← Book details So Da Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 55

Sashe 42

So Da Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gumi yana dalawa Atuwa harara, "Matsiyaciya. Idan ubanki ne ya sai gidan sai ki sani na fita. Allah ya kwashe miki" "Ya kwashe maka albarka dai. Ba kai aure aure ba. Ana zugaka kana dashare fuska. To ka aurowa kanka. Gida ya badu. Sai a rankaya a koma kauye. Don kuwa ni gaba nayi. Jammu Allah ya dasa mata kwandon arziki tayi aurenta na arziki . Shar da su itada yaranta. " "Banason wasa Rumalle. Na shika ki sau daya. Kar ki tunzuro na Kara wani shikan akan wani." "Kara 100 ma. Gida ya zama nawa. Daren farkon mu ka gayamun naje dakin Modibbo na dakko acikin jaka." "Banda haukan ki a ina ake kyautar gidah sukutum?" Kafin Rumalle tayi magana. Atuwa ta dire tsallen albarka hade da daga hannu sama ta kwakwaso rantsuwa kai kace ita aka bawa gidan. Ta nanawa cinyar ta duka. Hadi da rangada guda. Ta sauke aiyiriri a kunnen Ardo. Hade da cewa " A hayye landantsan tsan. Allah mai alheri. Wabillahil Rumalle taci gidah. Kyauta ta badu. Ba Kai zamudin.aure ba. Daren farko ka yiwa amaryar ma kyautar gidan ka jallin jal da Allah ya baka. Hau ta hau Arddo. Mijin Atuwa sahibin jimmamman. Ubansu Zaraah angon Rumalle mai gidah. Kayya kaiiiiiiiiiii" Masu tambaya. Duk books Dina Banda paid suna wattpad: missxoxo00 Instagram: @yerwaincense_and_more XOXOWRITES 2/12/22, 11:37 - Buhainat: *Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107* I'm on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb *SO DA ZUCIYA* *NANA HAFSATU* *34* Ardo takaicin Atuwa da ke zakalkalewa yasa shi jan dogon tsaki. Hade da kutuntumo ashariya ya 'dure akan Atuwa. "Bak'ar munafuka. Allah ya kwashe miki albarka Atuwa." Atuwa ta sheke da dariya. Kafin ta rangada guda ta saki. Jimmamman na daga tagar wundo tana leken su. "Ba kai uban aure ba. Kana yiwa Allah shisshigi kan haihuwa. Bakayi maraba da yara matan da kake dasu ba. Ka dau kaunar son yaya maza tamkar su din martabar su daban ce. 'Dayan da Allah ya albarka nce ka dashi ka dau son duniya ka dora masa. Ka tsani sauran yaranka mata. Har fada kake a baya kan cewar idan Modibbo ya tashi aure zaka dau gidan nan ka bashi. Mu kuma mu koma kauye ko ka shika mu. Toh gashi nan yanzu hau ta hau kan k..." "Idan kika kuskura kika karasa magana. Wabillahil sai na hau kan ki da bugu. Munafuka. Yauwa ke kuma Rumalle tsaf zan kai karar ki kotu akan wannan iskar zancen. Mahaukacin ina ne ni da zan dauki kadarata daya a duniya na baki? Ni ba sakarai bane." Rumalle ta tabe baki. Hade da zaro rake cikin kullin gyalenta tashiga gabtara kada kai. "Ni ba irin ka ba ce Ardo. Zan iya maka afuwar shikan da ka mun na kyaleka ka cigaba da zaman matan ka har nan da sati biyu kafin ka nemi wani muhallin ku kara gaba." Ardo cikeda takaicin yadda Rumalle ke magana cikin gadara da isa. Ya zare raken hannunta ya take shi a kasan takalmin sa yana huci. Hade da kokawar zare rigar yar sharar dake jikin sa. Jimmamman ta sheko a guje ganin zai yi tabargaza agaban yaran sa. "Cika ni jimmamman. Kyale ni na chasa tah. Har ni zata