← Book details So Da Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 55

Sashe 53

So Da Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

adaidaitan ya karbu number Dadan ya kira tukun sannan tace ya ajiyesu zata tura a daukesu. Hakan kuwa akayi cikin rawar jiki tasa direba ya tafi ya dakkosu a bakin durbar hotel a titi . Sai kallen unguwar sukeyi . Haka suka karasa gidan. Bakunan su a bude. Direban ya rakasu har kofar sashen Dadaa. Da kanta tafito da sauri tana murmushi. Atuwa taja baya ta callara guda. "A hayye kwal landantsan. Allah me alheri. Jammu kece haka ? Kamar an sawo sabuwa a inji. Jar Miya da iskar fanka ta gyare ki Jammu." "Hansatuwa kenan. Ku sbigo Dan Allah . Farillatu tagaban goshi. Yan biyu kyautar Allah zoku zazzauna. Rumalle ya wajen su Usmanu . ?" Atuwa tashiga shafa royal chairs din parlorn tana kada kai. "Allah me alheri . Jammu Allah ya dandaala Miki arziki. Billahil lazi rabona da ganin irin kujerun nan tun wani fim dana gani a talabijin din a.." "Kai Atuwa. Dan Allah ki Yi shiru. Ku zauna ku huta. Bari a kawo ruwa da abinci..kafin sannan ga bandaki nan ko zaku rage ciki. Don ba Wanda Zai rage abinci sai kun cinye tas." Atuwa da sauri ta bude bandakin da Jammu ke nuna musu da yatsa.nan ma ta rike baki tana kada kai. "Allah me alheri..wai bayin wanka ne wannan? Idan da ranka kasha kalllo. Kwal landantsan. Tab. Uhm. Yo ke shikan mokadadadden Ardo ai gaba ta kai ki. Qur'anin ubangiji bayin nan yafi gidan mu haduwa. " "Uhm rumalle da jimmamman zauna ku Debi abincin ku. Ku kyale Atuwa taci daga baya.." "Ku rabu dani na kashe tsutsar idanu na. A hayye landantsan. Ayiriri!! Allah me alheri. " Atuwa ta baje duwaiwukan ta akan masai tana sakin bahaya. "Gwara nasa albarka. " I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ci3ao6233sn3&utm_content=6k8ur6p *WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_* *ZAFAFANKU BIYAR sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA* *_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_* *GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA WARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi* *JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE* *_DEEN MARSHALL Mamuhghee_* *_HALIN GIRMA hafsat rano_* *_TAKUN SA billyn abdul_* *_SO DA ZUCIYA miss xoxo_* ABI'AR ZUCIYA huguma_* *DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN AI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL* 1000 *Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin* 6019473875 MUSAA ABDULLAHI SAFIYA keystone bank Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 08184017082 *IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU* 09134848107 _*HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_* #team zafafa biyar . ___________ 2/25/22, 18:55 - Buhainat: I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ynog1zhfit0q&utm_content=6k8ur6p PLS FOLLOW US ON IG JAZAKUM ALLAH KHAIRAN AS YOU DO SO DA ZUCIYA!! NANA HAFSATU ZAFAFA 5 PAID BOOKS PG: 44 Atuwa na gama bahayar ta saki nishi. "Jammu Ina butar?" "Ki duba wani dogon abu a gefan masan Kamar tiyo, ki