yasa muma abokan ki muke tayaki kuka saboda tausayinki, da kuma shak'uwar da mu kanmu muka yi da shi, kiyi hak'uri a yanzu yafi buk'atar addu'arki fiye da komai a duniya."

Bata ce mishi komai ba amma ta rage kukan da take ta faman yi, kwantar da ita ya yi, sannan ya tashi ya shiga shiga toilet ya had'a mata ruwan zafi ya kaita sannan ya fito ya jawo toilet d'in, kicin ya shiga kafin ta fito ya had'a mata tea me kauri sannan ya soya mata dankalin turawa, ya fito hannun shi rik'e da k'aton faranti ya d'ora plet d'in dankalin da kuma tea d'in da ya had'a mata, koda ya fito har ta shirya ta koma ta kwanta amma har yanzu hawaye bai tsaya da kwararowa ba a fuskarta.

Bayan ya ajiye kayan yace ta taso ta karya yasan yanda aka wayi garin yau na firgicin rashin da aka yi ba lallai bane ta tsaya karyawa.

Girgiza mishi kai tayi alamun ba zata ci ba.

Amir yace " dan girman Allah ki tashi ki karya," bata son yin musu in tana cikin tashin hankali irin wannan, hakan yasa ta tashi ta d'an ci ta sha tea d'in sannan ta koma ta kwanta.

Bayan wasu lokuta zazzab'i ya rufeta ta fara rawar sanyi, nan da nan jikinta ya gashe da zafi, hankalin Amir ya tashi ya rasa ya zai yi.

Hakanan ya sake d'aukarta suka yi Asibiti aka basu gado ganin yanda jikin nata yake a rikice har takai ga tana suma.

Bayan kwana d'aya washe garin ranar kenan b'angaren makaranta mamaci dai an birneshi, se dai fatan Allah yai mishi rahma, amma kowa ka gani cikin makarantar baya tare da farin ciki, duk mutuwar Sadeeq ta tab'a su, saboda mutum ne shi mai faran-faran da jama'a shiyasa suke kukan rashinsa.

An so bada hutun makarantar 'yan sanda suka ce kar a bayar suna so su gano wanda ya aikata wannan laifin, hakan ne yasa aka ci gaba da zuwa.

Su Abdul ne da su sani dukkanin abokan Amira dai suna harabar makarantar zaune suna jajantawa juna, suna cikin tattaunawa a kan idan an tashi zasu lek'a Amira su ga ya take daga nan su k'ara bata baki, kawai sai suka ji sallama a kansu, suna d'agowa suka ga 'yan sanda.

Babban nasu yace " waye Abdul a cikin ku?" Abdul yace " ni ne yallab'ai Allah yasa dai lafiya?"

'Dan sandan nan yace " munzo ne mu tafi da kai caji office domin yi maka wasu tambayoyi, sannan kuma ya nuna sauran yace duk zamu gayyace ku d'aya bayan d'aya domin jin bayanai daga bakunan ku," haka suna ji suna gani 'yan sandan nan suka tasa k'eyar Abdul suka tafi dashi caji office.