kawo wa zancen banza. Agidan uwar ubanta na bata gidah?".Ardo ya shiga kokarin zare hannuwan jimmamman dake rike hannayansa. Bayan a zahiri idan an barshi da Rumalle kadai sai ta hallaka shi. "Cika shi . Kafin na hade da ke na zaune. Agidan uwar ubanka borkindo dake Fanda ka ke. Banda tarin tsiya da abun kunya me ahalin ku ke da shi? Kaf banda ciki da waje dangin ku ne matsiyata. Wanda shanu hudu gare ku duk yawan ku. Wallahi banda kaddara meyasa zan aure ka Ardo?.wallahi ni ba sa'ar auren ka bace. Gidah Kuma ko ana ha maza ha mata sittin ta ubangiji ya zama nawa." "Jar uban can kai. A hayye landantsan. Allah mai alheri. Yau ana wata ga wata. J" Kasan gwiwar hannun sa Ardo ya sa kai wa Atuwa bugu a makoshi. Ta rike wuyanta tana kurma ihun zafi. "Wato ga mareniyar wayon ka ko? Shine daga magana saboda ita tafi karfin ka daketa. Sai ni mareniyar wayon ka. Burbudin kashin duwaiwukan ka ko! Toh wallahi ban yafewa. Kuma Allah ya kwashe maka albarka. " Atuwa ta karasa fada tana mulma wuyan ta da Ardo ya kai mata bugu. Rumalle ta mike daga zaman da tayi. Ta dau buta tayi hanyar bandaki tana yan wak'e wak'e. Tashige bandaki ba addua ba komai. Ta kwaye mazaunai tashiga kasayarwa tana waka. " A hayye sama ruwa kasa kudi. A hayye sama kudi kasa ruwa. Wahabu wahidin lillahi. Sama ruwa kasa kudi. Katsina ta dikko ma ana maka ruwa. Sama kudi kasa ruwa. Kaduna ma ana maka r......" Bata karasa wake waken data ke aciki ba. Ardo ya shigaa cikin bandakin ya janyota ..ko tsarki batayi ba... Domin wakar da take raira baitin ta ta karasa harzuka shi. "Ba sama ruwa kasa kudi ba. Wallahi yau zakisan ainihin sama ruwa kasa kudi. Baki isa ba kinyi kadan ki cinye mun dukiya dan malafar kan na tsoho me allura na gangaren litiya fanda. Uban kakanki kenan. " "Cika ni nayi tsarki kai dai kamar sabon tab'i." "Kin gama kasayarwa acikin gidan nan tunda ba naki bane. Almura da idanu yan kanana a ciki." Atuwa dake mulmula wuya ta kece da dariya. Kafin ta janyo gallan da Farillatu ta tsinto a shara. Ta shiga kidi tana rausaya kai. "A hayye landantsan tsan tsan. Durama a gidan Ardo. Akan me? Akan gidan Ardo. Meya faru. Ardodo. Daren farkon su yayi kyauta. A hayye landantsan. Allah me alheri. Ku chasu bamban ku chasu. Ku chasu bame rabaku. " Rumalle duk Ardo ya gama tukwikwiye ta yana neman bugata da kasa. Rashin wanke duwaiwukan ta da batayi ba shi yafi kona mata rai. Shysa ta kasa kokawa dashi. Atuwa ta ajiye gallon din hannunta tamike. "Ka chikata ta wanke bahayar mana. Fisabilillahi mata tana kasayarwa kaje ka cafkota. KO kyankyami bakkai Ardo? Allah ya kyauta." Rumalle data gaji cikin zafin nama ta tattaro kafafun Ardo ta nanashi da kasa. "Allah me alheri " Atuwa ta fada tana sarawa Rumalle. "Kai Usmanu ku rikemun shi kafin na fito." Rumalle ta fada hade da komawa cikin bandaki tashiga karasawa tana jan tsaki. Su Usmanu suka hau Ardo da kokawa. Ga gam suka rike Ardo. Baya da damar kwacewa saboda tsananin yadda suka tamke shi. Idrisu kuwa ya haye saman kafafun Ardo ya zaune "Charanchas Ardodo. Allah me alheri." Duk kuwa da a daddaure yake. Ardo bai fasa daga kai ya dankarawa Atuwa harara