matsa shine ruwan zai fito. " Hakan kuwa akayi. Atuwa taja shi ta wanke. Hadi da sake cewa, "To akwai omo da Zan wanke hannun?" "Akwai sabulun matsowa a roba. Ki matsa ki wanke hannun ." Atuwa ta dashare baki. Yayinda ta matsa kan liquid soap din tana dauraye hannuwan nata..hade da kalle kanta a mudubi tana kallon gashinta daya sha gyaran kumfar los. Fucewa tayi daga bandakin.. "Alhamdulillah! Yasin bahayar gidan yan gayu ma daban take. Charanchas zakaji ka zazzage komai. Habawa" Ta karasa fada tana shafe cikinta. "Zo kici abincin Atuwa dan Allah." "Toh jammu . "Zaman dirshan Atuwa tayi a tsakiyar parlorn da aka shimfide musu ledar abinci. Abinci mai rai da lapia aka dafa musu. Su jimmamman da Rumalle sai yagar tsokar nama ake. Suna korawa da lemo. "Wai harda dabgen naman kai? Ga kaji ga kifi gashasshe ga abinci ga Kuma kayan shayi . Du mu kadai Jammu?" "Harda biredi mai yanka yanka sahibin naki. Gashi can a gefen Farillatu. " Ai kuwa da sauri Atuwa ta janyo shi. Ta hada shayi mai kauri tana dangwalar biredin da romon naman kai. Harda hawayen dadi tayi tana girgiza kai. "Abu yayi dadi Jammu . Hakika Allah ya dubi hakurin ki ya miki sakayya da mafificin alkhairi. Dubi kece acikin gidan nan kin ciyar damu abinci masu dadi na gidan manya. Wanda abaya bamuda hanyar da zamu ganshi inde ba a biki ba. " Atuwa ta karasa tana jan majina kafin ta cigaba da cewa, "Dan Allah Atuwa kibar hawaye kici abincin dan Allah. Dubi su Farillatu sai kallon ki sukeyi. " Atuwa ta girgiza kai. Hadi da gabtar naman ta lashe yatsunta. "Dan Allah Jammu kiyi hakuri ki yafemun duk abubuwan da na miki a baya. Dan Allah . Kyawawan halayen ki da hakurin ki shysa kika girbi farin ciki a karshe s.." "Ya isa Atuwa . Allah ya yafe mana baki daya. Ni ce zan baki hakuri domin ke yaya ce awaje na. Tunda agidan nazo na same ki. Uwa uba ba zeyiwu ace kullum kece da laifi ba. Nima da nawa. Don haka kibar cewa haka. Kowa da irin tasa kaddarar a rayuwa. Allah ya buda mana baki daya . Yasa mu dace Aamin. Allah kuma ya yafe mana baki daya Hansatuwa. Ci abincin dan Allah . Ki bar zancen nan " Nan da nan su Rumalle da jimmamman ma suka shigaa neman gafarar Jammu . Ita dai Dadaa murmushi kawai take. Ta kuma sake yi musu addua baki daya. Tare da neman gafarar su suma. "Kuyi hakuri. Duk wani fada akan Ardo don Allah ku rage shi. Ku zage ku nemi na kan ku. Kowacce cikin ku ta fara sana'a. Samu biyar goma da ashirin yafi zaman hayagaga da ake agidan nan. Shi kansa Ardo zaku tallafa masa. " Haka dai suka yita hirar su. Baby sudies ya tashi daga bacci harira ta kawo shi. Nan suka cigaba da hira sunata yaba kyawun sa. Ba jimawa yan biyu suka dawo daga makaranta. Nan sabuwar hira ta 'balle. Har wajen yamma kafin su mike zasu tafi . Dadaa ta dakko kudi dubu 20. Ta mika musu, "Gashi inji bappan su Sudeis. Sai ku dauki dubu biyar biyar. Biyar din kwa bawa yara ko ku baiwa Ardo. " Godia sosai suka shigaa yiwa Dadaa. Da kuma kanta ta rakasu sashen su Haj jiddah suka gaysa dasu. Domin tuni sun shirya tsakanin su suna zaman lumana . Addayo taja musu kunne kanta tafi. Kuma sun lura yanzu jammun