Sashe 31
So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan an saka su a cell d'in ne Amir ya kalli Amira yace "malama ina da tambaya fa," Amira tace nasan tambayar, yanda aka yi na yi magana da 'kawata barista bayan ko da yaushe muna tare a gar'kame kake so ka sani koh, to kwantar da hankalinka yanzu zan fad'a maka, akwai ranar da aka kawo mana abinci har na ro'ki wanda ya kawo abincin a bani biro da littafi ya kuma bani har kana tambayata me zan yi dashi nace maka zan yi zanen lalle ne saboda ina son yin zane musamman na 'kunshi kala-kala saboda in munyi aure in ri'ka yi maka har kayi dariya, to a lokacin bayan mun ci abinci kayi bacci na rubuta wasi'ka cewa su taimakeni zan basu sa'ko su kaiwa Barista Yasmeen zan rubuta musu adress d'inta, in har suka kai min zan basu zoben hannuna wanda na siye shi 10k su siyar su ri'ke kud'in, bayan na gama rubutawa na saka a gefen farantin da muka gama cin abinci, can sai ga wani jami'i yazo d'aukar kwanikan a lokacin ne na mik'a mishi harda wasi'kar, bayan minti biyar sai gashi ya dawo yace in bashi sa'kon, yana tsaye na rubuta na m'i'ka mishi wasi'kar tare da sake yagar 'karamar takarda na rubuta mishi adress d'inta, har da lambar waya koda ya je ya tarar bata nan be sameta ba sai ya kira lambar, bayan minti talatin sai gashi ya dawo da yake ba nisa gidanta daga station d'in nan, ya shaida min ya bata har ta bashi takarda ma ya kawo min, ta rubuta cewa sa'kona ya iso gareta kuma ta karanta Allah ya kaimu ranar, na sallami d'an sandan nan ya tafi, Amir yace "ai har yanzu baki fad'a min abinda kika rubuta mata ba," Amira tace "ro'konta nayi ta taimaka min za'a kashe min miji, na bata labari a ta'kaice, sannan nai mata bayanin shari'ar da akai a baya, nai mata kwatancen kotun farko nace taje ta samo hujjojin da suka gabata a case d'in baya domin mu yi amfani dasu wajen samun nasara a case d'in, kaji yanda akai," Amir yace "lallai Yasmeen ta taimaka sosai amma ke kin fita taimakona saboda kece kika samar da hanyar taimakon, nagode Amira ta, tabbas ni da ke amana ne, kuma rabuwarmu aiki ne, Allah ya barmu tare," Amira tai murmushi, sannan tace "ameen, kai kuwa naga zan rasa masoyi ba dole in rud'e ba, koda yake ko mutuwar ne ma 'kafata 'kafarka sedai a kashemu tare," dukkan su sukai dariya.
Yau litinin, kuma a yau ne suka sake halartar kotu a karo na uku domin zama na 'karshe.
Bayan an karanto case d'in su Amir sai aka mi'kawa Alk'ali takardun domin gudanar da cigaban shari'ar, Al'kali ya d'an jima yana rubuce-rubuce, sannan ya d'ago kanshi ya kalli lauyoyin yace "kafin mu yanke hukunci kan wannan shari'ar ko akwai lauyan da zai 'kara cewa wani abu a cikin ku?" dukkansu suka ce "babu ya mai girma me shari'a," Al'kali yace "A bisa sauraron hujjoji da bayanan kowane b'angare, a bisa shaidun da Yasmeen ta gabatar mana na ha'ki'ka muma mun 'kara yin namu binciken mun tabbatar da gaskiyar shaidunta, saboda haka kotu ta yanke hukunci kamar haka: kotu ta wanke Amir daga zargin da ake mishi na kisa domin bashi da hannu kwata-kwata a ciki, sannan kotu ta bada izinin sake shi ya cigaba da gudanar da harkokinsa na rayuwa, kuma kotu tana gargad'in Insp Yahya kan ya ri'ka yin bincike kafin ya zartar da hukunci, karya sake bada shaidar 'karya akan abinda bai tabbatar ba, kuma karya sake turo mai laifi kotu ba tare da hujjoji bayyanannu ba, in ya sake haka to za'a hukunta shi kuma zai iya rasa aikinsa ta dalilin haka, bayan haka zai biya Amir million d'aya sakamakon b'ata mishi suna da lokaci da ya yi, da wannan nake cewa a nan muka kawo 'karshen wannan shari'ar," nan da nan Kotu ta d'auki ihu da fito saboda tsabar jin dad'i, 'yan sanda suka cire wa Amir ankwar dake hannunsa aka sallameshi, an zagaye su sai bashi hannu ake ana tayasu murnar samun nasara.
Insp Yahya kuwa ya kasa motsawa daga inda yake zaune, babu abinda ranshi ke yi banda suya.
Amir kuwa har sun kai bakin 'kofa zasu fita suka hango Insp, Amira ta ja hannun Amir suka 'karasa wajenshi, Amira ta kalle shi tana dariya tace " Insp Yahya sai ha'kuri fa nasan ba haka rai yaso ba, se dai ka sani cewa duk abinda Allah ya rufe ma'ana ya sirranta to babu wanda ya isa ya tone shi ya tonu, sai a d'au ha'kuri Amira da Amir dai Allah be ce yanzu zasu mutu ba tukun, sannan abu na 'karshe shine in kana so kai ka cigaba da tsira da ranka karka 'kara shiga harkarmu, in kuma ka 'ki to tabbas kwanan nan ba'kin ciki zai zama silar ajalinka," ta sa'kala hannun Amir cikin nata suka juya sukai tafiyarsu, suka barshi nan da takaicin da suka k'ara 'kunsa mishi.
