Sashe 48
So Da Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
jiddah da Iklima. Maheer ya karasa parking ahankali. Kafin Zaraah tabude kofa ya bude mata. "Mama barkan ku da dawowa " Ya durkusa saitin su Haj jiddah dake rufe motar da mukulli. Da alamun unguwa suka futa atare su biyun. "Lapia." "Barkan ku da dawowa." Cewar Zaraah .tafada cikin girmamawa. KO kallo bata ishesu ba. Sukayi gaba abunsu. Maheer ya dan daga murya yadda zasu iya jiyowa. "Zo wifey .. Zaki iya tafiya ko na goye ki ? Hau banbu hau?" Ya karasa hade da durkusawa wai tahau bayan sa. Zaraah duk kunya ta isheta. Gashi tasan da biyu yayi. Suna wucewa ya girgiza kai kawai. Hade da jan hannun zaraahn suyi sashen su kai kace irin shirin nan suke yi. ***** Bangaren Addayo suka wuce. Haj ikhima da idanunta sun rufe har suka shige ciki bata dena mita ba, "Makirar uwarta ta koya Mata komai. Shima can daya sullutu kamar ubansa. Marar kunya. Wannan mutane samun su cikin rayuwar mu bamu ji. " Bata karasa fada ba. Haj jiddah tayi saurin rufe mata baki. Ganin tamkar shashasha Addayo na gaban su a tsaye fa awajen parlornta. Ammata keta shararar bayani. "Barka da yammaci Addayo.." "Barkan ku. Kun dawo kenan?" "Mun da ..wo" Haj ikhima tafada ararrabe. Gabaki daya ta dubibice saboda baranbaramar da bakinta yayi "Ku Shiga, Yana ciki shima dan birnin. " Shigewa sukayi cikin parlorn. Dadaa da shi kansa Capt din kowanne Yana parlorn. Baby sudeis yana shimfide a kafafun captain daya mikar dasu. Gaishe shi sukayi. Ya amsa kadaran kadahan. "Sannunku da zuwa. Barka da yammaci." Dadaa ta fada cikin ladabi. Basu tanka ba . Yayinda Addayo ke hamkalce da komai .ta karasa cikin parlorn ta zauna. Wayarta ta dakko ta mikawa captain "Rike ka kirawomin harisu kace suzo yanzu. " Gaban Haj jiddah da Iklima kowanne sai daya amsa ras. Ba jimawa kuwa da Kiran kawu harisun ssai gashi da wani malami biye dashi a baya. kusan Mai karatu yasan abunda ya faru da mahaifiyar sudeis Wanda shine silar ciwon da captain ya samu . Wanda sai daya dau tsawon lokaci kafin ya farfado. Ciwon daya haddasa masa dena tukin jirgi da yake. Addayo ce tashiga Fara magana cikin nutsuwa hankali da Kuma tsantsar dattako. Dadaa na gefe tana sauraro. Maganganun Addayo kusan akan zamantakewar gidan captain dince. Yanayin mugun halin su Haj jiddahda tuggun da suka shirya. Ta karkare da zaman halin ko'inkula da suke da mijin nasu. Aranar tafuto ta sanar dasu game da abubuwan da takeda masaniya ciki harda yadda suka tsara komai da faruwar hakan. Tana gamawa kawu harisu ya dora daga inda ta tsaya. Kafin Addayo ta sake cewa, "Badan na hana dan birni ba dake shidin me jin magana ne. Da wallahi tuni ya warware auren KU.. saboda albarkacin yaran dake tsakanin ku dashi nabashi hakuri nace ya gafarta muku yacigaba da Zama daku. Wannan ne Zama na karshe . Idan har wani Abu ya sake biyo baya malam me sheda wlh babu yawuna aciki. Na lamunce masa ya rabu da ku ." "Kiyi hakuri Addayo" "Ki gafarce mu Addayo". Haj ikhima da Jidda suka hada baki. "Malam kayi jan kunnen dan Allah" kawu barisu yace da dattijon malamin Yayinda yayi basmala ya Fara da cewar, HAKKOKIN MACE AKAN MIJINTA. 1. Ya biya sadakin ta. 2. Ya rike ta amana cikin girma da arziki, da kyautatawa. 