Sashe 16
So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yau Litinin su Amira ne kan ti-ti za'a tafi kaisu makaranta Amira ce keta kalle kalle, a yayin da ita kuma Rukayyat ke danna k'aramar wayarta tana game, Amira ta hango wani bawan Allah zaune gefen ti-ti rigar shi duk ta yage sanyi yanata kad'a shi yana kakkarwa, Amira tace wa driver ya tsaya, yana tsayawa ta fito daga motar rik'e da rigar sanyi a hannunta, tana zuwa dai-dai inda yake ta mik'a mishi tare da fad'in " gashi kasa, ka daina zama iska tana kad'aka zaka kamu da mura, in sanyi kake ji ka tafi gidanku mana, wannan yaron ya tashi da k'yar ya karb'i rigar ya saka, ita kuwa Amira har ta juya da gudu ta shige mota driver ya ja suka tafi, wannan ya bi motar da kallo har ta k'ule a ranshi yana fad'in dama akwai ragowar mutane masu tausayi da taimako haka, gashi dai a karo na farko ya samu wadda ta taimakeshi lokacin da yake buk'atar hakan kuma ya rasa sai gata Allah ya turo mishi ita.
Amira kuwa suna hanya tana tunanin yaron nan da ta baiwa riga, tausayin halinda ta tsince shi a ciki take, Amira kenan yarinya ce me tausayi tun tana 'yar tatsitsiyarta.
Bayan an tashi daga makaranta aka zo aka d'aukosu suna kan hanya dai-dai inda ta ganshi da safe ta kalla har yanzu yana nan a wajen, wannan karon ma kanshi na duk'e kamar kuka yake yi, sai ta sake cewa driver ya tsaya da gudu ta sake fitowa taje har inda yake ta tsaya, sannan tace " me kake yi anan, tashi muje ka shiga mota mu kaika gida, kanshi yana duk'e kuma be d'ago ba kuka yake yana rik'e ciki, Amira tasa hannu ta d'ago kanshi tace " meyasa kake yin kuka? yaron nan yace yunwa nake ji, yau kwana na uku banci komai ba.
Komawa inda motarsu take tayi da gudu ta d'auko fura da nono ta bashi tace gashi kasha, ya karb'a tare da kallon ta yace " nagode Allah saka miki da alkhairi, " Amira batace komai ba sai ta juya tana yi tana waigowa ta shige mota akaja suka tafi gida.
Ko da isar su gida Amira na canza kaya suka ci abinci tace wa Mum d'inta tana so a fita da ita ta siyo abu, ba yanda Mum ta iya domin kuwa Dad d'inta ya bada umurnin a kaita duk inda take buk'atar zuwa, suka fita ita da sister d'inta Rukayyat, suna fara tafiya Amira tace wa driver hanyar makarantar su zai bi, suna zuwa dai-dai gefen ti-tin da take ganin yaron nan ta nunawa driven inda zai faka ya faka motar a inda ta umurta sannan suka fito ita da sister suka k'arasa har inda yake, zama ta yi kusa dashi ta kalle shi shima ya kalleta suka yiwa juna murmushi, sai tace " meyasa koda yaushe kake zaune a nan, kuma koda yaushe kaya d'aya kake nanatawa, baka da iyaye ne?"
Nan da nan idanun yaron suka ciko da k'walla yace " haka na taso bansan iyayena ba, na rayu a hannun wani dattijo wanda ya raine ni har na girma shi na sani a matsayin uba duk da ya tab'a fad'amin ba shi ya haifeni ba, a hannunshi na girma ya fara raba mana kayan maye muna siyarwa a tasha ni da sauran yaran dake gabanshi, a haka har muma muka fara koyon sha dan muji me ake ji a ciki."
Amira ta zaro idanu tare da fad'in "laaaa yanzu kana d'an yaro amma kake shaye-shaye," yaron nan yace " ke na girmeki fa amma kike cemin yaro," Amira tai murmushi sannan tace " to meyasa baka zauna wajenshi ba kake kwana anan?" yaron nan yace " Ai ya rasu yau sati guda kenan, kuma gidan da yake ciki gidan haya ne, masu gidan yana mutuwa suka koromu suka rufe gidan da kwad'o shine muka dawo kwana a nan."
Amira sarkin kuka kuka take yi sosai, Rukayyat ma idanunta sun cika da hawaye, bayan tasha kuka sai ta dafa shi tace " sunana Amira kai fa ya sunanka?" Yaron yace " sunana Ameeru," sai suka kalli juna a tare suka yi murmushi suna fad'in sunan su iri d'aya.
Amira tace " zan yiwa mahaifina magana ka dawo gidanmu da zama a saka a makarantar mu mu rik'a tafiya tare ko baka so?"
Amir yace " ina so mana na dad'e ina sha'awar inga ina zuwa makaranta amma ba hali."
Nan Amira suka yi mishi sallama akan zataiwa Dad d'inta magana duk yanda suka yi gobe zata dawo ta sanar dashi, ta ciro minti a cikin jakarta tare da kud'i ta bashi tace ya siya abinci, sannan suka juyo zasu tafi, Amir ya k'wala mata kira " Amiraaaa," ta juyo ya sake cewa " nagode Amira kina da kirki."
Amira tai murmushi ba tare da tace komai ba ta shiga mota a yayin da Amir keta tsallen murna yau zai ci me dad'i, yana d'ago da idanunshi yaga sunata yi mishi dariya nan da nan ya dakatar da tsallen shima yana dariya suka ja motar yana d'aga musu hannu suma suna d'aga mishi.