tafisu fada awajen captain. Don haka tuni suka mikar da kai. Sun tabbatar cewa yawan boko da dimbin ilimi ba shike sa ka zama tuta awajen mai gidah ba. Ga Jammu nan da batada bokon sai arabi. Ta Kuma aure shi a matsayin bazawara mai yara uku. Ta kwace musu kambun mulkin su ta hanyar bin captain din cikin sau da kafa hadi da dogaro da addua. Daga sashen su Haj jiddah Dadaa tayi sallama dasu Atuwa . Ta Kuma saka yan biyu suyi musu rakiya zuwa wajen sashen Zaraah . Tuni daman ta tura mai aiki ta gaya mata. Maheer da tun dazu ya gama shryawa shida Zaraah . Suna zaune ya zaunar da ita akan cinyar sa. Yana karanta mata littafin sa da yayiwa laqabi da so da zuciya. Kalaman ciki wasu sun sata dariya wasu hawaye. "Jon wuro. Ka kyaleni, yanzu fa su mama Atuwa zasu shigo. " "Ni da zasu yadda da sun bari mu munje mun gaishe su idan mun karashe gwangwaje amarcinmu." Zaraah tayi dariya kawai tana kasa da idanu . Hade da matse yatsun ta da suka sha jan lalle. "Ina kaunar ki zaraateey. " Ya karasa fada hadi da sumbatar saman idanunta.. "Ba kice komai ba. Zarateey. Ina neman wata kalma wadda babu wanda ya santa. Ina neman wata kalma da zan furta miki cewa ?..ke ta daban ce, ke kyakkyawa ce, kin zarce sauran mata. Zuciya ta da taki ba za su tabaa rabuwa ba har abada. Ina son ki." Ya karasa fada yana sake sunbatar gefen kunnenta. Ya cigaba da cewa , "Zarateey . SO shi ne abun da ya dun ule ZUCIYoyinmu waje guda har muka tsinci kanmu a cikin soyayya, ina fatan ba za ki bari wani d aramin abu ya zo ya raba tsakaninmu ba? KO? Uhmm? Zarateey?" Nanma ya sake kaiwa wuyanta sumba yana shakar ni'imantaccen kamshin E-attractive khumrah din yerwa incense and more datayi amfani dashi. "Zarateey! Tamkar gishiri ce a cikin rayuwa ta, idan na rasa ki zan yi rayuwa ne da babu armashi a cikinta. Zarateey na. Da akwai wasu tarin tsintsaye da suke wuni suna tattauna batutuwa a kan irin matsayin da na baki a cikin zuciya ta. Zan so ki ji irin abun da suke cewa, domin kuwa a lokacin ne za ki tabbatar da irin son da nake yi miki. Zo in nuna miki inda suke, Ya bakya cewa komai ne" ya fada yana sakar mata iskar bakinsa acikin kunnenta. Hadi da yi mata tafiyar tsutsa a jikinta. "Ka bari.... Kaji?" Sam yaki cikata. Sai ma sake rikota da yayi sosai ajikin sa yana kai wa goshinta sumba. "Zarateey! Kece murmushi na, da akwai miliyoyin furanni a cikin lambun masoya a wannan duniya. Da a ce zan tsunko kowanne fure na baki shi a hannunki, hakan bai isa ya bayyanar da adadin yadda nake son ki ba. Ke ce murmushi na, kuma ke ce farin-ciki na. Zuciyata ta renu da soyayyar ki zarateey. " Zatayi magana kenan aka shigaa kwankwaso kofar sashen nasu. Da sauri ta mike daga cinyar sa. Maheer ya janyota yana mai gyara mata zip din bayan rigar. "Ni dai zan jiraki a daki. Zamuje mu gaishe su. Gaisuwa ta musanman har gidah. " Da sauri ya shige dakinsa yasaka key. Yayinda Zaraah taje tabudewa su Atuwa bayan ta gyara jikinta. Rungumesu tayi daya bayan daya. Su Atuwa nata yaba tsari da kyawun sashen na Zaraah. Domin har yafi na Jammu . Don captain shiya zuba komai na gidan
Chapter 53 · 0% Book details