3.Kar ya cutar da ita kuma kar ya bari yana sane a cutar da ita ko ya bu e wata hanyar da za'a cutar da ita ya zamo garkuwa gwargwado iko a gare ta. 4. kada ya jinkirta wani bukatan ta ko hakkin ta, ba tare da wani kwakkwaran dalili ba yaji tsoron ALLAH. 5. Ya dunga wasa da dariya da ita a gabadaya rayuwar su na aure, kamar yadda Annabi muhammad (S.A.W) yake yida matan sa, hakan na sabunta soyayya madauwamiya a zuciyoyin su da rashin gajiya da juna da marmarin juna. 6. Yayi hira da ita kamar yadda Annabi (S.A.W) yake zama da matayen sa, suyi hira kuma ya saurare su. 7. Ya karantar da ita ilmi na addini kuma ya kara karfafa mata gwuiwa akai, ko ya kaita ingantacciyar makarantar sunnah ta samu ilmi ya dunga tunatar da ita hakkin ALLAH a kanta taji tsoron ALLAH, da kuma gyara mu'amulolin ta. 8. Ya dunga lura da Kuskuren ta yana mata gyara cikin so da qauna cikin rarrashi har ta gane, ya kuma dunga yabon ta in tayi abu daidai na kyautata wa idan da hali yayi mata kyauta ma akai iya karfin sa. 9. In tayi Kuskure da ya sabawa addini ya nuna mata tayi Kuskure, kuma ya taya ta da addu'a sa'annan yayi mata nasiha. 10. Kar ya zamo mai cutar da ita ta hanyar duka ko ya mari ta ko zagi. 11. Kar ya zamo mara sirri yana tona mata asiri ya zamo duk abunda sukayi a rayuwar auren su yaje yana fadawa mutane a waje, wannan haramun ne ba siffa ce ta miji na gari ba. 12. Yabi duk sare saren musulunci yadda musulunci ya nuna a kyautata wa mace ya kuma dunga sauke mata hakkin ta gwargwadon iko. 13. Ya zamo taimaka mata ko Yan uwanta a duk Lokacin da take bukatar taimako gwargwadon iko, kuma ya rike ta amana. 14. Ya zamo mai girmama iyayen ta, ya kuma nuna mata kulawa. 15. Ya siya mata duk wani kaya mai kyau na sutura ko na gyaran jiki ko kwalliya wanda za ta dunga masa kwalliya a cikin gida. 16. Ya zamo Mai kishin ta, domin ma ai wajibi ne ya zamo miji yana kishin matarsa da nuna Soyayya a gare ta. 17. Ya zamo mai ciyar da ita halal, yafita ya nemo musu abunda zasu ci halal kuma ya tsare musu mutuncin su. 18. Idan yayi mata laifi ya zamo Mai neman ta gafarta masa. 19. Ya dunga sanya mata farin ciki, har ya zamo fara jin ba wanda ya fita dacen miji nagari. 20. Ya dunga tayar da ita suna wasu ayyukan ibada tare, inda sarari suci abinci tare suyi hira suyi dariya tamkar mata da miji tamkar saurayi da Budurwar sa tamkar yaya da qanwa su zama tamkar aliba da malamin ta. 21. Ya zamo Mai tausaya mata da nuna mata lallai ita macece kyakkyawa yar amana mai mutunci yar gidan mutunci mai cikakkiyar ni'ima kuma sarauniya abun girmama wa. *HAKKOKIN MIJI AKAN MATARSA* 1). HAKKIN BIYAYYA GA MIJI. Wananna shine hakki mafi girma akan mace, wajibine tabi umarnin sa ko bata so ta kaucewa halinsa ko tanaso aikata abunda ya hanata. Wato yi nayi bari na Bari, amma fa biyayya tanada sharadi shine bazati bi Shiba, inya umurceta ta aikata abunda Allah ya hana. Koya umurceta ta bar abunda Allah ya wajabta. Sannan kuma ta kasance tanada ikon aikata abin da yayi mata umarnin. Anan yakamata miji ya kasance mai tausasawa da hikima da bi sannu wajen bada umarni da hani. 2) Ta zauna a gida ta kula da gidan da tarbiyar ya'yanta, kada ki fita ko ina saida izinin mijinki. 