← Book details So Da Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 55

Sashe 36

So Da Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

zaune tana kallon baby sudeis dake saka hannun sa a baki. Yara duk sun tafi makaranta. Capt muhd ya shigaa parlorn bakinsa dauke da sallama. Dadaa ta gayshe shi cikeda girmamawa. Ya amsa Yana mai daukar baby sudeis a hannun da. "Su Maijidda sun shigo kuwa?" "A'ah! Amman inajin basa nan don na je dazu kofofinsu a rufe." Capt muhd ya girgiza kai kawai yanawa baby sudeis wasa. Kafin yace, "Ki rabu dasu. Dama zaman TAKUN SAAKA nake dasu ai. Kema Kuma ba zasu so ki ba saboda kina kaunar su Maheer da marigayi sudeis . Kinsan meyasa?" "A'ah" "Saboda basa kaunar ci gabana. Sun so su halaka matata wadda tarasu. Wato mahaifiyar sudeis . Yayar babar Maheer me rasuwa. Sun so su halaka ta saboda tasamu albarkacin 'da namiji. Suna cewa wai nafuson ta. Da Kuma abunda ta haife. A shekarun baya suka shirya wani tsari da zai zama anyi hatsari gaba daya daga Jamila da Maheer da Sudeis din duk su mutu. "Dake Allah adali ne. Sai gashi naje fandan. Ta roke ni Kan zasu kara kwana. Ashe direba an kunce notocin cikin motar anan fandan suka aika wani ya tsara komai. Washegari muka shirya Ni da ita da yaran biyu wato sudeis da Maheer. Muka dakko hanyar gidah. Wanda nayi waya dashi a karshe kawu na ne Harith. Lokacin da hatsarin ya taho mana muna waya dashi. Ya jiyo sanda motar ta kwace muka fada wani kurgurmin rami. Kai na ya bugu. Airbag takare su Maheer Allah yayi sunada kwana a gaba. Ta murfin mota ashe ya bude Jamila ta fada ramin ta rasu. Ni daganan bansake sanin inda kai na yake ba. Ashe take na shigaa coma aka kaini asibiti a Qatar. Da taimakon kawu na da muke waya shi ya gano komai. "Maijidda da Iklima ba matan kwarai bane Jammu. Ba wai Ina gaya miki bane don kitsane su. No ki barsu da halin su kamar yadda Addayo ke fada. Badan Addayo ba wabillahil lazi dana sakesu duka. Tunda har sun san su had'a Kai suyi kokarin kashe mun mata da yara. Wadda sukazo suka same Ni da ita. Yar uwace agare Ni. Gari daya da komai. Akan kaunarta gare ni da yadda na dora raina akan Maheer saboda rashin mahaifiya da yayi. Ashe zagwan kasa suke su kashe su. Yaran su su gaji gado ko? Saboda yaransu su girma su rike companies dina ko? Saboda haka daga yau Ni da Addayo da yaran mu zaki aminta dasu. Babu ruwan ki da sabgar wa'incan. Inaso a karshe ki bani dama na aurar da Zaraah ga Maheer domin zumuncin mu ya sake kulluwa Jameelah. Banason Zaraah ta sani Kuma Kinji? Kin amince?" Ya karasa Yana mai fashewa da kuka. Dadaa ta mike ta koma kusa dashi tana hawayen itama, "Insha Allah bappan su . Da yardar Allah komai yazo karshe. Allah Kuma ya cigaba da kareku baki daya. Allah Kuma ya jikan su da rahama baki daya. Bappan su Zaraah ai 'yace awajen Ka. Don haka kanada dama da Kuma girman iko ga duk abunda ka zartar akanta ya halasta...." Ya Kai mata runguma mai ratsa jiki. Dadaa na kashe shi da salo kala kala. Sai dayaji zuciyar sa ta Sarara tukun sannan ya mike ya nufi sashen maheer. Ya same shi da maganar zaraahn. Maheer bai turje ba. Don shi kansa so yake ya cika amanar sudies duk kuwa da bayason zaraahn Cikin sati na gaba, capt muhd ya tashi da kansa bisaga jagorancin Maheer suka nufi rimin kebe da Alhaji dangoje. Suka zanta da Ardo dake dama an karbi kudin sudeis don haka atake awajen bayan anyi sallar la'asar. Aka daura auren' Maheer muhammad muhammad da amaryar sa Zaraah Ardo borkindo, akan sadaki mafi daraja #unedited 2/7/22, 09:08 - Buhainat: _SO DA ZUCIYA!!