← Book details So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 54

Sashe 52

So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan su Amir sun koma gidan su Dad da zama shi kuma Uncle ya d'auko matarshi da yaranshi suka dawo gidan da Abba ya basu halak malak, basu ri'ko komai ba kansu kawai suka kai, domin yace ya basu harda komai na gidan duk ya zama mallakinsu, a ranar da suka koma gidan ma saida Uncle yai kuka, tunani yake wai shine yau da wannan tafkeken gidan da kaya na alfarma ga kuma masu aiki da masu gadi, abinda ya kamata ace d'an uwanshi yayi mishi tun lokacin da yake da d'aukakar da kuma tarin dukiyar, gashi nan yanzu be ciba be bari sun mora ba wasu 'kattin banza sunzo sun yashe, ya dad'e yana takaicin wannan abu wai ace d'an uwanka yana da abu amma bazai iya taimakonka ba se wani bare can wanda basu had'a komai ba, nan dai yaci kukanshi matarsa na rarrashi sannan ya 'kara yiwa Allah godiya tare da zubawa Abba Ahmad addu'o'i.

Bayan komawar su Abba da sati d'aya, yau juma'a dawowar su Dad da Uncle da Amir kenan daga masallacin juma'a.

Yanzu kam halayen Dad gaba d'aya sun sauya, wani irin sabon tattali da 'kauna yake nunawa Amir, domin a yanzu ya tabbatar babu wanda yake 'kaunarsu da gaskiya sama dashi, kuma ya fahimci cewa ba'a sakaci da samun masoya na 'kwarai saboda ko ba komai duk halin da ka shiga sune basu gudunka, kuma irinsu ne suka yi 'karanci yanzu a duniya.

Shi kanshi Dad d'in a yanzu yafi jin dad'in rayuwarshi fiye da da.

Tun Amir yana d'ari-d'ari dashi har yazo ya saki jiki domin duk inda zasu tare suke zuwa hatta wajen motsa jiki, sha'kuwa sukai ta ban mamaki a tsakaninsu.

Yau ma bayan sallar la'asar Dad ne da Amir a wani fili na cikin gidan sunata buga 'kwallo.

Amira ce ta fito daga cikin gidan itama tana neman su Amir d'in, hangosu tayi sunata faman buga 'kwallo cikin nishad'i da kwanciyar hankali, tsayawa tayi tana kallonsu, fuskarta d'auke da murmushin dake bayyanar da farin cikinta.

'Karasawa cikin wajen tayi, saida ta shiga tsakiyar filin sannan taja ta tsaya tana kallonsu.

Dad yace "Doughter matsa mana," Amir shima yai magana "matsa mana ko so kike kija Dad ya cinyeni?"

Amira tace "Allah nima dani za'ayi 'kwallon," Amir ya kalli Dad, shima Dad ya kalli Amir suka kece da dariya suna yi suna nunata.

Amira tazo iya wuya, sai ta zauna ma a tsakiyar filin tare da sake murtuke fuska, su san cewa lallai da gaske take, tace "wallahi in dai bakuyi dani ba to kun gama wasan daga yanzu."

Dad ya 'karaso inda take tare da 'kunshe dariyarsa, yana 'karasowa ya dafata yace "kwantar da hankalinki, jeki ki kirawo Mum d'inki tazo ayi da ita, saboda ban yarda ku had'e min kai ba kuita yi ku biyu kuna cinyeni, gwara matana tazo ku biyu mu biyu."

Amira kuwa da gudunta ta shiga cikin gida Amir shima ya biyota ta jawo Mum d'inta tana fad'in "Mum zo muje," Mum tace "ke sakeni, ina zamuje kuma, ina zaki kaini?"

Amira bata fasa janta ba tace " kedai kizo muje kawai koma menene zaki gani, saida sukaje filin sannan Amira tace "'kwallo zamuyi kina b'angaren Dad, ni ina b'angaren Amir."

Mum kuwa ta biye mata, 'yan gidan gabada'aya da security's da masu aiki sukazo suka zagayesu suna kallo domin suga yanda za'a 'kare, aka karkasu, Dad da Mum, Amir da Amira.

