← Book details So Da Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 55

Sashe 27

So Da Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_* *GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA WARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi* *JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE* *_DEEN MARSHALL Mamuhghee_* *_HALIN GIRMA hafsat rano_* *_TAKUN SA billyn abdul_* *_SO DA ZUCIYA miss xoxo_* ABI'AR ZUCIYA huguma_* *DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN AI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL* 1000 *Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin* 6019473875 MUSAA ABDULLAHI SAFIYA keystone bank Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 08184017082 *IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU* 09134848107 _*HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_* #team zafafa biyar . ___________ 1/31/22, 18:50 - Buhainat: *Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107* I'm on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb *SO DA ZUCIYA* *NANA HAFSATU* ***Dadaa dasu Zaraah sun dau tsawon lokaci agidan na Ardo suna zaman makokin marigayi Modibbo. Abincin ranar rankataf Dadaa ce tabada kudi, Acikin wanda Haj Amina ke bata na atarwa. Don kuwa Ardo zama yayi a gefen rijiyar gidan badaru yana matse hawayen dake yar tsere a fuskar sa. Masu zuwa da cokali tafiyayye idan akayi rasuwa a ranar sun gane kuran su. Domin Ardo dai dai da tsinken ashana bai bayar ba na sanwar rana. Dadaa ta sake bai wa Atuwa dubu biyar kan a sake yin abincin makokin saboda gidah yan uwa sun cika taf kuma ace babu abinci, Sai hammar yunwa mutane ke tayi. Sai dare su Dadaa suka yi haramar komawa, Kowanne idanun sa jazir ciki harda yan biyu saboda tsananin sabon da sukayi da Hamman nasu. Zaraah kuwa dakyar Dadaa ta yakice ta daga makalkale rigar Hamman nasu da tayi dake ninke akan dan akwatun arfen sa.Rayuwa kenan! Ibrahim ne yazo daukar su Dadaan, Sai Haj Amina data bi yo shi don yiwa su Dadaan gaisuwa. Har ciki Dadaan tayi musu rakiya. Haj Aminan ta zube a kan taburma tanai wa su Atuwa ta ziya. min dai Haj. Modibbo sa yayi. ? Cewar Atuwa dake zaune a gefen dakin ta ta zubawa su Haj. Amina idanu tana musu kallon qurilla. Haj Amina dake gefen Jimmamman ta amsa ahankali. ajia baki waye ni ba ko? Haj Amina ta juya tana kallon Atuwa da gaba d ya ta mayar da ita kamar talabijin din kallo. Sam bata damuwa da kallon Haj Amina ba bare tsirarrakin mutanen dake wajen tasake cewa, i ce nan Atuwa da kika bamu kudi lokacin baya. Haj Amina ta an yi murmushi tana kada kai. h yaasin kika babbamu kudade charan chas sa lin nan ni da Jimmamman. kay nagane, Toh ya karin hak ri d... Bata karasa tambayar ba, Idrisu dan Rumalle ya shigo da gudu Usmanu na biye masa a baya. o nan dan undin uban ka ka bani farantin nan. Idan ka cinye ni kuam fa? Mama mama kinga ya hana ni abincin ko? Rumalle dake sosa kunnenta da guntun ice taja tsaki tana wurga musu harara, aci malafar kan uwar uban ka. Haba sai fitinar tsiya, Zaka bashi abincin ko sai na lakada maka na jaki.? ama kadan ne nanfa, Wani mutumi ya bani, Shi ne nan wai sai munyi