← Book details So Da Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 55

Sashe 32

So Da Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

FADIN NIJERIYA DAMA KASASHEN KETARE. 100% TESTED AND TRUSTED_ _27_ Yana umartar prefect din dake duty yayi tafiyar sa ofishin sa. Ya zauna akan kujera yana mai dudduba takardun dake gaban sa. Zaraah na karasawa zata shiga ciki prefect din ya tsayarda ita da sauran dalibai na bayanta "Kar ki shiga kinyi latti. Kuma na bayanta ku marmatsa can a hukunta ku." Prefect din ya karasa magana yana mai jujjuya sharbaceciyar dorinar dake hannun sa. "Minti biyu kawai fa na kara." Tayi maganar a sanyaye tana dubar agogan dake wutsiyar hannun ta. "Nima umarnin ustaz Maheer na bi. Shine yace a fara taran latti akan ki." Ta daga kai ta dankarawa kofar ofishin sa harara tamkar shi take gani. Tunda ya ambaci Maheer tasan da biyu Maheer din yayi hakan. Saboda tsananin tsanar da yayi mata. Ta gaira ba dalili. Ta rasa meta masa a duniya daya tsaneta. Take awajen tsanar sa tayi malaimalai a farfajiyar zuciyar ta. Tana karasa maganar sa a zuci sai kuwa gashi ya leko ta saman benen had'e da rike karfen barandar yana kallo kasan da suke. "Yaran yi musu 'dai 'dai ahankali. Ita kuma yi mata uku madaidaita." Bai karasa rufe baki ba ta dubi prefect din hade da mikar da hannun sa saitin dorinar sa. "Had'amun data sauran yaran. Ka kyalesu su shiga ciki." "Ustaz kana jiyo me tace?" "Eh yi mata wa zata nunawa zuciya.?" Ta daga kai suka hada idanu. Ta dankara masa harara. Shima ya wurga mata tasa hararar hade da yamutsar fuska. Ya shige ofishin sa shi kadai yana mita "Yar mitsitsiyar yarinya sai bak'ar zuciya. Allah ya kyauta." Prefect din ya daga bulala ganin Maheer ya koma yai saurin kasa da bulalar yana magana ahankali. "Shige kawai." "A'ah wallahi sai ka min. Yi sauri" Ya kada kai kafin ya saita dorinar ya tsottsola mata sau 6, Yana gama dukan ta karkade masa hannun daya duka awajen had'e da shigewa cikin makarantar. Kai tsaye ta shige ajikin su. Bakinta dauke da sallama. Sudeis da sauran dalibai suka amsa. Ta samu waje ta zauna tana matse hannun ta dake zugi. Sudeis bai ce mata 'kala ba. Sai ma cigaba da rera karatun sa da yayi. Ko da ya karasa karatun sa. Sam yaki bari su had'a idanu. Saboda tun a baya sun riga sun tsara yadda zasu gudanar da soyayyar su. Akwai ta gidah akwai kuma ta idan suna su daya. Dake kowa na gidah yasan da abunda ke tsakanin su. Hakan yasa sudeis yin takatsantsan idan suna bainar jamaa. A islamiyyar ma suna matukar kokarin 'kin bayyana tsakanin su. Sai dai suyi sak'on rantsattsun aikawa juna sak'o ta idanun su. Toh yau ma hakan take. Ta kwayar idanun ta ya gano akwai abunda ke damun ta. Don haka ya mata wani kallo mai tattare da ban hakuri da nuna tsantsar kaunar sa gareta. Ya dan shafa keyar sa yana mata kallon 'kasan idanu. "Ina matemakiyar Ameerah?" "Ga Ni ya mu'allim" Asiya ta amsa shi hade da mikewa tsaye. "Zo ki karbo muku littafan ku" "Toh ya mu'allim." Ya fuce yana waiwayon fuskar Zaraah. Data kauda kanta gefe . Ofishin sa ya wuce kai tsaye ya bawa Asiya littafan su. Ya dan zauna a kujera yana mai tunanin daya baro Zaraah acikin sa. Ganin shima