← Book details So Da Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 55

Sashe 33

So Da Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_* *GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA WARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi* *JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE* *_DEEN MARSHALL Mamuhghee_* *_HALIN GIRMA hafsat rano_* *_TAKUN SA billyn abdul_* *_SO DA ZUCIYA miss xoxo_* ABI'AR ZUCIYA huguma_* *DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN AI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL* 1000 *Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin* 6019473875 MUSAA ABDULLAHI SAFIYA keystone bank Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 08184017082 *IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU* 09134848107 _*HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_* #team zafafa biyar . ___________ 2/3/22, 08:32 - Buhainat: *Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107* I'm on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb *SO DA ZUCIYA* *NANA HAFSATU* _28_ Dadaa ta 'dan kalli jaririn tana mai datse labbanta saboda tsananin yadda take jin ciwo kadan kadan. "Ina bappan su Sudeis?" Dadaa ta tambaya sanin baya minti kalilan nesa da ita. "Yafi ta da sauri bayan ya rad'a wa jaririn suna." "Okay Allah ya dawo dashi lapia." "Aamin Dadar mu. Dadaa yaron nan fa da bappan su Sudeis yake kama. Amma idanun ki ya dakko ." Dadaa ta dan kallo gefen zaraahn tana mai saukar da idanunta akan jaririn kafin ta janye da sauri. Saboda gaba daya samun cikin jinsa take tamkar wasa. Sai bayan yafito ta tabbatar da gaskene. Domin gaba daya aranta tacire zancen kara haihuwa. Shekaru goma da yan kai kenan bata sake haihuwa ba sai yanzu. Ta Kuma samu albarkacin samun 'da namiji. "Dadaa yunwa fa yake ji. Kinga Yana faman tsotsar hannun sa." Dakyar da sudin keya. Dadaa ta karbu yaron. Ji take tamkar ruk'o aka bata. Wasu zafafan hawaye ne suka shiga reto a kyakkyawar fuskarta. Dai dai lokacin da wayar Dadaan dake hannun Zaraah tashiga 'kara. "Bappah ne." "Toh kawo'' Dadaa ta karba cikin sanyin jiki, Domin gaba daya tasan tabbas ba lapia ba. Abunda zai sa Capt yayi nesa da ita. Arana mafi farin ciki agare su, Lalle koma menene abu ne babba wanda ba yadda za a iya tsallake shi. Cikin sanyin jiki da murya ta daga kiran sa. Tamkar Koda yaushe tashiga gayshe shi cikeda girmamawa da kuma madaukakiyar kulawa agare shi. Shidin ma capt a nasa bangaren yana zaune shida Maheer ne a airport inda ake kokarin gano gawawwakin don mika kowanne zuwa ahalin sa. Hawaye ne ke kwarara a idanun na captain yayinda wani daga cikin ma'aikatan ya dakko burbushin wani sashe daga hannun rigar da Sudeis ya saka. Sai agogon sa da kyallen ya tukwikwiye shi. Tanan suka gano tabbas sudeis kwanan sa ya kare. Babu sauran wata sheda data nuna shidin ne. Ba yaga wannan sashi na hannun rigar sa izuwa agogon sa. "Jon wuro (Mai gida) Kayi shiru, Meya faru?" Dadaa ta tambaye shi cikin tausasshiyar muryarta mai dauke da damuwar da zuciyar ta tashiga. Na halin da yake ciki. "Zaraah na kusa da ke?" Ya tanbayeta a sanyaye yana kokarin daidaita muryar sa dake sarkewa saboda tsananin tashin hankalin da yake ciki. Tuni Dadaan ta hasko akwai matsala don haka bata nuna yadda zaraahn zata gane ba tace dashi. "Eh! Alhamdulillah" "To kisa tatafi wani wajen ba tare da kin nuna mata wani abu ya faru ba. Sudeis ne... Allah ya masa rasuwa." Yana karasa fada ya katse wayar.. Tuni jikin Dadaa ya fara kyarma. Ta ajiye wayar a hankali tana kokarin saisaita kanta ta yadda Zaraahn ba zata 'dago wani abun ba. "Yan biyu suna makaranta ne?" "Eh kin manta da safe muka Kai su ni da Ya sudeis?" "Oh eh! Toh kinaji komawa gida zaki ki dakko musu kayan gidah ki wuce makarantar tasu. Sai ku shirya ku tafi can rimin kebe. Kya gayawa Haj Mari ma." "Yanzu Kuma Dadaa? Wani abun ya faru ne?" Ta tambayi Dadaan tana mai kokarin gano wani abu. "Mezai faru? Nan dinne cika zeyi. Kuma kinga ace su Atuwa ba suji ba ai ba dadi ko?" "Dadaa a kirawo su mana ta waya." Wani kallo Dadaan ta watsa mata na ta shigaa taita yin ta. Ai kuwa Zaraah ba tasake cewa komi ba. Ta shiga harhada yan kayanta a jaka. "Kwana zamuyi acan din?" "Ko zuwa dare ko yamma haka. Kwa gayda mutan gidan." "Zasuji insha Allah." Saurin fucewa tayi daga dakin. Yayin da Dadaa ta rufe fuskarta da tafukan hannayen ta . Wasu zafafan hawaye masu dumi suka shigaa yar tsere a fuskarta. "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun. Ya Allah kafimu kaunar Sudies. Yaa Allah ka jikan sudeis ka gafarta masa kurakuren sa. Allah kasa yana aljannar ka mai girma firdausi. Yaa Allah ka bamu hakurin rashin sa. SubhanAllah!!" Daada ta karasa tana mai sharce hawayen dake diga daga idanunta. Wanda har sai da suka shigaa sauka akan fuskar baby sudies da take shayar da shi. "Hajia akwai abunda za'ayi?" Harira mai aiki ta tambayi Dadaa. "Babu komai harira."
Chapter 33 · 0% Book details