← Book details So Da Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 55

Sashe 43

So Da Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dauka wawa gara irin ka. Kayi haihuwa tayi 10 amma gaba daya bakada hankali. Hankalin ka daya ne wajen neman aure kawai. Gaba daya bakasan falalar haihuwar 'ya'ya mata ba. Toh ka saurara kaji: "Bincike ta bangaren tarihi da zamantakewa duk sun tabbatar da cewar 'ya'ya mata sunfi 'ya'ya maza tausayin iyaye da yin biyayya garesu. Zaka iya tarar da mutum ya haifi 'ya'ya maza guda biyar ko sama da haka duk sun girma amma abin da zai ci ma ya gagareshi saboda duk cikinsu babu mai tsayawa ya kula da rayuwarsa bayan tsufansa. Amma duk wanda ya haifi 'ya'ya mata koda kwaya biyu ne sai kaga sun taimakeshi, sun tallafi rayuwarsa komai tsananin talaucin da suke ciki. Haihuwar 'ya'ya mata babbar falala ce daga Allah wacce ke samar da farin ciki anan duniya, sannan ga babban sakamako a lahira kamar yadda hadisai da yawa suka tabbatar. Misali yazo acikin hadisi cewa Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yace "Duk wanda aka bashi 'ya'ya mata guda biyu ya kula dasu kuma ya tarbiyyantar dasu, to sune suturarsa (wato zasu kareshi) daga shiga wuta" Koda Manzon Allah (saww) zamu ga cewa acikin jumlar "ya'yan da Allah ya bashi, matan sunfi yawa. Kuma zuriyarsa ma ta hanyar yarsa mace suka wanzu. "Ya mace rahama ce, jin qai ce, baiwa ce, daukaka ce, mutunci ce, hutu ce, farin ciki ce, albarka ce, falala ce, kuma alfarma ce. Kuma hadisi ya tabbatar mana da cewa: matsayinta na 'ya ('diya) tana samar wa mahaifanta dalilin shiga aljannah. - Amatsayinta na uwa, tana samar wa 'ya'yanta Qofar shiga Aljannah. ? Amatsayinta na 'yar uwa tana samar wa 'dan uwanta hanyar shiga Aljannah. - Mace ce ta fara gaskata Annabi Muhammad (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) alokacin da Allah ya aikoshi. Nana Khadijah. - Mace ce ta fara samun darajar yin shahada (rasa rai ta dalikin kare addini). - Sayyidah Sumayyah. - Ta dalilin mace ne al'ummar Musulmai muka samu falalar yin taimama idan larura ta kamamu. - Nana A'ishah. ? Mace ce ta samu darajar samun sakon gaisuwa daga Allah (SWT) - Nana Khadijah. - Mace ce tayi jinyar Annabi (saww) a karshen rayuwarsa ta nan duniya, kuma a hannunta ya koma ga Allah. - Nana A'ishah. - Mace ce ta haifi Shugabannin samarin Aljannah, kuma ita ta tarbiyyantar das - Nana Fatimah. Wani Alkali yace "Acikin shekaru ashirin da biyar (25) da nayi ina alkalanci, ba'a ta'ba kawo min shari'ar 'ya mace wacce ta bijire wa mahaifinta ba. Amma nasha gain 'ya'ya matan dake barowa gidan aurensu domin suyi jinyar mahaifansu" Nagode wa Allah, yanzu haka ina da: A'ishah, Aminah, Fatima Mukarramah, Fatimah Munawwarah, da Ramlat. Fatana Allah ya rayasu, ya kula min da sha'aninsu ya tsaresu daga dukkan abun Qi, tare da dukkan 'ya'yan musulmai baki daya. Ameen. DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (10/06/1441) "ka ji manazarta suka ce. Saboda haka ka zauna Kayi tunani. Domin arzikin da kake matukar son samu a 'yayaa mazan ta iya yiwuwa ajikin 'yaya matan zaka samu ninkin fiye da yadda kake muradin so. Toh Allah ya zabi abunda yafi alheri. Yasa abunda hukuma ko ince shari'ah zata zartar ya zama shine mafificin