zai shiga damuwar da bai san dalilin ta ba, Hakan ya san yashi janyo littafin fiqhu ya shigaa karantawa. Dai dai lokacin da Maheer ya shigaa cikin ofishin bakin sa dauke da sallama. "Wa'alaykm salam babban Yaya" Zama Maheer din yayi a kujera dake kallon ta sudeis. "Ya nagan ka kai ma yau haka haka?" "Kai na,, Na ne yake dan ciwo babban Yaya " "Ko kuma dai dan an daki zaraahn ka dukan latti?" Tanan sudies ya gano dukan lattin da akayi mata ne ya haddasa mata canzawar yanayi. "Ko daya. Ita wayace tayi lattin? ai dole a hukunta ta" Ya fada cikin karshen gaskiyar sa. Fuskar sa ta fad'ad'a da murmushin jin ba wani abun bane na daban. "Ai na yarda da maganar ka lalle tanada zuciya. Dukan sauran yaran ma sawa tayi a mata du baki daya . Nace lalle anyi gwarzuwa." Maheer ya karasa fada yana tabe fuska. Shi dai sudies ya sake sakin tattausan murmushi kafin yace, "Ai nagaya maka tanada zuciya. Kawai kokari zakayi ka zare kiyayyarta a ranka. Ka maye masa gurbi da zallar so." "Zan futa a harkar ka gaskia. Inde muna maganar arziki ka shiga ratattaka maganar halayen ta. Tanada zuciya batada zuciya ba abunda ya shalle ni. Manyan mata ma basu isheni kallo ba bare yar jaririyar ka. Wannan sai kai." Ya karasa yana yamutsa fuska. "Kayi shiru dai babban Yaya. Sai kag,..ga reshe ya juye da mujiya. Idan Allah yayi Zaraah ce matar ka bay..." Bai karasa Maheer ya mike da sauri ya fita hade da dankarawa sudies kyakkyawar harara da guzurin dogon tsaki. Sudeis yayi dariya kawai yana girgiza kai. . . . Safiya ta zama rana, Rana ta zama yammaci, Yammaci ya zama dare. Lalle Allah qadirun ne ala manyasha'u. Cikin lokuta dake ta ja da yardar Allah. Zaraah sun shiga aji uku na karshen sakandire. Biyu ya kamata tashiga. Amma dake tanada saurin girma tuni ta kere yan ajin su a komai Ta zama cikakkiyar budurwa mai tashen yammatanci. Hakan yasa capt. da kansa yayi shawara da mai makarantar aka sauyawa Zaraah aji zuwa na uku maimakon na 2 . Tuni suka fara shirye shryen zana jarabawar 'kare sakandire. Zaraah ta kara wani irin madaukakin kyau mai dauke da haske, sheki da Kuma walwalin fata. Tanada kerarren shape mai daukar hankulan jama'a..hakan yasa ko da yaushe cikin hijabi take. Wata iriyar soyayya suke da Sudeis Wadda ta kai ga har an kai kudin aurenta wajen Ardo. Wanda Rumalle ta cinye rabi da kwatan su. 'ya'yan Atuwa ma an aurar dasu. Cokali Ardo bai saya musu ba. Gidah ya zama sai Atuwa da farillatu da. Jimmamman da yan biyunta. Sai Rumalle dasu usmanu. Rumalle tayi 'barin ciki har sau biyu. Hakan ya sanya Ardo fara cireta a ransa . Har mota ta rakashi tana cuno baki gaba. Maheer dake gefe yaja tsaki yana maka Mata harara. Itama ta rama hade da murguda masa baki. "Dalla Malam zo ka ja mota mu tafi. Idan ka dawo kwa cigaba." Sudeis dake soyewa da Zaraah ya dan daga masa hannu alamar minti daya. "Me zaki tanadar mun idan zan dawo! Uhm,,, Baby luv? " Zaraah ta rufe fuskar ta da tafukan hannayen ta da suka sha jan lalle. "Sai ka dawo din dai. Allah ya dawo mun da Kai lapia. Allahumma Aamin" "Aamin hayateey. Babban Yaya ga amanar Zaraah na nan. Dan Allah ka rike mun ita da hannu biyu. Gatanan amana dan Allah. Zuciyatah da kai daya ta