Sashe 35
So Da Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Usmanu. Nifa du zancen nan ca zan maka Jammu ta haife 'da namiji charan chas Ardodo" Ardo ya ware idanu. Cikin rawar jiki da baki yace da ita. "Sharota kikayi ko Atuwa?" "Wane irin sharota Ardo? Ba karya nake ba. Yanzun zuwan su Zaraah ai zancen haihuwar suka taho dashi. Kazo muje ku gaysa kaji da kunnen ka." Ardo dake tsaye yana fuskantar Atuwa. Cikin manyan kaya, 'kirar riga Yar shara shudi'ya da wando . Duk kayan sun cukwikwiye saboda azabad chasar da Rumalle tayi akansa. Duk ya kara figewa ya jeme. Ya koma tamkar tsoho. Yace da ita, "Allah dai ya kwashe miki albarka Atuwa. La'an" "Karka soma la'ance mun. Da yardar Allah sai dai kaga kwashewar albarka akan ka. Aikin kawai." Ta karasa fada, Hadi da buga tsakiyar zaninta ta watsa hannu sama tana mai surfawa Ardo bak'ar magana. Ardo ji yake tamkar ya fad'i kasa yayita birgima saboda tsananin yadda zuciar sa ke masa rad'adi. Wai Jammu ce ta be haife namiji? Yaje ya dawo haka ya dinga safa da marwa akan gadar rimin kebe . Can ya samu gefen wani dakali ya zauna bayan ya zabga uban tagumi. Duk wanda ya wuce sai ya kalle shi. Ganin bayan tagumin daya zabga harda 'karin magana shi kadai. Yana nuna sama ya nuna kasa. Tamkar mai kirgen bulan gini. Liman zai wuce yaga Ardo a zaune yana magana shi daya tamkar zaucacce. Fasa tafiyar yayi ya dawo gefen Ardo ya taba kafadun sa. "Malam Ardo lapia kuwa?" "Na'am jammu!" "Jammu kuma? Malam Ardo." Sai a sannan Ardo ya dawo hayyacin sa ya dubi liman dake mika masa hannu suka gaysa. "Ya mutan gidan kowa kalau?" Ardo ya sauke zuciya yana girgiza kai "Ina cikin makauniyar kaddara liman " "Toh pah! Ta mecece malam Ardo?" "Mata ta dana shika a baya ce tayi aure wai harta haife da namiji yau." "Shine kake zaune kana bayani Kai daya kamar sabon tab'i? Iyye?" Liman ya karasa fada tare da zama kusa da Ardo. "Wacce matar taka. Ai wanda ka shika sunada yawa. Wacce daga ciki?" Ardo ya daga kai zai yi magana sai ga Asabebiya kawar jimmamman data mata kitso. Ya zuba mata idanu yana binta da kallo harda lek'ar da kansa . Zai mike liman ya zaunar dashi cikin takaici. "Meye haka?" "Liman Asabebiya naga ta kara murjewa. Carkwadi. Yar na'innatuwa ce ko?" Liman yaja dogon tsaki. Yasa hannun sa ya bige yatsun Ardo dake nuna Asabebiya . "Mahaifinta aminin ka ne ko liman?" "Buhun uban ka Ardon nace buhun uban ka. Asabebiya shekaran jia waccen aka daura mata aure da Ansari me kyamis a farin masallacin unguwar yan doya " Ardo ya rafka uban salati yana jimami. "Amma Allah ya kwashewa An.." "Karka karasa. Kowa ma kwashe masa albarka. Dama inason zuwa wajenka zuwa na musanman. Amma tinda yauma mun hadu ai shikenan. Ina fatan kana saurarata!" Ardo ya kada kai yana mai duban liman sosai "Ina jinka yallabai." "Yauwa dattawan rimin kebe na gada mai doyi dana yan farin masallacin unguwar doya. Da hayin yin bola dana yan dusar hayi. Sunyi zama sosai akan ka." Ardo sanin ansaba hada masa kudi yasa ya mike ya zube akan gwiwoyinsa yana barbadawa liman godia. "Godia nake liman. Karamcin ku yayiwa kalamai kadan wajen zayyano godia ta agareku. Ka ciri dubu aciki a siyawa iyali kukar miya. Akuma mikawa dattawan mu godia kafin nazo da kai na." Liman ya yi murmushi yana kambama karfin hali da nakasar zuciya irinta Ardo. "Ba kudi bane Ardo . Atakaice dai dattawan sunce ba Kai babu Karin aure ba bu Kuma shika. Domin ka yiyyi na farko ka Kuma yi na karshe. Sannan dole ne ka tashi ka nemi Sanaa ardo. 