← Book details So Da Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 55

Sashe 45

So Da Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya kai ga talauci, to yau da gobe, sai ya samu wanda ya fi shi, shi ya sa hadisai da dama suke kwadaitar da mara shi ya bayar da komai kankantar abin da ya samu don Allah, gwargwadon karfi da iyawarsa, lamarin da zai sa ya ji shi ma ya bayar da tasa gudunmawar wajen taimakon wadansu. Shi bayar da dan kadan saboda Allah, idan mutum ya gan shi a Ranar Lahira zai yi ta mamakin yadda ya kai haka don girma, saboda Allah Yana kiwata masa shi ne a wajenSa, matukar dai abin da ya bayar din ya same shi ne ta hanyar halal. "Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, uk wanda ya bayar da wata sadaka (ko kyauta) daidai da dabino daya na halal ? domin Allah ba Ya karbar komai, sai mai tsarki (halal) ? Allah Zai karba da hannunSa na dama, kuma Ya kiwata (Ya tattale) shi, kamar yadda dayanku yake kiwon maraki har ya zama bajimi ? to Allah zai tattale shi har ya zama kamar girman tsauni a Ranar Lahira. ? Buhari da Muslim ne suka fitar da Hadisin. "Don ya kare mutane daga juya baya da kuma runtse idanunsu wajen bayarwa saboda Allah, sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya bukaci su bayar da sadaka komai kankantarta. In sun yi haka, za a samu kyautatawa da tausayi da rangwame da shaukin juna a cikin zukatansu da kuma tsakaninsu. Ya gargade su da su guje wa rowa da kankame dukiya, a hana ta zagayawa tsakanin jama mabambanta, lamarin da yake haifar da jafa da bala a tsakaninsu, a yayin da ya ce, u kange kawunanku daga Wutar Jahannama ko da da bayar da kyautar (ko sadakar) rabin dabino ne. ? Buhari da Muslim ne suka fitar da Hadisin. "Allah Yana son Musulmi ya zama na kirki, mai amfani ga al mmarsa, wanda kuma yake taimakawa a samar da kyakkyawa kuma kwakkwarar al mma, wadda kodayaushe tana cikin alheri, ko Musulmin nan yana da wadata ko talaka ne shi. Wannan dalili ya sa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya karsasa Musulmi ya kasance mai kyauta cikin kyauta-yi, gwargwadon iyawarsa da karfinsa, domin kowane irin aikin kwarai sadaka ne, inda ya ce, owane Musulmi lallai ne ya bayar da sadaka. ? Sai sahabbai suka ce, a Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), to in mutum ba zai iya haka ba fa? ? Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, ai ya yi aiki da hannunsa ya samu abin da zai biya wa kansa bukata kuma ya bayar da sadakar! ? Sai suka ce, o, in ba zai iya haka ba fa? ? Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, ai ya yi kokarin taimaka wa wanda yake cikin halin kaka-nika-yi (wato yake cikin tsananin matsi)! ? Sai suka ce, o, in ba zai iya haka ba fa? ? Sai ya ce, ai ya yi wani abin kirki, ya nisanci mummuna, wannan zai kasance masa a matsayin sadaka. ? Buhari ne ya fitar da Hadisin. Musulunci ya yalwata da rar kyauta-yi ta yadda ta hade kowane gefe na rayuwar Musulmi! Wato in ka rasa wannan abu, to da wuya ka rasa wancan! Wanda yake cikin talauci, ko kadan kada ya karaya ya ce ba shi da abin da zai bayar ko ya yi, wanda zai samu martabar