rabo dai dai. aku matsa ko sai na zazzabga muku bari? Ficewa sukayi dukkanin su, Yayin da Haj Amina ta musu sallama, Dada ta Kalli tsohon dakin ta a baya, Wanda hamamin kazantar su Idrisu ya sake munantar da dakin baki daya. Ya bade da kura. Tamkar yayi shekara da shekaru ba'a gyara shi. Ta sauke ajiyar zuciya kawai. Hade da riko hannun Zaraah dake kuka shab'e shab'e. Domin idan ka tsame Dadaa agidan nan ba Wanda Zaraah tasu tazo daya Kuma suka fi kusanci irin Modibbo. Hakika Zaraah tayi babban rashi. Addu'oi tacigaba da yiwa modibbo ahankali saboda yanayin yadda labbanta ke motsawa. Waje suka nufa don shigaa mota su koma gidan. Ardo dake zaune acikin jamaa Yan zaman makoki Yana ganin su ya mike tamkar dama sudin yake jira. Idanun sa 'kur akan Dadaa dake tsaye da su Haj Amina suna yiwa wasu ta'aziyya a gefe Cikin sauri ya yayibi takalmi wari da wari ya zura,Ashe tsabar rawar jiki warin takalmin Ladan ne daya, dayar kafar kuma na hannafi me shago, Hannafi dake shirin tafiya wajen aiki ya jawo rigar ardo da hankalin sa gaba daya yayi wajen su Dadaaa dake shirin shiga mota. "Ban warin takalmina Ardo." Cewar Hannafi daya duk'a ya riko saman silipas din da kafa daya ke wajen Ardo. "Karbomin nawa ma Hannafi" Ladan ya fada girgiza Kai. Domin gani yake mutuwar Modibbo ce ta susutar da Ardon. Ardon kuwa ganin Dadaa da yayi ne, Ta dawo kamar ranar daya faraa haduwa da ita ne yasa shi zuzucewa. Da sauri Ardo ya sab'ule takalman baki daya ya shigaa dokawa Dadaa kira, Kamar wata matar sa. "Jammu, Jammu, Jammu" Dadaa da har ta bude murfin mota zata shiga taja ta tsaya tana mai sarautar Allah idanu. Hakama hajia Amina data saki baki tana jiran cewar Ardo. Da sauri ta zagaya tana dan murmushi kadan. "Malam Ardoo mun gaisa ko? Ya Karin hakurin rashi?" Ardo ya bude idanu yanawa Dadaa wani irin mayata cen kallo. "Jammu!" Dadaa dake binsa da kallo shak'ek'e tace, "Na'am Ardo" Ardo ya hadiye wani 'dacin daya tokare masa a wuya. Na jin sunan sa data Kira gatsal yau babu ma sirken Malam din da take joganawa a sunan sa. Ya kada kai yana kokarin 'kakaro murmushi. Idanuwan sa nata karakaina a jikin tah Haj Amina ta sha gabansa hade da wangalewa Dadaa kofar motar ta shige. "Ardo Nace ya Karin hakuri?" Haj Amina ta sake cewa dashi, Ardo ya zura Kai Zai sake lek'a Dadaa, "Alhamdulillah Hajia. Jammu nace ki dakata muyi magana ko?" "wacce magana zakuyi Ardo? Ai bakin alkalami ya rigada ya bushe. In Sha Allahu. Jammu tamaka nisan da har gaban abadan ba zaka iya cinma taba. Yara ne dai Allah yayi zaku samu a tsakanin ku. Kuma har abadan da sunan ka zasu amsa a matsayin mahaifin su. Zumuncin ku ba zai samu tangarda ba Kai da yaran ka. Jammu kuma albarkacin 'ya'yan dake tsakanin ku dole zaku dinga gaisawa. Baya ga haka Kar ka ma kulla wa zuciyar ka wani abu ga me da jammu. Domin yanzun ta maka ni sa. Allah ya musanya mata da mafi alkhairi. Allah ya jikan Modibbo Mai gidana na maka ta'aziyya. " Haj Amina na gama magana ta shige cikin mota. Yayin da Ardo ke tsaye motar su Haj Amina ta bula masa kasa ta yi kan titi. Yatsan da yasa a baki ya chiza yana auna karshen zancen na hajia Amina datace Allah ya musanya Mata da