Nan aka fara buga wasa duk wanda yaci sai tsalle da murna, idan su Amir sukaci sai su rungume juna shi da Amira suna murna, idan su Dad ne sukaci suma haka sukeyi, rungume juna sukeyi suna murna.

Haka sukaita yi gwanin ban sha'awa sai burge jama'ar gidan suke yi, bama su kad'ai ba kowa ji yake yi inama shine yake tare da iyalanshi haka.

Haka sukaita yi har sukayi lilis, kuma a lokacin Amir da Amira sunci su Dad wajen sau takwas su kuma Dad d'in suna da uku, su Amira sun fisu da biyar kenan, a haka aka tashi su Dad suna fad'in Allah ya kaimu na gaba zamu rama, su Amir na yi musu gwalo suna fad'in zasu rame dai.

Haka rayuwarsu ta cigaba da kasancewa gwanin ban sha'awa, Amir da Dad kuwa wata soyayya suke gwadawa juna kamar d'a da mahaifi, sha'kuwarsu abun mamaki cikin 'kan'kanin lokaci kuma.

*BAYAN WATA UKU*

Bayan wata uku su Dad suna zazzaune a falo sai ga sallamar su Abba sun sake yi musu dirowar bazata.

Cikin tsananin farin ciki da walwala suka tarbesu, suka zauna aka gaggaisa, bayan sunci sunsha suka ce zasu tafi masaukinsu, da yake gidajen Abba a garin sunada yawa, sai suka yi musu sallama suka tafi.

Washe gari Abba ya sake zuwa shi da matarshi, bayan an gaisa sannan yai gyaran murya yace "wannan karon abinda yasa muka taho tare da yi muku zuwan bazata abu uku ne, na farko duk na taraku ne domin ku zama shaida na baiwa abokina wato mahaifin Amira naira million hamsin da kamfanoni na guda biyar da gidajena guda biyar, nayi iyakar 'ko'karina wajen ganin an binciko su Nura amma kwata-kwata babu labarinsu, ina tunanin basa 'kasar nan ma, abu na biyu kuma kai Uncle na baka kamfanina guda d'aya dake Abuja, idan zamu koma sai mu tafi tare dakai ka ganshi, sai abu na 'karshe shine, a 'yan kwanakin nan ina yawan yin mafarkin d'an uwana Salisu, dan haka inaso kai Amir ka shirya kai da matarka gobe in Allah ya kaimu muje kontagoran domin ganin halin da suke ciki."

Nan fa d'akin ya karad'e da koke-koken farin ciki, Dad cikin kuka yace "ha'ki'ka ka saka min da alkhairi wanda ni na kasa kwatanta hakan a kanka kaida d'anka Amir, ni nasan babu ranar da zan daina jin kunyar abinda na aikata muku, dan Allah ku yafemin, ni bansan ma me zan fad'i ba wajen gode maka Ahmad," ya cigaba da kuka.

Amir ne yai murmushi, sannan ya 'karasa kusa dashi yace "haba Dad menene hakan kake yi, yanzu haka zaka ri'ka yi idan jikokin ku suka fara zuwa suna ganin kana kuka wallahi dariya zasu ri'ka yi maka ba ruwana," duka d'akin aka kwashe da dariya.

Washe gari su Abba da su Amir suka shirya suka fito suka yi sallama da kowa sannan suka shiga motoci sai hanyar kontagora.

Suna d'aukar hanyar kowa yai shiru kowa da abinda yake sa'kawa a ranshi, shi kuwa Abba komai dawo mishi sabo yayi, nan da nan yaji hawaye na gangarowa daga idanuwanshi.

Basu d'auki lokaci me tsawo ba Allah ya kawosu cikin garin kontagora lafiya.

Ta 'kofar gidan iyayenshi suka bi Abba yace a tsaya suka fito suka shiga cikin gidan, ba kowa a ciki duk ya lalace, nan Abba yaci kuka mai isarshi na tunowa da iyayensu ya gode Allah sannan ya kallesu duka yace "nan ne gidan iyayena, yana gama fad'in haka ya fito suma suka biyoshi suka shiga mota suka cigaba da tafiya.