Muje zuwa

*🅱K CE😘💋*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘

RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (🅱K)*
```(Autar marubuta)```

SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
_(Mamie)_

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```{Gidan zaman lafiya da amana insha Allah}```

WOHOHO HABIBTY
💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃
*Zo mu zauna dake masoyiya na amince dake har zuciya, tunda kin mini so da gaskiya, zana kula dake zinariya😍😍😍😍😍😘😘😘😘😘💋💋💋💋💋*
_*Ya ilahi HABIBTY NAH QUEEN RUQEEY, yasin har na gama typing zan turo naga gagarumin yabo had'e da kirarin da kika rangad'amin a page d'inki na yau cikin littafin sharrin ashqeey, hak'ik'a so baya tab'a tsufa, nagode nagode nagode Allah ya k'ara mana aminci da k'aunar juna, yanda kike farantamin kema Allah ya dauwamar da ruhinki cikin farin ciki har k'arshen rayuwa, daga k'arshe nake cewa ki rik'e karki manta har abada 🅱K tana yinki💃💃💃💃💃😍😍😍😍😍😘😘😘😘😘💋💋💋💋💋*_

PAGE 20 to 25

Su Sani kuwa saboda tashin hankalin da suke ciki yasa basu tafi wajen Amira ba su dubo halin da take ciki.

B'angaren su Amira kuwa tunda Amir ya kaita bata farka ba sai cikin dare.

A hankali ta bud'e idanunta ta d'ora su kan Amir wanda ke ta faman zuba gyangyad'i kan kujera, kallon d'akin ta fara yi sannan ta fahimci a inda suke, nan da nan kuma abinda ya faru ya dawo mata sabo.

Kuka ta fara yi, wanda yai sanadin bud'e idon Amir, ya kalleta yace " wai sai yaushe zaki daina wannan kukan ne Amira, dukkan mai rai fa mamaci ne, ya kamata ki saka wa ranki hak'uri tunda ke da kanki kinsan kukanki bazai tab'a dawo dashi ba."

Da k'yar Allah ya taimake shi ya samu tai shiru ta daina kukan.

Washe gari jikinta ya yi sauk'i sosai ya had'a mata tea tasha sannan ya bata magunguna suma ta sha, likita ne ya shigo tare da sallama Amir ya amsa suka gaisa sannan likita ya gaishe da me jikin ya kuma k'ara dudduba ta, bayan ya gama ya kalli Amir yace " Matarka ta samu sauk'i an sallameku dama damuwa ce tasa jikinta ya rikice kuma a guji b'ata mata rai zai iya sanadin kamuwarta da hawan jini," ya rubuta mishi maganin da zata cigaba da sha sannan suka yi mishi godiya Amir ya biya dukkanin kud'in da ake binshi, dan lokacin da ya kawota kud'in jikin shi bazai ishe shi ya biya kud'ad'en ba, sai da yaje ya ciro.

Bayan sun fito daga asibitin suka shiga motar Amiran suka doshi hanyar gida, Amira ta kalli Amir tace dan Allah ka kaini makaranta inaso inga Abdul akwai maganar da nake so muyi dashi ne," Amir yace " a'a kiyi hak'uri sai kin k'ara jin sauk'i," rau - rau tayi da idanu alamun zata yi kuka, hakan yasa ba yanda ya iya ya karkato da motar hanyar makarantar su.

Suna zuwa bayan sun gaisa da su sani Amira take tambayar su ina Abdul, nan take suke shaida mata ai tun jiya 'yan sanda suka zo suka tafi dashi, kuma sunje da yamma sun hana su ganshi, sannan basu fad'a musu komai ba akanshi.

Amira tace "wai akan me suka kama shi to?" daga baya taji ance " saboda muna zargin shine ya kashe Sadeeq."

Gaba d'ayansu juyowa suka yi domin suga mai maganar, wani d'an sanda ne, a gaba bayanshi kuma ga wasu jami'an nan dukkansu sun sha uniform, ga dukkan alamu na gaban shine me maganar.

'Dan sandan nan ya kallesu yace " sunana insfecto Yahya (kafi k'arfin mugu), mun samu labarin cewa kaf makarantar nan Sadeeq bai da wasu abokai sai ku musamman ma ke Amira, saboda haka mun zo ne domin mu tafi daku station domin amsa mana wasu tambayoyi, sai ku wuce mu tafi koh, suma haka nan suna ji suna gani aka tasa su dukkan su har Amir aka tafi da su.

Ko da isar su insp Yahya ya kalli Amira yace " dake zan fara domin kamar yanda muka gani tare da hujjoji da bayanan da suka gabata a garemu ya nunar mana cewa Sadeeq da Abdul suna sonki, kuma a kanki ne aka kashe su."

Amira ta zaro idanu tare da fad'in " so, ni, a kaina kuma aka kashe shi, tabbas nasan mun shak'u da Sadeeq amma gaskiya babu wata kalma ta so da ta tab'a had'amu, haka shima Abdul d'in."

Insp Yahya yai murmushi sannan yace " ba lallai bane ke sun fad'a miki, amma duk suna sonki in kika lura da abinda Abdul yai miki cikin jama'a da kuma yanda Sadeeq yayi a kanki da furucin da ya yi shima Abdul ya mayar mishi da martani, sedai soyayyar tasu zata iya zama da bambanci, shi Abdul ta iya yiwuwa sha'awarki kad'ai yake, idan muka yi la'akari d rungumar da yai miki da yanayin yanda yake shafa jikinki, duk da dai a cikin maye ne yake, amma abinda ke ranshi ya nuna a wannan lokacin, a yayinda Sadeeq ke yi miki so na gaskiya, amma in baki yarda ba me zakice akan wannan hoton?"

Wani hoto ya nuna mata d'aya daga cikin hoton gawar shi da aka d'auka, ya rubuta sunanta b'aro b'aro a jikin hannun shi.

Bayan ta gama gani sai ya karb'a tare da sake mik'a mata wata takarda yace ta karanta, a cikin litattafan Sadeeq suka gani, karb'a tayi shima ta karanta an rubuta.

_Amira ina k'aunarki k'auna ta hak'ik'a amma ina tsoron bayyana miki saboda bansan yanda zaki karb'e ni ba, ko ki amince ko kice min a'a._

Daga k'arshe wasu hotuna ya nuna mata wanda suka d'auka su biyu a bayan hotunan duk ya rubuta _i love you Amira,_ wanda suke tare da Abdul kuwa sai ya soke Abdul d'in ya bar nasu, shima a bayan shi an rubuta _babu abinda zai rabamu dake sai mutuwa insha Allah._

Kuka take yi mai tsuma zuciyar sauraro, cikin kukan tace " wallahi be tab'a fad'a mun ba, ana gobe za'a kashe shi ya sanar dani cewa akwai abinda zai fad'amin washe gari, ashe so yake ya fad'a mun yana sona," ta cigaba da kuka mai tsuma zuciya.

Insp Yahya yace " yi hak'uri kiy shiru insha Allah zamu yi iya bakin k'ok'arinmu wajen kama wanda ya kashe miki masoyi."

Amira ta kalli Insp Yahya tace " duk da haka ni bana zargin Abdul shi ya kashe Sadeeq."

Insp Yahya yace " in ba shi bane waye to?"

Amira tace " bansan ko waye ba, wannan aikin ku ne gano mai laifin."

Insp yai murmushi sannan yace " abinda muke kan yi kenan, amma ke akwai wanda kike zargi ne a ranki?"

Amira tace " a'a bana zargin kowa dan bashi da abokin fad'a sam, da Abdul d'in ne ma basu wani cika shiri ba."

Insp yace " meyasa basa shiri?"
Chapter 4 · 0% Book details