ba.. "Allah ya kwashe miki albarka Atuwa. " Atuwa ta ja yar yarkaccacciyar kujerar ta ta zauna. Sam taki tarewa Ardo saboda tsananin yadda zuciyar ta ke 'kullace da shi. Ya cire su ya ajiye a matsayin matan sa. Bayan kowacce da igiyoyi biyu akanta. Ya shika su sau 'dad daya. Yadda ya yakice al'amuran yaran sa da yaran nasa baki daya tamkar ba shine ubansu ba. Cin su. Shan su. Tufatar da su, Makaranta kai dama dik wani hakkin su da ke kansa ya tattara ya ajiye a gefe. Tun wasu na jinjirai wasu kuma tun kan a haife su ya dora tsanar su a kambun zuciyar sa. Rumalle tafuto daga bandaki tashige daki ko takan Ardo dake mutsimutsi da hannuwa bata bi ba. Kaya ta sauya ta zura hijabi ta fice. Kai tsaye ta wuce gidan mai unguwa. Bata jima ba ta fito ta dawo. Tabarmarta ta dakko ta shimfida a tsakiyar gidan. Atuwa na ganin haka ta sake gyara zaman da tayi akan yar kujerar ta. jimmamman daii na daga kuryar dakinta a rakube. "Ku cika shi. Ga me unguwa Nan zuwa." Rumalle tabawa su Usmanu umanrni. Ardo cikin takaici ya fashe da kuka yana kwashewa Yan gidan baki daya albarka .. Ba jimawa sai ga zagin mai unguwa na doka sallama "Mai unguwa Yana neman iso. Assalamu Alaikum. Mai unguwa na neman iso. " "Shigo zagi. Ku shigo. " Mai unguwa da zagi suka shigaa. Nan Ardo ya fesa musu komai. Rumalle ma tafadi yadda akayi. Mai unguwa ya nisa kafin yace, "Abu na farko dai shine an kafa.maka dokar hana shikan da kake wa matan ka. Da Kuma kara karen auren da kake yi. Bayan gida bata koshi ba. Iyali ba suturar kirki da sauran su. Dole ire iren matsalolin nan su yi maka yawa. Kuma zahirin gaskia inada masaniyar kyautar gida daka yiwa matar ka Rumalle . Domin a satin auren KU. Ta kawo mun takardar shedar mallaka ta gidan nan. Ta Kuma gayan yadda akayi. "Zahirin gaskia banidaa ta cewa anan. Domin sheda de ta jima a hannu na. Kuma bazan iya cewa kyauta ta badu ko bata badu ba. Wannan sai dai sharia tashigo ciki. Amma kafin sannan inason ka san kai ne silar faruwar komai Ardo. Yawa yawan auren ka. Shi yake sa kake shiga cikin matsaloli. Sam yaran ka mata basa gaban ka. 'Da daya tal da Allah ya baka ka dorawa kulaficin so Allah ya dauke abinsa ya bar ka da halin ka. Yanzu kai wannan kadai bai isheka ishara ba? Matar ka kuna zaune da dadi ba dadi da yaran ku a tsakani. Haka kawai akan wata figalalliyar tinkiya ka shika ta. Sai gashi ta auri wanda yafi ka komai. Itada yaranta shar da su sun bar halin rashi sun koma na samu. "Dan mijin Kuma shike auren diyar ka . Ko wannan bai isheka ishara ba? Ko kuwa su Hajara yaran Atuwa ba auren sukayi ba? Kowacce kuma tana zaune gidanta cikin koshin lapia. Dadin aure ya sa ka bawa matar da kayi sabuwa gidan ka kacokam shi kadai daka mallaka a duniya. Nan bangaren babu abunda ya shafeni. Na tura zagi da takardar ya kai kotin gangare. Muje can ayi shari'ah "Amma kafin sannan inason jan hankalin ka Ardo kana saurara ko?" Ardo ya fyace hancin ssa da kasan rigar sa kafin yace, "Ni ban bata gidah ba Mai unguwa. Mahaukacin ina ne ni ?" "Mahaukacin rimin kebe mana. Shashasha, sakarai, Sauna. Wanda kaf rimin kebe ba Wanda aka
Chapter 42 · 0% Book details