Insp Yahya ya dad'e zaune daga 'karshe wayar Dad tasa ya d'aga tare da mi'kewa ya fita daga cikin harabar kotun, sauran jami'an da ke kewaye dashi suka mara mishi baya.
Cikin mota suka shiga suka ja, hanyar station suka nufa, Insp Yahya yaiwa Dad bayanin duk yanda shari'ar ta kaya a kotu da irin hukuncin da aka zartar a kanshi, Dad ya numfasa, sannan yace ya kwantar da hankalinshi zai biya kud'in da akace ya biyasu, kuma zasu sake d'aukaka 'kara wata kotun, Insp Yahya yace "ranka ya dad'e aikina nake tsoro kar na rasa kan wannan case d'in," Dad yace "kar ka damu, muna tare ai babu me dakatar da kai, ko an dakatar da kai zansa a maida kai, ko ka manta da matsayina na shugaban 'kasa ne, ko ka rasa wannan aikin inada wad'anda suka fishi wanda zan samar maka," Insp Yahya fa hankali ya kwanta nan da nan walwalarshi ta dawo, yaiwa Dad d'in Amira godiya sannan suka yi sallama.
B'angaren su Amir kuwa suna fitowa daga kotu suka tari me keke napep suka hau sai gida, gidan Amir suka yanke shawarar tafiya da niyyar bayan kwana biyu in sun huta sai su tafi gidanta su kwaso kayanta su dawo nan gidan Amir d'in da zama gaba d'aya.
Da isar su 'kofar gidan bayan sun fito daga napep Amir ya baiwa me napep d'in ha'kuri yace bari su shiga ya d'auko mishi kud'in, me napep d'in yace "ba damuwa," suka shiga Amira ta yada zango a falo, shi kuma Amir ya wuce ciki ya d'auko dubu d'aya ya kaiwa me napep yace ya bar canjin, me napep yaita godiya.
Yana komawa ciki yaga Amira uwar tsabta an fara kaye kaye saboda 'kura da d'akin ya yi, shima ya wuce ciki ya cire kayan jikinshi ya bar gajeren wando da singileti ya fito suka ci gaba da gyaran gidan tare, saida suka gyara ko ina suka kuma wanke inda zasu wawwanke sannan Amira ta tura Amir toilet yai wanka, ita kuwa ta wuce kicin ta shiga shirya musu abinci, amma saboda ta gaji taliya ta dafa musu, cikin 'kan'kanin lokaci ta kammala ta zubo a kula ta fad'a wanka, tana jiyo Amir na fad'in "nifa yunwa nake ji zan d'ibi nawa inci kawai," Amira tace "wallahi karka tab'a min abinci, in kaci baka jirani ba wuta bal-bal," Amir yai dariya, sannan yace "Allah ya shiryeki a bayi kike magana ko, yayi kyau."
Bayan ta fito suka ci abincin su suna ci suna hira har suka kammala, dai-dai lokacin sallar Azahar yayi suka yi alwala sukai sallah, suna idarwa bayan sun yi addu'o'i da nuna godiyarsu ga Allah suka kwanta abinsu ba b'ata lokaci bacci ya d'auke su.
Bayan kwana biyu Amir suka je gidan Amira suka kwaso dukkanin kayanta da abubuwan da zata yi amfani dashi ta dawo gidan mijinta Amir da zama gaba d'aya.
Haka rayuwar su ta cigaba da tafiya cikin walwalwa da jin dad'i.
*BAYAN WATA 'DAYA*
Amir zaune yake kan doguwar kujera a yayin da Amira uwar son jiki ta lafe a jikinshi kamar mage, yanata 'ko'karin d'agata tana 'kara ma'kal'kale shi, Amir yace Allah ki d'agani ko in yar dake, bakya ganin kin zama wata 'katuwa ne hatta nauyinki ya 'karu, gaskiya ina ganin zan kai ki asibiti a duba min ko mutane biyu ke danne min jiki ban sani ba," Amira tace "me kake nufi?" Amir yace "ina nufin a duba min ko ciki gareki mana," Amira ta 'kara kwanciya jikin shi sannan tace "ba wani ciki, kawai tsabar iya kiwonka ne," Amir ya bud'e baki zai yi magana kenan sai suka ji ana knoking d'in 'kofar su, nan da nan suka gyara zama sannan Amir ya bada izinin shigowa, domin su duk a tunanin su me wanki da gugansu ne yazo.
Insp Yahya suka gani ya shigo shi da wani mutumi yana wurga musu wani irin wula'kantaccen kallo, ba shiri dukkansu suka mi'ke tsaye cikin sauri, Amira tace "malam me ya kawoka gidanmu?" Insp Yahya yace "kwantar da hankalinki 'yan mata, wannan ba zuwana bane ni d'an rakiya ne kawai, ya juya ga wannan mutumin yace yi musu bayani."
Wannan mutumin ya kalli Amir yace "kaine Amir ko?" Amir yace "eh ni ne, lafiya?" wannan mutumin yace "sa'ko aka aikoni daga babban kotu dake gwammaja kan zargin kashe Sadeeq, sai kuma 'kararka da ake yi kan guduwa da wannan yarinyar ta kusa da kai, ga takardar," ya 'karashe magana yana mi'ka wa Amir takardar dake hannunsa.