'dan ka namiji daka laru akansa. Allah yafika kaunar sa ya karbu abinsa. Don haka dole ma tashi tsaye akan iyalin ka . Ka cire zancen aure ko shikar sa. Domin an shatale maka layi akansa ba zaka ketare ba. Kuma sunce idan kak'i aminta da dokokin su to ka tattara kabar unguwar rimin kebe. "Sai a biyu na biyu. Wannan magana ce zan maka jan kunne akanta Ardo. Ka cire mayatar son haihuwar 'yaya maza a ranka. Kai lalle a dole Sai ka samu namiji ? Wacce iriyar rayuwa ce haka? Kai bakasan yawan haihuwar 'yaya mata bama alkhairi ce sannan Kuma arziki ne. Banda kai da gaulancin ka ai 'ya'ya mata sunfi jin'kai. Mazan me sukeyi ? Inada su har 5, Amma kafin su kyauta ta mun. 'ya 'ya matan dake gabana sun temakamu. Hakama wadanda ke gidajen auren su duk suna kyauta ta mun fiye da 'kartin mazan da nake dasu guda biyar . Saboda haka kayiwa kanka fad'a, "Ka rungumi yaranka da iyalinka a matsayin taka kaddarar kenan. Sai kaga Allah ya yaye maka ya Kuma buda maka lamuranka Ardo. Yanzu kamar ayace kagani akanka. Ka shikata tayo wani auren ta haifi namiji. Don haka Wannan ya zama izina agare ka malam Ardo. Allah ya jikan Modibbo ya raya wanda suke raye da albarka. Allah Kuma ya buda musu su temake ka da al'umma baki daya. Aamin," "A,,,min" Ardo ya amsa a rarrabe. Zuciyar sa na matukar masa zugin hukuncin da aka yanke masa. "Da kun kyale na shika rumale. Liman a ruwan ciki na ta zauna tana mun shakar mutuwa. Ga gand'ama gand'aman yara har 3 da ta dawo dasu. " Liman ya hankalci dimuwae da Ardo ya shigaa , don haka ya shigaa tausasar zuciyar Ardo. Har sai da ya tabbatar damuwar Ardon ta ragu sannan ya zaro nera dari biyar ya mika masa "A kula da iyali a sayo musu kad'in miya ko dan nama ne a watsa musu . Nima albarkacin 'yaya na mata naci. Zannirah ce ta aikomin da dubu biyar dazu." "Masha allah! Allah ya saka da khairan." "Amin Ardo. Tashi ka tafi gida dan Allah Kuma ka rika Jan girman ka kana kokawa da matan ka ko cacar baki shysa suka renaka. Ka ja girman ka don Allah Ardo." Ardo dai tinda ya dafe kudin sa a aljihu ya mike. Ya dauki hudubar liman wata Kuma ya zubar da ita awajen. Kai tsaye ya wuce layin yan dusa wajen gaddafi me gurasa da nama. Yasa aka yanka masa gurasa da naman sa na dari hudu ya sayo leman roba na dari ya shigaa dannawa a baka yana korawa da lemon sa. . Zaman makoki sosai akeyi a gidan na Capt muhd. Anata kawo abinci daga makota da yan uwa hadi da abokan arziki. Ataya Capt jimamin rashin sudeis dansa a Kuma yi masa barka da samun baby sudeis. Kusan duk wani makusanci ga ahalin capt muhd. Sai daya shigaa cikin rudanin babban rashin sudeis da akayi. Yaron kirki mai tarbiya da dimbin ilimi. Mutuwar lokaci daya. Maheer ya shigaa matsanancin rudanin rashin sudeis. Tunda ya zauna akan runfar da ake makokin baya tashi sai