Sashe 52
So Da Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mata, " A tsananin so da kaunar ki bayan da kika samu nasarar sace zuciyata. Wannan zuciyar da ta kasance mallakina, ina mai farin cikin na mallaka miki ita a matsayin wata kyauta ta musamman. Na zama mallakin ki. Ki kasance mai ririta soyayyar mu kamar yadda na kasance. Na baki amanar kaina ki amince mu damke amanar juna. Kinji Batoul dina?" Kasa magana tayi. Kalaman sa na matukar zagaye mata dukkanin jikinta. Jin sa take cikin zuciyar ta. Ta rasa ya akai hakan ta faru lokaci daya. "Baki ce komai ba!!! Batoul ... Uhm? Kinyi shiru. " Hannunta tasa ta rufe fuskar ta. Cike da jin kunyar sa . Yanayin tafiyar tsutsar da yake mata ne yasata ture shi ahankali. "Ka bari Dan Allah. " "Wai ka bari. Shikenan ni banda wani suna? Na gaya miki bana wani son yaya ehe. " "Allah kai yayana ne" "Ki dena cewa Allah. Muna kwance gado daya. Manne da juna . A canzamun gaskia. " "Jon wuro.... " "Jon wuro as in meke nan?" "Yana nufin mai gidah da fulatanci." "Na amince. Amman dai nan gaba zaki sauya wani dole " Lakuce Mata kumatunta yayi. Ya mata kyakkyawan masauki a kirjin sa. Yana shafa jikinta. Hade da sumbatir gashin kanta Wanda ke tashin scented hair spray na yerwa incense and more. "Nasan zaki mamaki.... Lokaci daya na fito na nuna miki ina son ki. Bazan karya ba Zaraah . Tun ranar da Allah ya qaddara aurena dake na tabbatar hakanne mafificin alkhairi. Na tsinci kaina cikin matsanancin kishin ki. Ashe soyayyar ki ce keta taruwa acikin zuciyatah . Don haka ba wani cigaba da dogon turanci da zanyi domin da har na fara rubuta miki labarin zuciata a dan wani littafi danai masa laqabi da SO DA ZUCIYA!! Wanda Zan danka miki shi yanzu kuwa don ki tabbatar. " "SO DA ZUCIYA Kuma? " "Eh mana SO na DA ZUCIYAr ki ne suka hadu waje guda zasu fara gudanar da ginin tsanin soyayyar su. Zaraah na ki amince mu gina rayuwar mu cikin aminci da kaunar juna . I promise to be an excellent lover, best friend and favorite life partner . Ki amince mu gina rayuwar auren mu tamkar yadda iyayen mu ke fata. Ni Kuma nake muradin buri. Ki amince mu tabbatar mu Kuma wanzar da A LOVE SOO BEAUTIFUL!! Zaraah I love you pass my mind beyond my soul. Ina kaunar ki. Kauna marar algus. Kauna marar gushewa da izinin Allah.. Kin amince ? Kin amince? Umm? Zaraateey? Say something please. " Fashewa Zaraah tayi da kuka. Ita din gaban banza zataki amincewa da soyayyar sa? Mutum Mai tarin ilimi, dattako da sanin yakamata. Gashi dan manya mai jini a jika. Maheer ya mike da sauri ya kamota yana kallon idanunta "Kuka Zaraateey? Bar kuka please. Nayi shiru. Bazan k ...." "kai ne masoyina na hakika tunda har ZUCIYOYIN mu sun aminta da juna. Ina son ka kaima kana sona ina yi maka albishir din ka samu makullin bude daular zuciyata, ina kuma fatan zaka kara shiri domin fantsama a cikin kogin soyayya mai dadi. Ina yi maka fatan samun nasara a dukkan al muran ka, Na amince Jon wuro. Na mallaka maka ZUCIYATA, na kuma amshi SOYAYYAR ka da hannu dubu. Tabbas SO DA ZUCIYoyinmu sun qulla am inta mai dorewa ta har gaban abadan..." Maheer bai jira tasake cewa komai ba. Ya rungumeta tsam a jikin