Sashe 1
So Mahadin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (🅱K)*
SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
_(Mamie)_
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```
_*DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN K'AI*_
_*ALHAMDULILLAH GODIYA TA TABBATA GA MAHALICCINMU ALLAH (S.W.A) YA ALLAH INA MAI GODIYA A GAREKA DA NI'IMAR DA KAI MIN TA BAIWA, DA ARON RAI DA LAFIYA DA KA BANI ALHAMDULILLAHI INA K'ARA GODIYA A GAREKA,👏 YA ALLAH KA K'ARO MIN TARE DA DUKKANIN 'YAN UWANA MUSULMAI BAKI 'DAYA👏👏👏👏👏*_
_*YA ALLAH KA YI SALATI GA SHUGABANMU ANNABI MUHAMMAD (S.A.W) DA IYALEN GIDANSA TSARKAKA, DA SAHABBANSA BAKI 'DAYA.👏,*_
_*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S WALLAHI HAR GA ALLAH KUMA HAR ZUCIYATA INA JIN DA'DIN ZAMA DA KU, ALLAH YA K'ARA MANA K'AUNA, HA'DIN KAI, DA FAHIMTAR JUNA.👏😍*_
*AUNTYNAH AISHAN UMMA INA TAYAKI MURNAR KAMMALA DIGREE D'INKI LAFIYA, ALLAH YA KAWO AIKI NAGARTACCE DA ALBASHI ME TSOKA, AMMA FA KI SANI ALBASHINKI NA FARKO NAWA NE😉😂*
*ASIYA SEE-SEE SANNU BAIWAR ALLAH, ALLAH YA DORAR DA LAFIYARSA GAREKI👏😰*
_*INA MIK'O GAISUWAR BAN GIRMA GA DUKKANIN MARUBUTA HA'DE DA JINJINAR K'ASAITA, GAISUWA WADDA BATA K'AREWA HAR SAI RAI YA YI HALINSA, ALLAH YA K'ARA MANA K'AUNAR JUNA DA BASIRA.👏😍*_
_*WANNAN LITTAFIN GABA 'DAYAN SHI DAGA FARKO HAR K'ARSHE SADAUKARWA NE GA MA'ABOCIYAR HANKALI DA TUNANI, ILIMI DA HANGEN NESA, MA'ABOCIYAR KYAWUN HALI DA 'DABI'U ```MAMAN LABYB,,, KIN WUCE HAKA A GUNA, MATSAYINKI YAFI GABAN NAN, UBANGIJI YA 'DAGA DARAJARKI, ALLAH YA FARANTA MIKI RANKI ANAN GIDAN DUNIYA DA GIDAN LAHIRA WATO GOBE KIYAMA, TABBAS KINA AMINCI A FILI KUMA KINA AMINCI A ZUCIYA, NA FAD'A A FILI KUMA NA FA'DA A ZUCIYA, KECE MACE ME CIKE DA HALACCI A DUNIYA, IN AKWAI ABINDA YAFI SADAUKARWA DOMIN KARRAMAKI DA NUNA GIRMAN MATSAYINKI GARENI TO TABBAS ZAN YI.🙏🙏🙏🙏🙏😍😘*_
PAGE 1 to 5
Gidan marayu Amira ta fara zuwa matashiyar yarinya kenan ga tsananin kyawu da Allah ya bata ga kuma dukiya Allah ya hore, bayan sun gaisa da shugabar gidan sai ta bayar da taimakon kud'in da ta saba kawowa kamar koda yaushe.
Shugabar ta kalleta cike da farin ciki tace " Allah saka miki da alkhairi da irin wannan taimakon da kike yi mana."
Amira tai murmushi, sannan tace " ai dukiya ba komai bace dan ka bayar da ita ga mabuk'ata amfaninta kenan dama ka taimaki wanda baida ita sai Allah ya k'ara nunka maka mafiyinta, Addu'a kad'ai nake buk'ata daga gareku, kuma naji kuna buk'atar k'ara girman gidan za'a sake fad'ad'a wajen da yardar Allah, sannan duk abinda kuke da buk'ata dan Allah a sanar da ni, shugabar wadda Amira ta kirata da Mama tace to ba damuwa, Allah ya saka miki da alkhairi, Allah ya tsareki daga sharrin mutum ko aljan, mun gode sosai."