mai kyauta ko sadaka. Matukar dai ya mayar da hankali wajen yin abin da za a kalla a ce madalla, to yana matsayin kyauta ko sadaka, wadda za a ba shi gwaggwabar lada a Lahira, saboda maganar da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya fada, wadda Imamul Buhari ya fitar cewa, owane irin aikin kirki, sadaka ne. "Musulunci ya bayar da tabbaci ga kowa cewa yana da gudunmawar da zai iya bayarwa wajen gina al mma, ya karfafe ta, ya ciyar da ita gaba a harkokin yau da kullum ta yadda za ta kasance natsattsiya kuma tabbatacciya, wadda kowa zai yi alfahari da ita, alhali a karshe zai zama ya ci kyakkyawar riba. Allah Ya sa mu dace! "Musulunci adalin addini ne mai rangwame ga matsayin kowane Musulmi. Bai dora wa kowa, sai abin da zai iya dauka. Bai cewa mutum ya bayar da dukiyarsa ma, sai dai daga abin da ya ci ya rage. Ba ya zargin mai kadan. Ya ma fi son kowa ya samu damar biya wa kansa bukatarsa, domin hannun sama ya fi hannun kasa (wato mai bayarwa ya fi mai karba matsayi)! Amma dai duk abin da ya yi saura, to (Musulunci) yana kwadaitarwar a yi kyauta da shi cikin kyauta-yi, saboda shi Musulmin kirki ba ya kankamewar abin hannunsa, ya yi rowa, domin ya koya daga addininsa na Musulunci cewa bayar da sadaka (da kyauta), abu ne mai kyau, alhali kankamewa da rowa, abu ne mummuna, kamar yadda Hadisin da Imam Muslim ya ruwaito ya fada cewa: a kai dan Adam, idan ka bayar da abin da ya yi saura na dukiyarka, abu ne mai kyau gare ka; idan kuma ka ki bayarwa, ka rike abinka, to abu ne mara kyau gare ka. Babu zargi a kanka don ka rike abin da kake da bukatarsa. Ka fara bayar da kyautar ga wadanda suke makusantan bukata gare ka. Ka sani, hannun da ke sama ya fi hannun da ke kasa (wato ya fi kyau ka bayar da ka karba)! "Musulmin kirki ba ya mantuwa wajen yin kyauta cikin kyauta-yi, musamman wajen bayarwa daga cikin abin da yake saura a hannunsa, bayan ya fitar da bukatun kansa da na iyalansa, ko da cikin irin ajiyar nan ta shirin ko-ta-kwana, ko kuma ajiyar da za a ce an kirga shi cikin mawadatan al mmarsa. "Toh wanan duk romon fashin baki ne kan kyauta da kuma kyaauta yi a musulunce. Saboda shari'ah da zamu yanke tagaba akan haka taken ta yake. Sai mu dawo Kan shari'ar ku. Na gidah da malam Ardo miji ga Rumalle. Yayi kyautar gidan sa kacokam ga Rumalle. Inda Malam Ardon ya musanta zahiri lallen gaskia bai bata kyautar gidansa ba. Hasalima shi bayada masaniyar sanda yayi kyautar bare tabbacinta. Duk kunyi alwalar ai ko?" "Allah me alheri. Yau ana kwal landantsan. Kan balastin kayya kai. " Cewar Atuwa dake zaro idanunta kur akan mai shari'ah. "Duk wanda ya sake magana cikin ku zai yi waje. Ku kamar kananun yara." Cewar masu tsaron kotun. "Yauwa. Bazan iya yanke hukunci kai tsaye ba. Saboda nan kotu ce ta musulunci. Don haka kowanne cikin ku Ina nufin Ardo da Rumalle. Zakuyi rants uwa kan tabbacin bayarwar ko akasin haka. Daga nan sai mu yanke hukunci. Domin zama daya za'ayi wa shari'ar ku. Tunda abune na cikin gidah. Sai ku sasanta sauran a tsakanin ku. Basu qurani Anas." Anas ya dakko da hannu biyu ya fara mikawa Rumalle. Ta rike gam. Ta kwarara