sa. Dukkanin su suka shigaa zubar da hawaye. Kafin Maheer yai nasarar hade bakunan su waje daya. Suna hawaye suna nuna bajintar kaunar sumba mai ratsa jiki da bargo. Kowanne yana nunawa dan uwansa yafi shi son sa. Daganan suka sake tsunduma wajen bude wata fagen soyayyar. Mai gardi da bada kala. Alkalami yayi kadan wajen zayyano maku yadda masoyan suke gurzar soyayya tamkar cin kwan makauniya. I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ci3ao6233sn3&utm_content=6k8ur6p *WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_* *ZAFAFANKU BIYAR sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA* *_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_* *GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA WARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi* *JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE* *_DEEN MARSHALL Mamuhghee_* *_HALIN GIRMA hafsat rano_* *_TAKUN SA billyn abdul_* *_SO DA ZUCIYA miss xoxo_* ABI'AR ZUCIYA huguma_* *DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN AI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL* 1000 *Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin* 6019473875 MUSAA ABDULLAHI SAFIYA keystone bank Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 08184017082 *IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU* 09134848107 _*HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_* #team zafafa biyar . ___________ 2/25/22, 18:16 - Buhainat: I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ynog1zhfit0q&utm_content=6k8ur6p PLS FOLLOW US ON IG JAZAKUM ALLAH KHAIRAN AS YOU DO SO DA ZUCIYA!! ZAFAFA 5 PAID BOOKS PG: 43 Ardo na cikin baccin sa daddada. Mai hade da mafarkin yayi kudi ya auro mata yan nijar kyawawa. Sun haifa masa yara maza yan dagwai dagwai. Ya kuma zama hamshakin malami. Gashi nan dik inda ya zaga ana kiransa da gwani Ardo borkindo. Lallausan jikakken abu yaji acikin kunnen sa. A mafarkin kuwa gani yake wai dan da aka haifa masa ne yake wasa. Ashe wata kandararriyar akuya ceta makota da yunwa taci tacinye ta. Itace kunnen Ardo mai rufe da rigar yar sharar sa koriya da alama kama da ganye tai mata kama Jikake lubus. Ta laso kunnen Ardo . Da sauri Ardo ya mike. Gumi sharkaf ya kamashi. Dama a dakin marigayi Modibbo yake kwance ya dan saye kofar dakin. Ta haka akuyar ta shiga. "Wayyo Allah na. Wannan algungumar akuya matsiyaciya . Allah ya kwashe miki albarka. Dan tsabar reni. Saboda kowa da komai ya renani. Ace kina dabba ki kere duk ciyawoyin lungunan. Ki rasa inda zakije sai ki shigo mun makwanci ki gwaigwayi kunne na. Dan kan uban uwar ki? Wannan tsinanniyar akuya daga gani ta gidan lantai ce itace ke sasakar dabbobi suna abunda sukaga dama. Ina mafarkina mai dadi. Wannan tinkiya wannan tinkiya Allah ya kwashe miki albarka." Ardo ya karasa yana kokarin riko akuyar tayi waje da gudu tana kukan "Mb'eee, B'eee " "Allah ya kwashe miki albarka. Zakici gidan ku.". Ya kwasa aguje yai Kan akuya saiga Ardo zube a kwata yafada. Dai dai lokacin da Atuwa tafito sanye cikin atamfar ta da mayafi data sayo a kasuwar tsaye. (Kuncen kaya da ake sayarwa. Wanda Allah ya horewa niimar