Amira na komawa gida ta tarar da Dad d'inta ya dawo, yaro ba hankali da gudunta ta fad'a jikinshi shima ya rungumeta yana fad'in Daughter daga ina haka?" Amira tace "Dad so nake ka taimaka wa wani yaro ya dawo gidanmu da zama shima ka sashi a makarantar mu mu rik'a tafiya tare," Dad yace " a'a daughter hakan ba mai yiyuwa bane, zan iya yin taimako tunda wannan ba shi bane na farko da kika sa nai taimako, amma bazan had'a zuri'ata da bare ba, babu wanda zan yarda ya shigo cikin ''ya'yana in ba jini na ba," Amira ta fara kuka tare da tashi daga jikinshi, cikin sauri kuma ta haye sama ta shige d'akinta tare da sa key, Dad d'inta na cewa " kinga my Daughter, " ina bata juyo ba har ta shige, Uncle ya kalli Dad yace " yaya yau kai da 'yar lele anji kanku kai da baka son ko kad'an a tab'ata, inaga da ka taimakeshi d'in.........Dad ya katseshi ta hanyar d'aga mishi hannu tare da fad'in wannan maganar ma ba mai yiwuwa bace a barta kawai," daga nan suka ci gaba da hirar abinda suka zauna tattaunawa a kanshi.
_Ayi hak'uri da wannan_
Muje zuwa
*🅱K CE😘💋
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (🅱K)*
```(Autar marubuta)```
SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
```(Mamie) ```
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah) ```🤜🤛
*Ina rok'on mahaliccina ubangijin kowa mai komai, sarki mai ikon komai akan kowa ka baiwa MUMCYN TAWAN lafiya👏 ya Allah ka yaye mata, ka dauwamar da d'orarriyar lafiya a gareta,👏😭😭😭😭😭 TAWAN ki kwantar da hankalin ki cuta ba mutuwa bace da yardar Allah Allah zai bata lafiya.*
*RAHEENAT M. ABBAKAR*
_(My Heenat)_
&
*MARYAM KWARE*
_(My D)_
*Sannunku bayin Allah ina rok'on Allah ya dorar muku da lafiya*👏😭
*DAD'AD'D'IYAR SOYAYYA TUN YARINTA BATA TAB'A GUSHEWA HAR GIRMA*
PAGE 70 to 75
Ameeru yaro ne k'arami wanda a k'alla shekarunsa ba zasu wuce goma ba.
Tun daga wannan lokacin Amira ta shiga yin fushi da Dad d'inta, kuma kullum in zata tafi makaranta sai ta tsaya ta baiwa Ameeru kud'in kashewa da da abinci, duk kud'in da ake basu na kashewa ita tara nata take yi ta kawo mishi.
Akwai wata rana, yana zaune a gefen ti-ti domin baida wani wajen zuwa banda nan, gwara ma da yana tashi a shiga tasha ko cikin kasuwa domin samo abinda zai saka a bakinshi, amma yanzu baya zuwa ko ina saboda akwai me bashi.
Yana zaune ba dad'ewa sai ga Amira ta taho, tana zuwa ta tarar dashi yana kuka, zama tayi cikin sauri kusa dashi tana tambayarshi dalilin kukanshi, Ameeru cikin kuka yace " wani almajiri ne ya d'auke min tabarmar da na tara kud'i na siya nake kwana akai, da kwanon abincina, harda takalma na, ina k'ok'arin karb'a ya dukeni da aka taru ana tambaya yace wai nashi ne naje na sato, aka zane ni, jiba har ciwo ya jimin, ya d'aga hannunshi da guiwoyinshi yana nuna mata ciwukan, har gefen bakinshi ma ya fashe.
Kuka itama Amiran ta fashe da shi har Amir d'in ma yai shiru amma ita tana kuka, kallonta yake yana fad'in "kiyi shiru to nima na daina kukan ai."
Ya share mata hawayen da hannunsa, Amira ta mik'e tsaye tare da fad'in "ina zuwa," ta juya da gudu tai hanyar gidansu, ko da shigarta d'akin mahaifin ta ta shiga ta jawo drowar ajiye kud'in sa ta d'ibo masu yawa ko rufe drowar bata yi ba ta sake kwasawa a guje ta fito, da yake gidan su yana kusa da inda Ameeru d'in yake, koda isarshi ta mik'a mishi kud'in tare da fad'in ka siya wata tabarmar da takalmi, harda kaya ma ka siya, cikin farin ciki had'e da tsoro ya karb'i kud'in da bai tab'a ko tunanin ma zai rik'e irinsu ba ko a mafarki.
Ameeru yace " duka wannan nawa ne! kud'in ai sun yi yawa, ya zanyi dasu, k'wacewa ma za'ai," Amira tace " ai b'oyewa zaka yi inda baza'a gani ba, kad'an kad'an zaka rik'a kashewa, ya yi mata godiya, suka yi hira kad'an sannan tace bari ta koma gida kar a nemeta.
Tana kowama gida Mahaifin ta na fitowa daga cikin d'aki, yana tambayar waye ya bud'e mishi drowa, Amira tace " nice Dad," Dad yace " meyasa kika bud'e?" tace "na yi taimako ne da kud'in Dad, a makaranta malamin mu kullum yana yi mana nasiha akan me kud'i ya rik'a taimakawa mara shi, shiyasa na taimaki wani, kaima baka ganshi ba sai ka tausaya mishi in ka gan.........." kafin ta k'arasa magana Mahaifin ta ya daka mata tsawa abinda bai tab'a yi mata ba, aikuwa nan da nan ta razana tare da fara hawaye, ta ruga d'akin Mum d'inta tana kuka.