alkhairi. Gobe da yardar Allah sai muje muji yadda zasu yanke komi. Ni bari na tashi zanje ta'aziyya can kasan mil tara." Ardo ya mike yabi bayan Mai unguwa. Ya rakashi har kofar gidah. Mai unguwar ya sake bashi shawara hade da neman fatan alkhairi abisa abinda zai wakana a kotu. Ardo ya gangara can karshen layi ya takure. Gaba daya ya rasa meke masa dadi a duniya. SOn ZUCIYA ta kai shi ta baro shi. Bayan sallar ishai. Haj Mari . Da hajia Amina sune suka yiwa Zaraah rakiyar kai amarya. Zuwa sashen su itada Maheer. Dake can karshen gidan an sake kawata shi. Bayan sun kaita ta gaggaysa dasu Haj Jidda da Iklima da suke a matsayin mahaifan sa Mata. Dukkan su suka kasa boye hassadar su. Kuka kam Zaraah ta shashi kamar Wadda zaa dauke daga garin.. Sun kaita dakinta tare da sake bata shawarwari akan sabuwar rayuwar data shigaa na makarantar aure. Sun jima suna ja mata kunne. Kafin su mata sallama su tafi. Maheer dake cikin mota tun dazu. Sai a sannan ya futo ya rufe motar. Hannunsa dauke da ledoji. Ya Sha ado cikin manyan kaya kalar sararin samaniya. Ya mjrza hula zanna bukar.. yanata tashin kamshin baccarat rouge. Ya jefa mint flavored gum a bakin sa. Yana taunawa ahankali . Ya bude kofar ya sshiga ciki. Bakinsa dauke da sallama. Tafiya yake cikin takun kasaita. Ado da kamshi sun dabaibaye ilahirin gidan dake turare da turaren wutar yerwa incense and more.. Ya bude hanci ya shaki kamshin yana lumshe idanu . A haka ya karasa dakin Zaraah . Tana lullube cikin laffaya. Sai kamshi ke tashi hade da shesshekar kuka. Ya karasa ciki yana sallama a hankali cikin wata iriyar murya mai tattare da nutsuwa da cikar Kamala . Ajiye ledojin yayi a bedside drawer ya karasa kusa da ita. Taja can gefe tana kara sautin kukanta sosai. Maheer ya samu kansa da janyota jikin sa. Wata nutsuwa ta rufe su a take. Duk shure shuren da take Maheer yaki cikata. Ahankali cikin muryar lallashi ya shjga rad'a mata a kunnenta, "Haba Zaraah . Sarauniyar mata. Kukan ya isa dan Allah. Saurare ni da kyau kiji,.Ni fa yayan ki ne. Kuma nanda lokaci kalilan zan roki su Bappah su warware auren mu tunda ba ma son....juna KO ?" Ya karashe ahankali yana danne dariyar dake son fashewa. Zaraah tasamu kanta da daga kai. Yasaka hannun sa daya yana shafa bayanta alamar rarrashi. "Yauwa Zaraah.. Ko kefa? Yanzu dai bari na gaya miki abunda nakeso da wanda banaso ko?" Ta daga kai. Tayi luf tana shakar kamshin sa. Munafuka Ahankali cikin wani salo da kwarewa. Maheer ya tsinci kansa da fadawa Zaraah abubuwan da yakeso da Wanda bayaso ..ya karkare da, "Inada wani cuta...Ana ce dashi sleepwalking a turance. Yauwa saboda kakkiga wataa rana nazo dakin ki na kwanta cikin dare. KO na Miki na wani abun daban .Ba a hayyaci na nake ba. " Ya karasa fada cikin muryar umarni Kai kace gaske ne. "Zaraah! Kinji ko?" "Na ji. " "Yauwa. Kuma ta yadda su Bappah zasu yarda a raba aurenmu shine idan sukaga muna kyautawa junan mu. Bama nuna kiyayya da sauran su..zakiga lokaci daya da mun same su da maganar zasu amince. Kin gane ko?" Ta sake daga kai tamkar gaula.. Maheer ya saki murmushi kafin ya sake cewa, "Zamu cigaba da karasa karatun ki na islamiyya a gidah. Kafin ki koma makarantar bayan wani dan lokaci . Kinji ko?" "Eh" "Yauwa yar kanwata