kaya. Dan Allah ya dinga bada tsofi ga mabukata ko gidan marayu. Akwai dubunnai dake neman kayan tsummokaran da zasu saka ajikin su. Wanda kai Kuma awajenka gani kake tsummane na goge goge. ) Sai dadura gyatuma radau din jambakin ta take a labbanta. Tanata sauri . Taja ta tsaya ganin Ardo face face da kwata "Ardo uban iyali. Kwal landantsan. Allah me alheri. Ardodo yanaganka a kwata? KO kifi kake nema mana? Sahibin raina. Dan Allah ban..." "Idan Kika karasa Atuwa na rantse da malafar kan uban borkindo sai na chasa ki. Banda wulakanci irin na yan lungun nan ace kamar ni Ardo akuya tazo tana sudar kunnena s" Bai karasa ba Atuwa taja guda ta saki tana dariya . "Allah me alheri. Yau ana kwal landantsan. Ardo uban iyali ne a kwata charanchas haka? Ina a" "Atuwa Allah ya kwashe m" "Karka karasa Ardodo yau a farin ciki nake . Don haka bazan bata lokaci na ba gidan lantai z. " "Lantai dai matar balalle?" "Eh ita" Cewar Atuwa tafada tana kallon kanta a mudubin fashashshiyar yar hodar dake hannun ta . Sai dashare hakoran take tana jujjuya fuskarta gefe da gefe. "Wabillahil lazi kikaje gidan nan na shika ki?" "Shika wane iri Ardo? Dan duwala zan sayo na shafa kayan nan sai warin ruma suke. " "Nide na gayan ki. Don narantse da Allah idan na sake saka akuyar nan a idanu na sai na Mata dukan kawo wuka. Kana ganin akuyar nan kuranin Allah kasan son abun duniya ne da ita irin na uwar dakinta Lantai. Na hada su dika na kwashe musu albarka" Harara ta watsa masa hade da yamutsa fuska. Cikin gatsine gatsine hade da buga tsakiyar zaninta tace. "Bari naje gidan mai unguwa . Uwalliya na sayar wa." Tayi gaba tana watsa hannu sama. Da alama dai kwashewa Ardo albarka take. Yayinda ya shige gida bayan ya leka yaga ta dau hanyar gidan mai unguwa. Kaya ya sauya Kai tsaye ya wuce shagon Muhsina mai kayan kwalam da makulashe. "Muhsinsin,,," "Na'am Ardodo. Cincin din zaa baka ko sifuringiroyis (spring rolls) ko samusa (samosa)? Akwai mitifayif (meatpie) " "Ban cincin din da mitifayi na wazobia shima sai zobo." Ta dakko ta mika masa ta taga. Hadi da cigaba da tuyar awararta akan dan risho. Ardo ya samu waje ya zauna ya shiga ci yana korawa da zobon. Atuwa taje ta dawo tanata zabga sauri. Daga bakin kofa ta tsaya tana kwalawa su Rumalle Kira "Dan Allah kuzo mu tafi." Ta fada tana goye Farillatu data fito itama an shirya ta . Fitowar sukayi kowanne da dan kayansa gwanin sha'awa. Suka nufi titi kai tsaye. "Tsaya Dan sahu" "Ina zan kai ku?" "Nasarawa." "Nasarawa ina? Sashen hotoro ko su lamido kiristen ? KO kofar nasarawa" Atuwa tayi shiru tana kallon sa. Shima kallonta yake yana jiran amsa "Haka dai da maka makan gidaje. Amman dai unguwar sharbebiya ce da gidaje masu kyawu harda famfu .." "Basai kin karasa ba. Ina kike nufi wai?" "Kai mu nasarawa kai dai." "Nawa zaku biya" "Dari hudu." "Gaskia bazanje ba idan ba zaku bada dubu daya ba. " "Dubu dannan? Ina mukai maka kalar dubu?" "Zamu baka dari bibiyu." Cewar Rumalle hade da zaro tata ta bayar. Jimmmamman ma ta bata tata yan goma da ashirin. Atuwa ta dakko tata acikin bra yan dari guda 2 ta bayar. Dan adaidaita ya kwashe su sukayi gaba. Sai zagaye suke. Sai da dan