aminta. Kai kadai ne zaka rikemun ita fiye da ni kankin kai na. Kema Zaraah na ga amanar babban Yaya nan. Duk abunda yakeso idan har bai sab'a shari'ah ba ki masa." Maheer yaja dogon tsaki ya koma mota. Yayinda wasu hawaye suka shigaa reto a fuskar Zaraah. Ta rike murfin motar tana kokarin sanya idanunta cikin nasa. ko kadan bai bari sun hada idanu ba. "Haba habibi. .. Ni dai gaskia ka daina mun irin wannan maganganu kamar Wanda zai dad'e? Kuma ma karasa wanda zaka bawa ajiyata sai shi?" Ya girgiza Kai kafin yace, "Saboda ko nan gaba zaki tabbatar da maganganu na. Ya Maheer bani da na biyun sa wajen kulamin da Ke, Dan Allah ki sassauta kiyayyar da kike masa.. Nan gaba komai zai warware." Ya karasa fada hade da saurin janye idanun sa daga kanta ya shige motar suka tafi yana daga mata hannu. Har suka fice daga gidan sannan ta sauke nata hannun da sauri ta koma cikin sashen su da sauri don tenakawa Dadaa su tafi asibiti. Haihuwa tazo gab. Zuciyarta cike da kewar sudeis ta shige dakin Dadaa. A tare suka shirya Dadaa da taimakon Mai aikin Dadaan. Direba ya jasu sai asibiti. Capt muhd ma hankali arashe ya tafi asibitin. Dai dai lokacin da Maheer ya dauki hanyar gidah bayan sauke sudeis da yayi a airport. Kai tsaye ya wuce asibitin da Dadaa zata haihu saboda kiran da Capt ya doka masa na yazo yanzu ya ajiye dik abunda yake. Dadaa tadau tsawon lokaci tana labour. Yayinda likitoci masu karbar haihuwa suka tsaya akanta suna bata temako. Awajen awanni 3 ta dauka kafin cikin ikon Allah ta sauka lapia. Dai dai lokacin da gidajen talabijin dana rediyo suka shigaa yad'a labarin hatsarin jirgi da akayi. Jirgin emirate daya lula a sama ya fado ya kone. Gaba daya fasinjoji da kowa da kuma komai ya 'kone. Jirgin kuwa bakowane bane fyace wanda sudeis ya shigaa . Jirgin zai tashi ne zuwa daular Dubai. Inda zasuyi wani taro na musabakar Al'Qur'ani da za'ayi. Gaba daya Maheer da Capt dake waiting area sai suka rasa tacewa. Maheer ya shigaa laluban number sudeism hankulan su baki daya basa jikin su. Dai dai lokacin da Zaraah ta isa wajen su dauke da jaririn a hannunta, kyakkyawa kamar sa daya da Capt tamkar yayi kaki ya tofar. "Bappah ga jaririn" Hannun sa na rawa. Jikin sa na kakkarwa ya karbu jaririn. Yayinda Maheer ya fucea da sauri. Ambaliyar hawaye sun wanke fuskar Capt. Zuciar sa taki yadda da labarin hatsarin daya faru. Zaraah kuwa ta dauka kukan farin ciki yake. Ya Kara sa masa hudubar ya mika mara shi dakyar saura kadan ya jefar dashi ahankali yace da ita.. "Rike sudeis yaci. Sudeis ya tafi, sudeis ya dawo. Allah yabamu hakurin rashi" Ya karasa fada hade da fucewa da sauri . Bai jira wani abu ba ya tsare adaidaira sahu yace ta Mika shi airport Yayinda Zaraah ta koma ciki tana mai sanarwa Dadaa sunan yaro "Sudeis Muhammad Muhammad" #A LOVE SOO BEAUTIFUL!! #MAHEER & ZARAAH LOVE STORY #JOURNEY OF LOVE #AL HUB HAYATT I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ci3ao6233sn3&utm_content=6k8ur6p *WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_* *ZAFAFANKU BIYAR sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA* *_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin
Chapter 32 · 0% Book details