Zaraah. Allahumma Bareek!!" Ya karasa fada hade da samun kansa da sakarwa Zaraah zazzafar sumba a goshinta. Ya tabbatar wa kansa a yan kwanakin nan yafara jin wani abu game da Zaraah . Ta janye jikinta da sauri. Murmushi ya yi ..kafin ya janyo ledojin ya bubbude su, "Gashi kamar yadda al'ada ta tanadar. Kici ki koshi Yar kanwata . Bari Yayan naki ya tafi dakin sa. Sai da safe ko?" Ta samu kanta da girgiza kai da sauri. Maheer ya fuce yana murmushi. Ita kuwa dama kamshin kazar ya mata dadi. Nan danan ta wanko hannu a bandaki tayi bisimilla tana ci tana korawa da yogoberry. Ta nannade sauran ta ajiye .Ta yo wanka ta zura kayan bacci ta haye gado bayan tayi alwala. Ta tottofe jikinta da addu'oi tayi kwanciyarta. Cikin bacci tafara jiyo kyakkyawar rungumar da akayi mata. Tamkar wani zai kwace ta. Da sauri ta yunkura ta janyo wayarta ta kunna fitila .wa zata gani in ba Maheer ba Har zata tashe shi sai ta tuna maganar da yace mata akan cutar sleepwalking da yakeda ita. Dake batada man Kai saita koma ta kwanta. Dama abunda Maheer keso kenan. Ya sake kankame ta. Bayan kallo daya zakayiwa fuskar sa kasan shirya zancen sa yayi da sani. Asubah ta gari. SO DA ZUCIYA dake Shirin Zama abu daya Unedited 2/12/22, 11:37 - Buhainat: *Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107* I'm on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb *SO DA ZUCIYA* *NANA HAFSATU* *35* Maheer na ganin ta kwanta bayan ta kashe fitilar. Ya samu zuciyar sa da jin dadi da kuma nutsuwa. Ya sake rungumota sosai. Tamkar za'a kwace masa ita. Zaraah gaba daya ba yadda zata yi ne. Don bil haqqi gani take ciwon sleepwalking din nasa ne ya tashi. Don haka ta daure kawai ta koma ta kwanta tana runtse idanu. Ya sake rungumota yana shakar kamshin gashin kanta. "Alhamdulillah Ala Ni'imatul Islaam" ya furta kasan makoshi yana jan numfashi. Zaraah daketa tunanin yadda zata zame daga jikin sa. Tashiga tutture hannuwan sa. Maheer ya hanata ta hanyar janyo bargo ya rufe su baki daya. Ganin karatun na neman canza salo yasa Zaraah zare hannunsa da karfi. Hakan yasa Maheer ya yaye bargon ya mike kamar wani roba roba ya fuce daga dakin. Zaraah ta koma tabi lapiar gado ta kwanta. Tana sake tabbatarwa cikin zuciyarta lalle yanada ciwon sleepwalking din daya ce. Shi kuwa Maheer koda ya koma dakin sa. Samun kansa yayi da sakin lallausan murmishi. Bai koma bacci ba. Bandaki ya shige ya dauro alwala ya tada sallar nafila. Ya jima a sujjada Yana kwararawa Allah godia a bisa auren da yayi. Da Kuma samun albarka acikin auren nasu hade da adduar neman zaman lapia da samun yara masu albarka. WASHE-GARI Zaraah ta jima tana bacci bayan sallar asubah da tayi ta koma. Koda ta farka ta Yi matukar mamakin ganin yadda rana ta dallare dakin. Alamun gari ya waye. Da sauri ta mike tashige bandaki. Wanka tayo ta tsaya cikin bandakin tana yin turaren jiki dana lalle na dukkan na yerwa incense and more . Sai data kammala tsaf tukun sannan ta koma cikin daki. Ta shirya cikin wata riga da zani na atamfar Ghana mai launin ja da baki. Batayi wata kwalliya ba . Tadai shafa man baki da kwalli. Ta dakko katon hijabi ta saka Parlorn ta bude kofa ta leka. Caraf ta hango Maheer. Ya zauna akan kujera yana daddanna
Chapter 43 · 0% Book details