Daga nan suka yi sallama Amira ta fito ta shiga motar ta, ta d'auki hanyar gida.
tana cikin tafiya mota ta lalace mata a hanya, tayi - tayi ta tashi amma ina, kuma daga inda take akwai tafiya mai nisan gaske kafin ta k'arasa gida.
fitowa ta yi daga cikin motar tare da k'ura mata ido cike da takaici tana tunanin mafita a ranta.
Ta dad'e tsaye tana jiran giftawar abun hawa amma shiru kake ji, har ta ciro wayarta zata kira Dad d'inta ya turo mata da wata motar sai ta ji k'arar wata mota a bayanta, mayar da wayar tai cikin jaka sannan ta tsaya tsakiyar ti-tin ta rik'a d'agawa mai motar nan hannu, ba shiri ya ja wani irin burki a gabanta.
Wani had'ad'd'en saurayi ne ya fito daga cikin motar, sanye yake da k'ananan kaya ya sha tabarau ya fito tare da tunkaro inda Amira take tsaye.
Sai da suka yi kallon kallo wanda ke d'auke da wani sak'on da basu san ma'anar jinsa ba, sannan saurayin nan ya ja tsaki yace " mtswww ko wace mace da d'an k'aramin abu ya faru da ita sai ta fara k'ok'arin kashe kanta, wa ya sani ma ko auren dole za'ai miki kike k'ok'arin halaka kanki, to yanzu da kika tsaida ni me zan miki?"
Yana gama fad'in haka ya juya zai tafi sai tayi sauri ta sa hannu ta jawo shi, sannan tace " karka fad'a min maganar banza mana motata ce ta samu matsala shiyasa na tsayar da kai domin ka rage min hanya, kuma bana son tuk'in ganganci dan haka ka koma gefe nice zan tuk'a motar taka da kaina."
Saurayin nan ya tsaya yana kallon ta tare da mamakin k'arfin hali irin nata, se dai memakon ya ji haushi a'a saima ji yayi tana burgeshi, har taje bakin motar ta bud'e murfin motar, ta juyo inda yake tsaye tace " ka taho mu tafi mana ko in tafiyata in barka a nan," matashin nan ya rik'e k'ugu da hannu bibbiyu sannan yace " ikon Allah," a nan take ta k'arasa mishi da fad'in "sai kallo," tana gama fad'in haka ta fad'a cikin motar b'angaren driver ta zauna sannan ta tayar da motar, da yaga da gaske take zata iya tafiya ta barshi sai ya yi sauri ya k'araso ya shiga taja suka tafi.
Banda aikin kallonta babu abinda yake yi, zuciyarshi ce ke bugawa tare da jin wani bak'on yanayi a tare dashi wanda bai tab'a fuskantar kanshi a ciki ba, hakan yasa zuciyarshi ta aminta da cewa ya fad'a tafkin so duk da kuwa be tab'a yinsa ba, kuma be kula matan ma, amma halin da ya tsinci kanshi a ciki yanzu daga had'uwar farko ya tabbatar mishi da cewa ya fad'a soyayya, ita kuwa 'yar azarb'ab'i Amira banda uban surutu babu abinda take yi, a yayin da shi sam be ma san tana yi ba banda kallonta ba abinda yake, tare da zurfafa tunani kan son tantance gaskiyar abinda yake ji kuma yake zargi a halin da yake ciki yanzu.
Jin tana ta magana shiru be bata amsa ba yasa ta karkato da kanta wajen shi ta kalle shi taga ita kawai yake kallo, bud'ar bakinta sai tace " a haka dai gaka kamar wayayye ashe bak'auye ne kuma kan ta gane ne ban sani ba, dan naga alama wannan ne karo na farko da ka fara ganin mace a rayuwarka, haba wannan irin kallo haka sai kace zaka cinye ni," shi dai bai ce mata komai ba ya cigaba da kallonta, duk abinda tayi kawai burgeshi take yi.