3) Duk lokacin daya bukaceki ki amsa kiranshi, cikin sakin fuska, ki biya masa bukatarsa gwargwadon yanda zaki iya Saidai in baki lafiya ko Bakida tsarki, to saiki bashi hakuri, cikin tausasa kalamai, tareda sanyayamai zuciya. Kokuma in rashin tsarkine uzurinki to saiki sakarmai jikinki kuyi wasanni kala- kala har bukatarsa tabiya. Ki kuma yimasa alkawarin farantamai, dayin shagali da zarar kin tsarkaka. Dayawan mata sunayin kuskure, yayin da mijinta ya nemeta bata cikin tsarki, sukan bar mazan nasu cikin damuwa, da kewa har zuwa lokacin da zata tsarkaka. Yake yar'uwata akwai hanyoyi da dama wa inda Zakiba wajen biyama mijinki bukatarsa batareda yashiga damuwaba, ko kin sanyashi cikin kewa rashin ki. Akwai hanyoyi da dama wa inda zakibi wajen biyama mijinki bukatarsa........... 4) Kada ki yarda wani ya shiga gidansa saida izininsa, Koda kuwa yan'uwansa ne ko yan'uwanki. Musamman cikin dakinsa ko kujerarsa, ko shinfidarsa. 5) kada kiyi azumin nafila yana gari saida izininsa. 6) Kada kiyi kyauta da kayansa saida izininsa, Amma Babu laifi ki baiwa bakinsa ko naki abunci, ko kibaiwa mabukaci amma batareda Kinyi almubazzaranci da mugunta ba. 7) ki kula da aikace-aikace gida da kula da yara, kamar tsaftace gida, girki akan lokaci, wanke wanke da shara, da hidimomin shi kanshi mijin. Lallai ne yar'uwata ki hakuri tareda juriya wajen wadannan hidimomin masu yawa da nauyi, Kisani cewa ba aikin banza kike yiba, ibada ce babba. Kai kuma miji karunga taimaka mata, a lokacin da kake gida karkace zaka barta da aiki ita daya, inka tai maka mata Zataji dadi Hakan na kara soyayya da shakuwa tsakanin ku. 8) Wajibi ne ki kare kanki Babu ruwanki da kowa, sai mijinki Koda kannan miji kada ki saki jiki dasu. Ki tsare masa dukiyarsa, tareda tattala masa. Ki kula da ya'yansa Koda kuwa bake kika haifesu ba, kirki cutar dasu. Kisani inhar kika cutar dasu Allah zai musu sakaiya kuma soyayyar ki zata ragu wajen mahaifinsu. 9) Ki kasance me godiya ga mijinki, mai yada alkhairin sa da yabonsa. kama me boye shirrin mijinki da naki, kisani ciki badan tuwo kawai aka yi Shiba. Kiyi zama da mijinki zamana amana da rufama juna asiri. 10) Yar'uwata ki kula da jikinki ki runga caba kwalliya irin wacce yake so. Kirunga yi mishi shiga irinta garari, wadda zataja hankalinshi zuwa gareki. Ki yawaita yi mishi murmushi da rausaya murya, tare da da dadan kalamai na soyayya. A yayin da kike tare da mijinki Kirunga sarrafa jikinki tayanda zaki ja hankali shi zuwa gareki. Ki dage ki cire kunya, kisani tsakanin miji da matarsa babu kunya. Dan haka ki cire kunya ki tattali mijinki, kibashi kulawa. Ki natsu a lokacin da kuke tare Kirunga aika mishi da wasu zafafan kalamai, tareda soyayya me rikitarwa, wadda zata matar dashi kawace mace a yayin da ku ke tare. Yar'uwata kisani basaikin bi boka ba, balle wani malamin tsubbu, dan ki mallaki mijinki Kirunga kaima wani kato kudinki yana cin kaji, yaci Abun dadi, ki kasa zaman lafiya ,ki baki ciba wani kato yaci miki. Yake yar'uwata, kisani kyautata da biyayya, da tattali da nuna soyayya, da kulawa, Da rukon Amana da gaskiya, sukadai sun isa idan kika ruke zaki mallaki mijinki. Kidage ki koyi