magana da karfi . "Ni Rumalle. Na rantse da Quran mai girma da ke hannu na. Ardo mai gidah na . Yabani kyautar gidan Sa da muke ciki da bakin sa ya fada. Yace takardar mallakar gidan na dakin Modibbo a cikin jakarsa. Ai kuwa kwan biyu da takardar a hannu na kaiwa mai unguwa ya ajiye Mun. Saboda gudun rana irinta yau. Wabillahil kaf dangin su Ardo ya Mai shari'ah makaryata ne. Kakansu har yabar duniya shata ake Kiran sa saboda sharara karyar sa. " "Amma Rumalle Allah ya kwashe miki albarka. Ke bama ke kadai ba. Tun daga kan iyannani mai fura gyatumar uban ki. Na hadaku duka na kwashe muku albarka. Matsiyaciya yar matsiyata. Wabillahil lazi na 'kara Miki wani shikan akan 'dayan. " "Kottttt (court) Ya isa. Kada Wanda ya sake magana acikin ku. Ke tunda kin gama jeki. Kawo qur'anin. Kai Kuma zo ka karba." Ardo ya karasa da sauri har Yana tuntube ya fadi. Wandon ya Yi kasa zai Fadi. Atuwa dake bayansa tayi saurin mikewa ta gyara masa.. "Cikani dalla. " Ya buge hannunta. Ya karasa ya karbu qur'anin da hannu biyu . Gumi ya shjga kwararo masa duk kuwa da yadda ake sanyi. Saboda tsananin tashin hankalin da yake ciki . "Na rantse da qur'anin da ke hannuna ya mai shari'ah. Ni Ardo borkindo . Ban bawa Rumalle gidah na ba. Kaji Allah. Banda masaniya ko sa'ilin da akai haka yallabai. Wabillahil lazi karya take. " "Da tarnatsa shi ke karyar. Makaryaci ne. Jak" "Kotttttt! " "Anas karbi qur'anin ka mayar inda yake. Ku kuma ku zazzauna. Hukunci biyu ne zuwa 3. Domin wata shari'ar sai a lahira. A dan ilimin da ke cikin kai na . Hukunci na farko shine gidah bai kyautu ba. Domin wanda keda mallakin abunda aka kyautar yace bayda masaniyar sanda akayi. Na biyu dole ne malam Ardo ya bawa Rumalle wani dan kaso na cikin dukiyar sa. Ba wai ina nufin ya bata wani sashe a gidan ba. Kudi daga dubu 5 zuwa 7 . Banda kasa da haka. Zai bata ne a matsayin lasa mata zumar da yayi na kyautar gida dayace ya bata acewarta kenan. Iyakacin abinda zan iya yankowa kenan a matsayin hukunci daya zuwa na 2. Sai hukunci na uku. Dole ne Ardo ya fara bawa Rumalle hakuri abisa kyauta da yayi ya kwace acewarta. "Haka Kuma dole Rumalle tabawa Ardo hakuri abisa kagen kyauta da yace ta masa. Cikin lafuza masu dadi da girmamawa kasancewar shi din miji ne agare ta. Toh duka duka anan zan tsaya . Allah yasa hukuncin da muka zartar ya zama shine mafi adalci da Kuma kyautawa. Abunda muka yanke ba daidai ba. Muna neman yafiyar ubangiji. Allah ya yafe mana baki daya... Ayi hakuri dika dan Allah. Duk Wanda akawa ba daidai ba. Sai aje gida a sasata. Akuma cigaba da zaman hakuri da juna" "Kotttttt!!!" Suka hada baki wajen fada. Banda Rumalle dake hawayen takaici. Ardo kuwa dadi ne ya mamaye shi ya dubi Rumalle ya gasa mata harara. Alkali ya koma ciki. Yayinda Anas da saura suka tsaya kallon ban hakuri tsakanin Ardo da Rumalle. Ardo ya bawa Rumalle hakuri . Yayinda Rumallen sai da aka kada aka raya sannan ta bashi hakuri a gatsine. Ta kuma dire tsallen albarka kan lalle ya bata kudin da alkali yace a bata. Ardo ya fuce da sauri bayan an samu me tsaro dake biye dashi karya gudu.
Chapter 45 · 0% Book details