← Book details So Da Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 55

Sashe 30

So Da Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Ranar jumu'ah bayan an sakko daga sallah, dubban mutane suka sheda daurin auren captain muhd muhd. Da amaryar sa Jameelah Jauro Chenido. Akan sadaki mafi daraja.
Ba ai wani taro ba illa dai hajia Mari tazo takawowa Dadaa abubuwa da yawa na gyara. Daren ranar aka mik'a Dadaa dakin ta na sunnah. Sati na gaba Kuma su Zaraah zasu koma wajenta da zama baki daya.
Duk wani abu daya dace Haj Amina da Alhaji Dangoje sunyiwa Dadaa. Tamkar auren budurwa haka aka shirya mata kaya. Kudin da captain ya bata ma Haj Amina ta raka Dadaa suka sayo sarka da dankunne da zobe na zinare
Su Haj Amina da kwayanta tare da rakiyar Haj Mari suka raka Dadaa gidan na Capt. Sun dan jima awajenta kafin su mata sallama hade da adduar Allah ya sanya albarka da alkhairi a auren nasu
Tamkar auren farko haka captain ya dankaro kayan kwalam da kajin sa gasassu a leda.
Yadda ya dinga tafiyar Dadaa cikin madaukakiyar nuna mata kauna ta rikitarwa hakan ya sa Dadaa rungumar sa da hannu dubu
Suka raya daren ranar cikin nunawa juna bajintar kauna. Kowa ya shigaa nunawa dan uwansa yafi kaunar sa
Daren ranar Capt ya tabbatarwa kansa yanzu yayi aure. hakama Dadaa da saboda tsananin kaunar da captain ya nuna mata sai data zubar da kwallar farin ciki
Toh Allah ya sanya alkhairi Jameelan Captain Muhd,
I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ci3ao6233sn3&utm_content=6k8ur6p
*WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*
*ZAFAFANKU BIYAR
sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*
*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*
*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA
WARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*
*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*
*_DEEN MARSHALL
Mamuhghee_*
*_HALIN GIRMA
hafsat rano_*
*_TAKUN SA
billyn abdul_*
*_SO DA ZUCIYA
miss xoxo_*
ABI'AR ZUCIYA
huguma_*
*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN
AI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*
1000
*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*
09134848107
_*HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*
#team zafafa biyar .
___________
2/1/22, 10:22 - Buhainat: *Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107*
I'm on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*SO DA ZUCIYA*
*NANA HAFSATU*
Sai dasu Dadaa da captain suka cika kwanaki goma chas tukun sannan Haj Amina ta Kai su Zaraah gidan da kanta.
Tasha matukar mamaki na canzawar fuskar da su Dr jiddah suka Yi mata. Ita daria ma lamarin nasu ya bata. Ta murmusa kawai tana mai kambaama shirme irin nasu.
Wai su jan aji. Tuni Yar ragowar kulawar da suke masa suka tattare suka ajiyeta a gefe. Wai su zafin kishi. Captain yayi kokari wajen ganin baa samu rabuwar kayuwa ba. Amman fafur sun tsaya akan yadda suka tsara kan fita harkar sa.
Ganin yayi bakin kokarin sa sun kasa ganewa. Hakan yasa captain din tattaro kayan sa baki daya ya mayar dasu sashen Dadaa. Suka cigaba da gurzar amarcin su cikin lumana da kaunar juna . Yayin da su Hajia Iklima suka sake hawa dokin fushi. Wai su jan aji . Su a lalle dole ya sakko da kai ya basu hakuri ya rarrashe su tamkar wasu kananun yara.
Washarairai din da sukayi ne Dadaa ta kara kai mi wajen kula da Mai gidan nasu da Addayo mahaifiyar Sa. Son Addayo take har cikin zuciar ta. Hakan da take Yi ne Capt ya sake bude wani shafi daban a zuciar sa ya zura kaunar Dadaa aciki.
Takanas Addayo ta tasa captain agaba suka je gidan kawu harith suka tafi da Sudeis da kayan sa rankatakaf. A farko sudeis ya so yin tirjiya kan shi ba zai koma gidan da suka masa madaukakin wani tabo a zuciar sa da bazai taba gogewa ba.
Amma dake an tabbatar masa da mahaifiyar Zaraah captain din ya auro. Hakan yasa shi jin nutsuwa a zuciar sa. Tunda Alhamdulillah da Zaraah sa zasu zauna a inuwa daya. Lamarin kwarai matuka zai Kayatar. Don haka bai sake musu ba ya shirya kayan sa ya bisu. Bayan ya yiwa su kawu harith da Haj Laila sallama.
Sabuwar shafin soyayya sudeis da Zaraah suka bude. Soyayyar data ninku fiye da yadda kalmomi zasu rubuta. Tun Zaraah batasan menene so ba. Har sudeis din ya fayyace mata menene shi ta hanyar nuna mata zallar madarar kauna marar surke.
Sannu ahankali soyayyar da suke nunawa juna ta tumbatsa har kowa ya sa ni. Da farko captain yaso hada Zaraah da Maheer aure. Amman daya tabbatar da Sudeis ya nuna zaraahn yake so Kuma da aure. Sai ya tattara yabar zancen cikin zuciyar sa. Had'e da yiwa Maheer din adduar samun wata ta gari Mai alkhairi. Domin sam bayason Maheer din ya sake komawa kasar Cairo reshen makarantar da yake koyarwa ta al'azhar. Yafuson ya waiwayo gidah ya kula da makarantar tahfiz dinsu ya kuma yi aure ya zauna da iyalin sa.
Chapter 30 · 0% Book details