mafi alkhairi Dakyar yaja sanyayyun kafafun sa da babu takalmi acikin su. Sunyi furu furu saboda rairayin kasar dake wajen. Hakama Dadaa anata bangaren tashiga mamakjn kalaman na karshe da Haj Amina tace da Ardo. Batace komai ba har suka karasa gidah. DANGOJE's Koda suka karasa gidah Haj Amina bata yi wa Dadaa maganar komai ba, Su Dadaa suka cigaba da alhinin mutuwar Modibo. Sai bayan sati biyu da rasuwar Modibbo . Haj Amina ta sami Dadaa da maganar Capt. Muhd, Saboda tsananin yadda ya takura musu da zancen Dadaan. Ciki harda Addayo datazo gidan a bazata taga Dadaan. Wanda Dadaan da su Zaraah sam basuda masaniya. Kallo daya da Addayo tayi wa Dadaa da yaran ta gaba daya taji kaunar su ya kamata. Tabbas Dadaan zubinta kwarai yayi kamada su marigayi ya Jamila da Jamila. Dadaa fafur tace bata raayin kara wani aure, Zatayi zaman tarbiyyar 'yayanta dai. Haj Amina ta kada ta raya. Dadaa tace sam ita ta wuce shekarun aure. Haj Amina takanyi murmushi duk sanda Dadaa tafadi haka takance, "Kalli baya na . Na goyaki a baya yafi sau nawa Jammu. Shikenan tinda haka Kika zaba. , Kin nu na ban isa dake ba, Baki dauke ni tamkar Iyami ba kenan. Nagode" Takarasa tana goge hawayen data 'kakaro shi. Nan jikin Dadaa yayi sanyi. Ta yanke hukunci take awajen tana hawayen itama, "Na amince Hajia. Dan Allah kibar zubar mun da hawayen ki na amince." Haj Amina cike da farin ciki ta rarumi Dadaa ta matseta ajikin ta. Suka fashe da kuka baki daya, Wanda nake da tabbacin na farin ciki ne. Haj Amina ta 'kara da "Ina dattijuwar data zo kwanakin baya? Mahaifyar sace. Shi da ita sun kafe don inda gaban matsuwa ma wallahi sunyi Jammu. Sunason ke da yaran ki baki daya zaku koma can gidan. Ciki harda Zaraah. Yadda suka nuna kaunar su akan ku hakan yasa na aminta da zancen na Kuma kara da doriyar mu zamu dinga daukar nauyin karatun Zaraah harta kare makaranta izuwa jami'a. Da yardar Allah har ya zuwa aurenta. Don Addayon ma catayi ita kam tayiwa Zaraah miji. " Ta karasa tana daria Dadaa dai murmushi tayi kawai don tarasa bakin magana. Haj Amina ta kirawo su Zaraah da Yan biyu ta sanar dasu komai dangane da auren da Dadaar su zatayi. Da Kuma zaman su da zai koma can baki daya Kwarai matuka dukkanin su duk kuwa da kankancin shekarun su. Sunyi matukar murna sun Kuma amince da sabuwar rayuwar da zasu shiga. Dadaa dai tana gefe kawai. Kunya duk ta lullube ta. Sati daya da sanarwa Dadaa zancen Capt muhd. Ranar jumuah ya sanar dasu Haj Amina zuwan da zai yi wajen Dadaa da daddare bayan sallar ishai. Tun safiyar ranar Haj Amina dakanta takai Dadaa saloon and spa aka yiwa Dadaa wankin Kai aaka kitse yalwataccen kan da kitson shuka. Aka mata gyaran jiki da su kunshi. Dadaa dai tafito ras kamar sabuwar budurwar amarya. Kyanta ya tsatso. Karancin shekarunta suka bayyana.yankwanewar datayi na gidan Ardoo data koma tamkar babba. Yanzu duk komai ya baje. Takoma Jammu ta baya. Kai ba kace tayi aure tanada babbar 'ya kamar Zaraah. CAPT. MUHD's A bangaren na Capt muhd shidin ma hakan take. Tun kafin a sanar dashi amincewar Dadaa tuni yafi mai Kora shafawa. Yasa an gyare sashen daya ware shi daban a gidan. An zuba
Chapter 27 · 0% Book details