Basu d'auki wani dogon lokaci ba suka k'araso k'ofar gidan su Amira, ta tsaida motar sannan ta fita, ta kalle shi tace " nagode sosai da rage min hanya da kayi, Allah ya saka maka da alkhairi."
Saurayin nan wanda dama idonshi yana kanta yace " kina kyau da tuk'i kin iya gudu a mota," Amira tayi murmushi, sannan tace " ai da tseren mota da na k'afa ba'a tab'a wuce ni, in kana so ka tabbatar da hakan to gobe ka shigo makarantar mu ka gani, ta fad'a mishi sunan makarantar sannan ta juya tai shigewarta gida.
Shima saurayin nan ya koma b'angaren driver ya ja motar shi yai gaba, fuskar shi na d'auke da murmushi wanda yake bayyanar da tsantsar farin cikin shi a yau.
Washe gari a wani keb'antaccen fili na makarantar aka tanada domin gudanar da tseren gasar gudun da za'ai, ko ina ka duba cike yake da mutane, a yayin da wad'anda za'a fafata dasu kuma suke ta motsa jikin su suna tirenin kafin a fara.
Ana gaf da farawa abokanan Amira su Sani da Sadeeq, da Abdul, da k'awayenta Rahma, da Suhaima, da pretty suka zo wajenta suna k'ara mata k'arfin guiwa akan tayi k'ok'ari wajen ganin ta yi nasara, duk da dama kowane lokaci nasarar a hannunta take, har sun juya zasu tafi Sadeeq ya juyo ya dawo wajenta ya ciro wani abu wanda yake kamar sark'a ya saka mata a wuyanta, sannan yace " mamata ce ta bani ni kuma na baki, na tsari ne, kar kiji fargaba ko shakka a ko'ina muddin kina tare da Allah."
Amira tai murmushi sannan ta rungume shi tare da fad'in "ina matuk'ar jin dad'in zama da kai amintacce na, ina jin dad'in kulawarka gareni, Allah ya barmu tare," sannan tayi mishi godiya,
_(wasu d'aliban bance duka ba, basu d'auki rungumar juna tsakanin mace da namiji a komai ba)_
Bayan Sadeeq ya tafi tana cikin shiri sai ta ji motsi bayanta, tana juyowa taga wannan saurayin wanda suka had'u jiya da irin kayan su na tsere alamun shima yana d'aya daga cikin masu fafatawa a gasar.
Muje zuwa
*🅱K😘💋*

*Mamie ina rok'on mahaliccinmu Allah mai kowa mai komai ya d'orar miki da lafiya, Allah yasa kaffara ne👏😭*
*PAGE 5 to 10*
K'arasowa yayi inda take, sannan suka kalli juna, Amira tace " ka kyauta da kazo kallon fafatawar mu," saurayin nan yace " a'a ba kallo kad'ai zan yi ba, had'uwa dake ya sauya min ra'ayina, yasa na yanke shawarar shiga gasar tseren nima duk da yau ne ranar farkon fara shigowata makarantar ina nufin sabon d'alibi ne ni, amma na rok'i da a sakani cikin jerin masu fafatawa, farko dai sunana Amir, kuma ni sabon d'alibi ne a ajinku, ina yi miki fatan alkhairi, Allah yasa kiy nasara."
Kallon shi tai tace Allah gafarta malam Amir ya kamata fa ka gane ni d'innan ba tsararka bace, nai maka zarra ta ko'ina, kuma nan bada dad'ewa ba zaka tabbatar da hakan, ta kanne mishi ido d'aya tare da zabga mishi uban gwalo sannan ta bar wajen, alk'alan gasar ne suka fara sanar wa kan duk wani wanda yake cikin wannan gasa to ya tabbatar da ya shiga cikin fili, sannan kowa ya tsaya a layi kamar yanda aka saba yi a baya.
Bayan kowa ya shiga layi aka basu umurni da su shirya, kowanne daga cikin su ya shirya, sannan aka irga d'aya zuwa uku suka fara gudu.