dai idan zaayi sallah ya mike yabi jam'i ya koma ya zauna. Maganganun sudeis da suka zama tamkar wasiyya kwakwalwar sa ke tariyo masa duk sakanni. "Babban Yaya na baka amanar Zaraah na. Kai kadai na aminta da kai wanda zai rike mun Zaraah tsakani da Allah . Ka cire kiyayyar zaarah a zuciyar ka. Ka tarairayeta babban Yaya. Zaraah batada matsala saita zuciya. Dan Allah idan tahau kai ka sakko. Ka koya mata so da abunda ya 'kunsa." Yana tunanawa Yana hawaye. Ashe wasiyya sudeis ya bar masa? Hawaye nata kwarara a fuskar sa. Dakyar ya mike cikin sanyin jiki ganin takwas harta wuce da rabi. Kai tsaye ya dau mota ya dauki hanyar rimin kebe. Wannan zuwan ma da temakon map ya karasa unguwar. Almajiri ya tura gidan yace akirawo su Zaraah su tafi. Yaran ya shiga ya fito, "Wai suna gidan gate. Gidan Haj Mari ." "Kasan gidan ?" "Eh" "Muje ka rakani." Almajirin ya shigaa gaban motar suka tafi har gidan Haj Mari. Yaci saa kuwa har sun fito zasu tafi. "Zaraah...ku shigo mu tafi" Ya fada Yana mai zuge glass din motar . Gaban Zaraah ya fad'i don dadi, saboda da farko sai taga kaman sudeis ne. Don tanata jiran kjransa taji shiru. Ganin Maheer ne yasa tadan yamutsa fuska tamkar tamai shegen duka. "Zaraah! Shigo mu tafi don Allah." Ta bude gidan baya ta zauna. Yayinda raheelah tashiga gaba. Na'eelah kuma tazauna kusa da Zaraah. Ya hau titi yanata tafiya ahankali. Yanata sak'a yadda zaa sanar mata rasuwar sudeis. A haka suka karasa gidan . An share makoki ganin dare yayi kowa ya tafi. Na gidah na gidah Kuma sun koma ciki. Yana gama parking suka fice ko kallo bai isheta ba. Yanayin yadda ake shara adaren ne ga plates ma'aikata anata wanke wanke yasa Zaraah jin jikinta na bata wani abu. Suka shige sashen na Dadaa Kai tsaye. Yan biyu suka sheka wajen baby sunata kallon sa. Dadaan dai tana zaune tayi jigum. Kallo daya zaka mata kasan ba lapia ba. "Dadaa meya faru?" Dadaa tayi shiru tana auna yadda zata sanarwa Zaraah. Harira dake gefe tayi caraf cikin azarbabi tace, "Wannan ne ya rasu a jirgi sudens (sudeis )" Zaraah ta saki wata gigitacciyar kara tafadi a kasa sumammiya. "Gaskia harira an gayshe ki. Sam baki iya fadar mutuwa ba. " Da sauri aka kwashi Zaraah sai asibiti. Likitoci suka shiga bata temakon gaggawa.. Ta farfado amma bata magana. Sai ambaliyar hawaye dake sharara a fuskarta. Hakika zukatan mutane da yawa sun shiga rudani na halin da Zaraah tasamu kanta aciki. Ba cin abinci ba magana sai kuka kawai. Drip aketa durka mata sai allurori. Abinci ko ambata sai ta amayo dashi. . . Ranar suna ba'ai shagalin suna ba. Illa dai rad'in sunan da akayi a masallaci. An Kuma yi yanka. Kowa yabi jariri da addu'oin alkhairi. Allah kuma yasa ya gaji mai sunan sa. An sallamo su Zaraah daga asibiti. Amman tamkar an sauya zaraahn baya zuwa ta yanzu. Duk wata walwala da take tadena. Kullum cikin kuka take. Da sallolin nafilfilim har abada hannunta rike da charbi tana adduoin saman aljanna ga sudeis mai kaunarta. Kullum tana zaune a 'daki. Ba ruwanta da kowa da kuma komi. Dama sauran yan gidan sun debu Karan tsana sun dorawa Dadaa da iyalinta. Musanman yanzu data samu albarkacin haihuwa. Dadaa na