Nan da nan gari ya fara d'auka Ahmad ya shigo gari, mutane suka cika wajen motocin suna bin motocin da gudu suna murna da farin cikin sake ganin Ahmad.

'Daya daga cikin wad'anda ke bin jikin motar Abba ya tambaya gidan yayanshi suka yi mishi kwatance, suka karkata motarsu domin 'karasawa gidan.

Jikin wani katafaran 'kerarren gida sukai fakin, gidan babban gida ne kuma me d'an karen kyau da tsada, zamu iya cewa ma duk garin ko kuma ace duk unguwar da kewayenta babu mai 'kerarren gida na gani na fad'a irin na yayan Abba Ahmad.

Bayan sun shiga da motocin su sun faka sannan suka fito suka shiga cikin gidan, tun daga 'kofar gidan suke ganin 'yan sanda cikin kakinsu da kuma security's har suka shiga ciki, inda Amir da Amira suka ga abin mamaki kuma suka ga abinda yai matu'kar d'aure musu kai, Insp Yahya suka gani zaune cikin falon gidan shi da wata mata wadda suke matu'kar kama da Insp Yahya, kamar tasu har ta b'aci, saboda tsabar kama da ace tsohuwar namiji ce in aka ganta za'a ce Insp Yahya d'in ne.

Amir ya yiwa mahaifinsa rad'a yace "Abba kaga wanda yaso halakamu ni da Amira, kuma harda shi aka yashe dukiyar Dad d'in Amira, yana wajen ranar da abun ya faru, yau me rabani dashi sai Allah."

Amir cikin zafin nama ya kutsa cikin falon har gaban Insp ya sha'koshi tare da fad'in "nan ma ka biyomu ne ka kashemu, to kafin ka kashemu ni zan kasheka," Amir ya sha'keshi sosai da hannunsa duka biyun.

Abba ma yayi-yayi ya cire hannunsa daga wuyan Insp amma ya kasa, saida ya sharara mishi mari sannan ya sakeshi.

Abba ya kalli Insp da wannan matar da suka gani tare dashi yace "dan Allah kuyi ha'kuri da abinda ya faru, ku bamu dama mu zazzauna akwai muhimmin abinda ke tafe damu."

Matar nan tace "bakomai ku zauna ga kujera nan," kowa ya zauna sannan Abba yai gyaran murya ya fara magana, "ni sunana Ahmad ni 'kani ne ga Salisu wanda aka tabbatar mana da nan ne gidanshi, wad'annan iyalina ne, wannan matata ce sunanta Khadija, ya nuna Umma, sannan ya 'kara nuna Amir yace wannan d'ana ne, sunanshi Amir, wannan kuma matarsa ce sunanta Amira.

Wannan matar ta fad'ad'a fara'arta sosai tare da sake yi musu sannu da zuwa.

Insp Yahya kuwa jin wannan bayanin yasa ya fara du'kar da kai kamar tsohon munafuki, su kuwa Amir da Amira duk sun 'kosa suji matsayin Yahya cikin wannan gidan, a yayin da shi kuma Abba ya 'kosa a nuna mishi inda d'an uwanshi yake domin yaje ya ganshi.

Wannan matar ce ta bud'e baki alamun zatai magana sai Insp Yahya yai zumbur ya mi'ke yace "um ni bari in tafi zan dawo wani lokacin."

Wannan matar tace "a'a zauna tukunna mu gama yin maganar."

Insp Yahya ya bud'e baki zai sake magana Matar nan ta sake fad'in "ka zauna mana."

Ba yanda ya iya ya koma ya zauna, matar nan ta sake bud'e baki tace "

_Wai wacece wannan matar, kuma wanene Insp a gidan kodai akwai wajen wanda yazo ne? ina yayan Ahmad? ku dai ku biyo Autar marubuta dai_

Muje zuwa

*🅱K CE😘💋*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘

RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (🅱K)*
```(Autar marubuta)```
Chapter 52 · 0% Book details