_ _30_ _ZFF2022__ _(PAID NOVELS)_ _NANA HAFSATOU I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ci3ao6233sn3&utm_content=6k8ur6p *WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_* *ZAFAFANKU BIYAR sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA* *_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_* *GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA WARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi* *JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE* *_DEEN MARSHALL Mamuhghee_* *_HALIN GIRMA hafsat rano_* *_TAKUN SA billyn abdul_* *_SO DA ZUCIYA miss xoxo_* ABI'AR ZUCIYA huguma_* *DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN AI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL* 1000 *Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin* 6019473875 MUSAA ABDULLAHI SAFIYA keystone bank Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 08184017082 *IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU* 09134848107 _*HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_* #team zafafa biyar . ___________ Ana daura auren Maheer ya samu gabansa da matsananciyar bugawa. Ya saka hannun sa a hankali yana mai dafe saitin zuciar sa. Take wasu zafafan hawaye suka shigaa reto a fuskar sa. Alhaji Dangoje da Ardo sun fita izuwa farfajiyar masallaci suna mai rarrabawa mutane goro da alawa da dabino. Capt muhd ya sake matsawa kusa da Maheer. Domin gaba daya tausayin 'dan na sa ya sake dabaibaye shi. Ya rasa mahaifiya tun yana jariri. Kanwar mahaifiyar sa da rikon sa ya koma hannunta itama tarasu abisa tuggun da kishiyoyi suka yi. 'kani kuma 'dan uwa mafi kusanci agare shi shima Allah ya karbu abun sa. Maheer bayada kowa yanzu. Sai Capt muhd da kuma Addayo. Kasancewar kakanninsa na bangaran uwa dik sun rasu, Yan uwa ma fulanin tashi ne. Ba wanda keda masaniyar inda suka nausa. Ya dafa kafadar sa yana mai mika masa hankicin dake hannun sa. "Kayi hakuri Maheer. Ka yafe mun na yi saurin zartar da umarni akan ka batare da na baka lokaci kayi shawara ba. " Maheer ya goge hawayen dake tsiyaya a idanun sa sannan yace, "Bappah bakamun komai ba. Ai ko da ace bansan Zaraah ba. Bantaba ganin taba. Kuma ka auramun ita. Dole ne zan zauna da ita har karshen rayuwata bappah insha Allah. Dan Allah ka dena bani hakuri. Hawaye kuma da nake bappah ba akan auren nan bane. Su Inna natuno da sudies. Na tuno da yana raye da dashi zaa daura . " Ya karasa fada yana mai fashewa da kuka gwanin tausayi. Capt ya shigaa bubbuga bayan sa yana bashi hakuri. Shima hawayen ne ya shigaa zurara a nasa idanun. Yai saurin kauda kai don ma kada Maheer din ya gano shi. "Allah ya fi mu kaunar su Maheer. Addu'oi zamu cigaba da musu. Allah ya gafarta musu. Ya bamu hakurin rashin su. Hakika munyi babban rashi amma babu yadda zamuyi Maheer. Kayi hakuri kaji. Duk da bana shakku akanka nasan zaka rike Zaraah amana. Don Allah Maheer kada ka bari shedan ya shigaa tsakanin ku. Kuma kaga sai a hankali sabon ta da kai. Wannan daurin aurenma batada masaniya. Idan lokaci yayi za'a sanar da ita. Amman dai kayi kokari ku saba da juna tamkar yadda suka shak'u da marigayi..," Capt ya karasa hade da saurin goge hawayena dake neman fashewa ya koma kuka . "In shaa Allah bappah." "Yauwa to share hawayen naka ka tashi mu tafi."
Chapter 36 · 0% Book details